FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 21-30

Lafewa tayi ajikinshi jikin ta babu wani sauran karfi duk ta sake mishi nauyi tayi lagwas sai nishi take sama sama kamar wanda ciwonta na asthma ke shirin ballowa.

Ahankli cikin nitsuwa Ya sauke ta akan kujeran sa ya zare lab Coat din dake jikinshi tukuna ya dauki tissure pads yana dan share mata baki da inda aman ya bi ajikin ta
She look very weak sabida tayi aman sosai da sosai sai ya kishingidar da ita kadan ya shiga examining din ta,yaga in banda stomach cramps din babu wani abunda ke damun ta Sai panic stress din daya keson ya mamayeta.

shiga batrum yayi ya dauko towel tana ji yana cire mata kayan jikin ta amma bata iya yin komai ba sabida yadda kanta yake juyawa da jiri jiri ga tsinannen tashin zuciya dake cin ta kamar mai sabon shigar ciki.

Tin tuni ta soma fahimtar cewa hala abincin dataci ne ya jawo mata tsurewa
Tutturo bakinta takeyi a shagwabe dan dama har cikin ranta ba wani jin dadin abincin kasuwa takeyi ba,tafison in zataci abinci tacishi freshly prepared kuma da asalin duminshi.

tallafo ta yy suka shige batrum din atare, ruwa ya kunna mata abakin sink ta wanke bakin ta ya jawo ta sukayo daki snn ya bata maganin ciwon ciki kwalli daya ta sha
… Allah Allah take kar yace zaiyi mata wanka ganin duk zufa ya mamayeta wani langwame masa wuya tay tana nokewa kamar maijin bacci bacci,baima lura da abunda takeyi ba ahankli ya kwantar da ita akan gadon sa ya bude drawersa ya fidda ruwan flagyl ya dora mata a hannu wanda Ko minti 5 batayi ba ta bingere da bacci..

Ya dan jima yana tsaye akanta at d same time yana lura da iya adadin lokacin daya rage mishi ya koma makaranta.

Arayuwarsa bai taba shiga yanayi irin wannan ba,musammn alokaci daya fi bukatar nitsuwa da sallamawa ga karatunsa sai kuma gashi an samu akasin hakanne yaketa faruwa dashi.

Yau da ace ba wani muhimmiyar exams bane agabansa daya hakura kawai ya zauna da ita a gida ko dan ya fahimce matsalarta da damuwowinta.

Duk tsoronsa kar wasime ta shiga wani kunci da damuwa batare da ya sani ba,gani yay kamar duk abunda ya afku ba laifinta bane, kuma ba nashi bane,haka zaalika bana bilti bane data yanke hukuncin ficewa a rayuwarsu a lokcin da sukafi bukatarta a kusa da su,laifin duk na iyayen sa ne da suka share shi,
A tunaninsu biltice zata zame masa komi baida wani damuwa,yasha mamaki da har yanzu baiga kirar kodaya daga cikinsu game da case din bilti ba,yasan dai hala kawunta zai nemesu yay musu bayani kodan akan shariar da za’a gudanar tsakaninta da malam musa,amma yau sai yaga ana neman cika sati guda da faruwar abun amma haryanzu babu wanda ya nemeshi da alaman basu ma ji labarin abunda ke faruwa agidansu ba”

..shidai yariga ya yanke hukunci aranshi to imma jiransa sukeyi ya kirasu dakanshi bazai taɓa kira ba,akan mema zai kira?gabaki daya haushinsu yakeji aransa,.
Nauyi ne dai da suka kyalesa dashi akansa ya riga ya dauka kuma bayajin hakan zai maidashi baya saidai ya dada tarbiyantar da shi domin ya dada fahimtar wasu fadi da tashin rayuwa.

Karfe 11 da rabi saura ya dubi wasime yaga tana kan baccinta peacefully,aranshi baiso ba amma hakan ya sulale yabarta a dakin ya koma makaranta cikin gaggawa.

Gabaki daya hanklinsa baya jikinshi haka yay jarabawarsa ta yau,baida wani katabus sai famar juye juye yake aranshi da tunanin yadda ya barta a gida.

Can bayan sunfito daga hall dayaji kamar bazai iya daurewa ba,for the first time ya ziyarce offishin training in comand officern su ya roki alfarman sa da cewa amasa afuwa yau bazai sami daman tsayawa training har yamma ba sakamakon zai kai sister sa asibiti a dubata ta batajin dadi.

Da shike bai taba daukar wani uzuri awajen aiki ba da wurwuri ogansu ya fahimce shi snn ya amince mishi ya dawo gida.

Yana dawowa gidan dakin datake ya wuce direct,Samu yay har ta farka tana ta kwaza aman hucewar xazzabi.

Karasowa kanta yay ya rusuna gameda tallafota jikinshi nan da nan ya shiga taimaka mata ta dan kikkimtsa kanta,snn yaje har cikin kayanta ya zakwalo mata wani doguwar hijabi purpl colour wanda yakai mata har kasa ya bata ta zura ajikinta snn yajawo hannunta sukayo waje ya
Bude mata mota ta shiga ta zauna atake suka kama hanyar asibiti dan yau kwata kwata baida nitsuwar da zaice zai dubata dakanshi ayanzu.
A asibiti Layi sukabi har aka iso kansu,ya rikota tana binshi a baya ya kaita ciki likita ya dan duddubata.

bayani yay masa akan babu wani matsala mai yawa ajikinta abincin dataci ne kawai yake dan reacting ajikinta wanda yasa harta tsure ta shiga cikin wannan yanayi. Bisaga tambayoyin da likita ya dinga mata a karshe ya basu shawarar data rinka cin abinci mai kyau kuma dumamme. Wasu yan magunguna ya rubuta ya mikawa taheer papern domin suje su siya akan shi za’a na bata tana sha na tsawon kwana biyu.
Godiya yay ma docton ya riko hannunta sukayi waje tana binshi cikin tafiyarta mai sanyi she feels so calm nd safe inya riƙe mata hannu hakan nasawa taji sanyi acikin zuciyarta Tanajin kamar andamu da ita.

wajajen Ƙarfe uku suka bar haraban asibitin,
Kwantar da kanta tayi ajikin seat din motarsa ta lumshe ido batama san inda suka dosa ba jim kadan jinta kawai tayi acikin motar ita kadai,ta bude lumsashun idanunta tana waige waige taga har sunkai ga bakin wani katotuwar chemist yay parking,acan ta hangeshi yaje siyo mata magani..

Ajiyar xciya ta sauke akasalance tana mai dauke idanunta akanshi caraf sukayi ido hudu da kawarta najaha.,kallonsu ta dingayi taganta Tare da mahaifyarta sun jera suna takawa sun wani sha kwalliya da alaman biki ma zasu,duk dama batajin karfin jikinta amma haka ta daure ta bude murfin motar ta sauko kasa.

Daga dan nesa ta tsaya ata jikin motar ta shiga kwalla mata kira tana cewa “Najaha..najaha..
A dan takaice najahar ta juyo suna hade ido da wasime ta kwaso aguje ta zo ta rungumeta suna dariya kamar wanda suka jima basuga junan su ba.

Hannunta najaha ta riko dukkan su suna sake murmushi mai sanyi ma juna da yanayin mamaki akan fuskarta tace “wasime?toh me kikeyi anan wajen…kafin wasime ta budi baki ta amsa saiga maman najahar ta iso wajen,har kasa wasime ta rusuna cikin sanyin murya tace “mama ina yini?..matar tanata kallon ta cikin murmushi tace “lapiya yan mata kece wasimen da aketa bani labari ko?..”tsaye wasime ta mike kanta na kallon kasa cikin jin kunya ahankli,tace eh nice”.
Matar tace masha Allah ban taba ganinki ba kuwa ashe yau da rabon zan ganki Caraf Najaha ta amshe maganan, tace mama kema zaki fada itafa kullum tana kumshe a gidansu batako neman mutane, ba a fa ganinta ma sai a schll kuma fa sudinma makwaftan mune,mama aikinsan gidan professor oyiza ko?toh anan take…cikin gwalo ido da tsananin mamaki maman tace ma wasime”ohh dama ke yar gidan Professor ce ayyyya toh ya akayi bansanki ba?…take kan wasime ya kulle ta rasa me zatace dan harga Allah bata san me suke cewa ba dan haryau itadai bata san asalin sunan maman taheer ba kawai dai a matar qasimu tasanta Sai dan ji datayi kamar kowa Agidan yana ce mata mammy..

hannunta ta dan daga zata sosa gefen kunnen ta cikin tunanin amsar da zata bawa maman kawarta najaha.
Anan ne kuma najaha ta kalli plaster dake makale a vein dinta inda aka saka mata ruwan flagyl dazu,a mamakance ‘tace laaaah subhanallah meya sameki haka wasime?.Girgiza kanta tay cikin sauri tace “babu komi ai banda lpya ne Amma naji sauki..da fuskar tausayi maman tace ayyaaaa sannu kinji?Gyada kanta tay cikin sanyin murya tanamai maÆ™ale wuya da sigar tausayi a hankli tace najaha Dan Allah yaushe zakizo gidan mu?..satar kallon mamanta najaha tayi sann tace Nima bansani ba!ai daukawa nayima kinyi tafiya danajiki shiru,tace no ina nan banje ko ina ba, Nidaya ce fa agidan mu, yaya na baya cika zama saita dan kalli maman najahar ta dada marairaice fuskanta, murya kasa kasa tace”dan Allah mama kibarta tadan zomin kinji,murmushi maman najahar tayi tana kallon bakin wasime data furta maganan kamar wanda zatay kuka tace”..zan barta amma sai kinzo mana sau daya Kema.,wuyanta ta makale a sakalce tace
“Mama ai shine Yace kar naje koina.Kuma baiya dawowa sai can cikin dare,daga ido sama tay sai taganshi can yana tunkaro su cikin sauri da ledar magani a hannun shi,maza tay ta dauke kanta cikin yanayin dada shagwabe murya ta dada langwame wuyanta sosai ma matar tace..”mama Dan Allah toh inyazo kice masa kinaso inzo hala zaijiki sai ya barni..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button