FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 21-30

After all kowani dan adam a duniya yana da nashi iyakar da bazai taɓa yarda a ketare masa ba,kowa a duniyan nan nada wannan red line din da baison koda wasa ayi crossing masa.kusan dolene yay mata uzuri ya kuma fahimce ta don iya zaman sa da bilti yasan ita din mai hakuri ce da kawaici snn bazata taɓa aikata wani abunda zai cutar da wani ba.

Yasan ta rikesu da amana kuma da gaskiya.
Dan haka ya qudira aransa cewa Daga zarar yau ta yanke hukuncin rabuwa dasu to babu shakka yasan tana da wani boyayyar dalilan ta,wanda insha Allah shidai bazai yi judging dinta akai ba duk dama yasan abun zai iya cutar da zucyrshi fiye da na kowa.

Yaune akasa ranar saurarar shari’ar su ta karshe tsakaninta da malam musa,kuma ayaune akesaka ran za’a yanke masa hukunci daga nan a rufe case din kowa ya gama gabansa.

Gabansa ne ya cigaba da faduwa suna zaune tare da wasime data rakube a gefenshi tay shiru,duk wanda ya wulga ta gabansu saita bishi da ido tana kallon sa itadai haryanzu bata fahimci kome ya kawosu nan ba barema ta gane halin da taheer yake cikin na tashin hankli.

Suna zaune awajen har aka kammala shari’ar dake gaban nasu snn aka aiko jami’i daga ciki yay summoning dinsu cikin fadar shariar.

Hannun wasimé yaja suka shiga kotun suna samun wajen zama saiga bilti da kawunta da lawyansu da taheer ya dauka musu duk sun hallaro ciki.

Taheer ne a madadin iyayensa,binciken kotu ya tabbatar ma hukuma cewa iyayen nasa basa kusa snn basuda masaniya akan abunda ya afku.

Taheer din ne kawai daya zauna acan gaba sai satar kallon biltin yake wasime tana hango bilti ta tashi tsaye a daburce da mugun gudu tare da daka tsalle zata wuce wajenta acikin sauri taheer ya kamota ya zaunar da ita na dole cikin zare mata ido ahankli yace mata ta zauna in angama zasuje wajen ta tare dashi

tunda wasime ta zauna ta rasa sukuni acikin zuciyarta,gaba daya takasa samun nitsuwa banda waige waige babu abunda takeyi sai kallon bilti take daga can nesa tanajin kamar tay tsalle taganta atare da ita..

hakan yasaka bilti ta dinga sauke rauntacun hawaye masu sanyi tana jefo mata murmushi tun daga can tsumayin kewar junansu da tulin damuwa duk ya mamaye yanayin fuskokin su alokacin dukansu ji suke kamar shekaru dari sukayi basuga juna ba.

Wani shiru kotun ya dauka,jim kadan aka soma zantar da sharia

bilti tana zaune ne agefen kawunta ata dayan bangaren inda lawyar su yake,dai dai lokaci nayi jami’an tsaro suka shigo da malam musa domin a gurfanar da shi agaban kotu..

nan da nan aka soma zantar da sharia tsakanin su inda wasimé taji komi da komi da kunnuwanta

Kanta a sunkuye tanajin komi sai ta fashe da kuka mai sanyi kuma marar sauti,taheer najinta amma babu yadda zaiyi ya lallasheta tay shiru,shikansa ahalin yanzu bazai iya juyawa ya kalleta ba sabida baison Wani abunda zai kara raunata masa zuciyarsa bare ya sakashi zubda hawayen sa agaban mutane.

Confesion din da malam musa yay agaban kotu yasaka shi jin duniyarsa gabaki daya na rushewa.
Dan nadama yasashi fadin duk wani abunda ke boye aransa gameda bilti.

Haka komi ya wakana agaban idonsu cikin nasara, malam musa is now guilty beyond any perpetrated evidence.

Asirin Malam musa kaf suka tonu agaban idon mutane,snn kotu tay masa hukunci daidai da shi,za’a dauresa na yan wasu lokuta agidan kaso da zimman akoya masa hankli da nitsuwa..

Kotu ta wanke bilti snn ta saka ahalin musa sun bata hakurin cin zarafi da laifin dayay na yunkurin bata mata rayuwa

Duk wani adalcin da ya dace ayi mata anmata snn anbata daman ta zaba ko zata iya komawa bakin aikinta intana da bukatar hakan,ko a’a, kawunta ne ya tashi ya bada amsa wa kotu yace a’a basu amince data koma ba,dan haka bilti bata da bukar komawa ko ina,anan itama aka tambayeta kanta a sunkuye ta amsa alkali tace masa eh ta hakura da aikin bazata koma ba.

Wani irin L’umshe ido Taher yay na tsawon lokaci yana jimami jinkanshi yake a sukurkuce kamar ana sassare masa gwiwowin sa da bilti ta furta hakan agaban kotu.
Bai bude lumsashun idanunsa harsaida aka saka hakan acikin takarda.

cikin sauke nannauyar ajiyar zuciya ya bude raunatatun idanunshi cikin sanyin jiki sunyi wani jaa sun fita a hayyacinsu game da sunkuyar da kansa can kasa daga nan bai kara dago kansa ba kuma har saida aka kammala sharia.

Hannun wasime ya kama
Ya rike yana dadajin wani irin tukikin karayar zuciya,kallonta yay yaga kanta a sunkuye, kamar itama tay kukan harta gaji duk jikinta yay sanyi duk tarasa mesa bilti bata amsa agaban kotu cewa zata dawo musu ba.

Daga ita har taheer din babu kanta Dukkansu sun raunana barinma ita datake karamar yarinya mai karamin kwakwalwa.
Sam sam bata fahimce komi awajen ba damuwarta aynzu shine kawai bilti ta dawo gare su…

Shikuwa taheer babu ta inda zaka gane cewa yana tafasuwa ta ciki face kwayar idanunshi da sukayi sanyi suka koma sauya launi suka dawo jaa

Bayan an sallame su acikin kotu Jikinshi a muce yaja hannun matarsa sukayo waje suna tafiyarsu atare har suka tsaya ata jikin motarsu jikinsu a matukar sanyaye.

Ganin bilti acan nesa tare da kawunta yasaka wasimé ta fashe da asalin kuka mai sauti hannunta rufe akan fuskanta tanajan shessheka mai zafi.

Baice mata komi ba dan ayanzu shima ji yake kamar yay kukan koda zaiji sauki acikin ranshi,tun da ya taso fa baida wanda tafiye masa bilti,bilti ce kullum agefen sa. Rabuwa da ita gatsau yazo masa da wani ciwo da bakin ciki mai radadi dan ji yake tamkar rabuwa zaiyi da mahaifyar sa ta asali.

Bilti tana tsaye acan gefe tare da kawun ta zazzabi ne mai zafi ya hanata sakat, sake hannunshi wasime tay ta kwaso da mugun gudu tazo ta rungumeta tare da sakin wani matsanancin kuka mai balain tsuma zuciya

Jikinta rawa yakeyi tana famar shigewa jikin bilti
Idonta a rufe tana cewa

“Wayyo Allah na bilti na ina zaki tafi ki barni…

Bilti bata iya ko motsawa ba bare ta samu gwarin gwiwar cema wasime komi,rungumarta kawai tayi sosai ajikinta ta kankameta tanajin zafin kukan nata har cikin
Kokon zuciyarta..

Saiyau ta dada fahimtar yadda take matukar kaunarsu duka acikin zucyarta dan bazata iya fasalta tsananin zafin rabuwa dasu datakeji aranta ayanzu ba,saidai kuma ba’a son ranta ta yanke wannan hukuncin ba qaddara ne kawai ya rabasu.

Laifin da malam musa yay mata tasan bawani abu bane da zai iya rabata da rayuwar taheer
Da wasimé,amma bakin cikin dayake cikine yay mata yawa kuma kalubalen datake fuskanta ayanzu yafi karfin tace zatayi musu wani sadaukarwa mai girma.

Kwana biyu datake gaban kawu sam bata da sukuni ko kwanciyar hankli,duk wani farin cikinta ta rasa kullum da tunanin su take kwana take tashi Tanajin matikar tausayin su,tunanin yadda suke rayuwarsu sukadai a gidan yakan hanata cin abinci da bacci.

Acikin kwanakin nan damuwarsu ne kawai ya ramar da ita,tausayin su yasa ta dingaji aranta zata yafe wa malam musa dan kawai ta dawo dominsu.

Saidai abunda yan uwanta da kawunan ta suke zargin ta akai ne kwana biyun nan yayi girman da bazata iya fasalta ciwon hakan da komi ba.

Tasha mamaki duk yadda kawu ya nuna yasan gaskiyarta,da labarin abunda ya afku amma hakan bashi yasaka yabi bayanta wann karon ba,daman kuma dashi kadai kawai ta dogara arayuwarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button