BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

Cikin saurin na futa daga kicin d’in ina ji zuciya kamar zata fashe saboda takaici tabd’ija lallai akwai rigima mutu’kar matar nan tace zata zauna min a gida domin na lura bata ‘kauna ta ko kad’an nima take naji wata irin tsanar ta ta shiga zuciya ta, zama nayi gefan bed ina tunani matakin da zan d’auka kan Hafsa babu shakka tayi ganganci tace zata had’a miji dani… Aure bazan hanashi yayi ba, kuma Hafsa ‘yar Uwar shi CE bazan rabasu ba amma ko da wasa bazan d’auki raini daga gurin kowa ce shegiyar ba ciki kuwa har da ita Innah Suwaiba.

Waya ta dake kan drawor ta fara ringing Sam banyi tsammanin shine ba ina dubawa nagan my one and only da abunda nayi serving d’in numbar shi kenan.

Murya ‘kasa nayi sallama inajin ya sauke ajiyar zuciya kana ya amsa sallama ta, shiru nayi domin har yanzu akwai sauran ‘bacin ran su Innah Suwaiba a tare dani…. Yace.” Me kike cewa d’azu kika kashe min waya.”?

Shiru nayi ina tunani nace” inajin shi yace.” Kat ki ‘kara kashe min waya daga yau.” A hankali nace “Tom.”!! Ina baby.”? Ya fad’a cikin wani irin voice Wanda ya sanya ni jin wani yanayi nace” sun futa cefane da Iyami. “

Yanayin yanda yayi magana ya nuna min ransa ya ‘baci yace.” A kan me za ki bari a futa da ita kasuwa dole ne cefe nan.” ! Na sassauta murya ta tare da fad’in”Dole ne mana tunda bamu da wasu a bubuwam a kicin Rambo bayan nan, Doh-doh kuma kun tafi tar…… Kafin in ‘karasa ya katse ni a hargitse yace.” Kada ki kuskura ki ‘kara bari a tafi min da yarinya kasuwa ko ina gari ko bana gari Wannan si shirme ne ita Iyami me yasa baza je ita d’aya ba.”

Cikin zuciyata nace “Ikon Allah .”! A zahiri kuwa ha’kuri nake bashi ina fad’in ” Baby ce take kuka dole sai Iyami taje da ita.” Aiko saurara ta baiyi ba ya kashe wayar sa……
Wayar nake bi da kallo cike da mamakin hakinsa Sam shi idan ya d’auki zafi baya tsayawa ya saurari mutum… Na fi minti goma rike da wayar a hannuna, kana Naji motsin shigowar Iyami parlor na futo kamar babu abunda ya faru nace”Iyami kin dawo ne.”?

Tace”Na dawo yanzu baby nayi ta min kuka s hanya.” Nace.” Sakkota mu gani.” ‘Kokarin sakkota take daga baya ta sanya kuka Iyami tace” barta kawai a bayan nawa.” Nace”Ke da zaki shiga kicin yanzu.” Tace”Hakane fa yanzu da na shiga kicin din aje kaya nace”Ba’ki mukayi a gidanan ken….. Innah Suwaiba ta katse ta ta hanyar fad’in”Mu ba ba’ki bane ‘yan gidane sai dai kece ba’kuwa.” Iyami tayi saurin fad’in”A’a sannu Innah Suwaiba Ashe kece.” Banzan kallo tayi mata tazo ta zauna kan kujera hannunta rike da wani plate cike da doya da ‘kwai ta zauna ta fara cin abunta.

Iyami kicin ta nufa ni kuma na wuce d’akina rungume da baby domin nayi alk’awarin banza ‘k’ara shiga har Kar matar ba gaisuwa ma don ta zama dole ne.”

Waya ta na d’auka ina kirashi tana ta ringing ya’ki dauka har ta katse na ‘kara kira ta katse bai dauka ba, sai da na kira sau uku bai d’auka ba na hak’ura nace Fushi yake yi kenan take naji zuciya nima nayi min zafi nace karfa wannan guy ya samu hanyar wula’kantani don yaga na saki jiki dashi dashi har yake mun fad’a domin a rayuwata na tsani in kira mutum a waya ya kashe ko ya’ki dauka…. Wata zuciyar tace min Kin manta Irin zaman da sukayi da Mimi dama kuma granny ta fad’a miki shi mutum ne me d’aukar zafi amma bashi da rik’o, lokacin sai naji zuciyata tayi sanyi saboda nasan zuwa dare ya sakko dole zai nemi ya kira waya ko don yaji gwalantun babynsa da ya saba. Ranar haka na yini sukuku sai bayan sallahar Isha’i sannan na futo parlor. Granny Iyami Innah da Hafsa duk suna zaune suna kallo Cikin kwanciyar hankali abunsu…. Kai tsaye daining na nufa domin cin abunci granny tace”Kin futo kenan.” Ina tafiya nace”E Granny sannun Ku da hutawa. ” hankalinta na kan TV tace”Yawwa kinga hankalina ya d’auke gurin kallon Wannan wasa Dad’in mu ko dad’in kowa ina son kallon diramar nan. ” ta k’arashe maganar tana dariya… Ina kokarin zama nace”Ba kya kad’ai ba granny shirin dadin kowa ya shiga zuciyar mutane sosai.” Hira muke tsakani mu Innah Suwaiba na makamin harara ko kallonta banyi ba nagama abunda nake yi na bar gurin bayan nayi wa Granny sallama.

Ko da na shiga d’akinta wanka nayo jikina duk babu kuzari na duba wayata ya Kai sau biyar banda ko misscal d’insa ba, haka dai nayi shafe-shafe jikina sanyi ‘k’alau na shirya baby cikin kayan baccin ta kwantar da ita nayi saman cikins na kwanta rigingine waya ta na d’auka na lalubo numbar Munnu wacce muka rabu da ita tun ana ya gobe d’aurin auramu.

Buga d’aya tayi ta shiga Munnu da zumud’i ta d’aga wayar tana fad’in”Sai yanzu kika tuna dani saboda kin samu duniya ko.”? Nace”Munnu ke wannan ya dama Wallahi ni fargaba duk ta cika min ciki kinsan dai abunda yake faruwa ko.”? Tace”Ya Aminu ya fad’a min INA muku fatan alkairi Asmy.” Nagode Munnu kin San wani Abu.”? Tace “Sai kin fad’a.”

‘Wallahi Yayar Mahaifiyar Abban baby ce ta sanya ni a gaba masifaffiyar mata Babar du Hafsa mai warin.! ” munnu tace”Ikon Allah dama fa naji labarin ‘yan uwan sune.” Nace “Babu wai a ciki Munnu a takaice dai matar ta tattaro kayanta ta dawo gidan da ita da Hafsa.”

Salati Munnu take yi cike da mamaki tace”Kaji mu da mata ‘yar rainin hankali.” Nace”Wallahi munnu ni ba wannan ba ma da tazo da sigar son mu zauna lafiya sai mu zauna meye duniyar amma Baki ga irin abunda take min ba, ke d’azu fa har da mari.”! Munnu ta rike Baki cike da mamaki tace”Akan me ta mare ki.” Nan na kwashe abunda ya faru tsakanin da Hafsa na fad’a mata

Munnu tace”Meyasa baki ci kutumar Uban Hafsa ba wato ita Dan bata da hankali tana ganin a haka Amjadu zai aure ta lallai bata da hankali wallahi.

Nace”Hafsa dole in kiyaye saboda na lura matar na da matsayi a gurin shi kuma kema kin San halin d’aukar zafin guy kin San dai irin zaman da suka yi da Mimi shiyasa nake bin komai a sannu.: Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace”Kina da gaskiya anan kiyi hakurin zama dasu kafin kiga irin matakin da zai dauka nasan ki da saurin hasala da rashin hakuri ki danne zuciyar ki ga duk abunda zasuyi.’!! Nace ” Insha Allah Munnu.” Na muka cigaba da hira inda take tsokanata wai sai ta rigani haihuwa tunda yayana ya takura mata kullum Abu d’aya, nace”Munnu duk dake kema kikaje kina bankar maganin aunty Hauwa Dole ya Aminu ya samu guri.”
Tace” kuma Wallahi da farko na ji zafi amma da yayi na biyu na uku sai na daina ji sai dad’i. ” dariya nayi nace”Munnu baki da kunya wallahi bakin ki ya iya fad’ar dad’i. ” tana dariya tace”Sai kin ji yaya yake sannan zakice baki bazai iya misaltashi ba.” Ina dariya na kashe wayar ina mamakin futsarewar idon Munnu.

12:25 na dare ya shigo gidan ko ina shiru sai ‘karan Ac kai tsaye bedroom d’insa ya bud’e ya shiga a hankali gudun kar wani yaji motsin sa, wayoyinsa ya zube kan drowar gefan bed, ya shiga toilet ruwa ya had’a mai zafi yayi wanka tsaf ya futo jikinsa d’aure da towel mai fad’i da wani ‘karami a hannunsa yana goge jikinsa sama-sama saboda raunin dake kirjin sa don ma ya sha magani gurin ya dusashe don ba yayi masa ciwon komai yanzu sai dole bazai sanya Riga mai nauyi ba gudun ta Sosa masa ciwon…..wasu irin kayan bacci ya sanya a jikinsa irin na maza blue colour rigar mai mad’aurai daga gaba sai dogon wando har ‘kasa bai daure igiyoyin ba ya bar k’irjinsa a bud’e, turare ya fesa a jikinsa kana ya gaye bed cike da gajiya bacci yake ji sosai. Shiyasa baya bukatar damu dukanin su har babyn da safe sa had’u yasan dai duk zasuyi mamakin dawowar sa yau din bayan yace sai gobe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button