FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 21-30

hanklinsa adan tashe yake rarrashinta yace “It’s okay zai daina maki ciwon yanxu i promise, Kai kawai take gyada masa sai da yaga ta nutsu snn ya saketa

xamowa tay ƙasa ta kwanta ta rufe idonta jin duniyar gaba daya na juya mata, durkusawa yyi yana kallon fuskanta baice mata komi ba, bata wani dau lkci ba bacci ya dauketa awajen ya mike yayi disposing syringe da kwalban alluran ya dawo ya kwasheta ya ajeta gently akan gado.

Sai kusan karfe shidda na yamma ta tashi daga baccin, lokcin yana kan reading table dinsa har lkcn yana danna laptop dinsa, xaune ta mike da sauri tana kallon agogo ganin time yasa ta mike da sauri xata sauka ta cire towel din taga towel din har yyi stain.

Tsayawa tayi tana kallon wajen a dan sace,ganin haka yasa ya mike tsaye yace “meyene?girgixa masa kai tayi alaman babu komi snn ta mike zata nufi toilet da sauri ya bi ta da kallo,tana shiga ta nemi wani towel din ta saka snn ta cire na jikinta xata wanke wajen stain din,daga bayanta taji yace “leave it…..”

Kasa juyowa tayi ta kalleshi ta girgixa kai ahnkli kirjinta na bugawa muryanta na rawa tace “yaa akwai wani abu ne ajiki xan wanke..” juyo da ita yyi ta kallesa gabanta na faduwa sosai.

Kallon juna suka tsayayi for a moment,snn yace “Nace zan wanke miki ko..,sauke idonta kasa tay cikin jin kunyar sa sosai bata ce komai ba dan murmushi yayi yace ajiye anan.

Ajiye masa tayi batare da ta dago kanta ba tayi gudu taa nufi kofar ta fice daga toilet din sannan ta bar dakin nasa gaba daya,tana isa nasu dakin gabanta ya fara faduwa jin alaman footsteps a bakin kofar.

Jiki babu kwari ta nufi bakin kofar ta tsaya a baki baki sanda ta sauke ajiyar zucya kamin ta bude hade ido sukayi ya mika mata ledan tarkacen shoping din snn ya juya abunsa.

Tana amsar ledan ta rufe kofar kirif ta jingina bayanta da jikin kofar tana maida numfashi..

tafi minti uku awajen tana tsaye can snn ta isa bakin gadonta ta zuzzuba kayan cikin ledan akan gado.Idonta ya sauka akan differnt kinds of pad tampoons da panty liners,sai sky blue cotton panties guda uku aciki wanda daga gani kasan sabone yau aka siyeshi,zama yay ya manna mata pad din ajikin daya daga cikin pants din yadda ya kamata. ita kadaine a dakin amma haka ta dingajin kunya tana sadda saddan kai kamar ta nitse cikin
Kasa don kunya haka ta dingaji acikin ranta.

Murdawa cikinta ya karayi saidai baizo mata da pains ba,probably sabida Alluran da ya mata dazu,a hanzarce ta
Saka already fixed panties din gudun karta kara batamai towel dinsa.

Wani doguwar riganta na shan iska wanda yakai mata iya dunduniyar kafarta ta saka snn tabi lpyar gado ta kwanta.

Bayanl kwana biyu cikin nata ya warware tas sabida bakaramin kulawa da ita yakeyi ba

Akwana na ukun washe gari da sassafe ya fita exams dinsa tun wajen karfe 6:30,sai wajajen goma saura wasime tay wanka ta fito sanye da riga da zaninta na cote dvoire brown colour an mata dinkin fitted blouse top,tsintsiyane a hannunta tana kan tsaftace cikin falon gidan da mamaki taji dirin motar sa awaje cikin sauri ta aje tsintsiyar akasa ta dan leka ta jikin window taga eh shidine ya dawo…mamaki ne ya cika ta tay saurin barin wajen ta dauki tsintsiya da mopper duk ta kai bayan kofa a kitchen ta ajesu..

Jim kadan saita fito lokacin daidai ya doka sallama kenan a bakin kofa, tsayawa sukayi suna kallon juna daga can ta rusuna kasa tace “yaa ina kwana?

‘Lpya yace yana karasowa ciki bai tsaya da kasaitacen takunshi ba,sanda yace mata”Me kika ci?ko shima saina fada miki..

Turo bakinta gaba tay
Yace Yanzu ne zan daura.Kallo daya ya mata
“i dont have dat time
Kiy maza ki dauko mayafinki inmun fita kyaci abincin awaje.

Yana fadin hakan ya haura sama yay dakinshi
Ajiyar zuciya ta sauƙe tanabin inda yay da kallo, tunani tayi ashe jiya yace mata yau zasuje wani waje..dakinta ta wuce ta bude wardrob ta dauko wani light brown veil da golden flat shoes ta saka a kafafunta gyalen kuma ta rufashi har kanta snn ta sauko.

Bata dade da tsayawa a tsakiyar falon ba sai gashinan yana saukowa da ido take binshi ganin harya sauya kayan sa yay masifar kyau acikin wata milk colour shadda data nuna kuruciyar sa a fili.

He looks so innocent and calm ya saka dark brwn hula akanshi hannun shi
Rike da wasu files.

Wuceta yazo yay kamar bai ganta ba,taja karamin tsaki acikin zuciyarta tahau binshi abaya.

Bude mata motar yay ta shiga ta zauna suka kama hanya zuwa wani dan karamin kotun gwamnati dake cikin garin.
7/25/22, 19:19 – Kawata: FR30
Desperate 13:world over.

Mintina ashirin yakawo su wata madaidaicyar anguwa marar yelwatan jama’a sabida duk gine ginen ma’aikatan gwamnatin jaha ne ata wajen,titin dayabi tsakiyar layin suka tsaga direct suka mike ciki ciki, gefe da gefen su offishin ma’aikatan ruwa ne sai wani babban headqtar forestry nd agriculture dana bada tallafin rage zafin talauci,É—an gaba kadan suka kara snn ya shari kwanar dayakaisu har gaban wani madaidaicin gini mai tambarin kufofin sharia da alaman kotun sharia ne.

Kallon wajen wasime ta dingayi ayayin da taheer ya danna Horn dinsa tun daga bakin gate, mai gadi ne yataho ya basu hanya tare da masa quick security check snn aka kyalesu suka shige ciki.

Waje ya nema a harabar kotun ta inda aka tanadar wa motoci snn shima yay parking motarsa suka fito shida wasime.

A nitse suke tafiyarsu wasime na gefen shi tana binshi duk inda yaje,a gaban kotun suka samu waje suka zauna inda sauran mutane suma suke jira domin akirawo su ciki,shidai shiru kawai yayi yana kallon komi amma badon hanklin shi na jikinsa ba

Aransa Yasan yau komi zai Æ™are,zai kuma karbawa biltinsa hakkinta dai dai da abunda aka aikata mata na cin zarafi, snn kuma yau za’a hukunta dabban nan waishi malam musa akan abunda yay mata na ketare iyaka.

Wani jami’ i ne ya aiko akan cewa suje office su sameshi,mikewa tsaye yay tare da wasime yafara yin gaba tanabinsa abaya baya

Ganin kalle kallen wasime yafarayin yawa yasaka ya kamo hannun ta izuwa nashi ya soma janta a nitse har suka kaiga inda ake kiransan

Wasu files ya ciccike snn ya submiting wanda ya taho dashi suka dawo wajen zaman su inda ake jira kafin akammala shariar da akeyi a ciki snn akira sharia nagaba.

Addu’a ya dingayi acikin ransa sabida tashin hankli da bugun zciyar data dameshi tacikin ransa damuwa ya hanasa sakat,deep within his heart fata yake yau Allah ya sa bilti ta hakura tace zata dawo garesu

Aransa bakaramin bukatar hakan yakeyi ba, bacin wahalar dayakesha na daukar dawainiyar da bai saba daukar irinsa ba,harga Allah yayi kewar bilti a kusa da shi sosai..

bilti tamkar wata garkuwace wanda baijin akwai wani abunda zai iya cike masa gurbin amfanin datake masa a rayuwarsa dama familyn sa gabaki daya.

Zuwansa kotu dayay da wasimé yasan zai iya amfanan sa tawani waje. aganin sa hala in bilti taganta zata iyajin tausayin su ta sassauta musu tace zata dawo.

Althoug bawai ya tsaurara hakan acikin ransa bane,shide baiya fatar bilti ta dawo dan dole,ko ace badasan ra’ayinta ba,kawai yay hakan ne sabida zafin rashinta dayakeji aransa, da kuma matsuwar dake cikin zciyarsa na son dawowa da ita gida.
Bacin haka baida wani dalili ko mafita,inhar bilti tace bazata taɓa dawowa ba toh yasan dolensa ne yamata uzuri ya kyaleta tayi rayuwarta yadda takeso.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button