FITAR RANA 21-30

Dakinshi ya nifa ya sauya suturarsa izuwa kananan kaya masu kyau,after like 30minutes sai gashi ya dawo daki ya samu harta kwanta game da bada kofar baya..bataji shigowarsa ba kawai ta shako motsin mutum ata bayanta adan tsorace ta farga ta miÆ™e zaune akan gadon suka hade ido…
Yace jeki kidauko maganinki kisha..
Babu musu ta sauko ta dauko ledar maganin ta bude agabansa tukun ya amsa ya bubbude mata yana mika mata daddaya tana sha..tashin zuciya da amai ta dingaji amma haka ta matseshi ya koma ciki dan batason yace zai mata allura yanzu..”
yana fita a dakin ta tabe bakinta ta fada kan gado, ko yunÆ™urin rufe Æ™ofarta batayi ba tayi kwanciyar ta dan ko ta rufe in ya tashi zuwa buÉ—ewa yakeyi,…
Da yamma cahn bayan sallan isha’i,kanta ne ya tsananta ciwo kasala da ciwon kai ya hanata sakat..
Bata san daga ina ya samo abinci ba amma yau Indomie da soyayyen kwai mai shegen dadi kawai ya nemo mata taci tayi zaman ta a daki tana bitan littafin usulul thalatha part 2 da tauhidinta mai yatsu.
Tana Cikin haka taji an turo kofar, sanye yake da rigar armless green colour sai wandonsa fara kat kafafunsa da takalmi da alaman yanzun nan ya dawo daga masallaci..
a nitse ta juyo ta amsa sallamar sa, Coffe cup tagani black colour a hannun sa Babu yabo ba fallasa Yace me kike shawa’ar ci ?Ko jira na kike na xo na kawo miki anan din?..Batare da ta juya ba ta girgiza mai kai ta dada bashi keya..
“Yace Ke!!! Ya daka mata tsawa da yasa ta mike tuni tayi kneeling kanc gadon ta kalle sa da idon yarinta “yace kina hauka ne ina miki magana kina girgiza min kai kina juyamin baya?…adan tsorace tace Yaa na amsa fa baka ji ni bane” .girarsa na sama a dage ya watsa mata wani matsiyacin harara wasa da yatsun hannun ta ta dingayi a hankli ta firta cikin sanyin murya tace”nifa bana sha’awar cin komi kaina ne yakemin ciwo..ya dube ta kadan yace “kinsha magani? Tace a’a yanzu zan sha.Yace ok be fast abt it,inkina da wani matsala ki kirani ina falo..yana fadin hakan baijira amsarta ba yay waje..,addu’ar baccinta kawai tayi ta tofe jikinta da dakin tabi lafyar gado taja duvet ta rufe jikinta ta kwanta abinta bata fi minti goma a kwance ba bacci mai nauyi ya dauketa….
Na kudine,contact 08060712446
7/25/22, 19:19 – Kawata: FR27
Mr/mrs chef:bonding
Washe gari Æ™arfe hudu da rabi daidai wasime ta farka da addu’a a bakinta tanajin ganta garau duk wani motsin ciwo ajikinta ya dauke kamar ma batayi ba,tana zaune kan gadon tay tsam tana kallon agogo har karfe biyar yayi,sai da taji ana yunkurin shiga sallan asubah snn ta miÆ™e ta shige toilet, wanke toilet din ta farayi tukunna tayi wanka ta doro da alwala.
Adaidai kan lokaci tayi sallahn ta tazauna awajen bata tashi ba har saida karfe shida yay. zama tay tana dan azhkr dinta da yan addu’oi can sann ta tashi ta bar wajen ta koma gaban mirror tare da jan kujerar zama ta zauna tana duban kanta ajikin mirrorn…
manta ta na palmers coco butter ta dauka ta shiga shafawa ajikinta cikin nitsuwa,bayan nan ta dauki small prick brush tayi brushing kitson dake kanta tay oiling dinshi da coconut oil ta tsaftace shi ya dau qamshi mai dadi,wasime bawani dogon gashi ta mallaka ba amma baza’a kasata acikin wanda basuda gashin rufin asiri ba,in anmata kitson gaba jelarsa har kumatunta yake saukowa ya mata kyau,sannan yadda jikinta yake pure nd virgin hakama gashin kanta yake ba’a taba wanke shi da relaxer ko wani artificial chemical ba aduk da gashin baida wani tsayi yana da cika da baÆ™i hakan yasaka yake da kyan gani sosai a ido,gani tayi kitson dake kantan ya soma tsofewa, dan tagumi tay cikin rasa inda zataje ayi mata sabon kitso gashi biltin ta haryau dai shiru bata waiwaye su ba.
Lamarin bilti na bala’in damunta abune wanda inta tunashi atake takejin radadin ciwo da bakinciki dan kuwa ita kadai tasan metake ji acikin ranta na rashin bilti a kusa da ita.
Katse tunanin tay sannan ta isa wardrob din kayanta, tsayawa tunani tayi na kayan da zata saka yau wanda bazai takurata ba,wani gown din atampa fitted ta ciro ta saka ajikinta ya mata kyau snn ta fesa turaren ta, ta dau cleaner ta tsaftace dakin tsaf ta gyara kan gadon ta kunna chacoal buns ta saka turaren wuta.
lokaci ɗaya ɗakin ya dau wani kayataccen ƙamshi,sakkowa tayi kasa ta shiga kitchen direct,wutar kitchen din ta kunna takare mai kallo taga kitchen din na nan yanda yake, shiga tayi ta gama dube dubenta don taga ko meye mai sauki da zata iya dafawa,fridge ta bude, ɗan preseved tomatoe paste data gani tasaka hannu ta ciro ta dawo ta saka mangyada a tukunya ta dora akan gas ta shiga hada miyar sauce Mai hade da kifin sardines, albasa da tarugu da tafarnuwa duka ta yayyanka a choping board snn ta watsasu akan miyar tare da spices masu qamshin dadi bayan ta gauraya shi saita rufe.
Bai wani dauke lokaci ba
Ya soyu tas ta sauke shi kasa,cikin hanzari ta dora ruwan dafa farar taliya,duk tanayi ne tana tuno da yadda taga bilti tana yi bata ko kuskure.
Taheer na dawowa daga masallaci tun daga can yaga wutan kitchen a kunne sai dai bai bi ta kan kitchen din ba ya wuce sama dan a tunanin shi ko ta sauko ne cikin dare ta dauki wani abu acikin wajen, dakinshi kawai ya nufa bai kulaba.
7:30 dot wasime harta gama duk abubuwan da zatayi ta zuba komai acikin cooler ta tafasa ruwan zafi da citta da ganyen mint ta tace snn ta zubashi a flask kamar yadda taga bilti takeyi ta gyara wajen da tayi girkin yay tsaf.
Wanka taheer ya fada da tunaninta aransa harya kammala wankan tunanin ta kawai yakeyi aranshi koyau ta tashi lpya?yau baida wani exams din sassafe Sai wajen karfe goma zai shiga hall duk dama yaukam yasan hala inya fita agidan bazai samu damar dawowa akan lokaci ba,shirya kansa yy tsaf cikin wata black slim fit suite ya saka white shirt ta ciki qamshin turaren jikin shi na original tomford ya gama mamaye ko ina da dadin sa,tsayawa yay a agaban mirror yana famar brushing suman kanshi,Allah Allah yake ya gama ya sauko domin ya dubi lpyar wasime snn yaji mezataci don yaje ya siyo mata irinshi, by then ma yasan hala kawartan sunzo daga nan saiya tafi ya barsu tare.
Karfe takwas dai dai lokcin wasime harta gama share falo ta gyara zaman trow pillows da komi, ta kimtsa wajen yy kyau ta saka turaren wuta hadi da room freshner gidan ya bade da kamshi me dadi .
Abubuwan data dafa ta dauko takawo su kan dinning duk dama tana shakkar yuwar taher ya zauna yaci kwalemarta
Aranta kam tana mugun son yadanci.
Ruwan tea ta hada adan kofin tea cup jin cikinta ya fara murdawa,gashi tana son ta samu ta sha maganin safe,tana gama shan tea din ta haura sama ta dauki magungunan ta sha snn tadan kwanta domin ta huta kadan.
8:00ckl taheer ya fito sanye da suturarshi data masa mugun kyau,tun daga kan stairs yake jin kamshin turare da abinci mai daÉ—i a gidan.
sauƙowa kan stairs din yayi da mamaki ayanayin sa,ganin yadda gidan ke tsaftace ma ya dada rudashi,ahankli yake bin koina da kallo har ya karaso kasa kan dining table ya tsaya da mamaki yana kallon dan cooler da flask din dake kan dinning ɗin ganin anyi arranging komi harda su plates,cup da cutleries.
Matsowa yay bude coolern aroma din miyar ne ya soma bugar hancin shi, mai dawa yayi ya rufe aranshi yanajin wasime ta birgeshi.
yasan dai ko ta iya ma bazai wuce training É—in bilti bane,dan murmushi yayi snn ya haura sama dakinta ya tura kofar ya shiga batare da yay wano kakkarfan sallama ba