FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 21-30

Kece ai bakiji,ai saida nace miki kina rage wasan nan amma kika min kunnen uwar shegu,
yo hala haushin wasan naki yaji sabida wasan yay yawa wasime bakijin magana shiyasa bazaki dena ganin abun bacin raiba..da kinajina da duk hakan bata faru dake ba..maganin marar ji kenan yaudai kinga ishara ko!.?

Kuka ta dingayi tana turo bakinta gaba gaba har bilti tagama surutunta tayi waje batace mata uffan ba…
Akasa ta tumu ta dinga rero kukanta a hankli

Bilti tana fita tay hanyar dakinsa,da sallama a bakinta ta shigo ciki,Samunshi tayi azaune a bakin gadonsa yana latsa computersa hanklin sa gaba daya nakan abunda yakeyi.

waje bilti ta samu ta zauna after like 2min ya tura computer nasa gefe cikin nitsuwa ya juyo ya kalleta cikin bata dukkan hanklinsa nan suka soma tattaunawa akan rayuwar wasime.

Dama can shi Shawaranta kawai yake nema akan qudirinsa na sakata a makaranta.

Saidai bayason yasata a makarantar da yay nesa da gida snn yana son adinga saka mata ido asan duk wani abunda takeyi da wayanda take muamala dasu,dan haryau shidai bai cire ran saheeb zai sake neman hanyar shigowa rayuwansu ba.

Bakaramin dadin maganan nan bilti taji ba.
Dik dama taso da boarding schll kawai aka tura wasime inda zatayi saurin lanƙwasuwa ta kuma san ciwon kanta,but bisaga lamarin su da saheeb,saita dan fahimce cewa taheer bazai taba amincewa da aikata hakan ba sabida yasan akwai abunda zai iya biyowa baya in bata gaban idonsu.

Dama kuma akwai wani sabuwar private school da aka bude a kusa da gidansu mai suna al’iman international schl,ranging from primary one to ss3 babu nursery schl,makrantar yana nan a tsallaken titin anguwar su, so baida wani nisa da gidansun sosai.

Makarantar tay recomending masa don taji labarin ance schl din yana da kyau ana kuma kkrin basu ingantaccen ilimin boko dana islama
Uniform dinsu dark green nd white nd its modest. Daga kan yan primary 1 zuwa jsss 3 suna saka pinafor da white hijabs ne,Frm ss1 downward kuma suna saka normal riga da wando da hijab sai few christians da suke attending schl din suna saka beret a matsayin hijab..

duk wani bayani tayi masa har saida ya nuna ya gamsu yace mata toh gobe in ya fita zaije ya bincika schl din dakanshi inyamasa kawai zai sakata anan.

Yau Da murna sosai bilti tayi bacci,wasime kuwa ji take kamr an rabata da wani bangaren rayuwan ta da aka kona mata kayan wasanta haka kawai inta tunaso zaita zabura ta fashe da matsanacin kuka

Bayan kwana biyu taheer baice ma bilti komi ba,
Sai da akaci kusan sati sann ranar ya shigo da wani babban leda dauke da tarkacen unifoms da takaddu harda su jaka da takalminta mai kyau, da school lunch box, cover shoes dinta mai tsada ya siya mata.

Haka ya damka komi a hannun bilti tare da yin bayani akan yadda komi ya wakana,snn ya bata copyn file din ta yace ta adana shi da kyau, dayan file din kuma ya wuce dakinsa dashi.

Bude file din bilti tayi fusknta dauke da murmushi,a nitse ta karanta taga a primary four ya sakata ,ajinsu shine primary 4A..
Snn Ya biya mata full term fees harda na islamiya session dan haka tun safe karfe bakwai da rabi inta fita baxata dawo ba sai can wajen karfe biyar da rabi na yamma.

Saturdays and sunday kuma zallan islamiyane starting from 9-ending by 3pm.

Babu bata ‘lokaci bi’lti tahau shirye shiryen yadda abubuwan zasu kasance,Allah yasota da akwai enough time din dazatayi mobilizing din mind wasime kafin monday yay ta soma attending classes dinta..

Tin abin bai wani dara Wasime ba hartazo ta soma zumudin abun sosai acikin ranta,ganin an sissiya mata komi gasu nan sabbi kal kal ga sabbuwar jaka da takalmi,pencils mathset colours text books babu abunda bai siya ba.
Kusan duka salaryinshi na wata akan ta kawai ya karar.

Ana washe gari monday zata soma zuwa schl bilti ta sakata agaba akan taje ta gode mishi

Koda sukaje suka same shi…murmushi
Kawai ya musu baice komi.

Washe gari da asuba bilti ta tashi ta dafa ma wasime haddadiyar jollof spagheti mai yawa ta zuba mata a sabuwar school flask dinta pink colour da tahir ya siyo mata mai hade da water flask mai daukar warm nd cold water…tea mai kauri ta zuba mata aciki
Tabi ta saka mata shot bread acikin jakanta ta rufe mata shi.

Karfe 6 da minti arba’in wasime ta fito a shirye tsaf cikin sabuwar uniform dinta dayasha guga goye da jakar makrntanta abaya,tun daga can nesa bilti take ta satar kallonta dan Bakaramin kyau uniform din yay mata ba komi daidai jikinta akayishi kamar wanda suka gwada size dinta.

A nitse suka zauna sukayi breakfast tana dada ja mata kunne akan ta maida hankli tayi karatu tana mata nasiha masu shiga jiki,Suna kammala breakfast din kuwa saiga taher yana saukowa kasa tareda waya a kunnen sa yana magana da wani

Satar kallon sa wasimé tadingayi ganin ya saka complete uniform din soldiers,kayan tay masa masifar kyau farar fatansa saiya fito dau yay wani haske,soft looking lips dinsa suka bada wani irin pinkish red in colour mai daukar hankli,gabanta taji yana faduwa cikin sauri ta sauke kanta kasa kirjinta na bugawa da dan Æ™arfi,sautin muryanshi datake ji har cikin zuciyarta yana ratsa ta yana dada jefa zuciyarta cikin wani sabuwar yanayi wanda karanar kwakwalta bazai iya fassara shi ba,bata kara iya kai abincin bakinta ba,ta rike spoon din sai jujjuyashi takeyi acikin abincinta.Wani Shiru sukayi har ya gama wayarsa ya juyo da gefen idonshi ya kalle su ya jefa ma wasime wani takaitaccen kallo snn ya dauke kansa a fakaice..bayabo ba fallasa yy gyaran murya..”yace ma bilti ni zan fita, Tolu ya tabbata yakaita on time kuma ya dawo da ita on time..

Bilti tace karka damu na jaddada masa hakan

..baice komi ba kallon wasimen yay da gefen idon shi shibaiyi gaba ba baiyi baya ba,bilti tana ganin haka ta mike tabasu waje tay kamar kitchen zata”..

Kamar dama jiran haka yake bilti tana bada baya ya tako ya iso daidai kanta ya tsaya,gabanta ne ya rinka faduwa,ji tayi an riko kunnenta a hankli,narai narai tayi da idanuwanta ta dago a kasalance ta kallesa da wata fitinanniyar fuskar shagwaba wanda atake yaji ta shige cikin gangan jikinshi,zuciyarsa na wani narkewa kominshi yanayin sanyi,lumshe idanuwansa yay batare da ya shirya ma yin hakan ba,yana budewa yaga ta tsura masa kyawawan idanunta tana kallon kyakyawan fuskan shi a zauce tamkar wacce take shirin hadiyeshi..shima kallon kyakkwan fuskanta ya dingayi yanajin wani irin
Feelings mai karfi da shigewa ruhi tare da ratsawa cikin kwakwalwa da gangan jiki.

Da kyar yay control kanshi snn ya”kafa mata wani federal warning akan ta nitsu tayi karatu sosai,snn yace tasani cewa duk abunda taje ta koya a aji saiya yazo ya tambayeta a gida, inbata gaya masa daidai ba saiya yanka ta…

Sosai ta tsorata da yadda ya ce zai yanka tan duk dama yau din tanajin sauyin yanayi akanshi tanaji aranta kamar yafara dan burgeta,cike da fargaba ta amshi maganganun nasa tare da masa alkwarin zatayi iya bakin kokarinta wajen ganin tayi karatu..harya saketa ya kama hanyar fita bata dena kallon bayansa ba.

Karamin ajiyar zciya ta sauƙe tanajin kamar ta koshi da abincin nata.
Tattarawa tayi tabi bayan bilti da su takai kitchen ta ajiyesu.

7:00 cass tay sallama da bilti suke fice agidan tare da tolu,acikin wata 506 ash colour da taheer ya bashi akan kullum dashi zaina kaita schl, agidan baya ta zauna ta make tayi kak kamar wata big madam,dauke kanta tayi tanata kallon bakin titi ta window har suka isa schl din batace ma tolu cikanka ba,yana ajeta ta sauka ta wuce cikin makaranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button