NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍????✍????
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now????

NI DA YAYA LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144

Diditated to yaran albarka AHMAD(Affan),ABDULRAHEEM(Haneef)and AYSHA(Ikhram)Allah ya rayamunku bisa tafarki nagari ku da sauran yaran al-ummar musulmai amin????

Special gift to my yayu na gari Anty Sadeeya,Anty Aisha,and my k’anwa Jameela????????

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

????️27↪️28

Tana k’arasowa tace”me hakan ya naga ka mik’e,zaunawa yayi yana cigaba da kallonta,kusa dashi ta zauna warin da taji da hamami natashi jikinsa yasa ta kauda fuska sai kuma ta basar tace”na yarda xan baka abinda kakeso ajikina,

Ai da sauri ya kaimata wata chakuma,ta dakatar dashi,tace”ni ba hauka nace kamin ba ina da sharad’i idan ka amince to saina yarda dakai,

Da sauri yace”ki fad’i ko meye zan amince idai kema zaki amince da abinda nakeso,tace”karkaji komai nama amince,

Yace”to inajinki fad’i abinda kikeso nayi,tace”ba komai bane daman inason shiga kasuwa ne akwai abinda zan saya idan har zaka kaini ni kuma damun dawo zan baka abinda kakeso,

Shuru yayi zuwacen yace”ki fad’i kome kikeso ni kuma dakaina zan sayo miki,gabanta ne ya fad’i karfa abinda take niyyar d’aurawa ya kwance,tace”a’a ni dakaina nakeson zuwa ai bance ni kad’ai zani ba tare dakai zamu fita,numfasa wa yayi yace”shi kenan babu damuwa kije ki shirya sai muje,

Mik’ewa tayi gabanta na fad’u don ba k’aramin k’arfin hali tayiba,donma kar yace’wani abu cikin kayan da yasayo mata bata ta6asa ko d’ayaba ta d’auki wata doguwar riga,tasaka,ta yane kanta da kallabin rigar,ta dad’e zaune sannan tayi k’undun bala ta fito,

Shima ya cenza kaya,amma da ka kallesa abin ba tsari,murmushi yasakar mata,itama yak’e tayi yazo yakama hannunta suka fita,ya bud’e mata mota ta shiga,sannan shima ya shiga yana ta sakin murmushi yaja motar sukabar gidan..

*****************

Hjy Luba ta kalli k’asurgumin bokon da suke zaune gabansa bayan ta gama fad’a masa komai ta d’aura da cewa,boka inaso kayi min aikinda ko uwarsa sai yamanta da ita bare wata matarsa kasa duk duniya yajibaya k’aunar ko wacce mace sai ‘yata Khairat,

Buge-bugensa ya fara da surgullansa,wata k’warya ya d’akko me ruwa yaciki yace”kalli nan,cikin muryarsa mara dad’in sauraro da sauri ta kalla,fuskar Lameer ta hango cikin ruwan yace”shine wnn,da sauri ta gyad’a kai”k’warai shine,wata muguwar dariya yasaka snn wacce saida dajin gana d’aya yad’au amsa kuwwa ya ajeye k’waryar yace”wnn yaron da kike gani tun yana yaro an wankesa da addu’o’i da rubutun addu’o’i don haka yana cikin tsari snn ko da yaushe yana cikin ibada aikinmu bazai yi tasiri akansaba don yanzu hk na aika aljanu amma sun dawomin a waharce asiri bazai kamasa ba,

Khairat taja wani mugun tsaki tace”mum tashi mubar gurin nan wannan baisan aikinsa ba,rik’eta mum tayi amma ta fincike hannunta tace”idan bazaki tashiba mi xan wuce kema kya kawomi gurin irin wanda basusan aikinsu ba ni mai aiki kamar yankan wuk’a nakeso kikaini,

Mik’ewa Hjy Luba tayi tace”boka sai anjima,dariya ya kece da ita yace”duk gurin wanda zaku abinda na gani shizai gani saidai yamuku k’arya don yaci kud’inku,ke kuma da kika gaya mana mgn aljani d’an kilu ya fusata don haka zaki gani,yasake kecewa da dariya yana cewa “zaki gani”zaki gani”zaki gani”hhhhhhhhhhhhhhhh 6at ya 6ace,

Hjy luba tace”kin ganiko kinjawa kanki wannan bokan da kike gani k’asur gumin bokane,duk wani aiki danake sa sa yanamin wnn tunda kikaji yace hk to akwai matsala,

Tace”kinga mum zo muwuce shine zai gani matsiyacin boka kawai,haka suka wuce suna tafiya hjy luba na waige don yasiin ta tsorata,????

*************

Alhj Kamalu ne yadawo daga wajen tsafinsa,sai kaiwa yake da komowa zucoyarsa ji yake kamar zata tarwatse,abinda dodonsa ya fad’a masa ke masa amsa kuwwa,”Kamalu watan da dodo zaisha jini ya tsaya don haka jinin ‘yarka Khairat nake buk’ata hakan zaisa kaci gaba da samun nasara kud’i kuwa saidai aganka dasuuuuuuuuuuuu”

Toshe kunnansa yayi hawaye nazuba,duk duniya babu abinda yakeso da kauna sama da ‘yarsa khairat meyasa bai za6i wataba a danginsa ko mutanan gari sai tilon ‘yarsa abin sonsa ita kad’ai ya mallaka kuma yasan bayan ita bai k’ara haihuwa domin tuni aka masa abinda bazai k’ara haihuwa ba,don a tsarin dodonsu kowa haihuwa d’aya zaiyi,kuka yake sosai yana tausayin kansa a haka Hjy luba da Khairat suka iskesa,

Hjy luba ta fara tambaya “Alh lfy me ya faru kake kuka haka kamar k’aramin yaro?,

K’amk’ame Khairat yayi yanaci gaba da kuka,turesa take “Dad lfy meye hakan?,sakinta yayi yana share hawaye,yace”babu komai,kallonsa sukayi amma ganin baice masu komaiba sai suma suka sharesa,

…………………………………………

“Haba Lameer meyasa zaka saka damuwa irin haka aranka kazama wani iri kamar ba Lameer jarumi me karsashi da jarumta ba,tabbas muma abin nan nadamunmu domin 6atan mutim bashi da dad’i 6atan mutum sai kace 6atan takalmi amma fa dolene kayi hakuri tunda iyayenku meye basayi kullum sai an sauke Qur’ani me girma ga addu’o’in da akasa,manyan malamai nayi ga wanda mukeyi insha Allahu an kusa ganin Zainab jikina na bani Ummi na kusa damu,

Umman Zainab ce ke wa Lameer wnn mgnr,numfashi yaza sai kuma ya mik’e baice komai ba,Ammi ta girgixa kai tace”Husaina dama kin barsa kullum cikin haka muke da yaron nan amma ko kulani baiyi,Umma taja numfashi kawai tare da tagumi,

Bayan sun iso kasuwar k’auyen yace”To wanne guri zai kaiki,kallomsa tayi tare dajan numfashi tace”uhmm uhmm,da sauri ya kalleta cike da rashin yarda yace”uhmm me?tasaki wani murmushin k’arya tace”naga banga shagon siyar da kayan kwalliya bane,yace”nima ba sanin k’auyen nan sosai nayi ba yanzu ya za’ayi,

Kalle kalle ta fara sai tace”to ko zaka fita kayi mana tambayane,yace”ok haka ne bari nayi tambaya ina zuwa kawai ya fice………

Wallahi yau da kamar bazanyi ba,????????
Amma gashinan kunsan ance jiki da jini sai a sulo yaudai haka nakejin jikin nawa sai a hankali don Allah kusani a addu’a,

Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
????????????????

      *NI DA YAYA LAMEER*

             ❤❤❤❤
              ????????????????

GAJERAN LABARI

Story and written

By

Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍????✍????
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now????

NI DA YAYA LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144

Diditated to Fans

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

????️29↪️30

Tana ganin ya fice,itama ta sad’ad’a a hankali ta bud’e murfin motar ta fice da sauri,

Sauri-sauri take tafiya,ganin kamar yana binta tasaka gudu,yana dawowa yaga bata ciki gabansa ya buga,keiiii!ya furta a gigice,da sauri yabi bayanta,yana ta waige-waige amma kome kama da ita bai gani ba,cike da takaici ya koma gurin motarsa,

Ita kuwa Zainab babban titi ta koma duk motarda tagani sai ta fara d’aga hannu tana tsayarwa kamar wata mahaukaciya,haka motoci sukai ta wucewa sunk’i tsayawa,duk’ewa tayi a gurin tana kuka sosai don gani take boss ya kusan zuwa inda take,ji tayi ana danna mata wanu uban hune,a furgice ta d’ago zuciyarta na raya mata shi kenan tata ta k’are tunda boss ya isu..

Saleem shine aminin Lameer wanda suka taso tun lokacin k’uruciya tare sukayi karatunsu,ba’abinda Saleem bai sani ba gami da gidansu Lameer shima Lameer d’in yasan komai na gidansu Saleem domin dukkansu kai tsaye suke shiga gidan iyayensu,shima Saleem Doctor ne,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button