FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 21-30

Dan Tsaki yaja dan baison takuri, Saida ya dau dan lokaci snn ya sauke glass din motar just slighly gameda zuba mata mayun idanunshi masu darsa fargaba fuskan sa babu yabo babu fallasa yay kamar bai ganeta ba…”yace ke kuma fa?tana hade ido dashi kirjinta yahau bugawa atake tahau murmushi mai sanyi tana kikkifta mai idanu,cikin sanyin murya mai lulluÉ“e da karairaya tace “yaya baka gane ni ba?ko kallanta baiyi ba “tace “najaha ce kawar wasime”..cikin salon makirci da aka gama koya mata shafi shafi ta furta hakan tana wani kwarkwasa,ganin baice mata uffan ba jikinta yay dan sanyi ta shiga rusuna kai cikin maÆ™e sautin muryanta daya fito a makirce tana dan fari da ido tace”toh yaya na ina yini Barkan ka da dawowa?ya hanya…?
Ina fatan dai yanzu ka gane ni ko

kare mata kallo yy daga sama har zuwa kasa ganin ta zololuwa ga tsayi tar kamar ba yar 13yrs ba,gata dai fara ce amma bata da hanci saidan kyan fuska da Allah ya bata kadan.

dauke kansa yay akanta a shashance snn yy shiru shidai baice mata uffan ba..”Sai Can da ya gaji yadan juyo a gajiye ya dubeta yace”ke jeki ce mata ta fito yanzu ina jiranta..nagode!

Murmushin yake tay abaxata ganin yadda yay maganan kamar wani dutsi da alaman baima san metakeyi domin shi ba,Ranta bai wani so tarban da yay matan ba, ta dai shanye abun tahau jefo mishi fari da ido,a yangace sosai tayi juyi tana cewa”toh yaya na bara na kirata,yanzu kuwa..

juyawa tay tana tafiya cikin takunta daidai zaka rantse wata babban yarinya ce mai shekaru mai yawa,dan duk wani salon jan hanklin É—a namiji ta iyashi,shidei baice komi ba yanata satar kallonta tana barin wajen ya girgiza kansa tareda jin mamakin yadda yaga tana behaving sai kace wata mini call girl Aransa bai dai dau hakan abakin komi ba yadai bari ne akan duk yarinta ne yake damunta.

Mahaifiyarta datake laÉ“e a jikin kofa har wani Allah Allah take najahar ta karaso wajen ta domin taji labari,addua ta dingayi aranta Allah yasa taheer ya zamo na yarta najaha,bata hankara ba har abunda take ta fada a cikin zuciyartan ya fito fili,adan razane ta juya jin motsin mutum ata bayanta tana waigowa kuwa taga wasimé a tsaye,tarasa yaushe ne har tafito,kenan duk tajita kuma taganta tana famar yin laÉ“e kunya duk sai yabi ya kamata tahau kame kame nan da nan ta sakin mata murmushin yake cikin basarwa tace “au har kin fito ne wasima? A hankli Wasime ta gyada kanta tace eh “amma yanzun kika fito ko?..batace kala ba ta gyada mata kai,kanta ta dan shafa tana murmushin dole “tace Toh shikenan ma aiga can yayankin can ma yazo dauÆ™arki,’inkinje sai kice masa inji maman najaha tana gaishe shi na musamman,ya kuma mikamin gaisuwata wajen professor ace ina mata fatan alheri…
mungode da ziyara ko wasima?..murmushi wasime tay saiga isowar najaha wajen.
.
Satar kallon juna sukayi da mamanta snn suka washe bakin su atare suna mai duban wasime
..cike da barin ciki najaha tahau murmushin yake game da jawo hannun wasimen gefenta tace kawata zo muje in rakaki wajensa gashi can yazo”.

Wasime tadanja da baya tace “A’a najaha wallh nayafe miki kibari kawai ai dare yayi.

Jawo hannunta tayi na dan dole, ai baki isa ba niyau saina kaiki har gaban motar yayan ki,”wasime dake Allah Allah ta tafi saita amsa kawai tace toh shikenan muje yanzu kinsan yaya na baison jira.Ta juyo tace toh mama sai anjima na gode sosai.

Matar ta daga mata hannu tana cewa ‘karki manta da sako na fa?gyada kai wasime tayi..

Tafiya suka farayi hanklin wasime duka ya koma akan mijjnta sai sauri takeyi ji take kamar baxataje inda yake ba,a sace Najaha Ta dube ta caraf ta riko mata hannu ta rikota sosai tace”gobe dayaushe kike so nazo miki,kafin wasime ta kammala lissafin lkcin dayafi dacewa harta katseta cikin zumudi “tace karki damu
Mama ma tace zan iya kai miki har yamma har saima yayanki ya dawo sai in tafi…

da sauri wasimé ta kalleta cikin jin dadi aranta tace “wayyo Allah kawata aikuwa dana ji mugun dadi Toh kizo gobe da safe mana kin san da safe yake fita yabarni.

Jawo wasime baya tayi cikin rada mata magana a kunne tace “kai wasime wai ni saurin me kikeyi haka,kina wani yafiya fuuu kamar zaki tashi sama slow down mana ai bazai gudu ba ko.

Najaha bakisan yaya bane baiyson abata masa lokacinsa yanzu sai yay fushi yace bazan ma kara zuwa nan ba.

Dariya najaha tayi cikin salon makirci tana dada jajjan ta baya dan ta samu daman yin tafiyar yanganta koda zai gani daga can yace tafyar ta birgeshi…

kedai wasimé kincika tsoro wallh, Ai babu wani abu Kefa mace ce,mace kuma tamkar sarauniya ce a duk inda take, bai kamata kina tafiya kina wulga kafa cikin sauri Kamar wata tunkiya ba.

Wasime ta juya ta kalleta cikin harara “ke nice tinkiyarki? Dariya najaha tay tace ke nifa wasa nake miki, kyabe baki wasime tay…”hmm to walh zaki gamu dani dan bashi kika dauka..dan dariya sukayi atare wasime bata fasa saurinta ba har suka karaso tawajen motar..

bude motar yy a nitse snn ya fito ya tsaya a tsaye idonsa nakan matarsa.

ahankli ta sunkuyar da kanta kasa cikin shakar iskan farin cikin ganinshi daya mamaye zcyarta a boye,cike da sanyin murya ta kalli najaha tace najaha to ki koma gida sai naganki goben.

Alokcin Duk hanklin najaha nakansa bata maji abunda wasimen take ce mata ba sai kallon fuskarshi takey tana washe baki ayayin da kwayr idanunshi da hanklinsa gaba daya ya yattaru ya koma akan matar sa.

babu yabo babu fallasa yake dubanta sautin muryanshi cikin kulawa yace”are u done?

Batare da ta dago kai ba tace mishi “uhum…

Hannunta ya jawo a hankli,snn yace “Comon lets go”..

..tuni najaha tay sumar tsaye ganin yadda yakebi da wasime cikin kulawa kamar wata Æ´ar kwai,a nitse yakaita har wajen seat dinta ya bude mata motar ta shiga ta zauna snn ya zago yaga har lokcin najaha bata dawo daga duniyar data lula ciki ba

Aljihun sa ya saka hannu ya zari 500₦ ya mika mata,bata amsa ba ta daga ido tana kallon shi,sai yanzu taga dan karamin murmushi akan fuskansa yace toh karbi wann kije gida, nagode ko!..

Wani irin kallon sa takeyi kamar zata lashe shi zuciyarta kamar zaiyi tsalle ya fita daga kirjinta dan zaucewa.

bakinta na rawa rawa tahau sosa gefen kunnen ta a dan daburce tana wani matse muryanta cikin kissa da manakisa tace…”A’a wallhi yaya na da kabarshi kawai”
nagode zan shiga gida sai goben kawai innazo!
..baice uffan ba ya kama hannun ta ya damka mata kudin,yana kammala hakan atake ya bude motarsa ya shiga ciki ya zauna bai kara duban inda takeba yaja motar suka barta tsaye a wajen kamar wata dusa.

Najaha ji take Kamar tayi tsalle,zuciyanta yana figarta kamr wacce zata tashi sama dan murna da farinciki,tsayawa tayi awajen tana bin bayan motarsu da kallo harsaida suka bace ma ganinta,kudin ta kalla snn ta daka wani tsalle cikin murna ta juya a hanzarce ta nufi cikin gida.

“Mama mama” tun daga baki kofa take kiran mahaifiyar ta wacce already tayi tsayin daka a tsakar gidan tana jiranta.

Caraf sai gata ta fado cikin gidan da murna suna hade ido da maman nata ta taho cikin sauri tana washe baki “cikin hanzari maman ta riko hannun ta tace’ toh yaya?yar albarka ya naganki da fara’a ne toh gayamin meya faru..kudin ta soma nuna mata fuskanta dauÆ™e da annushuwa tace”mama kingani wallhi shi ya bani wannan kudin harda cemin yay ya gode.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button