BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

Asma’u yini tayi cikin fargaba sanin da tayi cewar mijinta ya tafi yawon kafen dole tasan akwai ma’kiya da suka saka shi a gaba mafi a kasari ba’a futa a dawo Lafiya shiyasa ta yini tana yi masa addu’a samun nasara da dawo wa lafiya hankalin ta bai kwanta ba sai da taji shigowar motar sa gidan sannan ta saki ajiyar zuciya taje ta d’aga labulen window tana le’ken sa har sai da ya shigo sannan ta sauke ajiyar zuciya ta zauna tana jiran sa ya shigo shuru har kusan minti ashirin tayi tunani ko yana d’akinsa zai yi wanka mik’ewa tayi da nufin zuwa kawai ta zo bude kofa taji maganganun su da Innah Amjad yayi wa Innar sa alk’awarin auran Hafsa auran ta dashi tun baije ko ina ba zai yi mata kishiya ita kuma tata ‘kaddarar kenan haka Mimi Tasha wahala akan shi itama gashi ko sati bata cika a gidan sa ba abubuwa sun cakud’e ta mata Innalillahi wa’ina ilahi raji’un. “!
Cikin wannan hali ya shigo ya same ta fitalar dakin ya kunna yaganta zaune daram kan bed! Asma’u duk kokarin ta na hana hawayen ta zubawa ta kasa zuba kawai suke yi sharrrrrr! Zuciyar ta sa wani irin Tara tsatsin kishi take yi.”!
[12/13, 9:32 AM] BintuUm@rAbb@le: Cikin yanayin tafiyar shi ya ‘karaso kusa da ita sam bai fahimci kuka take ba sai da ya kusan ci jikinta sosai yaji shashshekar kukan ta…. Jikinshi na kyarma ya zube wayoyinshi gefen bed din ya rugumota jikinsa yana sauke ajiyar zuciya tare da tambayar ta kukan me take, shifa ya tsani ganin zubar haweyen ta.
‘Kokarin kwace jikinta take shi kuma ya rike tam! Yana rarrashin ta Sam baiyi tsammanin taji maganar su da Innah ba tambayar ta yake yi me ya same ta take kuka…. Cikin zafin zuciya ta gartsa masa cizo! A hannu sosai yaji zafi a hannunsa ya ki sakinta duk ya rikice! Da kyar ta samu ta bude bakinta tace”Ka k’yaleni ni, tunda na lura kai kan ka kawai ka san…… Katse ta Yayi ta sauri yana rawar jiki yace.” Me nayi miki ne nifa bana son wannan kukan kiyi shuru ki min bayani ki daina magana kina kuka kinji.”! Yana maganar yana goga mata fuskar shi a tata wannan d’abi’ar shi ce da alama shu k’okari ma yake ya had’e bakin sa da nata.
Tace.” Duk maganganun da kuka yi da Innah naji su Kai ko kunya baka ji ba har da amincewa zaka auri hafsa wallahi bari in fad’a maka abunda baka sani ba zaka mai da gidan ka sansanin ya’ki domin tuntuni bama zama inuwa d’aya da wannan kucakar yarinyar me warin hammata! Ni kam na fad’a maka sai dai ka za’bi guda cikin mu ni ko ko ita domin wallahi bazan had’a miji da ita ba.”!
Yanda take fad’an maganar zaka San da ‘k’uruciya a tare da ita bayan nan Kuma tsananin kishi ya rufe mata ido Sam bata tunanin maganar da zata fad’a.
Maganar ta ta bashi dariya sosai amma sai ya dake baiyi ba sai ya sauya al’amarin ma ta wata sigar……. Haushi ya turni’ke ta tana yi masa magana yana wani Abu daban, ture shi take daga jikinta shi kuma yana ‘kara sakar mata nauyin sa har sai da yayi nasarar danne ta gaba d’aya ya tsira mata rukittatun idonsa masu kashe mata jiki.
Kauda fuskarta take yi ganin yana shirin yi mata abunda ya saba lallai ya raina mata hankali, sai ta fara ya kushe masa jiki tana turje-turje da ‘kafafun ta duk ta turje bedshirt din…… Yaso ya sanya mata ‘karfi kawai sai ya k’yaleta hade da sauka daga kanta… Toilet ya nufa domin yin wanka yana mamakin tsananin kishin ta a kansa.
Jikinsa daure da towel ya futo ya tsaya gaban dressing mirror ya feshe jikinsa da turare kana ya sanya Riga mai gajeran hannu….. Asma’u har yanzu tana zaune ta hade kai da gwiwa tana kuka, bai CE mata komai ba ta futa daga d’akin…
Mintuna biyar yayi ya dawo hannunsa rike da ‘karamin Cup Wanda yq had’o coffee a ciki ya zauna kusa da ita yana kurba yana latsa wayarsa.
Haushin sa kamar ya kashe ta wato ba zai rarrashe ta ba ma balle yayi mata musu akan maganar da ta kawo masa wayar shi ma yake dubawa ta tabbata kenan abunda kunnen ta yaji ye mata gaskiya ne.
Zuciya ce ta ciyo tace”Wallahi INA sane da masu sona da wa’inda basa so na Ni a rayuwata babu abunda zan cewa granny domin ta nuna mana ‘kauna dani da ‘yar uwata Mimi Allah ya. jikanta, duk abunda wannan matar take yi min baka cewa komai babu irin ‘kazafun da bata yi min ba dukol kayi shiru. To ni kuma nace bazan zauna da ‘yarta ba wallahi sai dai ka zab’i guda cikiin mu kuma duk wani Abu da take min taje na barta da Allah zai saka min.”
[12/13, 10:03 AM] BintuUm@rAbb@le Fuskar sa a had’e ya d’ago kansa yana kallonta “Kina da hankali kuwa Asma’u? Innah kike kokarin fad’awa magana a gabana uhumm.”!? Ya fad’a muryar shi babu dad’i!
Ba tare da na damu ba nace” Ai itace ta jawo meye ruwan ta dani a gidan mijina a matsayin ta na babba bai kamata ta shiga hurumin da bana ta ba tun da tazo gidan nan take zagina.” Cikin kuka take maganar….
Ido ya tsira mata fuskarsa babu wasa yace.” Ke Matsalar ki kenan tsaurin ido! Shiyasa kowa ya tashi zai fad’i aibunki ke baki bar yara ba baki bar manya ba uhumm ? Idan da mutumci ya dace ki fad’awa Innah Suwaiba wannan maganar ko da kuwa cewa tayi in auri mata uku a lokaci guda ai tana da iko dani ne.”
Asma’u taji kamar ya watsa mata barko no a ido idonta a rufe tace.” To sai me idan tace ka auri Hafsa bayan ita ka ‘kara da wasu biyu ko a kwalar rigar Asma’u wallahi ni dai nasan ta siya maka tashin hankali a cikin gidan ka, Wanda nasan idan Maman ka ce ita ta hak’ika baza ta so kayi rayuwa cikin tashin hankali ba, ita dai akwai wata manufar ta ita kad’ai ta sani.”!!! Sama-sama take maganar….
Babu wasa a maganar shi yace.” OK da kike yin wannan fuffukar kina tunanin zaki hanani abunda nayi niyya ne? Ko kina tunanin zan bujerewa maganar Inna Suwaiba akan taki, Wallahi ki shiga hankalin ki ni nan da kika ganni bana daukar raini gurin ko wace mace zan ‘bata miki rai Wallahi! Daga yau sai yau ki San irin maganar da zata dinga futowa daga bakin ki akan Inna domin duk rintsi Uwata ce ke ma haka dole ki girmama ta kamar yanda nake yi “you have to be serious.”! Ya fad’a cikin ‘bacin rai!
Asma’u kuka kawai take yi cikin zuciyar ta kuwa babu irin addu’ar da bata yi wa Innah Suwaiba Allah yayi mata katangar k’arfe da sharrin ta ubangiji Allah ya rusa maganar tun kafin aje ko ina ita tana ganin idan abun ya tabbata to babu shakka Zama Lafiya ya ‘kare tsakaninta dashi tana mugun sonsa Wanda shine ya jawo mata tsanin kishin sa.
Sosai take kuka Yana jinta Yayi mata shiru kurbar Coffe dinshi yake gefe guda kuma yana latsa wayarsa a zahiri ka kalleshi sai kace kukan NATA baya cin ransa cikin zuciyar sa kuwa shi kadai yasan yanda yake jin zafi da kukan ta, ranshi ya ‘baci ne da jin irin bak’aken maganganun da take fad’awa Innah Suwaiba ko kunyar idonsa bata ji ba, idan da zai bude mata zuciyarsa ta gani zata yi mamakin girman son ta da kaunar ta a ciki kawai yana dannewa ne saboda sanin halinta, shafa ya amsawa Inna ne kawai amma Sam bai shirya auran Hafsa ba yanzu bai sani ba ko nan gaba.
Asma’u ta gaji da kukan ta bacci me nauyi ya d’auketa cike da mafarkin ‘yan gidansu musamaman Ummansu ta ganta cikin farin ciki da walwala.
Jin saukar ajiyar zuciyarta ya gane tayi bacci shima ajiyar zuciyar ya sauke kana ya kashe wayar sa toilet ya shiga ya wanke bakinsa ya futo kai tsaye bed din ya nufa ya kwanta hade da shiga blenket din ya rungume ta jikinshi yana sauke a ajiyar zuciya k’amshin da jikinta yake futar wa ne ya gigita shi tuni ya fara ya mutsata yana kaiwa ko wanne shashe na jikinta kisses masu zafi! A rikice yake kokarin cire mata Riga… Furgit ta bude idonta ta ganshi yana kokarin hawa jikinta da sauri tayi nufin tashi ya mai da ita da hannu daya daya hannun kuma ya zare mata rigar jikinta tuni ya gigice ganin lafiyayyun Brest dinta masu gigita shi take ya rungume ta a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya.
Asma’u duk buge-bugen da take yi. Sai da Amjad yayi nasara a kanta ya samu biyan bukatar shi.