BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

Ina zama tana shafa addu'ar ta tace"Ca nake bak'uwa mukayi daga k'asar Hindu ." Dariya NASA ina rufe bakina tace"Kinyi kyau Maman baby sai kace yarinyar nan ta hindiya ya ma take da suna."? Wai ni take tambaya Dariya kawai nake mata ganin da gaske take maganar.... Iyami ce ta shigo tace"Yauwa Iyami yama sunan yarinyar ta wannan film din mai yawan fara'a."!? Take Iyami tace"  Johi chaula." Yanda Iyami ta fad'i sunan yayi mugun bani dariya dake wa kawai nayi nace"Granny ina ni ina wannan tsohuwar matar." Tace"Ai dama ba cewa nayi sa'ar ki bace cewa nayi kuna kama ko ba haka ba Iyami."? Iyami tace"Hakane Hajiya nima yanzu naga kammanin sun futo Sosai.."! 

Ni dai ban San sanda na fashe da dariya ba take dimples dina duk suka futo Iyami tace”Wallahi har irin dariyar su ma gashi kumatunta yana motsawa.” Ni dariya granny dariya nace”Ni kam Iyami ki daina had’ani da wannan tafi ni kyau nesa ba kusa ba ina ni ina ita ki duba da kyau don Alla…..Maganar tawa ta katse ganinshi ya futo daga bedroom din shi nayi saurin gintse fuskata ina kokarin kama kaina.. Iyami kuwa cigaba da k’od’a ni take wai nayi kyau har da rantse wa.
Kallonta yake tun daga samanta har kasan ta, tabbas ba karya Iyami tayi ba shima ya gani dressing din ya karb’a ta bai San me yasa pink din Abu yake mata kyau ba.. Sosai kwalliyar ta ta bashi sha’awa amma ko a fuska bai nuna ba, ya tsaya bakin k’ofa yana fad’in”Granny me yasa baku tashe ni ba gashi har lokacin sallah ya wuce uhumm!.” Tace”Wallahi yanzu nake tunanin ince Asma’u ta shiga ta duba Ku Ashe baka tashi ba sai yanzu.” Girgiza kansa kawai yayi ya koma ciki dakin jikinsa duk ya mace jin masifaffan k’amshin yarinyar.

Granny tace” Maza tashi kije ko da akwai abunda zaki masa.” Mik’ewa nayi babu kuzari a jikina na nufi dakin… Wani irin sanyi da kamshin dad’i suka bakunce ni. Duk da cewa ba yau ne karon farko da na fara shigowa dakin ba, sai da gabana ya fad’i dana tuno abubuwan da suka faru tsakanina dashi shekarun baya….. Baby na kwance kan bed tana bacci na karasa Cikin dakin sosai zama nayi gefen bed din ina jin motsin zubar ruwa a toilet din… Wanka yake yi bed din nake kallo duk ya ya mutse ga baby a kwance bare in gyara masa, can na hango wani k’aramin frem hannu nasa na dauko ina dubawa.. Mimi ce tana dariya Lokacin tana da cikin baby da alama shine ya dauke ta a wayarsa don shi din take kallo tana dariya lokacin tayi wannan ramar da haske amma tayi kyau sosai….. Hoton na rungume a k’irjina hawaye suka fara zubo mun nace da na sani ban shigo dakin ba..kuka nake sosai domin na ma mance a inda nake jin motsin bude kofa yasa nayi saurin goge fuskata Ina kokarin mai da hoton in da yake Cikin tsautsayi ya fad’i kasa take ya tsage gida biyu… Wanda yayi dai-dai da futowar sa daure da towel ido muka hada dashi. Nayi saurin sunkyar da nawa saboda ganin yanda ya futo.. Hoton nake dubawa gabana na fad’uwa. Karasowa yayi kusa dani bai ce komai ba ya sanya hannu ya karb’i frem din yana dubawa naga ya b’ata fuska cikin tuhuma ya kalleni kana yace.” Meye dalilin ki da zaki tsaga min hoto. “? Tambayar shi ta bani mamaki K’warai nace” Kamar yaya.”!?

Babu walwala a tare dashi yace." Ina tambayar ki kina tambaya ta. Duba b'arnar da kika yi min lokaci guda shekarar abina guda babu abunda ya same shi sai dalilin ki."! Raina ya b'aci amma sai na danne zuciya ta kawai na mike da niyyar tafiya domin nasan laifina ne da na shigo masa daki har na dauki abun shi.. Tsaki naji yaja kasa-kasa yace." Ke akan kowa ma sai kin gwada kishi." Sai da na futa daga d'akin tukkuna na fara tunanin me maganar shi take nufi? Ni a kan kowa ma sai na gwada kishi! Idan na fahimce shi yana nufin kishin Mimi ne ya sanya na fasa hotonta Ikon Allah."!! Abun ya bani mamaki matuka Mimi ko tana raye a duniya Allah ya hada mu auran Namiji daya bazan yi kishi da ita ba, to ko zanyi kishi a kansa sai inyi da Wanda bana ganin shi baya Raye a duniyar ma gabaki daya.

Nafi minti a shirin ina tunanin wannan al’amari daga bisani na share maganar kawai domin dai ni nasan Mimi tafi k’arfin komai a gurina kuma ina zargin domin ya kuntata min yayi min wannan maganar…. Parlor na futo domun bana son tsohuwar ta fuskanci wata matsala amma nayi alk’awarin guy nan ya shigo gona ta zan gasa shi kamar yanda yake min wulakanci son ranshi, Granny tace”Dama yanzu nake tunanin kiran ki ki futo muci abunci .” nace gani na futo granny Daining muka nufa Ni da Ita. Ko da wasa ban kalli shi ba na fara hadawa kowa nashi.. Yana zaune da airpix s kunnen shi baby na jikin shi tana wasa tana ganina ta dinga kokarin saukowa granny ta dauke ta tana fad’in”Bari taci abunci tukkuna.” Kuka tasa nace”Baby rigima Bari in gama zan dauke ki.” Cikin sauri na had’a mishi abunci na tura gaban shi granny tace”Dauke ta ni na hada da kaina.” ‘Yar dariya nayi nace “Bari in karasa lada na.” Lokacin kuwa baby har ta fara kuka abunda baya so kenan a rayuwar shi kukan baby a kufule yace.” Malama ki dauke ta ki k’yale cin abunci mana dole ne.”!! Granny tace”A’a!!! K’ato bana son son Kai ba, ji wani magana da kake cin abunci Dole ne mana idan bata ci ba ta yaya zata yi maka rainon yarinyar… Wayar tashi ya aje kan teble din yana kokarin karb’ar baby dake zillo sai tazo gurina, yaro kenan duk yanda take da Dadyn ta taki yadda dashi. Yaji kamar ya tashi ya gaggaura wa Asma’u mari a hasale! Yace.” Asma’u wai ba dake nake ba ne.”!? Idona na d’ago na kalleshi babu yabo babu fallasa nace” To.” Daga haka nayi shiru ja goge hannuna da tissues na karb’i baby daga hannun granny barin gurun nayi raina duk babu dad’i tsaki yaja ya cigaba da danna wayarsa ko kallon abincin banyi ba… Parlor na zauna cikin kujera da baby granny ta biyo da plate din abincin a hannunta tana ta faman mita “Ni wannan rashin. Kawaicin naka akan baby shine yake bani haushi dai kai wallahi duk yanda mutum yaso ya kyauta ta maka sai ka kaishi k’arshe ka canza halinka Haba! Ina dalilin Wannan Abu.”!!

5/12/2019
[12/6, 12:51 PM] .: BABBAN YARO
75

Shi dai shiru yayi mata yana latse-latse a waya ranshi nayi masa zafi domin har yanzu baby kuka take yi taki yin shiru Mik’ewa yayi ya karasa kusa dasu baby ya karba daga hannunta har
Hannunsu har yana had’uwa jikinta ya tab’awa yaji alamun zazzab’i, zama yayi kan kujera yana kokarin cire mata Riga jikinta ya kalli Asma’u da ta zuba musu ido shi da babyn yace.” Ki duba dakin kan drowar akwai maganin ta dauko min.” Asma’u ta mik’e jikinta babu kuzari, baby yake hurawa kunne yana rarrashinta granny tace”Zazzab’i ne yake damunta ko.”? Gyada kansa yayi kurrum. Tace”Hak’ori zan sa Iyami taje ta had’o mata dauri tunda ga ba nono take sha ba ballanta yayi mata magani… Ina mik’a masa kwalbar maganin na bar gurin. Kuma har yanzu yarinyar bata daina kuka ba fafur taki karb’ar maganin daga hannunsa sai bugewa take duk jikinsa ya b’aci granny tace”Wacce dai ka karaina kake wa tsawa da nunawa iyaka ita din dai zaka je ka nemi taimakon ta domin nima kasan baby ba yadda take dani ba.”

Shiru yayi mata yana matsawa baby tasha magani tana buge-buge dole dai ya mike da ita a kafad'a ya nufi dakin Asma'u da ita.... Ina zaune duk abun duniya ya dame ni ga kukan baby na damuna ka bakin cikin abunda yayi mun a kanta cikin wannan hali ya shigo dakin.


Kauda kaina nayi daga kansa domin wani irin haushin sa nake ji, Mik'o min ita yayi ba tare da tace min komai ba." Danne zuciya ta nayi nace"Me zanyi mata."? Kai tsaye yace." Ki bata magani tasha.'' Babu sauki s muryata nace"Kai da kake Ubanta baka bata sai ni 'yar karo."'" Hannu ya daga min da sauri yace." Ban nemi wata magana daga gare ki ba. Yarinyar nan tun da ta tashi bata yi kuka ba sai da kika zo gurin, duk kece sila kina ji ta fara kuka me yasa baza ki bar abunda kuke yi ba ki dauke ta, kece kika tunzurata take kuka har zazzab'i ya kamata."!! Cikin mamaki nake kallonsa ganin da gaske yake maganar nace"Kana nufin nice na d'ora mata zazzab'in kome. "? D'ora min ita yayi a jikina yace." Nifa ba haka nake nufi ba yanzu dai bata maganin sai muyi magana." Tsaki nayi niyyar inyi masa ganin rainin hankalin sa yayi yawa sai kawai na fasa na rike baby dake zura hannuta cikin rigata kamar me son tasha nono tana kuka da makyarkyata ban tab'a jin tausayin yarinyar ba irin na yau take wasu zafafan hawaye suka soma zubo min.......... Nace"Baby sannu kinji maganin ya mik'o min yace." Bata mu gani." Karba nayi na fara kokarin bata ta datse bakin ta.... Hannu na sanya na bude bakinta da sauri na d'ura mata maganin ta had'iya d'aga ta nayi ina girgiza ta sai shashsheka take yi ns rungume ta kam a jikina.

Yana tsaye a kanmu har Lokacin da nasamu baby ta sauke ajiyar zuciya bacci ya dauke ta, lura da yayi da hakan ne ya zare hannunsa daga cikin aljuhu ya fara kokarin d’aukar yarinyar dake rungume a jikina tana sakin ajiyar zuciya… Rike ta nayi kam a jikina ina hararasa Hankali nace “Zata tashi fa……… Bai ce min komai ba ya bar dakin na bishi da kallo cikin jin haushi kwantar da baby nayi na gyara ta sosai kana mike a hankali na shiga toilet domin dauro alwala, sallah nayi na kwanta kan daddumar bacci me nauyi ya dauke ni, Lokacin Amjad ya shigo ya tadda duk suna bacci daga ita har babyn sun bashi tws

Tausayi sosai Asma’u ya dauka kamar wata jaririya ya kwantar da ita kusa da baby hijab din jikinta ya ke kokarin cire mata ta bude idonta da sauri!! Mik’ewa tayi zaune tayi tana kallon shi. Ita yake kallo babu yabo babu fallasa yace.” Ki huta kema naga kin bacci a kasa ne.” Hannunsa ta kalla dake rike da hijab dinta yak’i saki….. Kauda kanta tayi tana kokarin sauka kasa dawo da ita yayi da hannunsa yana fad’in “Ina zaki je? Babu fuska tace” Zan shiga band’aki ne.” Sakin ta yayi ita kuma ta sauko band’aki ta shiga cikin rashin sanin abinyi, kawai sai ta tsiri wanka, shi kam cikin shiri yake domin futa amma ganin yanayin Asma’u ya tada masa da sha’awa yana jin ko ya futa bazai iya komai ba dama daurewa kawai yake yi domin kar ya nuna mata zulamar sa… Zama yayi yana jiran futowar ta

Asma’u ta manta d’auka ya futa daga dakin sai ta futo daure da guntun towel iya cinya hankalin sa nakan wayarsa yaga futowar ta ta kasan idonsa da yanda tayi saurin komawa da baya.. Girgiza kansa yayi kurrum ya cigaba da latsa wayar sa. Kayan ta tayi saurin mai dawa ta futo tana b’ata fuskar ta… Hankalinsa kan wayar shi yace.” Wanka me kikayi da rana haka.” Shiru nayi masa kawai ni so nake ya bar mun dakin naga ma futa zaiyi daga gidan dama duk a takure nake zaman shi a gidan kwana biyu kacal. Yace.”ko mafarki kikayi.”?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button