FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 21-30

Shiyasa wanibin suke saurin É“atawa da aminiyarta wasime sabida dabi’arta na shareta musamman intay mata maganan da bai gamsheta ba.

Gani take kamar wasime tana ja mata ajine sabida gidansu suna da danshi ba kamar su ba..ita kuwa ko mahaifi bata dashi gidan nasu ma ta hayace mamanta ne kawai daman take dan fita tay gwagwarmayan daukar duk wani dawainiyar rayuwarsu.

cikin sauke ajiyan zuciya wasime tace
“Ke yaya na yace inhar zaki dena irin wancan shigar zai bari kina zuwamin daga wata sati.

Juyowa najaha tay ta kalleta da mixed reactions Game da kankance idanu akanta “wani sati kuma meyasa sai wani sati.?

Wasime tace nima ban sani ba nima haka yace min…amma dai yace wai dan zamuje wani waje ne tare dashi.

Wani abu taji ya gulleta tay saurin dauke Kanta ta juya mata baya tana yatsuna fuska”ciki ciki ta amsa tana cewa “har ina zakuje haka?..

Rau da ido Wasime tay
Nace miki ban sani bako? Tsaye ta mike fuskarta a dore..toh ya isa nikam muje inada aiki a kitchen.

Wasime batace komi ba ta bi bayanta suka fita
Anan kitchen din suka zauna tana tayata yan aikace aikace har tagama haddace yadda akeyin zobo da kunun aya da fanke.

Bayan nan najaha ta dora musu indomie,tana lura taga wasime ta zari dari biyar acikin kudin da taheer ya bata ta mika mata akan taje ta siya musu juice yan kanana yan dari da hamsin hamsin a shagon kofar gida.

Najaha Bata nuna komi akan fuskarta ba amma sosai ta kullace abubuwa masu yawa acikin ranta musamman ma ganin kudi mai yawa a hannun wasime abun ya dagula mata saitin kwakwalan ta duk sai taji wani irin kishinta ya kamata,ko ba’a faÉ—a mata ba tasan taheer ne yake bata kudi

…wannan uban kudi haka?har wani imagining take acikin zuciyarta tana cewa inama da ace wa ita ake bayarwa take samon kudi mai yawa haka ai da tuni rayuwarta ya sauya.

Yau kwata kwata wasime bata gane kanta ba har saida maman ta ta dawo su biyunsu suka lume cikin daki suka barta a tsakar gidan tana zaune, bata san Dai dadewar me sukayi aciki ba suna fitowa taga sauyin yanayi atattare da najaha ta dawo da fara’arta ba kamar dazu ba.

6pm dot taheer yazo daukan ta,still haka najaha ta biyota wajen sa harda saka doguwar hijabi da zimman bin shawarar da mahaifyarta ta bata akan su sauya salo..

“Koda suka isa wajen shi haka najaha ta dinga susutar da fuska tana masa yanga da sunan wai tana bashi hakuri sai cewa take bazata Æ™ara ba,koya kula yabi ya tsime dan bata ishesa kallo ba,wasime ne dai data sakamai ido tanata jefar shi da fuskan tausayi tasaka shi dan dole yay hakri yay responding dan shirmen najaha bai taÉ“a dara sa ba a shirmammiya yake kallon ta,sai kawai ya daure yace mata babu komi da sakib fuska dan arabu lpya daga nan suka koma gida.

Washegari friday taheer na dawowa daga masallaci da misalin karfe biyu da rabi yana zaune a falo yana danna wayarsa kunnensa sakale da earpiece, tun daga nesa ya hangota tana saukowa daga matakala,kallonta yakey ya kasa dauke idanunsa akanta ko kiftawan kirki baiyi ba harta iso inda yake

Sunkuyar da kanta tayi cikin sarkewar murya tace “yaa Ina yini” kallonta kawai yake ganin yanayinta wani iri yace “Baki da lafiya ne?

Kin cewa komai tayi kuma taki É—agowa da kanta,tsaye ya mike yace “meke damunki Talk to me mana, whats wrong with u?” hawaye take ya cika idonta ta girgiza masa kai alaman babu komi, kallonta ya dingayi, sai kawai ya kama hannunta suka haura sama dakinshi ya kulle dakin,snn ya dawo. gefen gadonsa ya nufa da ita bayan ya soma dago asalin matsalarta yana kallonta yace “Since when?” Cikinta kamar yana jiran ayi mata wannan tambayar ya kara murdata Zaunawa tayi kan kujerar ta kwantar da kanta ajiki tana jajjan numfashi,a hankli yabita ya durkusa gabanta yace “inane ke maki ciwo?”Zamowa kasa tayi ahankli ta hade kanta da gwiwarta san ta fashe masa da kuka bata ce mishi komai ba,.

jin kukan nata ya dinga yi har cikin zuciyarsa ya dago kanta gameda dafa shoulders dinta da dan damuwa ayanayinsa yace “Au kukan ne zai cire miki ciwon naki Talk to me mana,ina ke maki ciwo yanzu?”. .

kalle kalle ta shiga yi can ta mike da sauri sai kuma ta tsaya cak ta damke cikinta,cikin sauri ya rikota jikinta a ragwabe ta rikito, xai yi magana kenan ta toshe bakinta tana kokrin kwace hannunta daga nashi ta toshe bakinta acikin sauri ya saketa ta mike tsaye ya kama hannunta suka nufi toilet

Tunkan su karasa ciki ta zube dirif akan gwiwarta agigice amai ta dinga kwazawa yana kallonta har ta gama tana mayar da numfashinta a hankli

Juyawa yy ya debo mata ruwa ya zuba mata ta wanke bakinta ya gyara wajen datayi aman snn ya fito da ita, kwanciya tayi nan tsakiyar dakin tana juye juye cikin azaban murdawan ciki bata tabayin ciwon period ba saiyau,duk dai taji ta tsorota tanajin tsoro sosai, can sai kuma ta fashe masa da fitinannyar kuka, take ya hade rai yace “Kinga idan baxa ki min magana ba ki tashi kiyi tafiyar ki.

mikewa kawai tayi da kyar xata bar masa dakin ba tare da ta kallesa ba,cikin sauri ya bi bayanta da sauri ya fixgo ta fado jikinsa,rufe fuskarta tayi da faffadan kirjinsa tay lamo tana rero masa wata shagwababbiyar kuka

sun kusa minti biyar a haka yana shiru yana jinta,can ya dago kanta a hankali yana kallonta da sigar tausayi a kwayar idanunshi yace “You are on ur period right?” Sauke idanunta kasa tayi bata ce komai ba sai aukin hawaye.

komar da ita yayi ya xaunar da ita a kan gadonsa ya bude lockern sa,da yake baya rasa magunguna da allurori na Dysmenorrhea.

A kwance ya tarar da ita ta dukunkune kanta awajen,bai kulata ba ya fara hada ruwan alluran yana gamawa ya dawo kusa da ita ya zauna yana kallonta,cikin sanyin murya yace “Kin ci abincin ma kuwa?Cikin muryan kuka tace “eh Na dazu sha ruwan zafi, yace Oh,toh let me inject you za ki samu relief kin ji?.. bai jira cewarta ba ya fara daga rigar dake jikinta,cikin sauru ta rike rigar da sauri don dama ita ba gwanar saka wani abu ta ciki bace banda pants dinta, ko pad batagama iya sakawa ba.

muryarta na rawa rawa tace yaa ban saka komai bafa kuma …kuma…
shiru yayi yana jinta sai kuma ya mike tsaye ya wace bathrum ya dauko wankakken towel dinsa ya fito dashi ya mika mata yace to tashi ki daura wannan muje kiyi wanka saiki saka wani abu.

,,jiki babu kwari ta mike zaune ta karba towel din ya dan dauke kansa ta daga rigarta ta cire kayanta ta daura towel din kafin ya hankara har takai bathrum ta rufe kofa.

Girgiza kanshi yy ya saka kai ya fita da key din motar sa a hannu.

Cikin hanzari yaje ya bude ma kanshi gate snn ya dawo ya kunna 506 din dake pake a tsakar gidan,daga nan ko tsayawa kulle gate din baiyi ba yaja motar izuwa nearest plaza cikin wani groceries shop mai hade da mini super market irin shagunan inyamuran nan.

Sharp sharp ya hada tarkacen pads,tampoons da su panty ‘liners snn ya dawo gida.

Samu yy tayi rub da ciki ta runtse idanunta tana maida numfashi,ahankli ya aje kayan agefen ta,snn ya bi bayanta ya zauna daf da ita yana kallonta

Cike da kulawa ya sauke towel din kasa yayi mata allura yana gamawa ta fashe masa da kuka sosai, dagota yy xuwa jikinsa ta rungumshi da sauri tana cewa wayyo cikina cikin numfashi mai wahalar fita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button