BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

To sai daf sallahr magariba sannan taro ya tashi kowa ya koma gida rike da k'atuwar Leda me hoton ango da amarya da kayayyaki a ciki abun burge wa sai muce Allah ya sanya alkairi.Misalin 11:00 na safe aunt Hauwa suka iso gidan ita da k'awarta Zainab, granny da Iyami suka samu a parlor suka gaisa da ita cikin mutumci nan ta nuna musu dakin Asma'u take suka mike aunty Hauwa tana rike da wata Leda me Zane- Zane suka shiga dakin.
Ina zaune kasan kafet ina shirya baby domin a gurina ta kwana taki yadda da Iyami ko kadan suka shigo jin muryar aunt Hauwa yasa na dago da sauri ina amsawa suka karaso dakin nace”Aunt sannunku da zuwa.. Zama suka yi bakin gado na juyo muna gaisawa nace”Aunt Ina Umammu Ashe dama hak…… Katseni tayi da sauri tace”Yanzu maganar k’orafi da tashin tashina ta kare tunda dai gaki jikin gidan sai kiyi hakuri k’walla nagoge kawai ina gyada kaina cike da takaici, tace.” Ba zama ne ya kawo mu ba matso inyi miki bayani.” Juyowa nayi ina kallonta aunt Zainab tace”Ni banga abun kuka da damuwa ba ke da Allah ya mallaka mi miji na tsrewa sa’a.” Da sauri nace”Aunt Zainab auran irinsu abban baby had’ari ne wallahi ki dubi yadda rayuwar Mimi ta kare duk a kansa.”
Aunt Hauwa tace”Ke bana so shirme itama tata kaddarar kenan kowa da tashi dama Allah yayi Mimi ba me tsawon kwana bace, kema kika iya zama dashi zaki dauke hankalinsa daga kan ko wace mace shiyasa ma nake kokarin gyara ki. Kuma wallahi banda gaddama gurin shimfid’a abunda yake tunzura zuciyar maza kenan har ta kaisu ha Neman Matan waja.” Aunt Zainab tace”Hakane kawata yaran yanzu sun kasa fahimtar hakan wai idan mijinki yayi miki laifi sai ki kaurace masa a shimfid’a to ba haka ake hukunci ba. Idan kikayi fada da mijinki kar ki FASA yi masa duk wani Abu da kika saba yi masa kawai idan kina so ki ga gazawar sa to ki rage walwala a gida ki rage fara’a ki kama kanki, Tom shi kuma a lokacin zai shiga halin damuwa zai San abunda yayi miki ne, kuma zaki bashi tausayi ki kara shiga ranshi, dalili zaiga dukkanin wani hakkinsa kina sauke masa, take idan me tsoron Allah ne zai zo ya baki hakuri to Kinga ko tanan kinyi winning d’inshi.” Aunt Hauwa aunty Zainab suka d’age suna kara wayarwa da Asma’u kai kan zamantakewar aure, kana suka fara yi mata bayanin yanda zata yi amfani da kayan mata ‘yan gaske Wanda da Kansu suka hada mata domin nemo mata martabar ta a gidan miji suka yi mata bayani sallah dallah suka mike da niyyar tafiya Kuka ta sanya tana fad’in sai kace wata mara galihu daga zuwa zaku tafi haba aunt Hauwa. “!!!
Cikin tsokana aunt Zainab tace”Aikuwa dai Gaskiya Dole muci kazar amarci gaskiya.” Hararata aunt Hauwa tayi tace”kin zama babbar kwabo wallahi idan ya shigo ya ganki kice me.” ? Da sauri na mike na bude wani firji dake can gefa Leda na ciro nazo na aje gaban su na Ciro robobin yugut da biyu masu sanyi aunt hauwa tace”Baki da hankali Asma’u waye zai ci wannan kajin da sanyi a jikinsu..”! Aunt Zainab ta bude ledar tana dubawa lafiyyayn gassasun kaji ne sunji kayan had’u guda uku sai dai babu wacce aka gutsira sunyi sanyi kadan dalili frijin ba a kunne yake ba… Zainab tace”k’aryar ki ta sha karya kawata inke baza ki ci ni zanci domin nasan wannan kajin karshen su zubar wa da kyawun su, nuna min kicin in shiga in gasa yanzu… Nace”Naga kamar akwai k’aramin kicin a parlor na bayan na babban parlor tace “muje ji nuna min.” Futa mukayi na nuna mata aunt Zainab ta kunna oven ta gasa kajinan tsaf sai kamshi da turiri suke ta zubo su k’aton plate ta futo take kamshi ya cika dakin nima naji mi yau na ya tsinke, kawai sai na zauna cikinsu muna ci muna hira, domin dama ko da na tashi ban karya ba, duk da cewar ga kayan karin nan a je… Fula’s din tea na jawo na hada tare da fad’in “Aunt ko in hada muku tea din.”? Gyada kai kurrum sukayi tare da fadin wannan ma ya isa… Kurbar ruwan shayin nake ina tunani Amjad tun a gurin Walima rabona dashi har yanzu banji motsin sa ba…….
4/12/2019
[12/5, 7:50 AM] .: BABBAN YARO
74
Aunt Hauwa sauri sauri take cin kazar a cewar ta wai bata so Amjad din ya shigo ya ganta sai yaga kamar rashin hankali, aikuwa kafin su gama ci muka ji alamun bude kofa aunt Hauwa ta zabura! Da sauri ta gyara zama ta koma gefan gado tace”Tashi maza ki tare shi daga parlor mana.” Ganin yanda tayi maganar babu wasa a fuskarta yasa na mike sa sauri Baby ta sanya kuka dawowa nayi na dauke na bude kofar.. Ina budewa na ganshi tsaye a gurun hankalin sa na kan wayar shi kome yake dubawa oho! Saurin kauda kaina nayi tsigar jikina na Mik’ewa take naji sha’awar shi ta kamani yana sanye da wata d’amammiyar vest ash color had’e da 3Queatr mai aljuhu na gaba da baya, fatar shi tayi wani fresh kwantaccan gashin da yabi lafiyyar fatar tashi shine yake gigita ni yake samun sha’awar shi… Baby ce take zillo sai taje gurin sa. Ya zura wayar cikin aljuhu ya karb’e ta daga hannuna yana dariya kamar bashi ba, sai wasa yake mata tana dariya, sai da suka gama sannan ya kalle ni babu yabo babu fallasa yace.” Kun tashi lafiya.”!? Kunya naji kadan abunda ya kamata ni in fara gaishe shi. Nace”Lafiya k’alau kaifa.” ?
Baby yake wa wasa bai ce min komai ba, sai nayi nufin komawa dakin. Gyaran murya yayi na juyo a hankali ina kallonsa yace.” Ke da waye ciki naji kamar sautin maganar mata a ciki.” Kai tsaye nace “Su Aunt Hauwa ne.” Wacece ita.”? Ya fada cikin rashin sani. Na Dan ji babu dad’i ganin yanda yayi maganar babu walwala a tare dani nace”Aunt Hauwa zakace baka sani ba.”? Jim! Yayi daga bisani yace. ” Sorry nagane ta a maimakon kimin magana nazo in gaisa dasu sai kiyi shiru wato da ban tambaye ki ba baza ki fada ba ko.”
Ajiyar zuciya na sauke nace”Zan fada mana yanzu ma na mance ne.” Shuru yayi min yana kokarin shiga dakin. Naji kamar in jawo shi in hanashi shiga ciki dakin Saboda yanayin kayan jikinsa, wani irin kishin sa nake ji bana so ko su aunt Hauwa su ganshi haka.
Sakin fuskarsa yayi sosai suka gaisa dasu aunt Hauwa kana ya futo ya same ni inda nake. Bai ce min komai ba ya bar gurin kafadar shi sab’e da baby… Jikina babu kwari na koma cikin dakin inda na har sun mike suna shirin tafiya kamar in sanya kuka haka nake ji. Nayi diriduri Neman abunda zan basu nake na rasa da sauri na bude wardrobe din da naga ya bude jiya na fara bin cikin ta da kallo. Wasu dogwayen riguna na ciru a daure na Ciro Mayafai biyu Leda na sanya na biyo bayan su da sauri. Nan na Tarar suna sallama da granny na bi bayan su INA mik’a wa aunt Hauwa abunda ke hannuna. Karba tayi mukayi sallama idona cike da k’walla nace aunt ki gaida min da Umma don Allah.
Tana tafiya tace”Zata ji insha Allahu. ” Rambo ne yayi musu magana yana nuna musu mota kai tsaye suka nufi inda motar take suka shiga Doh-doh yaja motar suka futa daga gate din… Ciki na koma zuciya ta babu dad’i kwata-kwata…. Na parlor na zauna kusa da granny dake kallon tashar sunnah tv malam Umar Sani fagge ba tambihi… Tace”Wannan yayyun naki suna da hankali da nutsuwa Asma’u. ” murmushi nayi kurrum ta cigaba da cewa”Dama inaso in kara kwantar miki da hankali cewar don Allah kar ki d’aga hankalin ki kan abunda kika ji Suwaiba na fad’a jiya kiyi hakuri da abunda tayi kinji ko.”! Murmushin takaici nayi nace “Babu komai granny Wallahi ni zuciya ta fes take wallahi ban sanya abun a raina ba, duk abunda ya faru dani nasan kaddara tace.” Granny taji tausayin yarinyar ya kara shiga ranta tace”Yawwa haka ake son mutum me saurin fahimta.” Sake wa nayi da granny muka dinga hira nake tambayar ta baby tace”Tana gurun babanta irin wannan lokacin suke bacci mutukar yana gida, shuru kawai nayi na kamo wani zancan.. Iyami CE ta shigo tana tambayar granny me za”a girka na abincin rana Granny tace.” Ga matar gidanan Ki tambaye ta mana.”
Dariya granny ta bani jin abunda tace, nace” Lokacin da banzo gidan ba ku ne kuka tsara abunku yanzu kuma sai ace a tambaye ni.” Cikin bada kulawa tace”ai hakkin ki ne dole a tambaye ki, don ta k’ato ne mai sauki ne ba komai yake ci a gidanan ba dama kece zaki koya masa cin abunci a gida. ” nace “Wallahi nima komai a dafa zanci.” Iyami ta bar gurin tana mana dariya……. Kiran sallahr azuhur ne ya tada mu daga gurin kuma har lokacin su baby basu tashi daga bacci ba… Wanka na soma yi na dauro alwala na futo tsane jikina nayi sannan na shafe jikina da humra wacce k’amshin ta ya Riga ya kama jikina, duk kayana na gidanmu har da Wanda na dinka na futar buki don haka sai na rasa Wanda zan sanya…. K’atuwar wardrobe din dai na bude na fara dube-dube idona ya sauka kan wasu d’aurarraun Pakistan, da sauri na jawo su ina kwance wa Allah yayi ni da son Pakistan sosai da dogwayen riguna wani ne ya bani sha’awa pink coulor ya sha ado da stons sai daukar ido yake take na cire shi daga ledar shi na sanya a jikina gaban mirror na tsaya ina duba kaina, wallahi ni kaina nasan nayi kyau sosai ya kamani daga k’irjina dai-dai kuguna ya bude dalili akwai tsaga gefe-da gefe duk da wando k’ato ne bai hana bayyanuwar hips d’ina ba, sumar kaina na taje na hade ta tsakiyar kaina tayi tsini sosai sai na Dora net din da nayi futar buki dashi….jikina na kara feshewa da turare ko da wasa banyi wani fente-fente ba a fuskata saboda nasan ba kasafai nake yin kyau ba fuskata duk sai ta dame…. Futa nayi kafata sanye da wani takalmi plate, granny na samu zaune kan kujera da carbi a hannunta.