FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 21-30

kowa a dangi ya guje sabida maraici da rashin gata ga mutuwar auren ta daya afku a mummunan yanayi.

Koda suka isarga magana wajen sauran yan uwa da dangi kaf dinsu suka haÉ—e mata baki suka juya mata baya kamar yadda suka saba juya mata,kowa yana cewa laifinta ne da hakan ya faru dan kawai batayi aure ba,aganin su babu yadda za’ayi mace kamarta balaggiya mai lapiya ta zauna hakanan batare da tayi tunanin biyan makanta bukata da wani É—a namiji ba.

Yan uwa da dangi kaf sukace basuji ba basu gani ba kuma basu yarda da ita ba,aganinsu dole ne yakasance da akwai gudumawarta akan abunda malam musa ya so aikatwa akanta.

Bakaramin bakinciki da damuwa Bilti ta shiga ciki ba dan akan wann maganar har kalman karuwa dangin tsohon mijinta sun ƙirata dashi.

Wasu suce dama Allah ne kawai ya toni asirinta asalinta marar kamun kaine da son xuciya,hala ma malam musa yasan tana aikata hakan ne shiyasa shima yace bari ya wafci rabonsa

..maganan banza da na muzantawa babu wanda ba a jefe bilti dashi ba.

Saidai duk a ciki babu maganan dayafi ƙonata kamar wnda kawunta ya furta mata, wanda dama da shidin ne kawai ta dogara shine mai dan kallonta da sauran mutunci yake kuma kkrin tsaya mata a duk halin da zata shige ciki.

Amma yau saboda yana under influence din yan uwansa da sukayi kudi suna dan bashi hasafi wanda shkansa yasan kwata kwata bason cigabanta sukeyi ba amma rudin zuciya da son abun duniya ya rufe ma kawu ido shima ya rufe idonsa yayi akan gaskiyarta yay mata mummunan fasssara irin tasu domin kawai ya burgesu.

Ko Datace masa ta hakura kawai da case din zata koma taxauna a bakin aikinta domin ta kula da rayuwar taheer da wasime .Hatsala kawu yay yahauta da mummunan fada haryana kumfar baki

cewa yake”Maimunatu wani ne zaki kawo wa cin mutunci da shashanci?kidena wani noke noke ki fito fili kicemin ke karuwa ce inji da kunne na,karuwancinki kawai kikeyi a gidan alhj qasimu,”bake kika haifi taheer ba da zaki wani kafa dalilinki na banza dashi.,maimunatu kifito fili Kice min kawai zaki koma bakin harkokinki na iskanci da bibiyar mazan banza a waje karki yadda ki raina mini wayo da sunan wani taheer.

Marar mutunci kawai,
Toh wallh kika kuskura kika koma gidan qasimu dani dake har abadan abada,kuma duk zamu tabbatar da cewa kwadayin abun duniya da halayyarki na banza ne sukajawo miki wann masifar,sann babu ni babu ke maimunatu ki tafican kinemi mai rufa miki asiri.

Har Nine zaki nemi ki tozarta?ki tuna fa nine wanda ya rufa miki asiri a lokacin da kowa ya guje ki,bilti baki isa ba,nace baki isa kizo ki tarwatsamin nawa mutuncin abanza ba.
Inhar kina son zama dani Kinemi miji kawai kiyi aure, aikin nan ya haramta agareki.
inhar kinason ki tsira da mutuncinki awajen mu ki rabu da gidan qasimu.

amma inba haka kika zabar makanki ba To fa kofa a bude take amma kisani daga zarar kin fita babu dawowa, Saidai kije can uwa duniya ta zame miki uwa da uba amma badai mu ba.

Maganganu kawu ibrahim yafi yi ma bilti ciwo fiye dana kowa.

Duk dama tasan bayinshi bane,yan uwane da dangi wanda tunda ma can sunajin haushi da kishin aikin data samu agidan su taheer bacin sunada duk wani labarin cewa tanacikin kwanciyar hankli da wadata batada damuwar komi dama can Burin su shine su rabata da wannan rufin asirin
sude sunfi son suganta a lalace tanabin korokoro layi layi tana neman abinda zata rufawa kanta asiri da kyar,daga cikin kawunan nata ma akwai masu sha’awar jikinta shiyasa da basu samu kanta ba suka hada kansu suke kokorin cusa ma kowa ra’ayin jin cewa ita yar iska ce tunda haryau zaman ta takeyi cikin kamun kai da tsoron Allah batare da namijin da zaina biya mata bukatunta nayau da kullum ba.

Sosai bilti ta raunana kuma dalilinta kenan na kashe wayatta tsawon wnn lokaci..

damuwa da bakinciki su suka taru sukamata yawa har ya saka mata ciwo,kullum bata cikin hayyacinta tana kwance a daki cikin jimami da kuka,wato a duniya inde har ka rasa iyayen ka duka toh sai yadda Allah yay da kai kawai.

Duk da halin damuwa da suka jefata aciki hakan bai saka kawu yin shiru ya kyaleta ba,ko kofi ta fito daukawa zata sha ruwa saiya bita da bakaken maganganu masu zafi yana hargagi yana cewa tay tayi ta fidda mijin aure inba haka ba kuma shi zai kawo mata nashi zabin mijin kuma dole ta auresa..

Rayuwa yay mata zafi saukin abun ma wai dan ta amince zata fita acikin rayuwar su taheer ta nemi mijin auren kenan.

Duk da haka yan uwa da dangi basu kyaleta ba suna kan tsangwamarta bakar maganan yau na daban na gobe daban.

Kukan da wasime takeyi
Ajikinta sosai ya daga mata hankli,ta rasa yadda zata soma taÉ“a ta bare ta rarrasheta, tasan wasime yarinyace mai taurin kai ga yarinta ba lallai ne ta iya fahimtar halinda datake ciki ayanzu ba…..

Shafa kanta bilti ta dingayi cikin salon rarrashinta amma hakan bai hana wasime furta abunda ke cikin ranta cikin matsanancin kuka ba.

Muryanta gwanin ban tausayi tanayi tana magiya Tace “Bilti dan Allah,dan darajar annabi kiyi hakri ki dawo gida.
Bilti in laifi nayi miki kiyafemin dan Allah.

Ai Naji kinata cewa bazaki zauna da mu ba,yo mu me mukamiki?
..bilti meyasa zakice hakan dan Allah..?bilti ki dawo kawai Allah nay miki alkwari zan canza bakin halina.

“Kinga fa na dena tsula fitsari,kuma ina tsafta inajin magana amma da bakinan komi wahala yakemin sai adinga barina agida nikadai ban iya ko abinci ba,kuma babu mai ko min kitso na higga uku dan Allah karki tafi ki barki kizo kawai mutafi ai yayana zai kaimu gidanmu yanzu.

Kuka wasime takeyi sosai kamar ranta zai fita yabar gangar jikinta a zauce ta kwace kanta ajikin bilti cikin tsananin tashin hankli tana mai girgiza kanta tsabar gigicewa..
Numfashinta ne ya soma yin sama sama tana shirin zubewa kasa taheer ya biyota da hanzari ya fixgota da karfi ya mannata akan faffadan kirjinsa.

kankameta yay sosai ajikinsa duk yabi ya rude ya gigice sai zufa kanshi yake fitarwa.

Koda suka hade ido da bilti babu abunda ta iyayi sai fashewa da wani matsanacin kuka.

A Yadda ya rugume wasime ajikin sa hakan itama ta taho ta rungumesa tana kuka mai rauni.

Gabaki daya taheer yaki ya motsa awajen daurewa yayi sosai yayi zuciya irinta maza bai zubar da hawayen sa ba.

Shiru kawai yay zuciyar sa na bugawa ayayin da yake sauraran kukan su duka ..

Murya gwanin ban tausayi Bilti tace
“Taheer dan Allah kayafe min…nasan zaka zo ka fahince dalili na nan gaba..babu son raina acikin duk halinda na jefaku aciki..kuyafe ni
Sann Kusani ina matukar kaunarku araina kudin tamkr yayan dana haifa acikina ne.

Taheer dan Allah karka kullace,karkace na kyale ka alokacin daka fi bukata ta..kayafeni
Snn Ka kula da kanka ka kula da matarka wasime ni nasan zaka iya taheer..
kayi min hakan ko badan ni ba kayi Adalci ma rayuwar ka dan Allah.

Kallonta ya dingayi idanunshi gabaki daya sunzanja kala sunyi sanyi…

tabbas yasan akwai babban damuwa tattare da bilti,kukan ta bai fahimtar da shi komi ba face azaban damuwa da
Kuncin datake ciki mai tsanani.

Murmushin datafi ciwo ya sakar mata cikin son ya rage mata nauyin dake cin zuciyarta wanda yake cin kirjinta kamar zafin wuta.

Muryansa a karkarye ya daure ya kwato makansa nitsuwa,ahankli yace…
“bilti ina fatan Allah ya yaye miki dukkan wani damuwarki,na tabbata kina cikin tashin hankli da damuwa yanzu,koda ma baki ciki,ni zanyi miki uzuri hala rashinki zai iya sakawa na fahimce wani abu game da rayuwata
,zanyi iya bakin kokari na wajen yin duk abinda kikeso.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button