FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 21-30

Waje ya nema a kofar gidan ya danyi parking Agogonsa ya kalla yaga har kar’fe tara da minti arbain yay..cikin gaggawa ya juyo ya kalleta yace…”me zan taho miki dashi?kanta na kasa ta hade rai a hankli cikin shan qamshi tace “babu”Tsaki yaja Bai kulata ba, murfin Motar nashi ya bude yanabinta da wani irin harara nan take ya hada ransa yace “Get out!A dan fusace ta sauka ta kama tafiya ta nufi bakin gate din gidan ko juyawa ta dan kalleshi bata karayi ba…

Galala yy da baki yanabin bayanta da kallo aranshi yana cewa “whats wrong with this girl?ya kada kansa cikin kyabe baki
Abun natan ma dariya yake son ya bashi”
..shidai yasan bazaici abincin yarinta ba…abu kamar na dole Harwai dan baici ba ana fushi dashi…?..jan motarsa yay ya bar wajen ta tsaya acn gefe har saida ya tafi snn ta sauke ajiyar zuciya tazo ta dauki coolerta tay cikin gidan bakinta dauke da sassanyar sallama.

A tsakar gidan ta tarda mahaifyar najaha lkcin ta fito kenan zata kwashe sharar falonsu data kammala..suna hade ido
Matar ta sakar mata murmushi mai sanyi tuni wasime ta tsuguna har kasa cikin sanyin murya tace “mama antashi lpya?..Da fara’a a fuskar matar tace a’a wasima ce yau agidan namu Lpya kalau…toh yaya jikin naki
Ohni Allah aida kin bari munzo har gidan mun dubaki,toh meyasa taherr zai barki ki fito?..kanta na kasa tace”bakomi mama aina warke.Yaya na ne ma dakanshi ya kawoni shiyatafi makarnta ne.

Matar tace toh lale marhaba zo karaso ciki

Mikewa tayi cikin nitsuwa suka shige ciki tare da matar alokacin najaha tana can kitchen tana yan aikace aikacen ta nayau da kullum

” To bari na kira miki najahar ko? .gyada kanta tay tanamai bin matar da kallo har ta fice jim kadan sai gasu sun dawo tare da yarta najaha.

As usual aguje ta karaso
Tana murnan ganin kawarta”Ke harkin warke kenan shine bazaki bari muzo miki ba?…wasime tay murmushi..”ai naji sauki ne sosai..najaha tace toh ai shikenan,nan ta kamo hannun wasimen tana janta.”zo muje can ina aiki ne..

Kitchen dinsu suka nufa direct, wasime ta dinga kallon kitchen din ganin tarin ayyuka dake jibge
Aciki,ga wanke wanke ga shara da mopping, acan gefe kuma an dauko doya da alaman fereshi za’ayi,”najaha tana kaiwa kan wanke wanken ta juyo tace “ki zauna mana bari na dan gama wanke wanken nan saina dafa miki indomie.. cikin sauri
Ta girgiza kai tace “uhm uhm nifa nakoshi…

“kai wasime haka zakice min ?to wallh nima innaje gidanku bazanci kome ba.

Tasan halin najaha sarai zata iya aikata hakan datace Cikin marairace murya Tace haba najaha ba haka bane wallh yanzun nan fa naci taliya a gida shiyasa na koshi,ai gashi can ma harna kawo miki,
“..juyowa najaha tay da murmushi tace
Dagaske ?hmm toh yau zanci girkin malama wasimé..fatan dai kin iya girkin?..wasime tace try me ..dariya suka hauyi najaha tace uhm uhm a Fadi gaskiya dai Ko yayan ki ne ya dafa miki?…”kyabe bakinta tay
Tace a’a wallh nina dafa abuna dakaina kedai kici kigayamin inyayi dadi..shi ko cima baiyi ba…tace toh meyasa? numfashi wasime taja
“Ai to shi gani yake kamar ban iya ba…dariya najaha ta fashe dashi..
Wasime ta takune fuska
“Au dariya ma zakimin

Tace kai Wasime katuwa dake ashe baki iyama abinci ba?Atake ranta ya dagule tace “Ke wallhy na iya..shine kawai… ai baima ci bafa…najaha ta tabe baki a yangace”Ai zanzo gidan naku gobe zaki gani innayi nawa dole ya ci …wasime Tace Allah ko?toh ai hikenan…inyaci nakin ai saiki koyamin irinsa ina masa.

Ahaka suka dinga hira wasime tana dan tayata da wasu abubuwan kamar su mopping da shara…can bayan sun kammala tana lura taga yadda najaha ta balain kwarewa wajen kunna gas duk tana kulawa da yadda take gudanar da abubuwanta cikin kwarewa,..nan da nan ta hada faten doya mai qamshi suna kammalawa suka fito falo suka zauna akasa kan carpet suna ci Sunakan hirar su ta dazu dan kadan wasime taci doyar tace takoshi.

Mahaifyar najaha dake lura dasu bayan sun kimtsa waje sun same nitsuwa anan ne ita kuma ta dinga kawo wasu tambayoyi ma wasimé tana tambayar ta abubuwa game da rayuwar iyayen taheer wani bin wasime saidai tay shiru dan batasan amsar da zata bayarba.

Ta lura sungama dago cewa bata wani iyayin komi ba,najaha kuwa babu abunda bata iya ba..She was raised by a single mother su biyunsu suke rayuwarsu anan babu wani namiji mai sunan uba atattare da su,mum din nata tanada wani local restaurant da suke budewa da daddare karfe 7 acan cikin gari babu kalar abincin da basu siyarwa Shiyasa hannun najahar ya fada akan abinci sosai ahalin yanzu batajin shakkar yin kowani irin girki..

Wasime kuwa ta rasa meyasa maman najaha take bala’in son jin labarin gidansu da kyar ma suka fahmce cewa daga ita sai shine a gidan yanzu.

Anan ma saida tasha tambayoyi har kaman
Abun zai bata mata rai amma haka ta daure ta shanye komi batare da ta nuna mata hakan ayanayinta ba.

Bayan sallahn magrib sun idar da sallah kenan saiga karar horn ana dokawa ata kofar gidan tuni jikin wasime ya soma bata cewa bazai wuce taheer bane ua dawo dama can ta matso da ta koma gida
Sam sam bata gane yanayin mahaifyar najahan nan ba.

Altho duk sun dauka uwa daya uba daya take da taheer basuyi la’akari da bambancin launin fata ba sai kawai ta barshi acewa ai baban taherr din ma ba farin fata bane,hala wasime ubanta kawai tabi shikuma taheer ya debo farar fatan uwarsa.

MiÆ™ewa wasime tay ta zari mayafinta zata leka kofar gida, caraf mahaifyar najaha ta yanke salla tare da tsareta tana cewa “a’ah wasime karki fita bari ni naje na duba..

Tana ficewa kuwa najahar ma ta saci jiki tabi bayan uwarta sukabar wasime ita kadai a tsaye,can dataji su shiru ta hau tattara tarkacen ta datazo dashi..coolernta ne da dan tsarabar kunun aya da zobo da maman najahar ta tsakura mata acikin kayan siyarwan su..

Daga waje kuwa uwa da Æ´a suna hango motar taheer maman tahau murmushi Tace ma yar “au ashe shidin ne fa..to maza kije ki sameshi..ki gaishe sa sosai, saiki ce masa kanwar tasa tana zuwa..

Da murna ayanayin najaha ta doshi wajen motar taheer tana tuna abubuwan da mamanta ta gaggaya mata akansa da iyayensa jiya bayan sun dawo daga biki …”

Abunka da yaro najaha tuni ta soma saka ranta akanshi Gashi nan fari kyakkawa kuma likitan sojoji…Ai mamanta ma tace itace daidai sa’ar auren sa,tace zasu dace da juna, kuma zasu rayu cikin kudi insuka hada zuria dasu,har wani sauri najaha takey tana jin tsananin farinciki aranta tace baridai taje tay mai murmushi da fari da idon da mamanta ta koya mata ko hala zata dan burgeshi….

Pls dont read witout paying for it, 300#
Via 0152983148
GTB 08060712446
7/25/22, 19:19 – Kawata: FR28
Desperate 13:Bring it on

Tun daga can nesa taheer yake kallon zuwan najaha yy tsam ya dauke idonsa akanta yay kamar bai ganta ba, aranshi baijin daya sauƙe glass din motar sa.A Cikin tafiyar yanga da karairaya najaha ta tako cikin takunta mai daukar hankli ta iso gaban motar taheer din ta tsaya.

“he is infact very exhausted yau ya debo gajiya sosai ajikinshi bana wasa ba,tsakivya dingaja acikin ransa cos Fuskar Wasimén sa kawai yy expecting din gani ayanzu domin su tafi gida ba fuskan kowa ba.

ajikin kofar gida maman najahar ce ta laÉ“e cikin sanÉ—a ta bada hanklinta gabaki daya wajen lekosu,tun daga can take kallon komi dake faruwa wani murmushi takeyi ganin najahan ta tana murza zarenta yadda ya kamata sai wano zuba rigima takeyi tana rangwadaa kamar ba yarinya Æ™arama ba,tsaye tayi awajen motar tana dan leka cikin motar cikin salo,a take ta matse siriyar muryan ta tace…”asalam alaikum
“Yaya taheer..yayana?cikin karairaya murya da yanga take tattaba glass din motar tana knocking ta waje tana fadin hakan,taheer yana kallonta da gefen idon shi ya basar da ita baice uffan ba,she even tot dat baijinta ne tahau waving dinsa da hannu tana famar washe masa baki ta waje koda ma zai hankaro ya ganta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button