NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

Su Khairat kuwa anji jiki,Hjy luba tuni ta amsa kiran Allah,khairat kuwa duk ta k’one ta cenza kamannin babu kyawun gani,abin da abin tausayi,

Haka Lameer ya koma gida yasanar da iyayensa nan suga dunga Allah wadai da wnn abu,

Alh Kamalu kuwa ai asibiti ihu ya dungayi yana fad’ar mugayen abunda yayi harda uwarsa da k’annansa da yabawa dodonsa da duk wasu da yakama,

Zuwa wani lokaci akaga cikinsa yayi girma sosai irin naban mamakin nan,uhmm kai abin fa babu kyawun gani da haka yarasu yana ihuuu,(Ya Allah kasa muyi kyakkyawar mutuwa kagara halayenmu ka hanamu aikata alfasha,don Allah yanzun ina amfanin bad’i ba rai Allah ya kyauta),

Alh kamalu dai an tafi cikin wani mayuwacin hali,ya Allah ka shirya masu hali irin nasa amin,

*************

Zainab kuwa tun bayan abinda ya faru,duk tadawo wani irin sanyi ta natsuwa kai bazakace ita bace,sosai yanzu ta mayar da hankali akan karatunta,

Babu wasa da shirme,ga girmama malamanta,

Akwana atashi babu wuya a gurin Allah,Shekaru hud’u kenan,a yau Zainab ta kammala jarabawarta ta SSCE ta kammala secondry,shekarunta sha takwas yanxu xuwa lokacin tayi girma sosai kyawunta yafito tazama cikakkiyar budurwa mai kyau da tsari ga natsuwa da kamala,

Kyakkyawar yarinya me manyan idanuwa ga hanci bak’inta mekyau da zubin hak’oranta farare tass,gashinta kuwa bak’i wuluk ga tsawo da yawa,

Idan tayi mirmushi kumatunta biyu sai sun lotsa kai da ka ganta saita burgeka,

Yaya Lameer ma an k’ara kyau,uhmm abin sai wanda ya gani cikakken namiji kenan da ko wacce mace zatayi alfahari ya zamo miji a gareta,sunyi kama sosai da Zainab d’imsa yanasonta so na hak’ik’a,gaskiya Yaya Lameer k’arshe ne wajen kyau da tsaruwa,

Tana zaune a farlourn Ammi ya shugo sanye yake da k’ananun kaya gaskiya yayi kyau,zuba masa ido tayi tunda yashugo aranta take aiyana kyau da had’uwa na yayan nata ji take inama ace shi,mijinta ne gaskiya tana k’aunar yayan nata,

Hura mata iska yayi cike da shagwa6a ta turo baki gaba yace”wnn irin kallo karfa ki cinyeni d’anye,tace”kai yaya Lameer kullum fa naga kyau kake k’arawa wllh,

Dariya yayi me k’ayatarwa yace”duk kyauna ai ban kai sarauniyar mata ba,yanzu,ma tad’i zani ko zaki raka nine,tuni ta zaro ido sai kuma ga yawaye sun taru mata tace”tad’i,kuma yaya,sai ta fashe da kuka tayi ciki da gudu murmushi yayi yabi bayanta da kallo aransa yace”dole in amshi matata hannun Ammi don yanzu ne lokacin da nafi buk’atarta,

Jikin Ammi ta fad’a tana kuka Ammi tace “lafiya me yafaru Ummi,cikin kuka tace”Ammi ba Yaya Lameer bane wai tad’i zashi don Allah kice kar yaje wajen wata,

Zaro ido tayi Tace”ehye,sai tasa dariya tace”ki kwantar da hankalinki Ummina kin kusan tarewa gidan,mijinki don yanzu haka shirye-shirye muke,tace”miji kuma wanne mijin?,nan Ammi tasanar mata duk abinda ya faru a baya na auransu da akayi da yayanta,

Ai tsalle ta buga ta rungume Ammi tace”kai amma naji dad’i Ammina gaskiya kun kyauta mana,da gudu ta fita cikin jin dad’in daman yaya Lameer mijinta ne lallai tafi,ko wacce mace sa’ar miji a duniya

(ni kuwa Ummu Affan nace a’a zee nimafa nafi ko wacce mace sa’ar miji????????)

Ammi murmushi tayi cike dajin dad’in Ummi ma tanason Lameer,Hussainarta takira tasanar mata wato Umman Zainab nan sukai ta dariya sukace yaran zamani kenan…….

Mu had’e gobe don jin k’arshen labarin

Taku a kullum meson faranta muku,

Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
????????????????

      *NI DA YAYA LAMEER*

             ❤❤❤❤
              ????????????????

GAJERAN LABARI

Story and written

By

Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍????✍????
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now????

NI DA YAYA LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144

Diditated to Fans

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

????️33↪️34

Sosai Ammi ke gyaran d’iyar tata,duk wani abu da yadace tana mata,

Tun lokacin da Zainab taji cewa yaya Lameer mijinta ne,suka dawo wasan 6uya don bata bari su had’u,wata irin kunyarsa takeji sosai,

Shi kuwa d’an anacin,kullum yana cikin gidan inda yadawo daga aiki,sai ta shige d’akin Ammi idan xai bita Ammi ta hana,tace”waiku yaran yanxu meyasa ne baku da kunya,

Sai yasosa keya kawai ya fita aransa yana cewa amma Ammi ai kinsan nayi k’ok’ari shekarun kusan bakwai ina renon matata aikuwa a jinjina mini,

Sosai aka shirya taron tarewa,inda akayi hidima sosai ta ‘ya’yan gata,

Daman tuni Lameer ya gama gininsa anjerawa Zainab komai gidan ya had’u iya had’uwa ya tsaru,

Inda a ranar tarewar aka kaita d’akin mijinta kuma Yayanta LAMEER

Fad’ar farin cikin da Lameer yake ciki 6ata baki ne,shidai yasan yana cikin tsantsar farin ciki da annashuwa,yarasa wanne irin sone yakewa k’anwar tasa,

Sosai iyayensu suka had’asu suka masu fad’a nasu xauna lfy sudai sunsan tamkar hanta da jini suke,Zainab bataji komai ba don tasan yayanta zai rik’eta amana hakan yasa ko kukan nan da amare keyi idan za’a kaisu ita batayi ba,

Wata abokiyar wasansu tace”kai Ummi ko kuka babu,tace”to mezanwa kuka nidaza’akai gidan yayana abin sona,nasan zanyi kewar su Ammi amma nasan danace yakaini zai kaini,dariya tasaka tace”ni gaskiya banta6a ganin amarya irinkiba kona k’aryarnan bazakiyiba,murgud’a baki tayi tace”to bazan ba,

Haka aka kaita gidanta,Wajen takwas na dare kowa ya watse itama tashi tayi ta d’auro alwala taxo tayi isha’i tayi shafa’i da wuturi,tana addu’a taji motsin shugowarsa,da sallama,addu’a ta shafa tayi saurin komawa kan gado ta rufe fuska,

Shi abinma dariya yabasa yayi murmushi snn ya ajiye ledar dake hannunsa ya zauna bakin gadon yace”amarya kinsha k’amshi,sake sadda kai k’asa tayi cike da kunya,

Yace baza’a bud’emin fuskar in ganiba ko saina biya,tace”a’a,tare da d’aga mayafinta kanta na k’asa,tafin hannunsa yasa ya d’ago fuskarta yace”Zainab kalleni,d’ago kwayar idanuwanta tayi,suna had’a ido ta sake k’asa da idanuwanta sbd kwarjininsa dayacika mata ido,

Yace”ki kalleni nace,da kyar ta iya kallonsa suka xubawa juna ido,yace”me kika gani cikin idona,turo baki gaba tayi cike da shagwa6a tace”ni banga komai ba,

Jawota yayi jikinsa yana sakin ajiyar zuciya yace”bakiga tsantsar sonki da k’aunarki ba acikin idanuwana,

Tace”nima ai ina k’aunarka yayanah,ajiyar zuciya yayi yace”Zainab tun ranar da aka haifeki nake kaunarki ke bugun numfashi nace ina sonki ina kaunarki Zainab don Allah nima kisoni,

Tace”inasonka yayanah a tun lokacinda na mallaki hankalin kaina nakejinka cikin jini da tsokata,

Murmushi yayi yace”tunda naga kin idar da sallah yanxu kina da alwala kitashi muyi sallah don nuna godiyarmu ga sarki Allah da ya nuna mana wnn babbar ranar,ba musu ta tashi,shima alwala ya d’auro yazo yajasu sallah raka’a biyu,bayan sun idar ya rik’e goshinta ya dunga kwararo mata addu’o’i,daga bisani ya jawo ledar da yashugo da ita,

Fulat ya d’auko da kofina ya dawo ya zuye musu kazar snn ya yago tsoka yace”bud’e bakinki,mak’e kafad’a tayi alamar a’a,ya janyota jikinsa yace wllh kici,ko namiki d’ure,

Turo baki tayi cike da shagwa6a,da sauri kuwa ya chafke bakin yana aika mata wani hut kiss,zaro ido tayi cike da tsoro????,

Ganin haka yasaki bakin nata,wata irin kunya taji aranta tace daman haka yaya Lameer yake,ashe a fili ta fad’a saiji tayi yace”yarinya na wuce nan,ai dama kin dad’e kinamin yanga da bakin nan naki ko?,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button