BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

Mai girma governor tsaye  a parlor shi hankalin shi a mungun tashe jin abunda yake faruwa a gari, shifa ya dauka yaron ya hak'ura Ashe kwance-kwance yayi musu sai da suka saki jikinsu mutukar sunan shi ya futo cikin wannan badakalar to babu shakka yasan ya gama amfani a garin kano yasan jama'ar gari sai sun kusa kashe shi da iyalinsa gashi daf ake da zab'e bayan nan kuma yasan daga sama gurin shugaban kasa sai ya fuskanci hukunci mai tsanani watak'ila ma sai ya daure shi.... Kaiwa yake yana kawowa cikin tunanin Neman mafuta.

Matar shi ta futo cikin kwalliya ta tardar shi cikin wannan halin nan take tambayar sa duk ya warware mata komai murmushi tayi tace”ka kwantar da hankalin ka mijina Kaine dai akan mulki kana da damar da zaka iya sawa ka hana kuma insha Allahu mulki sai ya dawo hannunmu mune zamu maimainta zama kan kujera daram!! Ka sanya su Lauje da fafake Kumurci tare da police suje su tashi taron idan ta kama ma su saki harbi da tiyagas tom zakaga kowa na kokarin guduwa domin ceton ransa. Nan su Lauje sai su dauko manager din su zo dashi mu kuma mun San inda zamu yi dashi ka San dai karshen zancan.”

Take governor ya yarda da sha’awarar matar shi ya tashi tsoffafin ya ranshi da police na gidan gomnati suka nufi gurin domin tashin taron da tarwatsa jama’a

Wani irin mari Amjadu yake kifawa Bashir yana tambayar shi dalilin da ya sanya ya aikata wannan mummunan aiki Bashir sai da ya suma sau uku domin Amjadu zagewa yayi ya dinga labta masa wata murtykekiyar bulala yana fad’i “Bashir baka da amfani a duniya nan tunda dakai za’a had’a baki ayi wa Allah da manzon sa izgilanci kai cire ta tawa ni me sauki ne tunda bawa ne makaskanci irin ka, da iyakar ni kuka tsaya abun bazai dame ni ba, dani da Ku kunje fa mu cikin masifa da tashin hankali da fushin Ubangji ko ka fad’a min wad’anda suka sanya ko baka fad’a ba min ba ni na sam su kuma karshen su yazo da izinin Allah.”!!

Manager ya fad’i a gurin yana wani irin nishi! Mai wahala kafin kace kwabo ya kara suma take Amjad din ya kwara masa ruwa sanyi karara ya mike a zabure!Wanda yayi dai-dai da sakin harbi a gurin ji kake tas!tas! tas! Kafin kace kwabo gurin ya hargitse!! Hayakin tiyagas ya d’ume gurin sai atishawa ake ana Neman d’auki!! Wannan ya basu damar shiga ciki Amjad na ganin su sun shigo a guje ya sanya su Rambo su dauke manager su b’oye ko ina ne domin yasan shi suke nema….. Bindiga suka saito dai-dai kanshi zasu harbeshi yayi saurin sunkuyawa!! Take suka wuce da gudu!!! Rambo dake sab’e da manager a kafad’a ya fara kokarin haura Katanga!! Lauje ya hango shi da sauri ya fuzge bundigar hannun wani d’an sanda ya saita k’afar Rambo ya bashi harbi take Rambo ya fad’o kasa shi da Maneger dake a sume!! Ihu Doh-doh ya kurma!! Yayo kan Rambo yana duba k’afar shi dake zubar da jini!! Ganin Lauje da wani d’an sanda sun yanko da gudu gurin ya sanya Doh-doh daukar Manager a kafad’a cikin jarumta ya fara kokarin haure Katanga… Lauje! Ya duba hannunshi, Ashe lokacin da yayi harbin jefar da bundugar yayi a gurin!! Da gudu ya juya da baya domin d’aukota! Amjadu ya soka masa hancin ta a k’irjinsa fuskar sa a mutukar murtuke!!! Lauje ya d’aga hannunsa sama! Cikin saranda! Amjad ya hade hannunwan sa biyu cikin jarumta ya murde su ya rike tamau! Suka fara tafiya har suka karasa inda Rambo yake kwance cikin jini yana nishi lokacin kuma Doh-doh ya samu nasarar dirga da Meneger k’asa ya nemi mab’oya Ashe bai tsira ba ‘yan jarida da sauran police d’in gidan gomnati sunga shi take suka rufa masa baya….. Wani d’an jarida shi ya fara isa gurin ya ji lokacin da menegar yake cewa”Duk wannan abun da ya faru daga gomnati ne me girma governor shine da wasu ‘yan kasuwa suka tilas tani tare da bani makudan kudi miyan goma sha biyar kan in b’ata sana’ar Amjadu domin ya durkushe a cewar su bashi da amfani kuma Asali shi din ba Dan Asalin najeria bane babu yanda za’ayi yazo ya dinga cin moriyar kasa saboda haka Dole a rusa company yaje kasarsu su ya gina musu shine ni kuma nazo muka hada baki da wasu daga cikin ma’aikatan company muka futar da kaya masu dauke da sunayen Allah da manzon sa.” Manager yana kuka yake maganar ya rike Doh-doh sosai yace.” Ka nemar min ga fara gurin ubangidan ka nasan mutuwa zanyi ko na rayu nasan governor bazai barni inji dad’i ba. Aikuwa wannan d’an jaridar ya gama nad’e maganganun manager a na’urarshi.. Manger ya fara wani irin tari kafin me ya amsa kiran ubangiji bayan yayi Kalmar shahada Allah kenan manager ya mutu da kalmar sha hada a bakin sa.

Ganin Police din gidan gomnati sun kusa iso wa gurin yasa wannan d’an jaridar Neman mab’oya wani siririn guri ya shiga ya b’oye yana gyara na’urar shi inda ya saita camera shi dai-dai gurin yana daukar duk abunda yake faruwa a gurin…. Menegr suke kokarin kwace wa daga hannun Doh shi kuma ya rike gawar tamau yak’i sakinta domin yana hango zuwan Amjadu gurin Wanda yake rike da Lauje!! Sai da suka iso gurin sannan doh-doh ya sakar musu meneger Amjad ya buga masa tsawa akan me!! Yace.” Sir Allah yayi masa rasuwa yanzu.””

“Hahahahaha”!!! Yaran gidan gomnati suka kwashe da dariya take suka saki gawar maneger ta fad’i a gurin…. Kumurci ya nuna Amjadu cikin tsageran ci yace.” Abunda kake son ji daga bakinsa baza kaji ba!! Ko bai mutu ba mu zamu kashe shi!!! Mu kaishi lahira! Hahahahaha!! Kai da kake D’an karoro d’an gudun hijira kazo garin mutane kana mana mulkin mallaka wallahi idan kayi wasa sai mu maida ka garinku na gado tsirara.!!! Amjadu yaji zuciyar sa na wata irin tafasa ga takaicin manager ya mutu bai fad’i komai ba ga takaicin maganganun da kumurci yake yab’a masa, cikin zafin zuciya ya saki Lauje! Da ya galabaita ya fad’i gurin kan Kumurci yayi cikin jarumta ya Kai masa naushi!!! Kafin kace kwabo fad’a ya hautsine tsakanin Amjad da Kumurci, fad’a da gabb’ai! Ba da makami ko bundiga ba…………

Tofaaa
Ran maza ya b’aci

7/12/2019
[12/7, 8:59 PM] .: BABBAN YARO

77

Sosai ake bata kashi tsakanin Amjad da Kumurci sai tada k’asa suke yi a gurin, Kumurci dake mak’ale da wata matsiyaciyar wuk’a mai mugun kaifi a jikinsa ya fuzgo ta da sauri ya d’aba ta kirjin Amjadu!!! Cikin zafin nama ya k’wace kansa daga rik’on da Amjad din yayi masa suka bar gurin a guje!! Doh-doh yayi kan ubanginsa da da gudu ya d’ago shi cikin tsanani. Tashin hankali jini tuni ya b’ata masu jiki, cikin tsananin jarumta Amjad ya mike tsaye hannunsa dafe da k’irjina da yake jin wani irin zafi da zugi a gurin ya rintse idonsa ya bud’e su kan Doh-doh yace.” Rambo yans cikin halin taimako. “!! Cikin tashin hankali doh-doh ya kamshi yana fad’in” Sir kaima a halin yanzu taimako kake nema, mubar gurin nan domin ns lura mutanan ran ka suke buk’ata!!!

Amjad ya mike tsaye a daddafe jini duk ya bata masa hannu Doh-doh us rike shi suna kokarin futa cikin jama’a, da sauri d’an jaridar nan ya futo daga mab’oyar sa ya k’araso gurin tare da kama gefan kafadar Amjad din yana masa sannu kana yace.” Yallab’ai insha Allah Kaine kake da nasara kuma insha Allah karshen mutananan yazo domin duk abunda ya faru a gurin nan ina dashi cikin na’ura ta insha Allah sai mun tona musu asiri.”!

Amjad yaji dadin wannan Abu take yaji k’warin a jikinsa duk da cewa yana jin jiki domin ba k’aramin suka wuk’ar tayi masa ba daurewa kawai yake yi suka futa cikin dandazon jama’ar gari dake ta hatsaniya da ta kura sai rigima suke da yaran gidan gomnati, futowar Amjad din ce ta dauke musu hankali, su kuma suka samu nasarar guduwa bayan sun faffasa galashin motar Amjad yayi raga-raga!!…. Sam wannan bai dame shi ba, burinshi kawai mai girma shugaban kasa ya San abunda yake faruwa a jahar kano domin daukar mataki akan governor bisa wannan danyan aikin da suka yi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button