BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

Kicin ta nufa tana baza kamshinta mai dad’i gaske Innah Suwaiba da Hafsa ta Tarar a tsaye suna yiwa Iyami masifa kamar wasu iyayen ta
12/12/2019
[12/12, 10:23 PM] .: BABBAN YARO
86
‘Kamshin turaran ta ne dauki hankalin su, suka juyo da sauri suna kallon bakin ‘kofa. Asma’u ta hade fuska sosai domin taga irin kallon da Innah ta watsa mata, cikin ladabi tace”Innah kin tashi lafiya.” ? Innah Suwaiba tace”Da ban tashi ba zaki ganki, don baki da kirki zakiyi min irin wannan gaisuwar kamar wata sa’ar ki, ko kuma shi mijin naki bai fad’a miki matsayi na a gurin shi ba.” ?
Cikin kwantar da harshe nace”Inna kiyi hakuri don Allah ba sai Abban baby ya fad’a min matsayin ki a gurin shi ba na sani dani dashi duk muna karkashin ki kuma ke a matsayin mahaifiya kike a gurinm…… Inna Suwaiba ta katse ta hanayar fad’in.
“Ke bana son kinibibi da iya samun guri da kin dauke ni a matsayin uwarki ai baza kiyi min irin wannan gaisuwar ba.”!
Shuru nayi mata ganin yanda take magana a hasale bana so ina fada tana fada babu mutumci yin hakan…..Iyami na kalla cikin taushin murya nace” Iyami me ake had’awa na kalaci.”?
Iyami tace”Yanzu dai zan fara aikin.” Cike da mamaki nace”Yanzu kuma.”? Tace” E wallahi na shigo kicin din ne nagansu suna aiki shine kika shigo wai bazan ta’ba komai ba sai sun gama.”
Raina ya ‘baci sosai Iyami macace mai ‘kokari da ganin girman mutum Sam bata raina mutum tana da mutumci bazan so abunda zai “bata mata rai ba. Nace”Innah da kinje kin huta Iyami zata hada komai na kari kamar yanda ta saba kome kike so ki karya dashi ki fad’a zata miki.”
Hafsa ta hasalo! Ta inda take fad’in”Babu wata banza da zamu tsaya ta yi mana iko da abunda muke da iko dashi ke kibar wani hura hanci a gidanan kina wani baza ‘kamshi ke kanki mu muke da iko dake saboda haka ki iya takunki.”
Duk ‘kokarin danne zuciyarta da nake yi abun ya faskara na kalli Hafsa fuskata a had’e nace”Kiyi shuru tunda ba dake ake ba.”! Innah tace”Baza tayi shurun ba sai ta saka baki domin itama watarana mai bada doka da oda ce a gidanan.””
Na bude baki kenan zanyi magana granny ta shigo kicin din tana fadin”Hayaniyar me nake ji ne a gidanan da safiyar Allah.” ? ‘Kasa nayi da kaina INA ‘kokarin mayar da hawayen da suke ‘kokarin min…… Innah tace”Yarinyar ‘kankanuwa ta tsaya a kaina tana ‘kokarin zagina da safiyar.”! Granny ta kalleta cike da mamaki tace”Asma’u baza ta zage ki ba Suwaiba don Allah mu zauna lafiya ki k’yale yara suyi abunsu.”
Innah Suwaiba ta hau matse hawaye tana fad’in ” Yau kam zan bar gidanan domin yafi k’arfin na duk da ina da iko da meshi kin nuna min ni bani na haifi Amjadu ba, Aisha ce Uwar shi abunda baki sani ba kuwa shine abunda yayi Aisha shine yayi Suwaiba. “!! Ni da granny muka bita da kallo cike da mamaki! Ta futa daga kicin din tana kuka.
Hafsa tabi bayanta bayan ta gama watsa mana mugun kallo dani dasu granny da suke tsaye suna mamakin wannan al’amarin….. Granny tace”Asma’u ko kinki ko kinso Dole yau in bar gidanan domin ni bazan zauna in tayar miki da hankalin gida ba dama dalili ne ya kawo ni gidanan saboda haka na bar zaman shi daga yau.”.
Hawayen da nake ‘kokarin danne wa ne suka zubo min na kasa cewa komai har granny ta futa daga kicin din….. Innah Suwaiba kuwa tana shiga parlor suka yi kicibus da Amjad ya futo daga dakin Asma’u yana dauke da baby a hannuna ganinsa sai ta ‘kara rururcewa da kuka tana fadin “Dole in bar gidanan yau domin an nuna min matsayina a cikinsa, kamar ni Suwaiba ‘karamar yarinya ta nemi fada min magana.”! Ta k’arashe maganar cikin kuka.
Amjad yace.” Inna wai me ya faru ne kike kuka kiyi shiru ki fada min.” Karaf Hafsa tace”Asma’u ce ta zage ta wai akan me zamu shigar mata kicin.”
Wani irin kallo yake watsa Hafsa kana ganin kallon kasan na tsana ne yace.” Yi min shuru ke na tambaya ko ita.”? Hafsa tayi ‘kum! Da bakinta tana sinne kai wani irin bala’in kwarji guy yayi mata take jikinta ya fara kyarma!
Inna kuwa jin tsawar da ya dakawa Hafsa yasa ta ‘kara kyami gurin kukan tace”ai ba karya Tayi maka ba, matar ka dai zagina tayi kuma a Gavan granny ta zage ni ta nuna mai aikin gidan ka tafi ni daraja dole in bar gidanan yau.
Amjad yaji kansa. Yana Sara masa Sam ya tsani hayaniya a rayuwar sa shi da zata tafi ta bar masa gidansa ma yafi son haka.. Amma don ya kwantar mata da hankali yace.” Innah kikace Asma’u ta zage.”!? Tace”Ba wai kuma babu karya a ciki naga ka tsaya kana mamaki dama yarinyar bata da tarbiyya shiyasa kowa yake gudun hada jini da ita.”
Karaf a kunne na, raina yayi mugun b’aci sosai jin irin kazafin da Innah take min har kokarin ‘bata suna idona ya rufe Sam na manta wacece ita, da kausarshiyar murya nace”Kiji tsoron Allah baiwar Allah sai fad’a kike yi na zage ki da girman ki da kome karya dai haramun ce babu kyau a cikinta na d’auka dani da Hafsa duk d’aya muk……….”Asma’u. “!!! Cikin tsawa ya katse ta yana mata wani irin kallo fuskar shi a mugun had’e!!
Innah Suwaiba tace” Koda naji ka gani ai a gabanka dai Yarinyar nan bata duba furfura ta ba take cewa ina ‘karya oh! Duniya kenan Nasan inda ta dauke ni a matsayin uwarta bazata fada min haka ba, hummm ko da yake duk laifin ka ne da baka nuna mata matsayina ba, Innah Suwaiba ta kare maganar tata tana me rurucewa da kuka. “!!!!
Asma’u ma hawaye ta fara sharewa tana mamakin wannan masifar daga yin aure yau kwana uku Shikkenan ta kasa samun nutsuwa wai yaya zata yi ne.”!?
A kausashe taji Muryar sa yace.” Ki bata ha’kuri yanzu.”!
Kallon fuskar sa tayi ta ganta a murtuke! Ya wani tsatstsare ta da ido, granny tace”Ba wai zan hana ta tabata hakuri bane amma ina so kafin ka yanke hukunci ka dunga bunkice ni dai da kunne na banji lokacin da Asma’u ta zagi Suwaiba ba, amma tunda abun ya zama haka ke Asma’u bata hakuri domin a zauna Lafiya. “! Hannu nasa na goge hawayen fuskata na kalli Innah Suwaiba dake zaune cikin kujera tana matsar hawaye nace” Innah kiyi hakuri don Allah.” Tace.” Oh-oh aike zan bawa hakuri ke da akazo gidan ki za’a takura miki.” Amjad yace.’Innah mu bar wannan maganar don Allah Insha Allah Zaku koma gidana dake Rijiyar Lemo da zama na bar muku kome kike bukata kiyi mun magana ni dan ki baki da banbanci da mahaifiyata Kuma Asma’u ma ‘yar ki ce tunda iyalina ce don Allah kiyi hakuri magana ta wuce.”
Inna Suwaiba bata so haka ba amma babu yanda ta iya tace”To nagode K’warai da gaske Allah yayi maka albarka ya jikan mahaifiyar ka, amma da nake cewa ko zamu je gidan gomnatin tare ne.”!
Cikin ‘kosawa yace.” Innah ki bari tukkuna in zama governor din sai a shirya shawarar abunda zai faru yanzu dai idan anjima zan sanya Doh-doh ya kaiku can gidan akwai kome a ciki babu abunda zaku nema.” Inna sai was he baki take yi tana shi masa albarka tace”To kafin mu tafi INA so muyi muhimiyar magana dakai.”.
Yace. ” tom Shikkenan ni dai burina ki kwantar da hankalin ki kuma ki dauki Asma’u kamar ni.” To Dan albarka kome ya wuce a gurina…… Ni kam tuni na bar musu gurin zuciyata kamar zata tsage saboda takaicin su gaba dayan su…. Kuka na zauna naci sosai a dakin.. Kafin ya shigo cikin shirin futa. Dauke kaina nayi daga kansa har ya karaso kusa dani ya sanya hannu ya dago fuskata hade da tsira min idonsa, lumshe idona nayi hawayen da nake makalewa suka zubo ….. Tsugunawa yayi ya tallafo fuskata ya fara aikunshi sai da ya tabbatar ya lashe ruwan hawayen da suke zubo min a fuskarta sannan yace.” Nasan Halin Innah Suwaiba da tada futuna Asma’u inaso kiyi hakuri da ita kamar yanda nake yi da ita ki dauke ta a matsayin uwa kinji ko kiyi min wannan alfarmar don Allah duk abunda zata tayi miki ki daina mayar mata da magana.”!!!