BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

Granny sai da tayi wata uku sannan ta dawo lokacin cikin Asma’u ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe a lokacin ne Kuma ayyuka suka tsananta ga governor domin ba k’aramin b’arna Alkanawi Yayi ba yanzu sun mai da hankali gurin ganin sun dai-dai ta komai a jahar kano.
Umma sau daya tazo gidan gomnati taga Asma’u ta sanya mata albarka tare da yi mata fatan sauka lafiya ta tafi cike da kauna da son yarta a zuciyarta
Aunt Hauwa kuwa ai tazo gidan yafi sau biyar duk da cewa akwai tsaro sosai amma babu yanda suka yi da aunt Hauwa domin wani sa’in gayya take yo wa ita kawayen ta lallai sai ta nuna musu itama babbar macace kanwarta tana auran governor.
Innah Suwaiba da Hafsa sunzo gidan ya kai sau goma securitys sun hana su ko da ra’bar gate din Saboda rashin sani har kuka sai da Innah Suwaiba tayi musu tana yi musu bayanin cewar ita mahaifiyar mai gidan ce suka ce basu San wannan tayi hakuri sai ya dawo tukkuna a lokacin suna Chadi….Haka suka koma gida jikinsu suk a mace zagi kuwa babu rij Wanda Innah batayi wa securitys din tana fad’in ” Idan governor ya dawo zai nuna muku matsayi na a gurinsa shegu tsinannanu.!
Da ta samu labarin dawowar shi sai ta sanya Hafsa ta shirya sosai suka nufi government house din zuciyar cike da kudure-kudure a cewar ta sai ta sa Amjad din ya kori wannan masu gadin da suka yi mata wulakanci sannan ta umarce shi ya sanya ranar d’aurin auran sa da Hafsa.: Ko da suka isa gidan sai suka yadda securitys har sun fi na kwanaki yawa tabbatar cewar mai girma governor yana ciki bai futo ba, taje ta tsaya tana musu magana dukaninsu Hausa bata ishe su ba domin kadan ne daga cikinsu hausawa turanci suke mata suna zare mata ido! Inna ta tsorata sai ta koma gefe guda tana haraarau Hafsa da ta tsinci kad’an daga abunda suke cewa tuni ta tsure! Domin cewa suke maza su bar gurin idan ba haka ba zasu Zane su da bulala! Inna na gama jin abunda Hafsa take cewa kawai sai ta fashe da kuka Wanda yayi dai-dai da shigowar Aunt Hauwa cikin gidan cikin dalleliyar motar ta. Ga mamakin Inna taga aunt ta bude mota ta futo kuma kaitseye ta durfafi securities din babu wani fargaba ko tsoro sai ta dunga mamakin ita kuma wacece ita? Gani tayi suna gaishe ta suna mata magana da turanci hade da nuna su da hannu abunda suke cewa shine wai tasan da zuwan su Innah ko kuma tare suke domin sun San ta saba zuwa gidan da jama’a .
Juyowar da aunt Hauwa tayi sai da gaban Innah ya fad’i ganin suna kama da Asma’u a zuciyarta tace”Babu shakka wannan yayar ta ce aikuwa hafsa tace”Yawwa inna ga aunt Hauwa nan sai tq shiga damu gidan.” Innah Suwaiba Tayi sakato da baki har aunt Hauwa ta karaso gurin ta gaishe ta cikin mutumci sannan tace”Kuzo mu shiga ciki gashi munyi sa’a duka mai grima governor yana nan bai futa ba.” Simi-simi suka bi bayan aunt Hauwa tayi musu jagora har katafaran parlor mai girma matar governor hamshakiya mandiya Asma’ulhusna.
Suna zaune a parlor ita da granny suna shira granny na saman kujera Asma’u na kasa kan wani irin lallausan kafet ta mike k’afafunta Shi kuma ubangayyar yana matsa mata granny tana fad’in “nauyin cikin ne yasa k’afar taki tayi kumburi nace anya kuwa Wannan cikin naki bana tagwaye bane.” Fad’ar maganar granny tayi dai-dai da shigowar su Innah Suwaiba cikin parlor
Innah Suwaiba tayi turus ganin abunda yake faruwa Amjad gurfane kamar wani bawa yana aikin mammatsa k’afafun Asma’u dake zaune da ciki turus a gaba daga ita har Hafsa jikinsu mugun sanyi yayi tuni Hafsa ta tabbatar wa da zuciyar ta cewar Asma’u tayi mata nisa kuma tayi mata fintikau ya kowa ne b’angaran tasan ko inna ta sanya Amjad din ya aure ta to tasan itace zata sha wahala a gidan Saboda tasan irin son da Amjad din yake wa Asma’u bana wasa bane jikinta yayi bala’in sanyi kamar yanda na innah yayi sanyi cikin sagewar gwiwa suka karaso cikin parlor granny tana musu barka da zuwa
Ita kuwa aunt Hauwa kunya ce ta ishe ta bata tab’a jin nadamar zuwa gidan ba irin na yau governor da kansa yana yiwa kanwarta tausa lallai babu abunda zasu cewa Allah tabbas yanzu ta k’ara tabbatar da cewar kauna da so tsakanin kanwarta ta dashi Amjadu din ajininsu yake. Bayan sun gaisa da granny dashi kanshi uban gayyar ta wuce dakin Asma’u cikin kunya.
Ita kuwa Asma’u a ladafce ta gaishe da inna Suwaiba dake faman ya’ke tana satar kallonta a fakaice har ta samu damar mik’ewa tsaye a daddafe Amjad din yana taimaka mata sai da ya kaita kofar d’akinta sannan ya sake ta ta shiga gurin aunt shi kuma sai sannan hankalinsa ya dawo jikinsa ya dawo cikin parlor Innah Suwaiba tayi muzu-muzu tana jin Shakkar ta fada masa abunda ya kawo ta gidan saboda yanda yayi mata mugun kwarjini a ido haka suka gaisa dashi jikinta sai kyarma yake yi Hafsa kuwa ba yarda ta hada ido dashi ba. Saboda kwarjini gami da tsoro duk masifar da Inna tazo dashi ta neme shi ta rasa sai ta fara jan granny da hira cikin rashin abinyi Ita kuwa granny biye mata tayi suka dinga hira kamar wani Abu bai faru ba…. Sunanan zaune Amjadu din ya futo cikin shirin futa…ya tsa Yana fadin”Innah zan futa ofis babu wata matsala ko.”! Baki na rawa tace”Babu komai Dan albarka Duk ka cika mu da abun alkairi wallahi bama bukatar komai mungode sosai Ubangiji Allah ya jikan mahaifiyar ka.” Ya amsa da “”Ameen kana ya futa yana mamaki innah da bata yi masa wani k’orafi ba sai yaga ma kamar tsoransa take ji..shu kadai ya ke dariya cikin mota Rambo dake gefan sa yana taya shi murmusawa hummm Rayuwa kenan Amjadu bai zubar da bodyguard dinshi ba a yanzu ma sune suke take masa baya kasamcewar duk wata gwagwarmaya tare aka sha dasu.
Bayan shekaru hudu abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa har da haihuwar Asma’u inda ta haifi twins duk maza masu kama da mahaifin su Allah bayanda baya al’amarin shi ana ya gobe suna Hassam din ya rasu sakamakon shakewar nuffashi dalili lokacin an haifi yaran da sanyi a jikinsu Amjadu sai da yayi kuka saboda ya yana son Hassan din kasamcewar ya Dan d’auko kamanin Asma’u kadan a lokacin sai Asma’u tafi shi dauriya. Hakadai ya ‘karaci kukan shi ya gama ya barwa Allah to da yake ubangiji sami’uddu’ai ne sai ya kara bawa Asma’u cikin tagwaye lokacin Husaini na wata goma sha daya ta haife su duk mata kuma masu tsananin kama da ita sai dai daya tafi daya haske Hasana farace tas kamar ubanta ita kuwa Husaini kamar Asma’u tayi kaki ta tofar har yanayin jikinsu da saurin bakinta gami da zafin nama irin na uciki Amjad ya Dora mata son duniya komai Husaina komai Husaina gata da tsokana da Neman fada amma shi a gurin sa bata laifi idan Maman su ma ta tsananta sai su kwana su yini yana surfa mata masifa wani sa’in ma sai ya dauketa ma wuta ya daina kulata akan ‘yayan sa sai taje tayi banbad’anci tukkuna zai dawo…. Lokacin baby ta girma sosai yarinya me fara’a da hankali kamar uwarta yanayin baby sak da na Mimi domin wani lokacin Husaina tayi ta haike mata tana tsagalgale mata Saboda tasan tana da daurin gindi a gidan… Ko a gaban Amjadu din kuwa abun mamaki sai yayi shuru ko ya mai da abun wasa ita kuwa Asma’u sai bayan ta tabbatar ya bar gidan take kama Husaina ta zane tas! Ta kuna mata muhimamcin baby a gurinta abunda zai baka mamaki ga wannan family shine duk sanda Asma’un take dukan Husaina Saboda halinta babyn ce zata zo ta rugumeta ta kuka wai sai dai a Doke su tare Asma’u takaici duk ya ishe ta Tayi ta fada tana cewa duk laifin baby ne da take wasa dasu….. Granny kuwa ‘yar kallo tq zama a gidan domin Sam bata shiga har karsu Saboda sun gama raina ta Ubansu ya gama shagwaba su baby da Husaini sune c kawai take mutuntata a gidan.