BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

Rungumeshi nayi sosai ina jin wani irin tausayin shi nace”Abban baby kayi hakuri don Allah Wallahi raina ne ya ‘baci shiyasa na mayar mata da magana amma insha Allah bazan sake ba.”!! Bayan ta yake bubbugawa cikin sigar rarrashi yake fada mata kalamai masu sanyaya zuciya har ya samu tayi shuru kana ya fada mata abunda zai futar dashi yanzu…. Asma’u tayi masa addu’a da fatan alkaro hade da samun nasara a rayuwa, bai futa daga dakin ba sai da ya ya mutsa mata jiki da salon soyayarsa ya futa ya barta da kewar sa.
Amjadu ne tare da dumbun jama’ar gari suke zagaye a birnin kano da kewayen ta dukanin wasu local goment da suke karshin jahar kano sai da suka zagaya yawon kamfen alhamdullahi babu wata local goment da shiga a ka jefe shi ko aka yi masa ihu! Ko wace local goment sun bada goyon baya, cike da samun nasara suka dawo gida.
12/12/2019
[12/13, 10:14 AM] .: BABBAN YARO
87
Amjad bai shiga gida ba sai da ya tabbatar da komai ya kammala a cikin gidan da ya mallakawa Mahaifiyar Asma’u gidane plate mai kyau sosai ginin zamani gida cikin jama’a kuma ‘yan boko dama yana da ire-ire wannan gidan yake ginasu saboda mabukata to gaskiya Wanda ya saka Umma a ciki nagani na fada ne komai na jin dadin rayuwa akwai shi a cikin gidan sannan yayi musu sallama Umma albarka kawai take shi masa ko a mafarki bata ta’ba tsammanin zata zauna irin wannan gidan ba na wane da wane, yanzu sun ringa sun gane cewar magauta ne hade da ‘yan siyasa masu Neman kujerar governor suka had’a wannan kutungwilar domin a tozarta Amjad din, a cewar su idan jama’ar gari suka ji cewar iyayen matar shi na yawon yaya zasu zage shi, to shima Amjad din tun kafin aje ko ina ya gane sharrin abokan adawa ne.
A ranar bai shiga gida ba sai kusan sha daya na dare domin sai da yaje ya dubo Rambo dake kwance asibiti yana samun kulawa sosai kuma bashi da wata matsala tunda Amjad din yana tsaye a kansa.
Yana shiga parlor yaga mace a zaune kan kujera tayi kirif da hijab! Ya tsorata domin baiyi tsammanin ganin kowa ba sanin da yayi dare yayi dukanin su basu yi bacci Ba.
Cike da mamaki yake kallonta yace.” Innah bakiyi bacci b.” ? Hamma! Ta buga Muryar ta da alamun bacci tace”ta ina zanyi bacci ina jiran ka ka dawo muyi muhimiyar magana wannan yaron yazo ya matsamin da lallai sai nazo mun tafi sabon gida wai Kaine ka umarce shi yazo ya dauke mu.” Amaj ya zauna cikin kujera cikin gajiya yace.” Nine nace Yazo ya kaiku gidan tunda mun gama magana dake tun da safe.”
Inna Suwaiba ta gyara zaman ta sosai tace”Har ka manta maganar da nace zamuyi da Kai ko.” Sosa kansa yayi yace.” Wallahi na manta Innah kin San abun da yawa kiyi hakuri.”
Tace”Ai ya wuce kam har kullum muna yi maka fatan alkairi da zamowa shugaba me adalci.” Yace.” Godiya nake Inna.”
Cikin kwantar da murya Innah tace”Dama Alfarma ce nake nema a gurin ka wacce nasan kana da damarta sai dai Idan baka yi NIYYA ba ko kuma matar ka ta hana ka amma abunda nake nema a gurinka Allah da manzon sa sun hallata maka shi kuma Kai kan ka zaka kara yin kwarjini ka zama cikkakan namiji mussaman yanzu da nauyi zai hau kanka yana da kyau ka amin cewa ‘bukata ta “
Cikin. “Kosawa sa maganar ta yace.” Innah idan muna magana dake tsakanin mu ne don Allah ki daina sako iyalina a ciki Asma’u bata isa ta sani nayi abunda ban yi niyya ba wannan tsakanina dake ne ji fad’i ko wace irin alfarma kike so insha Allah idan da hali ni zan miki alfarma innah ke kin wuce ki nemi alfarma a gurina.” Innah Suwaiba ta saki fuskarta sosai jin abunda Amjad din yace Tace.” Dama ina so ka auri ‘yar uwarka Hafsatu insha Allahu baka da matsala da ita nayi mata tarbiyya sosai zasu zauna lafiya da ita Asma’u mutukar wata futuna ta ‘bullo to babu shakka daga ‘bangaran ita Asma’u ne domin ni nasan yarinya ta me tarbiyya ce , bayan haka kuma Hafsa a kanka ta’ki sauraron d’imbun samarin ta da suke sonta da aure Tace dole kai take so, lokacin babu irin magiyar da banzo nayiwa kakar ka ba a kan mu hadaku aure ta bujere tare da fadin”Ita baza tayi maka dole ba katsaham! Muka samu labarin auran ka da wannan yarinyar me rasuwa ina nufin mahaifiyar baby ‘alamarin ya ‘bata mana rai sosai ganin muna a matsayin iyayen ka, ka kasa zuwa ka sanar mana shiyasa muka yi fushi muka koma gefe guda hade da zuba muTo. ido sai bayan ta mutu kuma shima katsaham! Muka ji auran ka da ita wannan d’in to da nayi bunkice sai na tabbatar da cewar kaima baka sani ba Allah ne ya nufin haka, to sai muka dauki abun a matsayin kaddara yanzu dukanin abunda ya faru a baya mun YAFE maka.”!
Ta k’arashe maganar ta ta tana sauke ajiyar zuciya.
Dama tun kafin ta fad’i maganar ta ya fahimci inda ta dosa, don haka bai wani furgita ba yace.” Innah idan muna magana dake a tsakaninmu ne don Allah ki daina sako sunan kowa ciki naji kina maganar cewa granny ta hanani auran Hafsa ki gafarce ni anan wallahi ba laifin ta bane granny tayi iya bakin kokarin ta gurin ganin ta ‘kulla auramu Allah bai nufa ba, idan tuhuma zakiyi to ni zaki tuhuma domin ni na nuna bana ra’ayin yarinyar Sam bana sha’awar auran zumunci, kiyi hakuri don Allah ki bar zancan ni Hafsa a matsayin ‘kanwa na dauke ta, insha Allah zan tsaya mata a kan kome idan ta samu miji zan yi mata aure kuma zan gantata amma maganar aure tsakanina da ita ki aje ta gefe.
Innah Suwaiba ta fashe da wani Mashahurin kuka tana fyace majina tace”Ta tabbata bani na dauki cikin ka ba yau tabbata ta bani ce na tsuguna na haifeka yau ta tabbata bani ce na shayar da Kai ba! Yau ka nuna min Aisha ce uwarka domin nasan ita baza ta ta’ba umartarka da abu ka bujere wa bu’katar ta ba, Alhmdullahi Allah yasa nima na Haifa da yau nasha takaici.”! Cikin kuka me futar da sauti ta ‘karasa maganar.
hankali a tashe yace.” Innah! Yi shiru don Allah ki daina wannan kukan da kike yi bana so, wallahi dukan abunda kika fada ba haka bane na fada miki a Yanzu bani da wata uwa da ta wuce ki kiyi hakuri kiyi shuru muyi maganar please.”!!!
Inna Suwaiba ta fyace majina kamar ba dare ba sai d’aga murya take yi ta cigaba da cewa”Idan da ka dauke ni a matsayin uwa ai baza kayi min musu a kan magana ta ba hummm.”!!
Amjad yace.” To kiyi shuru muyi maganar kinga dare ne kar ki tashi mutan gidan kiyi shuru don Allah.” Innah Suwaiba ta goge hawayen ta tana fad’in “To kai nake saurare.”!?
Ajiyar zuciya ya sauke ya dafe kansa mintu biyu tsakani yace.” Bukatar ki kawai in auri Hafsa ko.? Ko numfasawa bata bari yayi ba tace” Shine bukata ta yaron kirki.” Kallonta yayi idonsa yayi ja yace”Shikkenan Allah ya sanya alkairi. ” washe baki tayi tana zabga masa godiya tare da fad’in”Insha Allahu zaka yi alfahari da wannan auran tunda kayi min biyyaya.”
Mik’ewa yayi yace.” Innah ya kamata kije ki kwanta Shikkenan magana ta wuce na amunce. ” innah ta mike tana fadin “Allah ya tashe mu lafiya kaji yaron kirki gobe sai kara tusa maganar da tsayar da ranar d’aurin aure.”
Wuce wa yayi ba tare da ya tanka mata ba yana mamaki ta sosai shi yanzu babu maganar aure a gabanshi sai bayan za’be tukkuna kome ye sai ayi ya amunce mata ne kawai domin a zauna lafiya sosai yake mamakin rigimar mata.
Ina jin motsin shigowar sa ‘karamin Parlor na nayi saurin hayewa bed wasu masifaffun hawaye masu tsananin zafi suka kwaranyo min a fuskata.