BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

‘Karya kike yi sai dai idan kece kike kuka kina so in dawo ai na gane. ” ya fada yana siriryar dariya , cikin jin nauyi nace”Da gaske nake don Allah yaushe zaka dawo.”? Ajiyar zuciya ya sauke yace.” Idan na dawo d’in me zaki bani. ” ? Shiru nayi masa, yace.” Ok bari in kashe wayata.” Da sauri nace”Sai dai ka dawo d’in komai kake so.”
‘Yar dariya yayi yace.” Kinyi alk’awari ko.” ? Lumshe idona nayi ina jin wani fleengs nace”Eh” yace.” Ok sai jibi zan dawo zan huta anan tukkuna hayaniyar gari tayi sau’ki kinsan in na shigo gobe zasu takura min ko baki San abunda yake faruwa bane.”!?
Nace”Na sani munga komai a labarai Abban baby na taya ka murna kuma ina maka fatan alkairi har ‘karshen rayuwar ka.”!. Sosai yaji dadin addu’ar ta yaji yarinyar ta ‘kara samun wani matsayi a zuciyar sa yace.” Thank you my wife I will not leave you forever.”!
Naji dadin abunda yace cikin jin kunya nace “Thank u my life patner.”!! ‘Kit!!! Na kashe wayar cikin jin kunya gabana sai dukan uku-uku yake ina mamakin yanda na sake har nake magana dashi haka…. Nashi ‘bangaran kuwa rike wayar yayi yana sakin wani irin murmushi Wanda shi kad’ai yasan ma’anar shi, ya mike da kuzari a jikinsa ya shige toilet domin gasa jikinsa saboda wani irin ciwo yake masa ni kam nace” Dole ne ko don dambe da kasa kai da Kumurci!
Washe garin ranar Innah Suwaiba ta dira cikin gidan ita da ‘yar ta Hafsa had’e da ‘kullikan kayan su wai sun dawo gidan da zama domin labarin duk abunda yake faruwa ya isa gareta don haka arzikin d’anta ne tunda d’an ‘yar uwarta ne itama ta dawo kusa a ci da ita…. Mamaki kamar ya kasheni na dinga kallon matar na marasa a wane matsayi zan aje ta, gaisuwar da nayi mata ma a banzace ta amsa, Hafsa kuwa ido ne tsakanina da ita granny tace”Haba Suwaiba ai ko wani kika kawo cikin gidanan kikace yana so ya zauna zai zauna saboda darajar ki ba sai kin dinga tashin hankali ba don Allah ki dinga yin komai cikin nutsuwa da fahimtar juna.” Wannan magana da granny ta fad’a sai Innah tace”ai ta fad’a mata ba’kar magana ta inda take shiga ba tanan take futa ba. K’arshe dai granny bar mata parlor tayi domin baza ta iya da jarabar Suwaiba, dakinta na bita na tadda ta a zaune nace”Granny wannan matar tana so ta d’aga mana hankali a gida.” Tace”Sai hakuri Suwaiba taki sanin abunda ya dace Wallahi kiyi hakurin zama da ita ni kam ‘kato na dawowa zan tattara in tafi inda nafi kauri.”
Nace”Babu inda zakije granny kina gidanan domin ni dake zan zauna gaskiya. ” tace”Yanda nake da matsayin a gidanan haka Suwaiba take dashi domin a matsayin uwa take ga mijin ki saboda haka ki kula da kyau.” Kuka NASA nace “Wallahi kin San Allah bazan zauna da ita ba sai dake domin ina ganin idan ta cigaba da yimin wannan halin nata watarana zan rama ko in zage ta.”
Ganin ina kuka yasa granny fadin “Shikkenan kiyi hakuri mu Bari tukkuna mai gidan ya dawo sai muji ta bakin sa.” Hawaye na nagoge nace”Me zan girka miki na rana.” ? Tace”ki bari Iyami sai tayi ke kije ki huta mana.” Nace”A’a ki fad’a min dai.” Tace”yi min towon alkama da miyar kuka.” Nace” Tom” futa nayi daga d’akin na tadda Innah Suwaiba ita kad’ai ta d’au ‘kafa daya ta d’ora kan d’aya kicin na wuce ta Bini da banzan kalo tana Jan tsaki .!!
Me zan gani Hafsa na tsaye ta kunna gas sai fasa ‘kwai take yi gefe ga Uwar doya nan ta tsame ta cikin wani kwando ta d’ora mai zata fara soyawa….. ‘Bata fuska ta nayi nace”Hafsa meye haka kikeyi min a kicin duba don Allah gurin a gyare duk kin bi kin zubar da ‘bawon ‘kwai da doya Haba don Allah.”!!
Hafsa da ada take bala’in tsorona itace yanzu ya juyo tayi min wani banza kallo ta d’auke kanta daga kaina ta cigaba da abunda take….. Wani irin zagi na kurma cikin zuciyata amma a zahiri nace”Ko bakyajin abunda nace ne.”!!! A wula’kance tace”Ina ce da akwai me aiki da zaki wani dame ni da surutu, idan na gama aikina sai ta zo ta gyara.”
Gyad’a kaina nayi nace”Yayi kyau.”! ‘Karasa wa nayi kusa da ita kawai na murd’e gas d’in na kashe had’e da dauke man da take soya na aje kaskon gefe kana na kalleta fuskata babu annuri ko na kwabo nace”Futa ki bani guri in gama abunda zanyi in yaso sai ki dawo kiyi kome Nene. “””
“Baki isaba.”! Tafad’a kanta tsaye gashi ta tsare ni da ido har da ri’ke ‘kugu gaskiya nayi mamakinta nace” OK sai inga yanda zakiyi min iko a gidana.”!
Wata irin shewa ta buga tace”Masu gida manya, hahahahaha da dai bamu San komai bane sai kice wani abu, to mun San komai aure ne akayi shi dake da My love d’ina bisa ‘kaddara da har zaki dinga wani famkama da hura hanci kin auri me kud’i tom bari kiji ba a sanja ‘yan uwa har karshen rayuwa ke kuwa fa my love zai iya sanja ki har abada ya kawo wata saboda haka ni nan da kika ganni jinin mu d’aya da Amjadu za’a iya tsaga jikinsa a tsaga nawa a ga jinimu yazo d’aya saboda haka ki iya bakin ki Wallahi idan ba hakaba wannan gallafirin auran naki zamu iya yin sanadin sa.”
Naji wani irin takaici ya rufe ni jin abunda Hafsa take cewa danne zuciyata nake yi ina kokarin hanata aikata abunda tayi niyya nace”Hafsa kin San halina ba tun yau ba bani da kyau ke kanki kin sani bana so muyi irin wannan zaman daku ki iya takunki ki bar shiga hurumin da bana ki ba, idan kin ‘kiji zaki sha mamaki wallahi.”!!
A hasale tace”Ke kar ki kawo min maganar banza da wofi da dai da kikayi min abunda kike so a skull lokacin ki ne yanzu baki isa ba wallahi kutumar ubanki zanci la’ada waje kuma in zauna……. Kafin ta ‘karasa na tsinke ta da wani irin gigitacan mari! Ta rike kuncin ta da sauri tana kallona da ido jazur tace” ni Kik……. Kafin ta ‘karasa na kifa mata wani a d’aya kuncin nata, nace”Ina fatan yanzu kin tuno wacece Asma’u Sulaman ‘yan a waki.”!!! Ihu! Hafsa ta kurma ta d’auki soyayyan man dake cikin kasko ta watso min da sauri na kauce saboda nasan da zafin sa zai iya ‘kona ni. Kaina tayo aikuwa santsin mai da ‘bawon doya ya kayar da ita cikin man dake da sauran zafi kafin kace kwabo fatar hannunta ta kwailaye! Ina tsaye ina kallonta tana kuka.
Granny da Innah Suwaiba suka shigo kicin d’in hankali a tashe! Innah Suwaiba kaina tayo tana fad’in”Shine kika ‘kona min yarinya saboda kina ba’kin cikin zata zama kishiyar ki shine tun yanzu kike so ki nakasta min ita Dan ubanki! Mari ta kai min a fusace.!!!
8/12/2019
[12/9, 10:38 PM] .: BABBAN YARO
80
Nayi saurin dafe kuncina ina kallon matar cike da d’umbun mamaki! Ta cigaba da cewa”Shikkenan kawai saboda ta shigo tana soye-soye a gidan d’an uwanta sai ki ‘kona ta da mai saboda sharri da ba’kin ciki to Bari kiji wallahi ki sanya a ranki sai kin zauna da ita a matsayin kishiyar ki, domin ita tudu biyu taci ga aure ga ‘yan uwan taka.”!
Ta ‘karashe maganar tata cikin kumfar baki.
Hawaye masu zafi ne suke zurarowa a daga idona tace”Kina tsatsare mutane da idon ki na rashin kuny…… Kafin ta ‘karasa granny ta katse ta ta hanyar fad’in”Wannan ba girman ki bane Suwaiba abunda ya kamata kiyi kafin ki yanke hukunci shine ki fara tambayar su me ya had’asu ba ki za’bi taki ba Asma’u ma ‘yar ki tunda tana auran d’anki.” Granny ta ‘karashe maganar cikin sigar rarrashi.
Botsarewa tayi tace”Kina kallo fa ta ‘kona mun yarinya wane irin ba’asi zan tsaya tambaya anan ga gaskiya a zahiri duk bakin cikinta baza ta ci arzi’kin ita kad’ai to kaji.”!!