FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 21-30

Kanta ta shafa tace Karki damu ni dama wasa nake miki kinga ai bakida lpya karki damu kanki zamu zo hargidan mu dubaki,.. maman naki tayi tafiyane ko?..bata ko amsa ba sai gashi ya iso wajen,matar tana hade ido dashi ta ganesa tsaf sai murmushi take famar jefo mishi,atakaice ya dubeta babu yabo babu fallasa yace “ina wuni maa,da faffadan murmushi akan fuskartan ta kallesa tace “lpya kalau,taheer ko?
Bai amsa ba ya saki karamin murmushi

Tace “Ashe prof tana da Æ´a mace ayya ai duk bamu sani ba Toh ya jikin kanwar naka naji tace bataji dadin jikin ba.

..kansa ya sosa kadan yace “jiki da sauki..tace toh Allah ya kara sauki insha Allah gobe zamuzo mu dubata tare da najaha,ke bazakiyi gaisuwa bane?..

cikin jin shakkarsa najaha ta rusuna har kasa tace Ina wuni yayan wasimé ?Murmushin dole ya kufce masa ganin duk shirmen su iri dayane da mutumiyar tashi, yace yaya kike?
Acikin sanyin murya ta amsa tana mikewa tsaye tace lpya lau…Maman tace its okay toh mu zamu wuce,wasima Allah ya kara sauki ko?insha Allahu gobe inmunzo miki Kema saikizo mana watarana inkin samu sauki ko?,tana fadin haka ta kalli taheer da dan sakin fuska tace”yaya taheer ai zaka barta ta zo din ko?..fadada murmushin sa kawai yy baice uffan ba …wasimé ta gyada kanta a hankli sukayi sallama har suka bar wajen ita dashi suna tsaye basu motsa ba

Baice mata uffan ba yaje ya bude mata kofar motar ta shiga ta zauna sann ya zago wajen seat dinsa shima ya shiga tare da ajiye ledar magungunan daya siyo a gidan baya suka kama hanyar gida.

Bayan sunci kamar minti biyar haka akan hanya suna tafiya batare da wani yay motsi acikinsu ba adan sace ya jiyo ya kalleta game da jefo mata tambaya a kasaitance kamar ba da ita yake ba yace suwaye wayannan din?..sanyayar idanunta ta dago ta kallesa cikin sauke boyayyar ajiyae zuciya tace “yaa najaha ne da mamanta..girarsa na sama a dage “yace uhum?waye kuma ita.dan shiru tay snn Tace Æ™awata ce a makaranta kuma tare da ita muke bitan karatu a islamiya..shiru yy baice komi ba har saida suka iso daf da kofar gidan su najahar yana ta kallon gidan dake baida wani nisa da nasu gidan baifi gida uku zuwa hudu ba atsakani,batare daya kalleta ba yace i think nan ne gidn nasu ko?
..kallo daya tay ma wajen da mamakin sa aranta tace eh.Ya hade rai atake cikin yanayn tuhuma yace”ke ya akayi kika sani yaushe kika taba zuwa nan din?Rau tay da idanun ta..yaya banfa ce naje ba ai ita ta gayamin,ta amsa masa a shagwabe. hararta yay baice komi ba har sanda Suka shiga gida snn ya kashe motar haryanzu suna ciki suna zaune,a nitse ya juyo yanata kallon sunkuyayar kanta tausayinta ya gama sanyayashi,kullum saiya dingaji a zcyarsa kamar a takure take.

Makure kanta awaje daya tayi shiru can taji kamar ana shirin kawo hannu kan shafaffen tumbinta ACikin sauri ta wara idonta akanshi jikinta yahau rawa rawa,wani murya mai sanyi wanda bai saba mata magana dashi ba yasa cikin kulawa sosai yace..”Are u okay? Kallon cikin idanun shi ta dingayi tare da dora hanunta akan nashi yace…”ko cikin bai dena ciwo bane har yanzu?kasa amsa shi tayi tana mai dada kankame jikinta cikin rawan dari,rangwafowa kadan yy daf da ita ya kara dora hannun shi akan cikin nata yana shafawa cikin hura mata sassanyar iskan bakinshi akan fuskanta “Hey am talking to u!.Ya dada shafa cikin nata, wani yarrr taji shocking nabin sassan jikinta ayayinda gabobin jikinta ke sacewa a hankli”..a kasale ta bude idonta da sukayi sanyi saboda rauni, ta kalleshi kwayar idanun nata sun ciko da ruwan hawaye masu rikitarwa”..saita rasa mema zatace mishi kawai ta fashe mishi da sassanyar kuka mai tada hankli..lumshe idanunsa yay yana sauraran ta ahaka,ji yy gaba daya hanklin nasa ya tashi ya juyo yanata kallon ta acikin shesheka mai zafi da ciwo tace”..yaa dan Allah yaushe bilti zata dawo?..nifa..nagaji ne kuma inajin tsoro kullum sai arinka bari nas nikadai..nide dan Allah ka kaini wajenta…”cikin matsanancin kuka ta karashe maganan cikin kuka har saida yaji dama bai tambayeta komi ba.

Shareta yay cikin dauriya ya saka kai ya fita acikin motar ya nufi hanyar gate yaje ya kulle snn ya dawo ya sameta ta hade kanta da gwiwarta tana ta rera kuka…

Hannunsa yasa da karfi ya raba kanta da cinyar snn ya kamota da karfi ya fincikota kasa ya rungume ta ajikinshi kafin nan sukayi cikin gida.

Har suka kai daki bata dena sauke hawayenta ba,numfashinta take ya soma yin sama sama kamar da wasa ciwon asthmanta ya tashi tafara juye juye tana jajjan numfashinta sama sama a wahalce.
Inhaler ta yaje ya dauko ya saka mata a bakinta ta zuƙa tunkan ta dawo hayyacinta ya wani jawota jikinshi ya rungumeta sosai ahankli ya jefa hannunshi ta bayanta yahau patting dinta acikin nitsuwa.

Haka ya dingayi yana shafata cikin lallami harta yi shiru ta nitsu.
Dada lafewa tayi akan kirjinshi duk jikinta yay sanyi tay lamo tanajin saukar bugun zuciyarshi.
,..lokacin idanunshi gabaki daya suka kada sukayi jaaa yanajin kamar ya sauko da fushin sa kawai ya dauketa yakaita abuja wajen mamanshi hala zatafi samun nitsuwa acan.

Shima badon san ransa yake barinta acikin gidan a wannan yanayi ba,yasan abune mai wuya a kulle ka kai kadai a gida musamman ma a matsayinka na yaro wanda bai mallake hanklin kansa sosai ba.
Shafa gadon bayanta ya dingayi a hankli ayayin da mind dinsa yay nisa a cikin wann tunanin,lamo tay tare da kankame bayan rigarsa tanajin kanta very safe with him around her aranta cewa take inama da ace zai na zama da ita haka tana kallonsa kullum hala da baxata taba jin damuwa sosai ba..

Dan dago fuskarta yay suna kallon juna cikin sauke nanauyar ajiyar zuciya yace “am sorry kinji?”..i knw u wont get me now..amma kiy hakuri kinayin duk abunda nace miki jarabawa nakeyi shiyasa bana samun lokaci..did u get me?batace komi ba Kanta kawai ta kawar gefe da yanayin damuwa yabita cikin tallafo fuskarta yaga tana fidda sabbin hawaye masu rauni…zuciyarsa a karye yake kallonta yace..”
“Meyene matsalar?

Muryanta kamar wanda zata fashe mishi da kuka mai tsanani tace”nide bana son zama anan ne nikadai basai nabika muje wajen jarabawar ba?

Double smirks ne ya kufce masa “yace Kina hauka ne?

Bakin ta turo masa gaba yanayin ta na shagwaba tace”Toh ka bari inje gidansu najaha mana gobe,yaya kaji dan Allah?Na maka alkwari bazanje ko ina ba bayan nan kuma kana dawowa gida nima sai na dawo i promise i wont dissapoint you…

Take Ya riko hannunta yanajin wani iri wani iri acikin ransa..cike da tausayinta aranshi yace”toh naji, iya abunda kike so kenan?..cikin turo baki gaba gaba ta gyada masa kai ahankli tace eh, yace toh its ok saiki dena cikamin kunne kuma ko?…”ya miÆ™e tsaye yana furxan iska ta bakinshi harga Allah bawai yana son hakan bane anma kodan sabida kwancyar hanklin ta yanajin zai iya daurewa, da gefen idonshi ya dan kalleta muryansa ciki ciki yace”Naji ma matar tana cewa gobe zata zo miki ko?tace eh..ya dauke kansa akanta..”toh saiki tsaya suzo din ke inkin samu sauki kyaje gidan kidubasu…but only for once..

Tay saurin makalkale wuyrta tana kallonshi a wani sigar daya nakasa mai gangan ciki irin bata amince da for once din dayace din nan ba,hararta yay
Ya harde fuskan sa” .toh meye hakan kuma?
Dada narke mishi tayi
Cikin salo”Yaya Toh zaka amince tana zuwamin din?ai maman ta tace innaje sau daya ma zata barta tana zuwamin koyaushe shiyasa nake so inje..”Wani lumshe idanun sa yy jin yadda ta riko yatsun hannun sa da tender palms dinta tana sauÆ™e mishi wata muryan magiya kasalalliya,cikin sanyin murya tace…”yaya inje din, kaji dan Allah?ince mata tana zuwa min din?…”hmm” kawai ya kalleta yace cikin sauke wata gajiyayyr ajiyar xciya,ahankli ya kwace hannun sa anata ya juya yay waje yabarta anan batare dayace mata uffan ba, Kallon kofar ta dingayi harya bace ma ganinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button