BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

Mai citta ya futo daga mota a gigice! Yana sa’be babbar rigar shi da ta gama jikewa da gumi fad’i yake'” kuyi hakuri don girman Allah kar Ku tab’a min Lafiya ta kar ki dake ni don Allah kuyi hakuri.”
Mari!! Wani daga cikinsu ya kaud’a masa! Cikin tsawa! Yace.” Cire wannan babbar rigar ta jikinka ko yanzu muyi maka zigidir.”
Da sauri! Ya cire babbar rigar ya jefar yana goge gumin fuskarsa, d’ayan yace.” Yi mana tsallan kwad’o.”! Babu musu mai citta ya dinga buga tsalle a kan titi shi kuma matashin na haurin sa da k’afar shi Mai citta sai zufa yake yi gwanin tausayi dukan shi yake yi a d’uwawu yana fad’in “Maza!!! Tsallan kwad’o da sauri! Allah sarki me citta ya dinga buga tsallan kwad’o yana nishi su kuma suna tayi masa dariya had’e da d’aukar shi vedio a wayoyin su domin sunyi nufin tozar tashi shi da ‘yar shi mara tarbiyya…….. Kasancewar jajiberan za’be ne yasa garin yake a hargitse babu Wanda ya fahimci abunda yake faruwa a gurin kowa na hidimar gaban shi dama kuma dare ne motoci jefi-jefi ne suke wucewa a titin sai da suka tabbatar da mai citta ya galabaita sannan suka k’yale shi suka dawo kan Hibbah da ta kusa suma saboda fargaba da tashin hankali….. Cikin iskanci suka jawo ta ta k’arfi ta fad’o kasan mota d’ankwalin ta ya kwance ta dauka zata d’aura suka take cikin tsawa dayansu yace.” Ke ‘yar iska ko wato kin shiga gidan redio zakiwa Governor mu k’azafi ko tom sai kin fada mana uban da yayi miki ciki kika lakabawa bawan Allah……. Hibbah tana kuka take basu hakuri babu Wanda ya saurare ta a cikinsu sai iskanci suke mata gashi suna kokarin yi mata tsirara a titi.
Cikin kuka tace.” Don Allah kuyi hakuri zan fad’a muku.” Take suka saurara mata mai babbar wayar ne ya sai ta camera yana daukarta tace.” Wallahi bashi bane sharri nayi masa domin. Ya aure ni.” Suka ce tom ki fad’i sunan Wanda yayi miki cikin.” Take tace” sharri ne ba gaskiya bane mun shirya maganar ne nida mahaifina muna ganin I Dan muka shiga gidan redio muka fada to zamu ‘bata masa suna.”
Mari suka dunga gaura mata suna harbin ta da k’afafun su… Daga bisani suka sakata tsallan kwad’o kamar yanda suka saka mahaifin ta….. Hibbah na kuka take tsallan kwad’o har ta isa gurin Baban nata da yayi mutukar galabaita tana kuka shi kuma yana share gumi.
Su kuwa matasan tuni sun bar gurin kai tsaye gidan redio komai da ruwan ka suka nufa domin. Kai musu rahoto suji kuma su gani duk maganar fa mai citta yazo Yayi karya ne…… Take suka fara turawa a wayoyin mutane a’lamarin ya watsu a media kafin Safiya kowa ya gane gaskiya mutane sai tur da Allah wadai suke yi da masu irin hallin mai citta.
A ranar Asma’u da Amjadu kwanan rigima suka yi gashi dai ranace ta farin ciki a gare su tunda Allah ya baiyana gaskiya…. Matsalar daga Asma’u ne ta inda take tayi masa shan’kam shi da yada masa magana cewar duk abunda ya faru laifin sa ne shine ya jawowa kansa raini da neme Neman matansa na tsiya…
Amjadu kam lallab’ata yake mussaman da fuskanci tana da ciki Bini Bini sai ya bude cikin yayi ta mata sambatu wai nan hira yake da babyn shi addu’a kuwa kullum sai yayi Allah ya bashi da namiji shi idan San samu ne ma Asma’u ta haifi ‘yaya uku lokaci guda…. Ni kuwa nace”Amjadu komai na Allah ne domin shine mai bayarwa da hanawa.
13/12/2019
[12/14, 11:48 AM] .: BABBAN YARO
89_90
Ga maibukatar cmplt. Sai same ni a wannan numbars 08089965176_07084653262
????????????????????????????
Wannan pege d'in sadaukarwa ne ga duk wani d'an kwankwasiya Amana Mussaman Madugu uban tafiya Dr Rabi'u Musa kwankwaso
⛑⛑⛑⛑⛑⛑⛑
Alhamdullahi anyi za’be an gama lafiya yanzu sauran zaman jiran sakamako, to abun dai ba sai an futo an fad’a a zahiri dai Amjadu duk yafi ko wane d’an takara yawan ‘kuri’u jama’ar gari sai murna suke yi domin suna ganin sun Riga sun gama cin za’be, Amjad kuwa yana gida tun bayan da ya futa ya sanya ‘kuri’ar shi ya dawo gida ya futini Asma’u yini yayi yana abu d’aya duk ya jigata ta, ya zamana da ‘kyar take motsa jikinta aikuwa ta dinga kyalaya amai! na futar hankali Wanda tun da ta samu cikin ba tayi irin shi ba, granny ta dinga fad’a kamar ta ari baki, dama tun daga ya’ki futa take fad’a tana cewa”Shikkenan ya ‘ki ya futo ya sanya yarinyar mutane a d’aki yana sasakarta ko tausayi babu.” Ita dai Iyami dariya kawai take yi tace “In banda abunki granny yau sharabon da kika ganshi ya zauna a gida irin yau, yau d’in ma dalili ne kuma kinga baza ki hanashi ya kusanci iyalinsa ba.” Granny tace”Duk da haka dai wallahi Iyami futunar ‘kato yawa gare ta, ace ka shiga d’aki ka kulle tun safe Dan jaraba ko yunwar cikinka baka ji humm Allah dai ya kyauta.”!
Iyami dariya takewa granny ta ‘mike tana fad’in “Granny kenan ko dai kishi kike yi ne.” ? Da sauri Granny tace” Babu wani kishi ina tausayawa baiwar Allah ne.” Cikin dariya Iyami tace”To ai aikin lada take yi kuma idan bazan manta ba kwanaki da bakin ki naji kina mata magana cewa ta tsaya ta kula da mijinta ta bashi hakkinsa saboda kar ya futa yabi matan bariki.”
Granny tace”Ai Ba irin wannan nake nufi ba Wato Iyami kema na lura kina goyon bayan ‘kato ko.”? Iyami tasa dariya tana fad’in”Dole ne in goyi bayan ubangidana shugaba mai adalci ubangiji Allah ya taya shi ri’ko yayi rik’o da hannayen sa Allah ya bashi ikon d’aukar nauyin jama’a.”
Granny taji dadin addu’ar Iyami shiyasa take sonta Iyami macace mai karamci da mutumci sun fi shekara goma a tare duk masu aikin da tayi tafi sha’kuwa da Granny kuma tafi sonta saboda tana kyautata mata, itama kuma tana kyauta ta mata gwargwadon iko idan Iyami zata je ‘K’auyan su Shatara ta arzi’ki granny take had’a mata Iyami tayi buhu-buhu da kayan masarufi ta kaiwa ‘yan uwanta na can da suke ganinta da daraja saboda tana mutukar taimaka musu.
Iyami kicin ta nufa domin had’a sanwar dare ita kuma granny tayi zaune a parlor tana jiran futowar masu gidan, Baby ce ta rarrafo tazo ta kama granny ta mike tsaye tana mata gwaranci Granny ta dauke ta tana fadin “Nasan Iyayen ki kike nema Yo idan suka ji kukan ki ai sa futo Dan dol… Kafin ta rufe bakinta baby ta tsandare da ihu! Tana nuna d’adin Asma’u da hannunta.
Rarrashin ta granny take yi fafur yarinyar ta’ki yin shiru sai ya zamana ma kamar ‘kara ingiza ta take yi. Iyami ta futo daga kicin da sauri tana fad’in” Baby rigima ai tunda ta fara wannan kukan nata komai zai tsaya.” Granny tace”Tayi min dai-dai Wallahi ke dai je ki cigaba da aikin ki.”
Iyami tace”Granny bari dai in tsaya in dama mata madarar ta kin san Abban ta baya son kukan ta abu komai a sannu dama Kuma yau ba abunci mai wahala zanyi ba.”
Granny ta mi’ke tsaye da baby a hannun ta kai tsaye bedroom d’in Asma’u tq nufa tana fad’in”Iyami baza kiyi mana girkin dare ba mutukar kika tsaya rarrashin Wannan ‘yar rigimar sai magariba tayi bakiyi komai ba, dole su futo haka.” Iyami tabi Granny da kallo cike da mamaki.!
Granny kuwa dukan ‘kofar d’akin take yi da hannunta tana fad’in”Kai d’an anace ka futo haka Haba! Wannan jaraba dame tayi kama! Ni kam na tsani wannan d’abiar taka, ku futo Ku d’auki ‘yar ku ta cika wa mutane kunne da kuka.” ! Baby ta ‘kara tsandara Ihu! Tana zillo dole sai ta sakko.