FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 21-30

,… cikin jin dadi maman tace “masha Allah..ta saka hannu ta amshe kudin ta soke tana cewa toh kawo wannan zan saka miki a asusunki..
kinga in Allah yay shine mijin naki ai gwara mufara tara kudin sayan kayan gararki tun yanzu.
Kisaka komi aranki Aina fadamiki bawani jinkirin da zakiyi tun Kina danyarki sharaf zan kaiki gidan mijinki.

Najaha tay dan murmushi cikin sanyi murya tace mama
Amma meyasa naga kamar baison magana dani,naga duk abunda kikace nayi masa nayi masa,amma sai naga bai wani kulani ba Sai wani shashshan qamshi yake
…jan hannunta tay cikin murmushi tace yaro ai yaro ne su najaha kenan, toh shakuriminki Karki damu da wannan ai haka dama kyawawan maza suke da son jan aji da rigima,yanzu kibar wann tunanin muje ciki zan koya miki yadda zaki nayi masa inkinje gidan gobe,tun ran gine tun ran zane,bazanyi wasa da wata dama ba dan haka kema kidage kar kiyi wasa da damarki najaha.

Gyada kai najaha tayi aa ladabce suka shige ciki atare.Ajiyeta tay ta shiga zayyana mata salo salo na makirci da kisisina harda wanda ya wuce kwakwalnta da adadin shekarun ta.

Washe gari da sassafe najaha taci wanka ta shirya tsaf cikin wata pink satin material mai tsantsi an mata riga da sket dake ita tana da garinjiki duk ta kawo girma,kayan bakaramin matseta yay ba,ko daga kafarta ma da kyar takeyi duk cinyoyinta basu da katabus tun ba aje koina ba suka hau mata ciwo.

Fitowa tay fuskan nan
Yaji kwalliya ubansu cikin rangwada ta same maman ta atsakae gida tana kan shara wani juyo tace”mama na fito nayi kyau kuwa?.Aje tsintsiyar tay ta kalleta tace masha Allah woww my doter Kinyi kyau”.najaha tay murmushin jin dadi..

Tace sai kuma a dage kinji?..tace mama karki damu bakida matsala
Wallah harnaji nafara asalin son shi,gashi fari kyakkwa…maman batace mata uffan ba ta cigaba da gyaggara mata powder dake fuskanta.

A fannin su wasime kuwa tun data farka karatun qur’anin ta takeyi.
ayayin da shikuma taheer yake gwagwar mayan shirya kansa cikin wata kananan kaya domin ya samu ya wuce wajen jarabawa.

Karfe bakwai da rabi ya fita batare da ta sani ba sai can ya dawo hannun sa dauƙe da ledar soyayyen chips da grilled fish dayay musu oder ata wayan shi kwana biyun nan bakaramin kashe kudi yakeyi wajen siyan abinci ba,ko jiyan cikin dare da yunwa ta ishe shi kusan ma ince shiya shanye sauran ruwan shayin da wasime ta zuba musu a flask wanda yakisha da safe Still baiyi tsammanin ta iya yin tea har haka ba.

Dakinta ya nufa ya sameta a kwance gaishe sa tayi yana satar kallon yanayinta haryau dai hanklinsa ba akwance yake akan zaman datakeyi a gidan ita kadai ba..abun na damunshi acikin ransa saidai haryau bai san mezaiy akai ba.

Bayan ta rusuna ta gaishe sa sai ya miƙa nata ledar abincin daga nan bai wani dade a dakin ba ya barta danta ci..

Kitchen ya nufa ya hado makansa coffe ya sha snn yaci kifin duka ya tattaba chips din dan kadan ya bar sauran awajen snn ya haura sama domin kammala shiryawa.

Ko minti biyu baiy da barin wajen ba sai gata ta sauƙo,tattara wajen dayaci nashi abinci tay
Snn ta shiga kitchen din tayi musu charmonille tea mai kauri wanda yaji madara. A dan tray tasaka zata kai mai har dakin sa,nan kunnenta ya jiyo mata sauti awaje kamar ana buga gate acikin zumudi ta aje tea din akan center table tayo hanyar waje cikin sauri tana Allah Allah taje tacikaro da fuskar najaha.

Tana kuwa buÉ—e gate din sai gata ta shigo tana wani washe baki cikin tafiyarta datakeyi da kyar duk kayan ya matse cinyoyinta ya hanata sakat.

Rungumar juna sukayi
Wasime ta ƙare mata kallo cikin yanayin tsokana ta tuntsire da dariya tace kai najaha wannan wankan fa kamar wani zakije gidan biki?jifa yadda ya matse ki,abu sai kace dole?

Haushin dariyar najaha taji amma sai ta matse..cike da rigima tay rolling idanunta tace kedai bari kawai kawata wannan wankar shi ake kira wankan swagger,
toh ina mace in babu kwalliya, Kema ai kinsan kwalliya dabia ta ce ta tun usuli,ai bakiga kome bama sai randa akace nakai 18yrs..

Wasime ta kara fashewa da wata muguwar dariya…”uhum su najaha manyan mata, anyways sannunki da zuwa bari na rufe gate sai muje ciki.

Tsayawa najaha tay
“To wai ina shi yayan naki daya kyaleki da rufe gate kardai harya tafi schl?zuciyan ta na bugu ta fadi hakan dan bata son ace yau ta kure adaka tazo domin shi snn kuma ace tay asarar kwalliyarta abanza.

Wasime dake kkrin jan gate batama san me najaha take yi ba tace
“Ke Yaya na yana cikin dakinshi ina ga hala yana shiryawa ne baima san na fito ba dan Allah muy sauri mukoma ciki kinsan yahani zuwa nan.

Wani sanyi ne ya ziyarce zuciyar najaha tace”toh muje ciki ko?gyada kai tay suka shige ciki atare
A falon su suka tsaya
Cikin hanzari wasim3 tace zauna anan najaha barin kai masa tea dinsa ina zuwa.

Batace uffan ba har saida wasime takai hannu zata dauke tea din wuf tay ta amshe a hannunta cikin makalkale wuya “Kai wasime muje mana wajenshin tare kinga saina gaishe sa yasan nazo ko?

Gyada kanta tay tace toh muje din ai ba matsala

Atare suka dunguma zuwa dakinshi najaha ta rike cup din shayi zuciyarta cike da sake saken yadda zatay.

Ahankli wasime ta saka hannu ta shiga kwakwasa kofar lokacin yana tsaye a gaban mirror ya kammala shirin sa tsaf cikin kanann kaya light brown pants na fenty da wani white t shirt yana famar taje suman kanshi jin ana kwankwasa masa kofa

yasha mamaki jin haka dan wasimé bata saba zuwa inda yake a wannan lokacin ba,juyawa yay ya kalle kofar atakaice snn yace
“Come in…wasime tana turo kofar najaha tay saurin tureta gefe ita ta soma cuso kanta ciki rike da kofi a hannu.

Da mamaki ya juyo yana kallonsu shi harya manta ma datace yau zatazo ma wasime.

Fuskansa babu yabo babu fallasa yace musu
“Lapiya?…

wasime zatay magana caraf najaha ta amshe maganan a bakinta cikin salon wata kisssa harda dan rusunawarta Æ™asa tace “barka da safiya yaya na..katashi lpya?

A dake ya kalleta ya kalle kayan dake jikinta yadda ya wani matseta duk tay wani iri bakyan gani, atake ya soma feeling disgusted bai amsa gaisuwar nata ba ya daga ido ya kalli matarsa cikin hade rai da salon cin fuska a dake yace “hey wacece wann kuma daga ina kika samota?

Turo baki gaba wasime tay tana dan makalkale masa wuya cikin shagwabe tace yaya najaha ce fa baka ganeta ba ne?

Wani mtsiyacin kallo ya watsa mata muryan sa adan shake yace “nop.

Wani Galala Wasime tay tana kallon sa da fuskar mamaki sai tarasa meyake nufi amma badai yace mata harya mance da fuskan najaha ba

A sudade najahar ta mike tsaye tay tsamo tsamo tana kallon su kirjinta na bugawa da karfin ganin yanayin yadda taga yana behaving da salon rashin mutunci a fukskr sa,duk sai jikinta ya dau sanyi…

Wasime ta matso gareshi daf tace
“yaya,kamanta itace fa jiya ka kaini gidan su wanda nace maka zata zo min yau muzauna kafin ka dawo?…idonta yake kalla ransa a harde yace “Shine zata zomin gida haka da matsattsan kaya?wannan wani irin shigar banza ce..ask her to go back nd change idan ba haka ba ta koma gidansu yanzun nan bana cike da iskanci.

A dan tsorace wasime ta juya kan najaha ganin kamar ran mijin nata ya baci,suna haÉ—e ido taga harta fara zubda hawayen tsoro,a cikin yanayin fushi da sanyin jiki ta aje kofin tay wucewatta waje tana kuka

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button