NOVELS

SAWUN BAYA 1 & 2 COMPLETE HAUSA NOVEL

Compiled by Mrs Uthman ????

???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM PAGE 1- 2Typing…????️ Nariga kowa zuwa, yau nice afarko babu wani katon da zai zare min ido” Wata kyakyawan yariyace ke fadin haka lokacin da take kokarin gyara mayafinta tare da bude Qur’anin dake gabanta, ta maida hankalinta sosai” Gyaran muryan da taji yasata dago kanta ahankali ta kalli gurin, wani kyakyawan saurayi ne ke tahowa cikin farar jallabiya data karbi jikinsa sukai matukar dacewa da farar fatan sa, Cikin sauri yariyar ta dauke kanta tare da Kara matsawa can gaba gaba cikin hade fuska tare da turo baki” Nesa da ita ya zauna beko kalli inda take ba, zaman kusan minti 10 sannan wani saurayi wadda baka iya banbanceshi dana farko ya taho ya zauna daf dashi yana me shafa kansa” Wasu ‘yan Mata ne guda biyu suka taho tare, suna tafe suna hira cikin nishadi saida suka zauna sannan suka yi shiru a daidai lokacin waccen yariyar ke fadin nariga kowa nice farko” Atare ‘yan Mata suka kalli wannan saurayin, cikin sauri suka dauke kansu gudun kar suyi Ido biyu” Tahowan wani dattijo mutumi yasa su saurin mikewa gaba dayan su, yayin da hakan ya Kara bayyana shigarsu Mata da maza cikin farin kaya, wani abun Mamaki yadan kayan su yake fari kar hakama fatar su take faritas, gaba dayan su, zaune suke afarfajiyar wani katon gida da aka kawata shi sosai tare da yalwataccen fili , hanci kuwa gunsu ba’a magana wannan yana wane wancen” Dattijon ne ya isa tsakiyar katowar dardumar dake gurin ya zauna ahankali ko wannen su ya nemi guri ya zauna, shiru gurin yayi tsayon wani lokaci, zuwa can dattijon yayi gyaran murya cikin harcen buzanci yace dawa zamu fara? Cikin sauri yariyar dazon tace nice farko☝️ Muryan wannan saurin taji yace nine” Kallon yariyar Dattijon yayi adaidai lokacin da tamike tana kokarin karasawa gaban dattijon yace” Koma ki zauna yayanku ne zai fara” Turbune fuska tayi cikin shirin kuka tace” Abbanin narigashi fah???? Naji ki zauna tukun dattijon yafada fuskansa dauke da murmushi” Gaban Dattijon ya zauna ya tankwashe kafarsa cikin natsuwa ya shiga raira karatun al’qur’ani me girma” Kowa sauraronsa yake cikin nutsuwa yana futar da kowaccen harafi yadda ta dace, kowa zazzakar muryansa yake sauraro amman banda yariyar nan banda hararansa babu abun da take zuba masa” Bayan ya kammala mikewa yayi ya bar wajen yayin da malamin yabishi da kallo cikin murmushi harya bacewa ganinsa sannan sannan ya maida hankalinsa gurin sauran” Daya bayan daya suka bada haddar su yayin da bayan sun gama suka shiga yiwa Dattijon tambayoyin game da abun da ya shige masu duhu bangaren addini, haka ya dinga basu amsa cikin wasa da dariya” Bayan sun gama tare suka taso gaba dayansu suna tafe suna hira harda Dattijon cikin farin ciki da walwala” Ratsowa suke ta cikin wasu hadandun ginengine nazamani duk acikin wannan katon gida, da alama bangare bangare ne domin dai gani nayi sunawa junan su sallama kowanne da anxo daidai part dinsu yake shige cikin dagawa juna hannu har ya rage daga dattijon sai wannan yarinyar dan haka ya roko hannunta cikin son kallon fuskanta dake cike da bacin rai” Kina fushi har yanzun dan kin riga yayan ku Kuma nabashi dama ko? Cikin kwal kwal da Ido tace, Abbanin aini narigashi ne wlh nadade sannan yazo haka yake kullum, daga baya yake zuwa kuma saiyace shine zai fara” Hannunta ya matsa kinaji ko?, Ki kwantar da hankalin ki, Babban ai Babban ne koba haka ba, Kuma Banda abunki Munirah duk wurin nan wa kikaga zai iya cewa ya rigashi?, Ki daina tsiyawa kinji ko? Yawo ta hade tare dayin murmushi sannan suka shiga cikin gida tare” Misalin hudu na yamman saurayin tsaye hannunsa harde akirjinsa yake kallon yariyar dake rawa ko Ina najikinta motsawa yake cikin kwarewa take girgiza sassan jikinta batare dajin nauyin jikin nataba yadda take karkarya jikinta wajen nuna kwarewarta yasa saurayin ya shagala sosai wajen kallonta, sosai rawar tata ke burgeshi gaba daya dukiyarta girgiza suke tamkar zasu tsinke subar jikinta” Kusan awa guda tana abu daya daka can ta tsuguna ta kashe Mp nata sannan ta gyara lafayanta tafara tawa kamar ba itace tagama rawa yanzun nan ba” Shima saurayin bayan tabacewa ganinsa ahankali ya koma ya zauna tare da ajiyan zuciya yana me dawo da rawar tata cikin idonsa tamkar yanzun nan yake kallonsa” Wani saurayin ne ya iskosa gurin kujera kusa dashi ya zauna tare da fadin Wai Kai meyasa aduk sanda zan sameka gurin nan saina sameka ranka abace? Kawar da kansa yayi sannan yace, bakomai” Jimmm yayin sannan ya sake cewa kaje kaji Kiran da Annanin take maka kuwa? Can ya sake kawar da kansa sanan yace zan dai je” Yaushe? Idan na shirya” Shikenan amman gaskiya ya dace kaje da wuri, duk minti nawa ne, zaman nan namu ya isa kaje ka dawo” Wanan karon bece komai ba mikewa kawai yayi ya fara takawa cikin nuna isa da takama” Binsa dayan yayi da kallo sannan ya tabe baki ya saki ajiyan zuciya” Ai duk acikin gidanan Amukarnin Sagir yafi kirki, shi bashi da Jin kansa Kuma yana mgn da kowa, bashi da fadin rai” Nikuwa nafi ganin kirkin Amukarnin Sadiq ….. Ke Kuma jibeki, meye Kuma Sadiq?, kullum cikin kunci bashi da wata walwala rannan nasa kullum kamar yaji sakon rasuwar Umma da Abba” Dariya daya budurwan tayi, nidai baruwana kubari karyazo wucewa yaji ku” Nibanjin tsoron shi wannan Sadiq din ne har za’ace masa me kirki? Jifa tambayan tayi wa ‘yan mata 2 dake zaune awajen wadda idan basanin su kayi dakyau ba baka iya banbancewa” Ni bani da matsala da Sadiq amman indai zancen kirki ake Mubarak duk yafi kirki” Karamar ce tace toh gara gara mashi din amman Sadiq ai bashi da mutunci wlh dama ba’ayoshi cikin zuri’armu ba, ni bantabajin natsana wani halittaba kamar inda natsane shi, ke nifa idan inajin haushin mutum so nake ya mutu kawai in daina ganin shi, kinga ko wannan yariyar da muke gaba nida ita banjin tsanarta kamar inda nakejin tsanar Sadiq Tafdi Aunty Lubunah kinajin ta fah Wai gara Amukarnin Mubarak akan Amukarnin Sadiq, duk gidan nan wake kama mutun ya zane idan ba Amukarnin Mubarak ba, ai shine mara mutunci nakarshe mugunta ta mishi yawa” Wannan karamar cikin tasu ta sake cewa ai gara azaneka da adinga hararan ka, in banda munafunci mutum bazaicewa kowa komai ba sai hade fuska da harare harare shiba komai ka masa ba, ga fadin rai, shifa gani yake kamar yafi kowa Dariya suka saka ganin haka yariyar tabar wajen tana tafe tana mgn wadda basajin me take fadi” Ganin tabar wajen daya daga cikin tace” Masifaffiyar yariya kawai, Allah ne ya tsare batazo asakon Shi ba, da gidan zaiyi wuyar shigowa, su Abbanin kuwa da kullum cikin sulhu suke ko raba danbe” Babu abun da zai faru ko hakane ma, toh me zata iya masa Aliya?, duk wannan surutun da take navanza ne tunda bazata iya fadi agaban shi Haba ki duba kigani fah Lubbunah duk gidan nan Amukarnin Sadiq din ne Babba, kowa girmamasa yake, amman banda Munirah, Sadiq take kiransa, ko mgnr sa taji anai agida karkuga yadda take cika” Dariya suka sake yi gaba dayan su sannan suka mike su ukun suna cikagaba da tattaunawa akan yadda Munirah take nuna kiyayyarta ” Wannan yariyar ce zauna gaban wata ‘yar dattijowar mata, tufke gashinta take tare da rabashi tsoro biyu ya kwanto Kan kafadunta, shafa bayanta dattijiwar matar tayi tare da fadin ko kefa kinga har kinyi kyau goshin ki yayi haske sosai, yanzun maza ki tashi karsu tafi su barki” Shayin dake gaban Dattijowar ta dauka ta kafa Kai ta shanye sannan ta aje kofin ta nufi kofar fita tana gyara lafayarta” Binta da kallo Dattijiwar tayi tare da murmushi harta fice sannan ta fara kwashe kayan data barbaza Mata agurin komai ta maidashi mazaunin sa” Jerowa sukayi su 3 kamar yadda suka Saba saidai suna fitowa daga gidan Malam suka hangi mutun kishin gide adarduma ko ba’afada ba sunsan waye agorin” Lubbunah ce tace Munirah ga Amukarnin Sadiq can yana Shan iska” Ina ruwana ni, ai daman nasan shine basai an wani gaya min ba, Kuma ma ni kadaice agurin da zaki wani ce Munirah” Dariya sukayi, yayin da Aliya tai saurin wucesu ta isa tahau dardumar, koda suka karasa gurin Lubbunah tsayawa tayi tana mishi sannu da hutawa amman banda yariyar da aka Kira da suna Munirah, gaba tayi abunta, yayin da saurayin yabita da kallo yana me amsa sannun da suka masa da hannunsa, sannan yai gyaran murya cikin hausarsa da Bata fita sosai yace ku tsaya anan gaba dayan ku” Aliya ce ta mike daga darduma ta isa inda Lubbunah ke tsaye itama ta tsaya adaidai lokacin da Lubbuna ke fadin Munirah kidawo nan” Juyowa tayi batare da ta kalli gefensa ba ta tsaya cikin su cikin tsananin jin haushi” Sau daya ya kallesu ya kawar da kansa gefe , tsayuwar kusan minti biyar sukayi sannan ya bude baki daker yace, kananan yara su koma gida” Gaba dayan su Munirah suka kallah, ganin su har yanzun atsaye yace ko baku gane bane?, ke Aliya dawo gaba” Cikin sauri ta tafito cikin su ta tsaya agaban” Kawar da idonsa yayi sannan yace, daga Kan Aliya duk wacce batakai Aliya tsayiba ta koma gida” Munirah suka kallah yayin da cikin fushi Munirah ta nufi hanyar da zata sadata da cikin gidan su batare da tama gwada ba” Ganin wucewan Munirah yace ku bace anan gurin” Tana juya baya kuka ya kwace mata, tunda take da wayaunta wani abu betaba hadata dashi ba, haka Kuma mgn ta fatar baki betaba hadata dashiba’ asalima ko gaidashi Bata yi, Kuma bayau ya saba ganin fitansuba ba dan haka taji ranta yabaci sosai” Cikin sheshshekar kuka tashiga part dinsu tare da kwala Kira……. Annanin!! Annanin!!! Munirah Yaya, lafiya?, Meya same ki? Kinga Sadiq ko????? Sadiq kuma?, Munirah waye haka? Amukarnin Sadiq ne???? Bakinta da buga da karfi, yayin da Munirah tai saurin dafe bakin nata tare da Kara karfin kukanta” Sadiq din ne kike Kira gatsal babu wani girmamawa?, Sa’ankine shi? Toh bashi bane ya koroni, Ina ruwanshi dani???? Cikin Mamaki matar ke kallonta, sannan tace, amman kinsan gaba yake dake ko?, Kuma dolene ya hukuntaki idan kinyi badaidai ba…. Ai yanzun banyi komai ba, Kuma koma nayi wani abun acireshi acikin waddan da zasu hukuntani, gara abar Amukarnin Sagir da Amukarnin Mubarak su kasheni akan shi ya dunguri kaina” Tsananin mamakine ya kama matar tanawa Munirah kallon tuhuma tace duk meya kawo haka? Annanin nifa natsaneshi, dama ba’yoshi cikin zuri’ar gidan nan ba, Kuma insha Allahu mutuwa zaiyi rayuwarshi bazatai tsaye ba….. Bege bakinta tayi akaro na biyu tare da fadin rayuwarsa bazatai tsayi ba, tunda ransa ahannun ki yake, kekuma sai abar miki jiran duniyar” Kuka tacigaba dayi kamar ranta zai fita, yayin da lokaci bayan lokacin take motsa bakinta saidai ba’ajin me take cewa, ganin haka ta jawota ta rungume” Jikinta ta shiga ta kwanta tana me share hawaye, shafa bayanta matar keyi harna tsayon wani lokaci, zuwa can bacci ya dauketa, gyara Mata kwanciya tayi sannan ta rufeta da bargo tabar dakin” * Bushe bushen da takeji cikin kunnenta ya tabbatar mata 4pm tayi, tashi tayi cikin sauri ta nufi toilet, wanka tayi cikin sauri2 ta shirya cikin farin labaya turare tashafa nan danan kamshi ya cika dakin, Busan da tajuyo ya mantar da ita komai dan haka da rawanta ta fito tana girgiza kafadun ta cikin nutsuwa da nuna kwarewarta” Cikin rawar tata takaraso filin da aka tanada dumin gudar da wannan al’ada tasu” Gaba daya ahalin wannan katafaren gidan ke zaune agurin, Banda iyayensu maza kowa na wannan guri, yayin da manya iyaye ke zaune akujerun dake zagaye da gurin, ‘yan matan kuwa suna zune akan katuwar daddumar dake gurin suna rawa cikin kwarewa” Sadiq da Sagir ne zaune daga gefen iyayen su mata, shigowan Munirah da rawa hankalin kowa ya koma kanta daganin rawarta zaka tabbatar wa kanka lallai dan gado sai dan gado” Shigowan Munirah ya zaburar da Sagir mikewa yayi yana rausayawa irin nasu na maza dagani kasan yanajin dadin yanayin, duk da cewa shekarunsa sunkerewa Munirah nesa ma ba kusa ba, amman be hanasa kama hannuntaba cikin nuna gada sukayi ba haye ba yake rausayawa da ita” Tun shigowan Munirah Sadiq yaso barin gurin, saidai ya kasa yin haka, hannunsa ya zuba cikin aljihun rigar sanyin dake jikinsa Tare da daura kafarsa daya kan daya” Guri daya ya zubawa ido, ta gefen ido yake kallon yadda kirjin Munirah ki girgijewa yayin da lakaci bayan lokaci yake matse cinyan sa” Sun dade sosai ita da Sagir suna rawa irin tasu wadda suka gada, daga can Munirah ta zauna cikin jirin ‘yan matan da suke gurin yayin da Aliya ta mike ta isa kusa da Sagir cikin nutsuwa take taka nata rawan, mikewa Sadiq yayi har yanzun ahannun sa cikin aljihunsa yana takawa daya bayan daya yabar wajen, hankalin kowa komawa yayi kansa har yai nisa suna hangen sa” Misalin 6pm Sagir ne ya shiga wani katafaren dakin bacci wadda haduwar sa ya isa, Sadiq ne ya fito daga wata kofa, goge kansa yake da alama wanka ya fito” Kallon Sagit yayi sannan ya zuna batare daya kallesa ba yace” Har kagama rawar? Nagama yabashi amsa Kai tsaye” Gutun tsaki Sadiq yaja, kazauna cikin yara kana shirme katon banza kawai” Rawa dai Kuma naga ai ban kaika son rawar ba” Kawar dakai yayi yana fadin da ba” Kaidai ka sani, yanzun ba wannan ba, kaje Kiran Annanin kuwa? Mikewa yayi ya fara murzawa jikin sa mai yana fadin, zandai je” Yaushe? Duk sanda ka shirya” Bangane sanda na shirya ba” Yana kokarin zira jallabiyarsa yace” Ina nufin idan ka shirya kaini” Wanni irin kallo Sagir yai masa na takaici sannan ya mike ya nufi kofar yana me Jan tsaki” Sadiq ma bayan Abba yabi da kallo, shima tsakin yaja sannan ya fesa turare sosai ajikinsa, hularsa ya dauka yana gyara karinta har ya fito farfajiyan gidan” Yana tsaye gaban motar ya daura hular akansa sannan ya bude motar ya shiga ya zauna, yana kokarin tada motar ne ya hangi wata farar dattijuwa dake tsaye jikin window hannunta yasha Jan lalle bakinta dauke da hakurin maka dayai matukar Mata kyau, murmushi ta sakar masa wadda yasa shi dole ya murmusa batare daya shirya ba” Ganin murmushin sa Dattijiwar ta fadada nata, tana me daga masa hannu” Shima hannun ya daga mata sannan ya tada motar yabar gurin yana me sakin ajiyan zuciya” Dattijiwar kuwa fadi take, Allah ya tsare min kai aduk inda kake, yadawo min dakai cikin kushin lafiya, ya Allah narokeka ka hana wannan bawa naka aikata sabon ka” Komawa tayi bakin gadonta ta zauna, yau Sati biyu kenan tana aikawa a kirasa amman yaki zuwa, tuni take da tabbacin sakonta ya sameshi, ajiyan zuciya taja sannan ta lumahe idonta cikin yanayin damuwa” **** Misalin 11:30pn wannan Dattijowar matar ce tafe afarfajiyar wannan Babban gida tana tafe tana waigen bayanta kasancewar bata saba fitowa daidai wannan lokacin ba” Gaba daya kofofin bude ta same su dan haka ta dinga ratsawa ahankali harta isa dakin baccin sa wadda ta tura kofar ahankali, saidai harta iso bakin gadon be farka ba yana baje Kan makeken gadonsa Banda kamshi babu abun da hancinta ke jiyo mata” Durkusawa tayi ta sunbaci goshin sa, yayin da jin sanyin a goshin sa yasashi saurin bude idonsa” Ido hudu sukayi dan haka ya saki murmushi sannan ya Mika hannun shi ya roko nata adaidai lokacin da yake kokarin zama” Itama zama tayi bakin gadon hannun su nacikin na juna” Annanin kece da wannan daren? Nice Sadiq, namatsu in ganganka” Cikin murmushi ya sunbaceta tare da Kara murza hannunta cikin nashi yana me lumshe idon sa” Sadiq nafi kwana goma Ina aikowa Kiran ka, halan sakona be same kaba ko? Karyar dakai yayi cikin shagawaba yace Annanin gajiya nake fah” Ajiyan zuciya tayi sannan tace, toh sannu my son, yanzun tashi ka zauna sosai muyi mgn” Tashi yayi kamar inda tace sannan ya zuba Mata Ido” Maganar zuwa Agadez ne Sadiq wannan karon maihaifin ka yace kaine wadda zaka wakilce shi” Cikin hausarsa dabata fita sosai yace” Bazani ba ni gaskiya Annanin…… Hannu tasa ta rufe masa baki, haba Khalipha, Duk gidan nan kaine Babba wannan karon duk cikin su babu me zuwa, kaine Babba dan haka sun yanke kaine zaka wakilce su” Ni kadai Kuma?, Ai bani kadai bane dansu Annanin ace muje duka mana” Dariya Dattijowar tayi sannan tace duk karatu suke ai, Sagir Kuma yana Kan aiki Kai Kuma ai hutu kake ko? Nima ai jibi zan koma” Goshinsa ta dungure, murmushi yayi kadan sannan ya sunbace ta, lumeshi idonta tayi tare da dafa kansa tace, Allah yamaka abarka ya Kuma kaika lafiya ya dawo dakai lafiya” Daker Ya motsa lebensa yace Ameen, amman ahadamu duka mu uku mutafi, Annanin saiki yadda intafi Ingal nikadai saikace bakya sona Haba Sadiq kaifa bansanka da ragwanta ba Kai kadai sukace” Yamutsa fuska yayi tare da lumshe idonsa Sunbatan sa ta sake sannan ta mika hannunta ta shafi wuyan sa, sosai ta yamutsa fuska tana Kara tura hannun nata wuyan sa Khalipha meya faru ka rame haka?, Kana cin abinci kuwa? Kawar dakai yayi inaci Annanin sosai” A’a Sam mikewa tayi cikin sauri ta nufi kitchen ta dauko kofi sannan ta dauko galan din Madara ta cika kofin dashi ta dawo takai masa bakinsa ba musu ya bude bakin sa batare da wani Bata lokaci ba ya shanye” Kallon kofin matar tayi sannan ta kalli Sadiq gyatsan dataji yaja yasata fadin” Kanawa kanka horon yunwa, kashigo cikin gida kaci abinci kake ganin asarah konasa a dinga kawo maka…. A’a Saboda me? Kawar da kansa yayi ni banason masu aiki suna zuwa min part dina” Tabe baki matar tayi sannan ta mike tana me kare masa kallo, shima gyara kwanciyarsa yayi tare da daga mata hannu” Murmushi ta masa tare da fadin Allah ya tashimu lafiya” Cikin zullumi da tunani ta isa part dinta zuciyarta cike da fargaba, shiganta daki yayi daidai da Karan shigowan Sako cikin wayarta dauka tayi ta duba, Sakone daga Khalipha, murmushi tayi me hade da takaici tana karewa sunan nasa kallo me Kuma zaice bayan yanzun nan nabaro dakin sa…… Mmn Yazeed???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ PAGE 3- 4Typing…????️Bude sakon tayi cikin zakuwa take karantawa, Annanin kicewa Abbanin ya neman min abokin tafiya banason zuwa ni daya” Ajiyan zuciya tayi bayan tagama karantawa kiransa tayi har Saida ta kusa katsewa sannan ya dauka” Kayi bacci da safe zan masa mgn, haka kawai tace ta katse Kiran batare da tajira shiba” Aje wayar tayi cikin takaici taja tsaki sannan ta mike tai Shirin kwanciya” Washegari Wani makeken falo ne cike makil da jama’a kowanne fuskansa dauke da murmushi, karyawa suke cikin fara’a kowa na diban abun da zaici, wanni Dattijo ne dake zaune agefen yace, Alhamdulillah yau gurin ya cika da alama kowa yana nan” Kadai duba dakyau malam wannan matar ce tayi mgnr fuskanrta babu sakewa” Waige kowa yafara cikin su zuwa can Sagir yace Ummi wannan ai bazaizo nan ba ko yazoma bazaici komai ba” Meyasa?? Wadda akakira Malam ne yayi wannan tambayar” Cikin rashin sakewa wannan matar tace Malam muskilancin Sadiq ai har abinci be bari ba” Lumshe Ido yayi zuwa can ya bude ku barshi aiba karamin yaro bane yasan ciwon kansa” Sagir ne yayi murmushi yace ko zaici abinci baya wuce cukali biyu zuwa uku shima yanaci yana yatsuna baki” Dariya ‘yan Mata dake gurin sukayi gaba dayan su ganin duk anjuyo ana kallon su sukayi dif yayin da Munirah tayi karaf tace, Abbanin daman anawa abinci yanga ne?? Shidai nagani Munirah, duk wadda bazaiciba yabari, duk nan gidan bamu da karamin yaron dahar zan tsaya bata lokàcina wajen yin fadan aci abinci” Eh mana saikace wani Sayyid din Aunty Khadija” Wlh kuwa Munirah kema dai kyafada” Abbanin tunda bazai gyaru ba ku hadu kaida su Baba ku koreshi” Dariya aka sakeyi karo na biyu banda Aliya data daure fuska sosai, cikin tsananin jin haushi tace, ke Munirah wai Sa’ankine shi? . Ina ruwanki dake nake mgn na to?, Cikin yanayin tsiwa da rashin kunya tai mgnr ganin haka wannan Dattijon yace, a’a Munirah banson tsiwa, aini mancewa ma nake dawa nake mgn, Aliya Gaskiya tafada” Kitchen Aliya ta nufa ranta bace yayin da Munirah ke fakan idon iyayen nasu tana hararan ta” Ahankali aka dinga tashi wajen daya bayan daya har ya rage saura Munirah ita daya, ganin har yanzun Aliya Bata fitoba yasa tamike ta bita kitchen din adaidai lokaccin da Aliya ke kokarin fitowa hannunta dauke da Basket din data shiryawa Khalipha abinci” Wa zaki kaiwa abinci?? Ina ruwan ki? Bayanta tabi har suka fita part din ganin inda ta nufa yasa Munirah fadin, wahala zaki bawa kanki dan wlh bazaici ba”???? Batare da Aliya ta juyo ba tace badai ruwan ki” Dariya Munirah tayi aikuwa barin jiraki har kidawo inga ikon Allah” Kama kofar dataga Aliya tayi yasata kara fadin, wlh Aliya karki Kai masa abincin nan bazaici ba dan ruwa ne shifah” Ganin ta shige ta nemi guri ta zauna tana fuskanrta dauke da murmushi” Zamanta befi minti 4 ba saigashi Aliya ta fito yadda ta shiga haka ta fito da kayanta niki miki” Tun daga nesa Munirah tafara dariya yayin da idon Aliya ya cika da ruwa, koda takaraso hararan Munirah tayi tare da fadin banza kawai” Gwalo Munira tayimata har yanzun batabar dariyar ba ganin Aliya tanufi gida tabi bayanta da dariya” Sosai Aliya ta kule dan haka tana dire basket din ta rufe Munirah da duka” Danbene ya kaure atsakanin su wuyan da Munirah taji yasata cizon Aliya kota Ina” Zafin da radadi yasa ta saketa babu shiri tana me duba wuyanta tare da damtsen hannun ta da gurin yayi jazur” Jinjina Kai tayi cikin nuna Zaki sani ta juya a fusace” Ummi! Ummi!! Ummi!!! Dattijiwar da Aka Kira da suna Ummi ce ta gyara zamanta Aliya gani lafiya” Kofar Aliya ta turo, Ummi kinga Munirah ta jijeni ko? Cizo Kuma?, Cizon lafiya? Janye rigarta tayi gefen kirjinta ta nuna mata hakuran Munirah dake kwance cikin fatar Aliya sannan ta sake nade hannun rigarta” Jimmm Ummin tayi zuwa can taja tsaki cikin baccin rai tace daga ke har Munirah Ina tunanin baku da hankali garin yaya ta cijeki? Kasa mgn Aliya tayi, illah hawaye dake zubo mata kawai, shigowan Munirah yasata saurin share hawaye cikin tuhuma Ummin tace, Munirah meye ya hadaku har kika cijeta? Ummin haka kawai ta rufeni da duka fah, ba’abu da namata” Kallon Aliya Ummi tayi dan haka tai saurin cewa Ummi dariya take min” Ya muku kyau, karkubari kucigaba, dan iskanci harda su cizo, saikace kananun yara, mayyace ke zaki kama jikin mutun har kihudashi da tsabar iskanci, kodan kinga ana cewa kece karama dame suka fiki dan ubanki, duk cikin ko babu wacce aka mata aure yanzun bazata zauna ba, kushiga hankalin ku” Kuka Aliya tafara domin ita kadai tasan zafin da takeji, itako Munirah ganin Ummi ta wuce itama ta fice adakin” Part din tabari gaba dayanta tana tafe tana gyara mayafinta daya zame garin danbe adaidai lokacin da Sadiq da Sagir suka fito kallo daya Khalipha yai mata ya dauke kansa yayin da yake karasa kare mata kallo tagefen idonsa, ganin inda take fama da lafayanta yasa shi jan tsaki tare da bude motar ya zauna” Muryar Sagir yajiyo yanawa Munirah wasa saidai baya iya tantance me yake cewa dan hankalin sa ba agurinta yake ba” Har suka kama hanya bebar Jan tsakin ba ganin haka Abba yace Wai lafiya kuwa” Tsakin dai ya sakeja, lafiya lau saidai nifa bana son rashin nutsuwa” Sagir be fahimci inda zancen sa ya nufa ba hakadai yabar zancen dan yasan bazai taba fitowa dashi ta inda zai fahimta din ba” ******Misalin 8:30pm Sadiq da Sagir ne zaune abayan part dinsa suna shan iska inda Sagiq ya daura kafa daya Kan daya, Mubarak da zuwan sa kenan yanzun ya basu hannu suka gaisa sannan ya zauna gefe, hirace ta kaure tsakanin Sagir da Mubarak lokaci bayan lokaci Khalipha nasaka baki idan akai abun dariya kusa Murmushi kawai Sadiq keyi” Aliya ce tazo gurin bakinta dauke da Sallama Mubarak ne yace lafiya? Lafiya lau nakawo maka Karan Munirah ne” Munirah?, meya faru? Cizona tayi, Amukarnin har gurin ya fashe” Hada baki sukayi wajen fadin cizo? Eh har guri biyu ma da hannun na da kirjina” Sai wannan lokacin Sadiq ya kalli Aliya cikin Ido sannan ya kawar da kansa” Mubark ne yace jeki ki kirata” Gyaran murya Sadiq yayi sannan yace ke zonan” Juyowa tayi ta tsaya kusan miti biyar sannan yace mugani” Cikin rashin sabo da yanayin ta shiga warware lafayanta na hannun tafara nuna masa sannan ta nuna masa nagefen rigarta bayan ta zame rigar dake jikinta” Lumshe Ido yayi sannan yai Mata alamar ta rufe da hannun sa cikin siririyar muryarsa yace” Sannu, da safe Sagir zai kaiki asibiti kiyi hakuri kinji” Sanyi taji cikin ranta ko banza dai ya fahimci an cuceta tunda har yace tayi hakuri duk da haka Saida tasake cewa naturota? Cikin kawar dakai taji muryarsa me dadi nafadin kibarta da Allah kinji ko? Karyar dakai tayi alamar ba haka ranta yaso ba juyawa tayi kamar zatayi kuka” Aliya!! Cak ta tsaya jin ankira sunanta cikin wani salo da babu wadda ya iya Kiran sunan kamar haka” Lumshe Ido tayi cikin ranta take fadin, muryar sa akwai Dadi” Zo, taji ya sake fadi Juyowa tayi cikin nutsuwa tare da kokarin sakin ranta ta dawo gaban shi ta tsaya” Dagowa yayi ya kalleta cikin Ido sannan ya Mika Mata hannun shi” Motsowa tayi sosai ta daura hannun nata akan nashi kamar yadda ya bukata” Rutse hannun nata yayi cikin nasa yana me lumshe idon sa” Itama idonta ta lumshe dalilin wani taushi dataji irin wadda Bata tabajin sa jikin wata ba, da wani irin sanyi cikin ranta take fadin, taushin hannunsa kona mace albarka, budewa tayi, kusan atare shi dashi suka bude, ido daya ya kashe yayin datai saurin sunkuyar da kanta kasa Da hannunta dake rike ahannun sa yaiwa alamar ta kalleshi, cikin sauri ta dago” Kanshi ya karyar gefe alamar tayi hakuri” Murmushi tayi yayin daya saki hannun nata ahankali” Juyawa tayi tana tafe tana murmushi tare dajin hannun sa har yanzun cikin nasa” Bayan tafiyan Aliya Abbas ya shiga jero matsalolin Munirah yayin da Sagir ke tare mata nan Khalipha ya Kara fahimtan yariyar bataji Sam” Washegari tun cikin baccin sa ya farajin kida nashi, koda be bude idonsa ba yasan Munirah ce ke rawa tashi yayi batare daya shirya ba, dabi’ar tace kullum saitayi rawa agurin nan cikin ransa yace, ko meyasa ta zabi nan din dumin yin rawar tata?, Wata zuciyarsa cemasa tayi sabo da part din naka yayi nisa da gida ne Kuma batason aji kidan ahankali ya mutsa bakin sa Amman ni take zuwa ta dame ni” Mikewa yayi dagashi sai gajeren wando hannunsa yasa ya ware labulen window batare daya bude gilas din ba yake kallonta” Banda girgiza nononta babu abun da take, sosai ya maida hankalinsa kanta, itako tuni lafayanta ya zame yana retoh akasa yayin da hakan ya Kara bayyana suran jikinta kirjinta da kagashin kanta kuwa sai tsalle suke tamkar zasubar jikinta” Wannan karon Sadiq zama yayi kamar wani wawa binta kawai yake da kallo daga can ta kashe Mp ta ta rarumishi ta wuce batare data gyara mayafin nata ba” Bayan wucewanta ajiyan zuciya yayi sannan ya saki labulen cikin wani irin yanayi ya nufi toilet” Zuwa can ya fito yana share jikin sa tare da fesar da iskanr bakin sa” Shiryawa yake jikinsa babu wani walwala be Ankara ba yaga goma saura, cikin sauri ya kwashi wayoyin sa yana kokarin fita Aliya ta shigo rike da basket din abinci” Kaucewa yayi yana kokarin barin dakin yana fadin” Kash Aliya sauri nake akwai inda zani” Bayansa tabi da kallo, ayya Amukarnin kaifa kace saiyau zakaci” Dan tsayawa yayi kadan Aliya karki damu idan nafita zanci wani abu” Falon ta biyosa yana kokarin bude kofar da zata sadashi da waje ta sake cewa, Amukarnin dan girma Allah ka kaci, idan ba haka ba Munira zata min dariya” Dariya Kuma?, akan me zatayi dariya?? Daman tace karna kawo maka kona kawoma bazakaci ba, jiya ma dataga na fito dariya taita min shinema ma har mukayi fada ta cije ni” Dawowa yayi cikin sauri ya zauna da hannun yai mata alaman ta zuba masa, wani irin farin cikine ya lullube Aliya yayin da tashiga zuba masa cikin nutsuwa ta gefen ido yake kallonta yana me yaba nutsuwarta” Bayan tagama shirya masa ta dago ta kallesa wayarsa yake dannawa cikin kwanciyar hankali kamar bashine yake sauri yanzun ba” Cikin fargaba tace Amukarnin gashi nagama fah” Batare daya kalleta ba yai Mata nuni data bashi abaki, dan zaro Ido tayi tare da mikewa ta dawo gefensa ta zauna” Kofin tea ta fara mika masa harya karba yakai bakinsa ya yamutsa fuska tare da kallon cikin kofin cikin kausasarsiyar murya yace, Aliya banson madara fah” Kash Amukarnin kasha dan Allah nariga dana hada fah” Banso Aliya” Karfa tayi da sauri ganin yana shirin sakar mata kofin, besake dagowa ya kalleta ba harta ce masa gashi” Wannan karon ma alama yai mata data bashi abaki” Bakinsa ta nufa da kufin lokaci daya ya shanye ya janye kansa, kallon cufin tayi acikin ranta tace Allah yasa babu zafi sosai, Chips ta debo cike da cukali tasa masa abaki babu musu ya cinye har tamasa cukali 3 kamar yadda akace haka yake ci, saidai tana jaraba Kara masa taga ya karba kusan cukali 7 yayi sannan yace, nafa goshi” Murmushi tayi dan gaskiya yau taji dadi sosai ahankali tagama tattara kayan ta zubasu cikin basket din, sannan ta mike tana fadin, Amukarnin kafasa fitane wai” Kibani ruwa mana” Wani irin kallo ta masa dan tasan ba kowa ne yake shan ruwa da safe ba, kitchen din dake bangaren sa ta nufa ta dauko ruwan, abakin kofa ta samesa yana shirin fita hannun sa ya mika mata tasa masa ruwan sannan ta dauko basket dinta tabi bayan sa” Munirah nazaune indata zauna jiya taga fitowan Sadiq yana kokarin shiga motarsa Aliya ma ta fito da alama yau yaci abincin ta fada cikin ranta” Harya tada mota ya juyo Aliya tace Amukarnin kaga Munirah ko? Jira fa take nafito idan taga bakaciba tamin dariya, wlh naso kacinye shi tas” Kiranta yayi ta karasa gaban motar ahankali yace, kidaina saka waccen yariyar alisafin ki, idan zakiyi abu kiyi kawai baruwan ki da ita ko bakisan mahaukaciya bace? Yamutsa fuska Aliya tayi Amukarnin wlh ko bance mata ba ita take shigo min, itafa ko su Abbanin ne suke zancen ka saita saka baki” Maida hankalin sa yayi gaba daya kanta me take cewa? Inda Munirah take zaune ta kallah sannan tace jiya dataji ana zancen bakacin abinci haka taita zuga Abbanin harda cewa Wai su koreka sannan dana fito zan kawo maka breakfast tace ai tasan bazakaci Wai Kai dan ruwa ne” Lumshi idonsa yayi yayin da Aliya taita jira ya bude kokarin tada motar data kula yanayi yasata matsawa yayin daya figi motar yabar wajen” Wannan karon Munirah batacewa Aliya komaiba Saidai bayan ta aje basket din a kitchen ta fito taga Munirah ta shiga wucewa tayi abinta danyau batajin surutu” *Misalin 8:00pm ‘yan matan ne su 3 zaune cikin wani kawattacecen falo suke hira ciki harda Munirah datafi sakewa wajen hiran sai kwasan dariya take yayin da Lubbunah ke basu lbr” cikin nishadi yau babu fada tuni Aliya ta sake ranta daga fadan da sukayi da Munirah duk da cewa haryanzun gurin bebar Mata zafi ba duk da Alluran datasha” Misalin Tara da rabi Munirah ta mike cikin hamma tace nidai bacci nakeji natafi na kwanta” Ita kadai ta ratsa farfajiyar gidan harta isa part din su, tunkafin ta shiga taji Muryan Malam na fadin” Wannan karon bazamuje dukkan mu ba mungirma yakamata mukoyawa yara Kuma” Yayi kyau hakan malam itama Kuma zataji Dadi sosai, tsohuwar soyayya zata tashi….. Katse mahaifiyar tata tayi da fadin, Abbanin zaku Ingal ne? Eh Munirah amman wannan karon mutum daya ne zashi” Ayya Abbanin, nifa bantaba zuwa ba, haka suyita min gori koda yaushe……. Ankoyi haka Munirah duk yadda za’ayi dake ya dace ai tafiyar nan, kije ki fara shiri kafin inji inda tafiyar zata kasance” Cikin farinciki sosai Takoma dikin ta, wanka tayi sannan tai Shirin kwanciya kamar yadda ta Saba kowanni dare, tsakiya gadon tabi ta kwanta” Adaidai wannan Lokacin Sadiq ke rufe idonsa yana budewa kome ke damun sa? Zuwa can ya tashi zaune cikin Jan tsaki ya kalli agogo goma da rabi ya gani cikin sauri ya mike jallabiyarsa ya dauka ya saka sannan ya dauki carbin sa ya fice” Abun da yajima beyiba yau shi yake kokarin yi part din Malam ya nufa kansa tsaye cikin tafiyan sa ta isa isa takama takama wadda duk wadda yasanshi yasan shi da wannan tafiyar” Yana kokarin tura kofar da zata sadashi da falon Malam yaji malam din ya kirasa daga bayan sa” Juyowa yayi yaga malam zaune qur’anin gabansa da alama karatu yake” Tsugunawa yayi gaban Malam ya gaidasa yayin da Malam din cikin Mamaki yake tambayan sa lafiya dai ko? Eh lafiya inason zanga Munirah ne” Mamaki ne ya kara kama Malam sosai saidai ko tantama bayayi wani laifin tayi harta kuresa agogon hannun sa ya kalla sannan ya dago yace idan ka shiga kace anuna maka dakin ta” Godiya yayi sannan ya mike da Sallama abakin sa ya tura kofar” Dattijiwar dake zaune falon ce ta amsa cikin tsabar Mamaki tace” Khalipha kaine? Tsugunawa yayi ya gaidata sannan yace nine Umma ya kwana biyu” Lafiya lau Alhamdulillahi” Malam ne yace anuna min dakin Munirah” Kofar dake kallonsa ta nuna masa nan zakabi har dakinta” Mikewa yayi babu wani nauyi ko jin kunya yayin da Dattijiwar daya Kira da Umma take cike da mamaki domin Bata taba ganin hakan ba………..Mmn Yazeed???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ PAGE 5- 6 Typing…..????️Yana tura kofar wani kamshi ya daki hancin sa, be gama Jin mamaki ba saida ya shiga ciki, komai nata fari kar, har kayan gadonta, zanin gadonta, waige waige yaitayi komai yana zaune agurin daya dace babu alamar kazanta ko wani kura, komai kyalli yake yana daukan ido” Juyawa yayi ya kalli makeken gadon wadda sai ayanzun ya kulla da mutum agurin, tsakiya gadon ya hangota rufe cikin farin bargo gashin kanta da fuskarta kawai kake iya gani” Lumshe idonsa yayi sannan ya fara takawa ahankali ya isa bakin gadon, kafarsa daya ya daga ya daura akan adon yayin da yaji kafar tasa ta lume cikin katifar” Lumshe Ido yayi lallai yariyar nan shiyasa take iskancin dataga dama ya fada cikin ransa” Kusan minti 5 yayi akanta Amman Bata motsa ba, dan haka yama rasa mezai Mata ne, tunanin juyawa ya fara sai dai sosai yakejin dacinta dan haka yasa hannunsa ya yaye bargon data rufa dashi” Zaro idonsa waje yayi sosai ganin a yadda take kwance ahankali ya lumshe idonsa sannan ya sake waresu akanta, wanni irin kallo yake mata wadda ya kasa dauke idon sa akanta, Sai da ya kare Mata kallo sosai sannan yafara yiwa kansa fada tare da ganin hakan be dace ba, kawar da idonsa yayi badan yagaji da gani ba, nonon datake girgizasu wajen rawanta yau gasu kiri da mazo agaban sa, kamar basune suke shan wahala gurinta ba, waigawa yayi ya Kara kallon ta, gajeren wandone wadda bekarasa guiwa ba farikar ajikinta, tare da rigarsa wadda ta sauka kan wadon kadan, sai dai da alama wuyan rigar yamata yawa dan gaba daya nononta waje suke yayin tai wani irin kwanciya abankare” Kansa ya shafa cikin rasa abun yi yayin da wata zuciyar ke umartan sa maza ka fita karkayi abun kunya” Nufan kofar yayi, yana kokarin budewa yace cikin ranshi, idan antambayeta da safe Kuma tace ban shigo bafah?, gashi na dade aciki bare Kuma nace tayi bacci ne, me natsaya yi toh???, Kansa yakara shafawa akaro na biyu sannan ya saki kofar ya dawo da baya cikin waigen bayansa” Hannunsa yasa ya jawota bakin gadon kara gyra kwanciyarta tayi tare da jawo bargon ta rufawa jikinta” Cikin fada ya fusge bargon yai jifa dashi, har yanzun baccinta takeyi babu alamar zata tashi kafarsa daya ya dauka ya daura Kan nononta tare da takewa yana me cizon leben sa” Cikin sauri tasa hannunta ta ture kafar, sosai ya danne nonon dan haka ko gezau kafar tasa batai ba” Itako wani irin radadi takeji tare da wani irin nauyi kamar an daura mata wani katon dotse wani irin Kara ta kwallah wadda har malam dake wajen part din nasu Saida yajita, itakuwa ganin Sadiq saman kanta gaba daya Kara gigicewa tayi mafarkine ko gaske” Addu’a tafara karantawa tana tufa masa duk da haka batabar kara ba, tare da kokarin ture kafarsa daya take nononta sashi” Idan kika sake tabamin kafa da shegen hannun kinan zaki gane baki da wayau” Jin mgnr sa yasa tafara tunanin ba mafarki take ba, dan haka tashiga fadin, wayyo Allah nashiga uku mena maka?, Zaka kasheni fah karajin zafin da dake ya tabbatar mata Kara matsewa yake, dan haka tafara fadin wayyo nonona nonona, Wayyo Annanin kina ina Amukarni Sadiq zai kasheni, Abbanin kuzo dan Allah kuceceni nashiga uku wallahi” Duk ihun da take Malam da Ummanta sunajin ta hatta Aliya dake bacci fitowa tayi afirgice saidai tana kokarin zuwa dakin Munirah wannan Dattijiwar ta dakatar da ita tana fadin, hukunci yake Mata jeki kwanta abun ki” Shikuwa hankalinsa kwance kamar bashine akewa kuka da magiyaba ganin babu sarki sai Allah babu me cetonta tafara fadin” Amukarnin dan Allah kai hakuri zan mutu wlh, kadagani dan Allah wayyo nonona nashiga uku kayi hakuri ka dagamin nonona dan Allah” Jin tabashi hakuri ya sausauta Mata tare da fadin ki mutu mana dan ubanki meye amfanin ki” Nidai Kai hakuri Mamana da Babana suna Sona ai zanyi amfani wajen su, dazafi Amukarnin ko mafarki nake nidai Kai hakuri ka dagani nawahala wlh” Murmushi yayi ganin inda take zufa gaba daya jikinta rawa yake Kara sausautawa yayi sannan yace dan Ubaki wayene kikecewa aljani? Arude tace ni?, Kayi hakuri wlh bansan zancen ba idan nasan zancen wutar rahamani tacini” Mari yakai mata yayin data sake fashewa da kuka kin fada mara kunya kawai ko banine kike cewa dan ruwa ba?? Cikin matsancin kuka tace nafada wannan nasan nafadawa Aliya haka” Jinjina kansa yayi meye Dan ruwa Dan ubanki?? Nifa nufina……Ina jinki nufi ke me? Cewa tayi fa zatakai maka abinci nikuma nace Mata kotazo ma vazakaci sabo da kai….. Kasa rawasawa tayi dan haka yace saboda ni dan ruwa ne ko? A’a Ina nufin kafi son abun da ya dangaci ruwa baka cika son abinci ba” Jimmm yayi cikin tunani, tare da gamsuwa da nufinta domin duk wani wadda yasanshi haka yake fadi dan haka ya sauke kafarsa Kan lallausan katifar tare da fadin toh naji Aliya Kuma da kika ciza fah?? Ajiyan zuciya tayi Jin ya dagata, zaune ta tashi tare da gyara wuyan rigarta ta koma can kuryar gado tana fitar da hawaye tare da hurawa nononta iskar bakinta” Badake nake mgn ba? Ai itace ta tsokaneni”Ta tsokaneki ko kika tsokane ta?, Toh ki saurareni da kyau duk wani iskanci da kike Ina sane dake acikin gidan nan duk inda kike ko aina kikayi nasan dash,i taraki nake Kuma ki guji haduwata dake ta biyu, wlh kika yadda ana mgnta acikin gida kika saka baki idan nakamaki saina canza miki kammani, ki rike wannan, kokarin jawota yayi dan haka ta kwallara Kara” Kwafa yayi sannan ya juya ya fice adakin” Itako Munirah Kara tasaka domin sai yanzun takejin azabar nataso mata” Sadiq kuwa yana fita dakinta ya zuba hannunsa cikin aljihunsa koda ya fito falo Dattijowar na zaune inda yabarta sallama yaj Mata yayin data amsa cikin sakewa” Aliya ce ta mike da saurinta tana kokarin shiga dakin saiga Munirah ta fito cikin kuka kamar ranta zai fita” Wuce Aliya tayi dake kokarin tarar ta adaidai lokacin da Malam yasawo kai cikin gidan ta nufesaAbbanin kadaiga Amukarnin Sadiq yashiga har daki yai min duka ko? Lefi kikayi Munirah saiki gyara halin ki inba hakaba ke zakisha wahala wace kisa kayan kirki” Karan kukanta ta Kara wlh ban masa komai ba Amman ya biyoni har daki Ina bacci yamin duka ya tattake min nonona” Tsaki Malam yaja tare da wucewa dakinsa yana mejin kukanta tabbas dajin kukanta da yanayin ta tasha wahala saidai babu yadda za’ayi ya iya mgn akan wannan, da Alama kuresa ne tayi Haka taitama Ummanta kuka tun tana shareta har ta shiga rarrashin ta, ranar dakin Umman takwana kwata kwata basuyi baccin kirki ba dalilin wani zazzabi me zafi daya rufeta” Washegari da safe ta tashi da wani irin mugun haushi wadda baya rasa nasaba da sharri da Aliya ta Mata saidai bazata iya mgn agaban iyayen nasu ba domin suna son suga sunso junan su basa son fada a tsakanin su, haka taita Satan hararan Aliya kamar jira take 7am nayi tabar part din” *Cikin dare be samu bacci yada ya dace ba dan haka bayan ya dawo masallaci ya kwanta baccin daya daukeshi 10:30am sannan ya tashi, hasken daya gani sosai yasashi saurin tashi, kanshi tsaye ya nufa toilet wanka yayi sannan ya fito Saida ya gama gyara jikin shi tsaf cikin kananan kaya tare da feshe jikinsa da nau’in turaruka kala kala, kallon kansa yayi cikin madubi yai wani guntun murmushi sannan ya nufa Kan gado ya dauki wayarsa ya fice adakin” Motarsa ya shiga yayin daya kalli part din Malam afili yace aljana komai nata fari kamar fatalwa abun ko tsari babu tsaki yaja sannan ya fice agidan” Karan wayar sa yasashi saurin Mika hannu ya dauka Sagir ne bayan sun gama wayar yana kokarin ajewa ya hangi tarin missed call dake wayarsa kallon wayar yayi yayin dayaga 11 missed call duk daga Annanin sannan akwai Sako guda daya shima daga gareta cikin sauri ya gangara bakin hanya domin betaba ganin ta masa irin wannan kiran ba ko ta taba to baya iya tuna lakacin sakon ya bude kamar haka” aduk lokacin da sakona ya sameka karka Kara minti 5 bakazo ba, inason ganin ka” Fuskarsa dauke da mamaki ya fara kiranta saidai har yamata kira biyu bata daukaba dan haka kawai ya juya hancin motarsa zuwa gida yayin da yake sharara gudu dan ya isa akan lokaci” Minti 13 ya dauka ahanyar kafin ya isa Kai tsaye part din nasu ya wuce” Afalon ta ya sameta yayin dayai saurin rissinawa yagaidata amsawa tayi fuskarta adan hade kadan, kallonta ya sakeyi sannan yace lafiya kuwa banga kiranki da sakon ki ba Saida nai nisa da gida, Kuma nakira baki daga ba” Aicewa nayi kazo ba kakirani awaya ba” Eh daman zan gaya mikene nayi nisa minti 5 bazata kawoni gidaba Annanin, laifi nayi ne? Bakayi komai ba mushiga ciki, mikewa tayi ta nufi beatrom dinta yayin da yabi bayan ta yana me hadiye yawu domin ya fahimci akwai wani abun Annanin bata masa haka” Yana saka kansa cikin dakin ya hangi mutun kwance Kan gado yayin daya karasa cikin dakin ya fahimci Munirah ce dan haka yai saurin zuba hannun sa aljihu tare da hade fuska” Sadiq me Munirah ta maka har kamata irin wannan dukan? Kawar da kansa yayi tare da lashe leben sa” Dakai neke mgn” Daker ya bude baki yace yanzun dan tayi laifi namata hukunci harsai anturke ni akan haka ni daban ne agidan nan naga ai sunayi laifi Kuma Mubarak na hukuntasu ba’a taba turke kowa ba saini? Babu wadda yataba masu irin wannan dukan Sadiq, Kuma bantabajin ka dake wani ba acikin gidan nan akan me zaka fara akanta, haba mana itace karamar ku kashinta beyi kwari ba akan wani dalili zakasa wannan kwafceceyar kafar taka ka tottokare mata kirji, kasheta zaka yi?, Matsa ka taba jikinta kaji” Kallon gadon yayi tare da saurin kauda idonsa” Kataba jikinta kaji yadda zazzabi me zafi ya rufeta” Basai nataba ba, hade ransa yakarayi sosai” Inason kaji halin da take ciki ne ai” Bana bukata ni, badai kince karna kuma irin wannan ba, to ki gaya mata niba tsaranta bane ta kiyaye wannan, idan Kuma ta kara shiga gonata abun da zanmata wlh bazata gane hanyar kawu karata ba, hannunsa ya daga ya nuna ta cikin yaren buzanci yace daga yau sai yau idan nasake ganin ki a part dinan saina kikifa miki mari Juyawa yayi afusace yabar dakin idonsa jawur” Sosai mahaifiyar tasa ta zaro Ido afili tace watau fadan dana maka beyi amfani ba” Cikin sanyin ta zauna kusa da Munirah ahankali ta dafata, Munirah me kika masa ne? Umma Aliya ce takai mishi gulmata itace munafukar data hada komai” Aliyar ce Munafuka Munirah?, kinga wannan bakin naki shike wahalar dake, toh ni dakizo guna ki zagi Aliya ai gara ki zagi Sadiq din” Umma fah taki jinina shiyasa takaimashi gulmata dan tasan ishima yaki jinina, kumani duk wadda ya tsaneni nitsanar sa nake har abada sakko da kadarta tayi kasa tare da fadin tafiyata zanyi ma” A’a ki kwanta ki huta abun ki” Nibazan zauna ba, kema ai bawani fada kika mishi ba Kuma bakice mishi yabani hakuri ba kinaji yana cewa zai mare ni” A’a Munirah nifah kinga matsalata dake kenan kanin kine shi dazai baki hakuri, yayanki ne kuma yayi ba daidaiba namishi fada me kikeso Kuma” Cikin kuka Munirah tavar dakin yayin da ita ma Dattijowar ta nufi kitchen” Bayan sati daya ‘yan matan ne zaune Zaune afarfajiyar da aka tana dan shatawa tasu irin ta al’adan buzaye” Waka suke rairawa da bakin su sunayin rawar atare yayin da duk cikin su Munirah tafisu iya takawa, su kansu rawar tata burgesu take yayin da suke kokarin taka irin tata rawar” Duk abun da suke yayyen su maza na hangensu amma Sadiq saika rantse wani gurin yake kallo, Abba ne yace dan uwa dan Allah jiba kartan banza manya dasu Amman duk Munirah tafisu iya rawa” Cikin yaren buzanci Sadiq yace natsana yariyar can wlh, idonta soye yake bata da kunya” Shima Abba canza harce yayi nikuwa burgeni take tana da wayau da kanayin hira da ita zakasan haka” Wannan Kuma ai saikai” Amman ai kana mgn da Aliya” Mikewa yayi batare daya bada amsa ba yabar wajen” Rawa suke sosai batare da sun San Sagir din da Mubarak na kallon su ba, bayan minti 30 da tashin Sadiq ya dawo hannunsa dauke da wata Babban leda, wuce su Sagir yayi ya nufa gurin dasu Aliya ke shakatawa ta bayan su ya tsaya tare da lankwasa harcen sa yace Aliya” Juyowa tayi tare da Sakin murmushi” Shima murmushi yayi yana me binta da kallo” Ahankali ta karaso gaban shi kanta akasa tana wasa da hannunta fuskarta dauke da murmushi har yanzon yayin da shima yake binta da kallo yana me murmushi sosai” Sosai yanayin ya burge Lubbunah dan haka ta saki baki tana kallon su fuskanta itama cike da fara’a” Ledan dake hannun sa ya mikawa Aliya amsa tayi batare data kalleshi ba, muryarsa taji yana fadin, kin iya rawa Aliya” Dagowa tayi ta kalleshi, idonsa daya ya kashe eh sosai rawarki ta burgeni” Sunkuyar da kanta tayi ahankali tace nagode Amukarnin” Karki damu, yana kokarin juyawa yaga Lubbunah sai murmushi take, da hannun sa ya kirata tare da saka hannun sa aljihu yacciro kudinsa dake aljihun duka yamika mata gashi ku raba keda Aliya” Godiya muke Amukarnin???????????????? Juyawa yayi batare da yace komaiba” Lubbunah da Aliya kuwa komawa sukayi saidai wannan karon ba rawa sukayi ba zama sukayi akan katuwar darduman suka zube kudin” Lubbunah ce ta kirga 35k ne yayin da Lubbunah ta cire 5k ta aje agefe tana fadin muba Munirah wannan sai mu raba wannan biyu” Kallon Munirah Aliya tayi sannan tace murabasu daidai kawai Lubbunah” Jimmm Lubbunah tayi zuwa can tace gaskiya ni Ina bukatar kudi Kuma ai mu biyu yace, akwai wani takallmi da nake son saya 16k yake kinga saima kin ara min 1k Karasa kallon Munirah Aliya tayi data zauna saman kujera tana kallon can gefe kafarta daya Kan daya tana girgiza su” Dauke kanta tayi sannan tace da Lubbunah, shikenan kidauka saiki raba mana sauran biyu nida Munirah” Mikewa tayi cikin Jan tsaki Allah ya kyautaangaya muku ni matsiyaciyace kamar sa, niba mayya bace wlh aini bama kuba koshi yabani da kansa bazan amsaba, bashi da abun da zai bani, beyi arzikin da zaimin kautaba har yanzun ku gaya mishi ya Kara kaimi” Wucewa tayi fuuu tana rangwada yayin da Aliya ta bita da kallo cikin rashin Jin Dadi” Tana dafda shiga part dinsu Sagir ya fito yauwa Munirah nemanki nake daman me Sadiq ya bakune naga sai Murna kuke…… Sai Murna suke dai Amukarnin, ni bashi da abun da zai bani” Kama baki Sagir yayi tsabar mamakine ya kama shi, cikin Ido ya kalleta” Bashi da Abun da zai baki?? Toh me zaibani????? Amukarnin bece dani ba Kuma Allah nema ya taimakeshi bece dani din ba ni beyi arzikin dazai bani wani abu ba” Dariya Sagir yayi cikin ransa afili kuwa cewa yayi, wannan gaskiya ne Munirah, kudinsa din banza yanzun me kike so muje in saya miki” Ni banso bacci zani inyi” Yadda tai mgnr cikin sangarta da shagwaba yasashi ya karyar dakai cikin sigar lallashi yake fadin” Haba mana Munirah, kidaure muje ki zabi duk abun da ranki ke so, ko nima bani da arzikin da zan saya miki abu ki amsa?? Cikin shagwaba tace ni a’a nashi ne banso” Toh muje yanzun mudawo” Nidai saidai kaje Kai daya ka sawo min” Jimmm yayi sannan yace shikenan me kike so? Ni koma menene” Shikenan shiga ciki zan dawo yanzun” Juyawa yayi yayin da yaji Muryar Munirah tace, Amukarnin karka dade” Kar indade Kuma bayan nace muje kinki zuwa???????? ‘Yar dariya tayi batare data shirya ba sannan tace kazabo min abun da duk wadda yagani saiya rude” Banza yayi da ita yaciga da tafiyarsa, Munirah na kallon sa harya isa gaban motar sa ya bude ya shiga ya zauna sannan ya waigo ya harareta” Lumshe idonta tayi ta bude sannan tafara takawa cikin sauri harta isa gaban motar be kallota ba Kuma tasan yasan da zuwanta” Zagayawa tayi ta shiga ta zauna har yanzun fuskarsa hade take dan haka tadanyi Murmushi sannan tace, Amukarnin kana fah da kirki Kuma dan nace kaje ka sawo min saika kama fushi” Dauke kansa yayi tare da daura guiwan hannunsa Kan window motar cikin hade Kiran sama data kasa” Hannunta ta Mika takama bakin gemunsa dake gyare tsaf kan farar fatan gemunsa tadan ja kadan, tana fadin Amukarnin Sorry, cikin dariya take mgnr yayin daya kwace gemun nasa yana fadin bazan hakura ba sai munje tare” Ganin bazai saki ran nasa ba haka ta hakura suka tafi tare saidai kowa cikin fushi yake dan tunda suka kama hanya ta hade ranta” **** Aliya ce tsaye cikin dakin baccin su ita da Lubbunah, ledan da Sadiq yabata ta bude tare da fadin, Wow???????????????????? Gaskiya Amukarnin Sadiq ya iya zabe, riga tagani doguwa cancadediya milik colour daga kasa ta bude yayin da kwalliyarta yake gwanin ban sha’awa sai takalmi dogo me dankaran kyau tare da lafaya mekyau wadda ya shiga sukai matukar dacewa da rigar sai yanzun ta kulla Ashe rigar harda dogon wandota take dashi Wanda daga kasa ya matse, cikin dauki da murni ta tafi nunawa mahaifiyarta” Annanin kinga kayan da Amukarnin Sadiq ya saya mi???????????????? Kai Masha Allah Amukarnin ku ya burgeki gwada mugani” Dakin mahaifiyar tasu ta nufa ta cire rigar jikinta sannan ta bude zip din dake bayan rigar ta zurata, kokarin saka hannun take Amman yaki shiga ganin haka ta fito fallon tana fadin, Annanin ji inda rigar tamin” Kash wannan riga Aliya ai tai miki kadan maza jeki cire” Tura min zakiyi Annanin wlh Ina sonta” Mikewa Mahaifiyar tata tayi tafara kokarin Amman Ina tariga data Mata kadan, ganin haka Annanin tace, ai sai hakuri Aliya babyn robace ki daza’a kama atura kije ki cire saiki gaya masa ya mayar ya canzo wata idan anan kasar ya saya” Cikin sanyin jiki ta nufi dakin zuwa can ta fito da ledanr gaba daya tace gashi Annanin nabarwa Munirah takalmin ma yamin kadan duk abata” Masha Allah kin kuwa kauta Aliya Allah ya miki albarka” Ameen Annanin amman fah karki gaya mata nasan aka gaya mata Amukarnin Sadiq ne yabani wlh bazata saka ba” Murmushi Dattijiwar tayi sannan tace rabu da shirmamma” * Abbanin kaga kayan da Amukarnin Sagir ya saya min” Iyeeee ‘yar gatan yayyenta, sunyi kau, daman Ina neman ki, kifara shiri zuwa jibi da daddare zaku wuce Ingal insha Allahu” Alhamdulillah ya Allah, shirye nake Abbanin wannan kayan ma da Amukarnin Sagir ya saya min dasu zanyi tafiyar” Cikin murmushi mahaifiyarta tace ai gama wasu kayan dazon Khadija ta kawo miki, wurga Mata ledar tayi yayin da Munirah ta shiga warewa” Wow???????????????????????? Gaskiya Aunty Khadija naji dani daganin kayan nan ba akasarnan aka saya ba, zanje kasan da bantaba zuwa ba zan bude idona da sabon kaya sabon takalma masu zafi, barin je in nunawa Amukarnin Sagir” Falon tabar kayan yayin da ta nufi part din su Sagir, ta isa har dakin baccinsa, Amukarnin namance bangaya maka ba, wannan karon dani zasuje Agadez” Tashi yayi sosai ya zauna, a’a wannan karon mutum daya ne zaije” Narantse maka Abbanin yace dani za’aje Kuma jibi da dare zamu wuce, zan tafi sabon kasa wacce bantaba zuwa ba, cikin ‘yan’uwa na dangina, insaka sabbabin kayana da sabbin takalmana sannan in shiga cikin su inyi rawa in karkada kafaduna, Amukarnin zan hau doki sannan inyi busa Ina hurawa Ina rawa” Juyawa yayi ya kalleta cike da haushi sannan yace, waya gaya miki doki suke amfani dashi saidai kihau rakumi irin na waccen gidan wadda Sadiq ke hawa” Yauwa aishi nake nufi, ai yafi sama, so nake injini Asama Amukarni, ragumi na tafiya dani Ina rawa akansa” Kice dai kina son kije ki yaki mutanen Ingal?, an gaya miki akwai wani rawa da zakiyi ki yake su, koko so kike kije kina rawa wani yace yana son ki?, ni gaskiya vana goyon bayan wannan tafiyar” Dagowa tayi ta kalleshi suka hada Ido meyasa Amukarnin? Shiru yayi tare da kurawa waje daya Ido zuwa can yace Ina tsoron kar wani yace yana son ki???? Aini ba abun da yakaini kenan ba, Kuma ma duk ga yayyena sai suce ni suke so?, Ba wadda zan kula Amukarnin, bude idona kawai zanyi, nima inji amunda kukeji” Mikewa tayi cike da murna tabar wajen yayin da Sagir yabi bayanta da harara” * Enisilim kaine da kanka” Nine Sadiq, Kai din ne kanayin wuyar gani, nabawa mahaifiyar ka sako ta gaya maka akan tafiyar ka Ingal, nasamu lbrn sakon ya same ka Amman bakazo muyin mgnr ba” Kansa ya shafa cikin rasa abun fada” Shima kansa ya shafa tare da sunbatan goshin sa yace” Shikenan, yanzun Jibine tafiyar saika fara shiri” Tam Amman Annanin bata fada maka alfarman dana nema ba?? Mgnr kanason abokin tafiya ko? Eh Abbanin” Tagaya, munkuma samu mafita jibin zaku tafi ku biyu ne” Nagode Enisilim” Karka damu” Juya baya yayi yana kokarin fita Sadiq yace nidawa Zamuje ne?? Dawowa mutumin yayi da baya yace zaku tafi kaida Munirah” Jimmm Sadiq yayi tare da runtse idonsa da sauri, Abbanin kana nufin Tamudiriccin Munirah???Mmn Yazeed???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ PAGE 7- 8Typing……????️ Eh tare zakuyi tafiyar zata maka rakiya” A,a Abbanin banso irin wannan tafiyar ba irin wadda zanyi da Tamudiriccin bane, musamman ma ita Munirah” Jimmm mutumin yayi zuwa can yace, da Munirah zakayi tafiyar dalilin bata taba zuwa ba” Shiru yayi har mutumin ya fita be dago kansa ba, komawa yayi ya kwanta tare da rufe idon sa” Baccin ne yaki daukan sa dan haka yasauke kafarsa tare da daukan waya ya Kira Sagir ya sanar dashi son ganin su da yake shida Mubarak, cikin kanganin lokaci sai gasu cikin shirin bacci alamar sun kwanta” Lafiya kuwa irin wannan kira haka? Enisilim ne yazu min da wata mgn , nagaji da irin wannan abun da ake min, nadauki hutu ne dan in dan huta, amman antura ni Agadez, duk wannan Kuma be ishe suba yanzun Kuma Wai da Munirah zanyi tafiyar” Sagir ne yace aikai kace kana neman abokin tafiya, gashinan ka samu ai” Ai danace haka cikin ku nake nufi, ba ahadani da Tamudiriccin ba, banson yariyar kwata kwata idan tana kusa dani raina bacci zai rinka yi” Mubarak ne yayi ajiyan zuciya sannan yace meye aciki, ni in nine tafiyan zanyi da ita tamin iskanci in karkaryata in barta ahanya” Abarta ahanya Kuma?, Sagir yayi tambayan yana mebin Mubarak da kallo” Eh ‘yar iskar yariya ce da kuke ganinta da wasu idonta ficifici” Idonta ba ficifici bane Mubarak, ku daina nuna tsanawa yariyar nan mana, haba dan Allah, meyasa duk kuka tsaneta wai, ni banson ta da tafiyar ma, duk yadda zanyi in hanata tafiyar saina yi bazata je ba, kaikaje tunda baku son ganin ta” Toh waike meye naka da antada zancen Munirah ka dinga wani kunbure kunbure kana tada jijiyoyin wuya? Kanwata ce” A’a wlh dadai wata akasa” Kamar me musali?? Sonta kake” Laifine idan nasota? Ba laifi bane amman Kuma anji kunya ” Meye abun kunyar, bata da martabar da zan sotane?, Ka gaya min meye wata ‘ya mace zata nuna mata? Wata irin muguwar dariya Sadiq ya fashe da ita wadda basu taba ganin yayita ba tare da bin Sagir da kallo, Mubarak ma dariya yasaka tare da fadin yau abun boye ya fito fili” Kafa Sagir yasa ya hanbare Sadiq da haryanzun dariya yake batare dayace komai ba, saurin kaucewa yayi yayin da bebar dariyar ba idonsa harda hawaye dan dariya” Sosai Sagir ya kule bana wasaba dan haka yahau gadon yana mekai masu duka, Mubarak ramawa ya shigayi yayin Sadiq ke takurewa waje daya yana cin dariyarsa har yanzun” Sosai sukaci uban gadon tare da tattake shi kartin maza gamza gamza har uku kowanne cikin su baya ragawa gadon, sauka kan gadon Sadiq yayi tare da ficewa adakin” Bayan kusan binti 30 ya dawo da alama wanka yayi goran ruwa ahannun shi yana kurba tare da ajiyan zuciya” Kwance ya samu Mubarak Kan gadonsa yayin da Sagir ya fito wanka yana goge jikinsa” Murmushi Sadiq yayi bayan ya kalli Sagir yace, Sagir kace wannan karon ‘yar gida za’ayi mun huta zuwa Agadez dauko amarya” Riga Sagir din kisawa yana fadin eh din, tahowa yayi ya amsa ruwan hannun Sadiq sannan ya zaga bayan Mubarak ya kwanta shikuwa tuni bacci yafara daukan shi” Kuna nufin anan zaku kwana? Gashi kuwa kana gani” Toh ni in kwanta aina? Akan mu Sagir yabashi amsa” Tsaki Sadiq yaja tare da fadin Amman gaskiya zaku takura min wlh” Can kurya ya kwanta yana mecigaba da tsaki Washegari tun a masallaci ya nemi Sagir da Mubarak ya rasa dan haka shikadai yadawo dakin sa” Bacci ya koma yayin da ya daukeshi har 11:00am bayan ya tashi wanka yayi cikin shirin zuwa daukan karatu ya fito, tun kafin ya isa gurin kowa ya hallara dan haka yana dosan wajen kallon ya dawo gurin sa” Shikuwa Sadiq sosai yanayin ya burgeshi yayin da akoda yaushe yake alfahari da gidan nasu, ko kadan basu yada al’adarsu ba kusan dukkan su suna girmama yaren su tare da alfahari dashi aduk inda suke” Daga gashiga Babban gate din gidan nasu zaka tabbatar da gidan buzayene ka shigo, yayin da daga gefen dama akayi ginin kasa irin ginin da suke amfani dashi a Agadez gefen hagu kuwa gine gine ne masu zafi irin na zamani Kashi kashi, gida ne Babba sosai na ban Mamaki tare da manyan motoci masu dumi jere rairas acikin wannan gida, Akwai Babban masallaci acikin wannan gida wadda yake farkon shiga gate din wannan gidan daga ban garen dama wadda aka yishi da bulon kasa domin su anasu al’dar sunfi darajasa duk arzikin wani me arziki a Agadez zaiyi wuya kaga ya guji ginin kasa dan haka dashi sukayi yawancin gine ginen dake da mahimmanci agurin su kamar masallaci da gurin da suke daukan karatu sannan farfajiyar da suke gudanar da sagulgulan su na gargajiya tare da gurin Shan iska sune ginin da akayi da bulon kasa irin ginin Agadez” Sosai abun ya bada ma’ana yayin da gidan nasu yake daukan hankalin jama’ar unguwan domin kuwa dayawan su suna baro mayan masallatai sutahu nan Sallah saboda burgesu da masallacin keyi, haka Kuma jama’a nayawan kawo bakin su har suyita daukan photo acikin gidan bangaren al’darsu dakuma ginin su a zamanance” Part din Sadiq ne kadai anan gefen da ginin kasan yake yayin da yazama acan karshi soboda be fiye son hayaniya ba, tun zuwansu Nigeria aka fitar masa da gefen sa lokacin yana da shekara goma aduniya” Mahaifin Sadiq shine na biyu agidan su yayin da yake da Babban yayan su wadda tun yana Samar taka kasuwanci ya dawo dashi Nigeria yayin da ya dauko matarsa ya taho da ita wadda itama haifafiyar yar Agadez ce cikin wani gari da ake Kira Ingall wadda Suma duk haifaffun can din ne, anan Nigeria suka haifi yaran su biyu Mubarak da Lubbuna mahaifin su Alhaji Mustapha yana tsananin basu kulawa ta musamman” Shikuwa mahaifin Sadiq irin sana’ar Alhaji Mustapha yake wato sayarda gwalagalai tare da kanin su jafar inda daga baya yayan su ya bukaci dasu dawo Nigeria su gudar da sana’arsu tare, ran mahaifiyar su beso ba amman tanason hadin Kan yaranta dan haka ta hakura, bayan kasuwanci ya kankama duk suka kwaso iyalan su, yayin da Sadiq yafi sukkan su girma, mahaifiyar Lubbunah da Mubarak Hajiya Murja itace Babba agidan, Hajiya Fatima ke bimata wadda itace mahaifiyar Sadiq da Sagir wadda take Mata ga Alhaji Abubakar sai Hajiya Aisha itama yaranta biyu ayanzun Aliya da Munirah, yayin da Mahaifin Aliya da Munirah yafi shahara bangaren malumta ayanzun shahararren malamine wannan Garin Abuja dakewayenta suke alfahari dashi, wadda sukewa lakabi da shak Jafar wannan shahararren family suna zaune ne a Abuja Nigeria yayin da mahaifan su da dangin su gaba daya ke zaune Agadez cikin Ingall tun asalin su sun gada arzik,i kudi, gonaki, zinarai dakuma arzikin raguma acikin arziki suka taso yayin da iyayen Suma cikinta suka taso dan haka basu San wani abu talauci ba, haka Kuma suna da ilimi na zamani yanzun Kuma suma sun koyarwa yaransu neman illimi na addini da Kuma nazamani” Ayanzun haka banda Aliya da Munirah duk sun kammala karatun su aiki suke inda Lubbunah ke aiki agidan ridio nan cikin Abuja Mubarak kuwa babban likitane dake aiki karkashin gwamnati, Sagir Kuma ma’aikaci ne a ma’akatar wutar latarki ta kasa, shikuwa Sadiq ma’aikacin bankine wadda yake rike da mukamin Personal financial advisers” Ayanzun dai Aliya da Munirah ne ke kokarin kammala karatun, yayin da Aliya ke bangaren kiyon lafiya, Munirah ke karanta lawyer” Wannan kenan, Abangaren sauran kannan Shak Jafar Mata kuwa su Uku ne, idan an hada su shidda kenan, duk suna Agadez da iyalan su illah yar kanwarsu Khadija da suka rike anan Abuja har suka aurar da ita, wadda ayanzun yaranta biyu da mijinta bafulatanin Sali da suka hadu nan cikin garin Abuja” *Muyar malam yaji cikin kunnensa yana fadin Sadiq meke damuna ka? Dawowa yayi daga dogon tunanin da yayi tare da fadin bakomaii” Tabe baki malam yayi sannan yace karufe mana da addu’a Kallon gurin yayi yaga ashe har anyi karatun angama gyaran muyar yayi sannan ya bude baki ya fagatar da addu’a Malam ne ya fara mikewa sannan Sadiq din” Hango Munirah yayi tanata murna tare da yawan kallonsa da alama yau cikin farin cikin take Kuma sai Satan kallon sa take tana murmushi” Malam ne ya daga murya yace Sadiq kana shiri kuwa? Eh Enisilim inayi Yayi kau ” Part dinsu ya nufa yayin da Aliya da Munirah kebinsa abaya” Sagir ne ya kalleshi yace, Sadiq tunanin me kake har malam yayi maka tambaya har uku hankalin ka gaba daya baya gun karatun” Nidin? Kai kuwa, bayan yamaka tambayan har sau uku baka amsa ba sai Munirah ta daga hannu” Tsayawa Sadiq yayi cak, Munirah Kuma??? Eh Munirah” Ta amsa din Kuma? Ta amsa” Tunawa yayi da irin kallon da take mishi dan haka ya tsaya tare da juyawa ya kalli part din su dasuka shiga yanzunan, jinjina kansa yayi sannan yawuce cikin sauri yabar Sagir agurin Tun dawowan su daga karatu Munirah ta hada kayanta cikin manya manyan akwatuna har biyu yayin da mahaiyarsu tasaya mata tsarabar da zatai tafiyar dashi” Gaba daya gidan tagama karadeshi da lbrin tafiyarta yayin da kowa na cikin gidan ke fadin Ingall zasuyi Babban bakuwa wacce basu taba yiba” Misalin Karfe 5:12pm Munirah ce zaune gaban Hajiya Fatima tana fadin, Umma idan muka isa gobe abu na farko dazan farayi hawa Rakumin, kinsan niko Rakumin wa zan hau?? Sai kin fada” Rakumin Tsoho” Toh ai indai wannan ne Sadiq ya rigaki hawa tun yana karami rakumin tsoho yake hawa kuma har gobe yaje saiya hau” Toh aikuwa danahau yabar Kara hawanta, Wai ku gidan nan kuna bani mamaki komai sai ace Sadiq, Sadiq, Sadiq Sadiq baku da mgn sai tasa Kuma kowa, kodai ya asirance ku ne? Dariya Hajiya Fatima tayi yayin da Munirah tace Allah kuwa balakin haushi abun ke bani” Ingaya miki Dalili Munirah?, Sabo da shine jikansu na farko ya shiga ransu sosai” Tabe baki tayi cafdi, dan basu sanni bane, da sun ganni sunbar Kara son shi, himmm wlh Umma harna kosa gobe tayi, inganni Ina shiga cikin Agadez jinafa zanyi Ina zillo Umma” Dole kiji kina zillo tunda ke mazarice” Saurin juyawa tayi bayanta Sagir ne fuskarsa ahade” Annanin ki fada mata saidai ta koyo rawa acan badai ta yake su ba” Anya kuwa Sagir tafa iya rawar tamu, kasan yar nagada ce” Idonsa ya kittawa Annanin tasa yayin datai saurin kawar da idonta tana fadin” Anya kuwa Sagir ba kishi kake ba? Cikin sauri ya shafa kansa tare da saurin juyawa yabar falon” Hajiya Fatima maida kallonta tayi gun Munirah, Munirah toh kodai ‘yar gida za’ayi ne keda Sagir? Saurin kallon bayan Sagir din Munirah tayi adaidai lokacin daya bugu kofar dan haka Munirah tace” Wlh Umma kin bashi kunya” Toh tunda gaki basai ki gaya min ba” Mikewa Munirah tayi cikin yarensu take fadin bara na tambayoshi nadawo” Dariya Hajiya Fatima tayi itama cikin yaren nasu tace ja’ira” Aliya bakisan gobe zani Agadez ba? Kanta akasa tace nasani” Amman shine bakizo muyi sallama ba har saida nakiraki da kaina” Naso nazo Amukarnin sai Kuma nayi tunanin karna takura maka” Jimmm yayi sannan ya mika hannunsa ya rike nata, ni baki taba takura min ba Aliya kuma inajin dadin yadda kike nuna girmamawan ki agareni duk kinfi yaran gidan hankali” Sosai kunyarsa ta rufeta yanayin dakin su biyu kawai yasata Jin wani irin yanayin, dan haka tai saurin zame hannunta” Hannun nata yabi da kallo sannan yace kayana Zaki hada min” Cikin sauri tafara hada masa kayan, domin tasaba hada masa kayan aduk lokaci da zaiyi tafiya saidai wannan karon ya tsora mata Ido sabanin da dayake bada Umarni kawai ya fice” Hartagama tanaji ajikinta kallonta yake ahankali ta waigo domin tabbatar wa kanta ko kallon nata yake yi” Ido biyu sukayi ya daura kafa daya Kan daya yana me mata wanni irin kallo” Banson kallo yafada batare daya cire idon nasa akantaba, saurin juyawa tayi tana hada kayan tana fadin, kazauna ka zubamin Ido Amman ni kana cemin bakason kallo, murmushi tayi zuwa can ta sake juyawa” Nadai Gaya miki banson kallo ko? Juyawa tayi tare da gimtse dariyarta, mikewa yayi ya fice yayin da Aliya tabishi da kallo sannan tayi dariya tana fadin, karfin hali” Wai Abbanin meyasa bazamuyi tafiyar da safe ba wata tafiyace Kuma da daddare saikace ‘yan fashi???? Dariya mahaifin nata yayi batare daya shirya ba baki da dama Munirah, to waya sani ko Dan fashin ne haka yakeyi shi baya tafiya Saida daddare yama riga ya Saba” Lumshi Ido tayi Yauwa Abbanin nidawa zamu?? Au Mamanki bata gaya miki ba?, Zaku tafi dare da yayanku Sadiq” ???????????????????????? Abbanin, nida Amukarnin Sadiq? Eh daman yayi korafin bayason tafiyar shi daya, amman banda rashin ji kinsan shi bayason hayaniya” Yadda gabanta ke bugawa yasa jikinta ya fara rawa, aini Abbanin indai dashi ne bazani ba” Meyasa?? Nidai wani lokacin zanje kubarshi kawai yai tafiyarsa” Ai nariga nagaya musu zuwan ki sunata murna kusan ma sunfi murna da zuwan naki dan basu taba ganin ki ba dan haka dole kije har biki suka shirya wadda za’a gabatar dazaran Kun isa dan haka kicigaba da shiri” Kwallah ne suka shiga ziraro mata layi bibbiyu tare dajin wani mugun tashin hankali irin wadda Bata tabajin sa ba???????????? cikin yaren su tare da shashshekar kuka tace, Abbanin tafiya nida Amukarnin Sadiq har Ingall mu biyu kadai……Mmn Yazeed???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ Page 9-11Typing……????️Wai har kuka kike ne?, Toh da dawa kikayi tunanin zakiyi tafiyar? Abbanin nina zata acikin kune zan tafi da wani????” Jimmm malam yayi zuwa can yace” Kije kici goba da shiri gobe zakuyi tafiyar, ni banga abun tashin hankali ba” Abbanin daman dai da Amukarnin Sagir ne” Duk dayane Munirah, Sadiq ma ai yafi Sagir kirki bedai son hayaniya ne” Cikin kwalkwal da Ido tace danasani ma bance zani ba” Hawaye take sharewa yayin da Mahaifin nata yake fadin danasani keya ce Munirah, nidai nagaya miki kicigaba da shiri” Miewa tayi tana me share hawaye tuni ta shiga hankalinta duk rawan kannan babu ita tana tafe zuwa dakin mahaifiyarta Banda tunani babu abun da take, tare da share hawayen data kasa tsaidasu” Koda ta shiga dakin Annaninta tasamu zaune Kan sallaya, yayin data zauna tasa dagumi” Waigowa mahaifiyar tata tayi ta kalleta, sosai damuwar da take ciki yaki boyowa kwalla ke taruwa tana maidasu” Addu’a mahaifiyar tata tashafa sannan ta bita da kallo, Munirah meke damun ki? Dagowa tayi ta kalleta idonta jawur yayin da tana bude baki kuka ya kwace Mata, Annanin kinji Wai ni da Sadiq zamu tafi tare mu biyu kawai” Jimmm tayi sannan tace toh Munirah dan wannan kika data hankalin ki?, Sadiq ai dan’uwanki ne, wani abu ne dan tafiya ta hadaku tare, shifah idan ba shiga harkansa kikayi ba baruwan shi dake, ko wani abu kika masa ma da wuya yayi mgn sai dai in kureshi kikayi irin na kwanaki daya biyoki har daki ya daka” Annanin nifa ko bazai dakan ba banson ganin shi, ko kallon mutum beye saidai kika yana wani rurrufe Ido kamar tsohon munafuki” Duka mahaifiyar tata takai Mata yayin datai saurin kaucewa, cikin bacin rai mahaifiyar tata ke fadin” Sadiq din ne munafuki ko?? Girgiza kai tayi a”a Annanin ni mancewa nake bansan nafada ba” Shiru tayi tana binta da kallo zuwa can tace, Munirah ni har rasa inda zanyi dake nake, yaron nan ba sa’anki bane, amman saikice masa Sadiq babu wani girmamawa, yanzun Kuma abun yayi kamari munafukine ma gaba daya ko? A’a Annanin cewa nayi fah kamar Munafuki” Baki mahaifiyar tata takama sannan tace tashi kibani guri tundake bakijin mgn” Annanin nabari toh” A’a karki bari jikin ki ko nawa, kicigaba dan Allah karki fasa ,mikewa yayi tabarta agurin” Itako munira ta kasa zaune ta kasa tsaye misalin 8:30pm ta nufi part din Hajiya Fatima inda Kai tsaye ta nufi dakin Su Sagir sanin datayi shida Mubarak suke kwana wajen yasa bata cika son zuwa ba, dan haka yanzun ma tura kofar tayi ahankali, ganin Bata hango kowaba ta tura kanta, Ido biyu sukayi da Mubarak yayin datai saurin komawa da baya” Zonan dan Ubanki” Cikin sauri ta koma tana me fadin, Ina wuni Amukarnin Mubarak” Munafuka kawai da ai bakiyi niyar gaisheni ba” Ni da bansan da mutun bane shiyasa” Bakisan da mutum ba kika shigo me kikazo yi anan? Nazo neman Amukarnin Sagir ne” Aifah, shine Zaki lekoni ki koma dan ke ke baki da hankali ko, toh me Zaki mishi? Zan gaya mishine gobe zamu tafi, Shirin kukan dayaga tanayi yasashi fadin” Toh jeki anji Allah ya kiyaye hanya idan yadawo zan gaya mishi” Tana juyawa ta maida hawayenta yayin da tana isa falon ta waigo ta kalli bayanta tare da fadin banza kawai” Cikin sauri tabar part din tana tafe tana waiwayen bayanta” Kasa cin abinci tayi ranar tunaninta yadda za’a tayi tafiya ita da Sadiq kadai, wata alaka Bata taba hadasu ba bare Kuma har ta shiga motar sa” Haka cikin darema kasa bacci tayi idonta biyu har gari ya waye” Saida mahaifiyar tata ta tsaya akanta sannan ta iya karyawa yayin da Aliya ke Satan kallonta tana dariya domin tasan bazai wuce tsoro bane ke damun ta” Meye kike wani Satan kallona???? Dariya Aliya tayi sannan tace, cewa nayi ashedai kina tsoron shi…… Ni banwani Jin tsoron shi, Ina ruwana dashi, yadai sake ya cuceni ne dole nace mishi Allah ya isa, ko acikin raina ne” Dariya Aliya ta sake kwashewa dashi sannan tace” Wlh kinajin tsoron shi, idan ba hakaba mezaisa ki rude har ki kasa cin abinci? Tsaki Munirah taja ai kina shiri dashi tunda kina shishshige mishi, ki gaya mishi nace banjin tsoron shi iyaka dai duka ko?, to ki gaya mishi duk sanda ya saka hannu ko kafarsa ya dakan ban yafe ba, ko aka zallicini Allah ya isa, ko ban bude baki bafada ba, Kuma tafiya zanyi dashi dole, tunda shi ba Allah bane, bashi da wuta bashi da aljannah….. Cikin tsawa Mahaifiyar tasu tace Munirah, wato kedai kunnen Kashi gare ki ko? Turbune fuska tayi, Annanin fah na aiki moda ne ta gayawa randa” Ran Aliya abace tace moda bazata gayawa randa ba dan ubanki,q idan kin matsu kije ki gaya mishi” Mikewa Munirah tayi tana nufar dakinta tana fadin kanki kika zaga ai” Sosai ran Aliya ya baci mikewa tayi zata bita Hajiya tace yi hakuri Aliya rabu da ita” Gobe war haka kuna Agadez, Mubarak ne yayi mgnr yayin da Sagir yace ai gobe akwai manyan baki” Sadiq ko bece komai ba dañna wayarsa kawai yake yi” Kasan kuwa jiya da daddare tazo neman ka fah” Haba dan Allah toh me yahana ka gaya min” Mancewa nayi, Kuma na tambayeta tace tazo maka sallama ne, shine nace anji Allah ya tsare zan gaya maka” Tsaki Sagir yaja tare da mikewa yana fadin barin ganta” Katuro min Aliya, yaji Sadiq ya fada kallonsa kawai yayi sannan yacigaba da tafiya batare dayace komai ba” Bajimawa saiga Aliya ta taho tun kafin ta karaso Sadiq ya mike ya fara kokarin shiga falon sa yayin da Aliya tabi bayan sa tanawa Mubarak sannu” Hannu ya daga Mata yayin da bayan ta wuce tunani barkatai ya shiga yawo azuciyar Mubarak domin kuwa gani yake kamar shima Sadiq son Aliya yake yi” Mikewa yayi yabar wajen yana me cigaba da nazari” Idon Aliya akasa batare data dago ba tace” Amukarnin Kai saikace baka son kallo ni Kuma sai kaita kallo na” Idon ki ke ganin kamar ke nake kallo Aliya Amman ni abun da nake kallo daban kalli can kigani” Wani dan kyakyawan kejin tsontsaye dake dauke da tsotsaye kusan 15 kowanne launin sa daban ya nuna mata, ni kinga abun da nake kallo can idan Kuma baki yadda ba ki dauko ki dawo dashi kusa dani kikani nima gani zanyi kamar ni kike kallo” Mikewa tayi da sauri ta dauko ta dawo shi kusa dashi yayin data koma wajen zamanta, cikin sauri tace Amukarnin fada fah suke yi, Kuma kamar daya suka tararwa” Kedai yita kallo har kiga yadda abun zai kaya, tagumi kuwa tasa tare da zubawa tsun tsayen Ido shikuwa zaman shi ya gyara yayin daya zubawa Aliya Ido, kamar me kallon mudubi saidai shi idonsa alumshe yake Kuma lokaci bayan lokacin yana lasan lebensa tare da hadiyan yawu” Kusan awa daya ta kwasa batare data sani ba, haka shima Sadiq har yanzun bebar kallonta ba, ajikinta taji dan haka tai saurin juyowa suka hada Ido kasa cire idonsa yayi saidai ita kunya ta kamata ta sunkuyar da kanta tare da mikewa ta nufi kofa” Tsaya Aliya taji ya fada” Tsayawa tayi ta juyo ta kalleshi yayin daya mike ya fara takowa gurinta” Acikin wata irin murya wadda bata sanshi da itaba yace” Anjima zan wuce me zaki bani intafi dashi matsayin tsaraba” Cikin rashin fahimta tace bani da komai Amukarnin idan Kuma kasan ina dashi ka tuna min” Ke baki sani ba bareni Kuma, hannunsa ya Mika Mata tare da fadin” Mugaisa Jimmm tayi cikin yanayin tunani Amman tasan be dauki gaisawa da mace abakin komai ba dan tasha ganin yana gaisawa da mata dan haka ta Mika hannun nata” Runtsewa yayi tare da lumshe idonsa, ahankali ta dago ta kalleshi ganin inda ya lumshe idon sa wani tunani ya darsu aranta dan haka ta fara kokarin janye hannunta” Jinda yayi tana kokarin zamewa yasashi kare riketa dakyau tare da jawota ta fada Kan faffadan kirjinsa, hannunsa yasa ya rungumeta dakau yayin da tsoro da fargaba suka Kara shiga ranta” Jitayi ya sausauta rukon dan haka tai saurin jaye kanta yayin daya hade ransa tamau kamar bashi yai mgn yanzun fuskarsa sake ba, gashi lokaci daya ya mayar ya dinke” Wanni irin kallo ya Mata me kama da harara daker ya bude bakinsa yace baki da kwari ko?, Daga dan tabaki saiki fado kaina? Amukarnin kaifa kajani” Komawa yayi ya zauna ya daura kafa daya Kan daya badaiki da kwari, injaki in kaiki Ina? Kallonsa tayi ta sunkuyar dakai zuwa can tace intafi? Jeki mana, abun da ya fada kenan ya fara dannan wayarsa” Juyawa tayi yayin da takejin wanni irin nishadi cikin ranta sosai Amukarnin Sadiq ke burgeta dan haka har yanzu baza hancinta take wani irin kamshin sa me dadi takeji cikin jikinta” Tana shiga falon su cikin fada mahaifiyar tata tace daga Ina kike? Annanin Amukarnin Sadiq ne ya kirani” Bangane ba Aliya, Wai akwai wani abu tsakanin kune?? A’a Annanin babu komai fah cewa yayi in hada masa kayan sa” Jimmmm Annanin tata tayi zuwa can tace wuce kibani guri” *Sadiq ve samu ganin Munirah ba Saida yamma lokacin dayaje nemanta wanka take yana baro part din Kuma ya fice be dawo ma sai yamma dan haka ita ya fara nema a part dinsu ya sameta tana kwance jikin Annaninta idonta rufe Amman tanajin muryar Sagir ta bude idonta” Amukarnin da bakazo bako hmmmm Me zakimin idan banzo ba din, aiki dasai kizo part din mu” Ai nazo jiya akamin jaraba” Murmushi yayi, yayin da Annanin tai saurin mikewa tabar wajen” Amukarnin Wai Ashe da Sadiq zamutafi Kuma tare?????? Eh aishiyasa tun farko naso na hanaki zuwa” Aida kagayamin dashi zani, wlh bazani ba ko sama da kasa zata hade, Amman yanzun Abbanin yace dole sai naje” Yayi daidai ai, dole kidan nutsu dan idan kinmai rawan Kai zakisha wahala” Ainayi Allah ya isa Amukarnin ko kallona yayi ya rufe Ido Allah ya isa” Subuhanallahi, Munirah?, Meyasa bakyajin mgn ne? Nifa wlh inajin mgn, kuma ni duk abun da nake Ina sane nake yi, jina da nashine beyi daidai ba, da zai mutu danaso” Idan wasa kike ki daina, banason irin wannan mgnr, ke kike haukan ki, be damu dake ba Kuma idan kin tsaneshi ni kika tsana, hakama idan kinso ya mutu, banajin dadin kalaman ki akan shi” Saboda dan uwankane ko?? Eh haka din ne, ke yanzun zakiji dadi ince natsana Aliya, dazata mutu danaso? Toh kace mana, inaruwana da ita ni, ai itama munafukace” Dariya ne ya subuce masa batare daya shirya ba wani irin kallo ya mata sannan yace Allah ya shirye ki Munirah” Juyawa tayi ta hade rai sosai kamar zatayi kuka” Kara matsawa yayi kusa da ita me Kuma ya faru Munee” Bakai bane fara min masifa akan wani can daban” Lumshi Ido yayi fuskar shi dauke da murmushi, sosai yake son ganin shagwabar ta saidai Kuma beson baccin ranta dan haka yace” Toh kiyi hakuri kinji? Kara turo baki tayi nikatafi kawai” Haba Munirah ta kinason mu rabu ahaka ne? Toh sai me ni Ina ruwana? Ni da ruwana Munirah, bazan ji Dadi ba, da daddare zan kasa bacci” Bawani nan” Allah da gaske nake, ko munrabu kina murmushi yau daker zan iya bacci bare mun ramu kina fushi dani” Toh bakai me dan uwa ba” Nabari ai ki saki ranki” Toh dani dashi wakafi so? Nafi sonki yayama za’ayi a hada, murmushin dataga yanayi yasata itama ta saki murmushi tare da fadin” Wai dashi zamu tafi, ni bantaba zama kusa dashiba’ bare har muyi tafiya me nisa dashi hade rai tayi tare dayin kwal kwal da idonta” Babu abun da zai faru, na tabbatar idan bakice mishi ba bazai ce miki ba, kidai kiyayi bakin ki kawai, Kuma ai baku kadai zaku tafi ba Sadiq yace zai tafi da driver sa *Anass* Wow Alhamdulillah kaga zanyi hirata da Anass har kasa naji sanyi” Himmm Munirah kenan kidaibi ahankali, Anass driver ne kawai Kuma shima gidansu zai wuce sai Sadiq ya bukaci ganinsa zaizo Sadiq kuwa gida daya zaku zauna” Duk da haka dai da Dan sauki kaga ko banza bakina bazaiyi wari ba” Dariya sosai Sagir yayi tare da jinjina kansa” Ji yayi kamar karya barta dole yamike saboda Kiran sallar mangariba dayaji anayi yayin da Munirah ta wuce domin yin wankan tafiya” Wanka tayi ta fito, yau da Aliya da Lubbunah duk suna dakin Munirah, yayin data shirya cikin kananan kaya farar riga me dogon hannu da farin sakita yayin data yane jikinta da jan lafaya sosai tai kyau tare da haskawa kana hangen bakin gashin ta dake sheki yana daukan ido” Dogon takalmi tasa daya Kara fito da wankanta Annanin ce ta shigo ganin Munirah tas tace dakyau auta ta, kinganki kuwa? Annanin son kuwa kin wadda ya rasa ko? Sosaima, ai kinfi kowa agidan nan kau” Da gaske Annanin har mazan? Mazan banza” Murnace ta kamata yayin data rungumi Annanin” Tuni aka fitar da kayanta itama Kira kawai take jira karfe 8:00pm Malam ya Kira mahaifiyarta awaya cewa Munirah ta fito” Gaba daya suka fito, Annanin Aliya da Lubbunah sai Munirah dake rike cikin hannun mahaifiyarta, tun aharabar gidan jikin su duk yai sanyi domin ganin direbubin gidan sukayi kowa cikin shirin fita yayin da motoci fin 10 ake kokarin fita datasu” Annanin kuwa tana shiga Babban falon wan mijin nata jikinta ya Kara sanyi, kowa na gidan yana gurin, Sadiq ta hanga kusa da mahaifinsa cikin kananan kaya, Bari karrr, gashin sa kwance lufluf yana shike da daukan ido, wandon sa ya wuce guiwa yayin daya matse daga kasa, hakama takalmin sa fari tass tare da agogon dake daure a hannunsa” Sau daya Munirah ta kalleshi cikin ranta tace ko kyau, halan kwallo zai buga” Agogon hannunsa ya kallah batare daya kalli kowa ba yace Abbanin jirginmu 10:00pm zai tashi” Mikewa akayi gaba daya akayo waje yayin da kowa ya nufi motarsa” Kusan kabadaya gidan suka fito domin musu rakiya zuwa filin jirgin, sosai jikin Munirah yai sanyi Sam Bata zaci hakaba yanzun sai take ganin kamar lahira ake rakata ita da Annanin kadai amotar dan haka ta fara kuka, Annanin zan dawo kuwa sai Ina ga kamar bangon duniya zani” Karki karyan mun da guiwa Munirah duk yaran gidan nan da kike gani sunje Kuma sun dawo lafiya babu abun da zai faru insha Allah, kidai kiyi addu’a, kishiga cikin ‘yan uwanki kinji ko, karki kyamaci kowa, kishiga cikin kowacce al’da tasu zasuji dadi ko baki iyaba kiyi iya bakin kokarin ki, sannan kici duk wani irin nau’in abinci, zanyi farin ciki da haka, abu nakarshe da zan rokeki karkiyiwa yayan ku rashin kunya, dan Allah Munirah ba sa’anki bane, lokacin da aka haifeshi ko Aliya ba asan za’a haifa ba bareke, ki lura dakyau acen suna girmamashi fiye da tunanin ki karkisa amiki kallon rashin tarbiya dan Allah Munirah” Kanta ta daga cikin kuka sosai, tsoro be Kara kamataba Saida suka isa filin jirgin, hasken fitulo kawai take gani kamar rana, yayin da take ganin kowa na sakkowa cikin motar lokacin har matafiyan sun fara shiga cikin jirgin lokacin da suka iso Anass ma tuni yana ciki, dan haka Suma cikin sauri sauri sukayi sallama gaba Sadiq yayi bayan yayi sallama da kowa yana kokarin hayewa jirgin Sagir ya kirashi ganin inda Munirah take dari dari dalilin Bata Saba ba” Waigowa yayi yayin da yai masa nuni da Munirah” Juyawa yayi yacigaba da tafiya batare dayace komai ba” Ganin haka Mahaifin sa ya sake Kiran sa, tsayawa yayi yayin daya rike hannun Munirah yayi masa nuni daya rike hannunta” Cak ya tsaya har Munirah ta karaso wajen da hannunsa yayi Mata alamar tada shiga gaban sa cikin sauri ta wuce yayin daya bita abaya yana me takawa da sauri dan haka itama dole ta Kara sauri dan gani take kamar so yake ya taketa” Saida suka tabbatar da tashin su sannan suka kama hanyar gida, yayin da Abbanin ya buga waya domin sanar dasu tasowan bakin su” Tun acikin daren kakansu wadda suke Kira tsohu ya hada masu tafiya taryo su, yayin da wasu zasuje da motoci falin jirgin wasu Kuma zasu jirasu a mahada tare da raguma, tun alokacin suka fara fara tafiya domin tafiya ce me tsayo kafin suzo gari……. Mmn Yazeed???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/Page 12- 14Typing…..????️Allah sarki Munirah tafiya ta hada me baki da kurma, duk jikinta yayi sanyi, bazata samu kulawa daga gurinsa ba’ banso kuka hadasu tare ba” Alhaji Abubakar ne yai murmushi sannan yace” Karki damu, idan yaga dagashi sai ita dolensa ya kula da ita” Kafin Hajiya Fatima tai mgn ta hangi Sagir ya wuce su aguje” Fuskarta ta fadada da fara’a tare da fadin” Duba Sagir hankalin sa duk ya yamutse” Akan me? Nidai Ina tunanin son Munirah yake yi fah, dan xumuncin nasu yai yawa” Jimmm, yayi cikin yanayin tunani zuwa can yace” Allah yasa hakan ne, ba asashen ki bane, zanyi farin ciki da hakan, amman naso ace Sadiq ne ya fara nuna ra’ayin shi akan aure ba Sagir ba, amman duk da hakama ba wani abu bane kani yana iyayin aure yabar wansa” Aikai bakasan wani abu ba Alhaji, shifah Sadiq wacce ‘yarce ma zata yadda tasoshi, nidai wlh Ina budurwa bazanso Sadiq ba” Saboda me? Himmm kaidai Alhaji ka dinga mishi fada ya dan dinga fara’a, sannan da wuya kika ya daga idonsa ya kalli mutum, hatta ni uwarsa Dana kawoshi doniya bare wata can” Banda abunki Fatima ai saiya kalli wata ke be kalleki ba” Bani kadai nake korafin hakan ba, su Mubarak ma sunayi, saiyaga dama yake kula su, mutum yana irin wannan tamtamkewa Ina zai same matar aure?, Sannan idan ka lura dashi ko motsi be cika so ba, ni inaga saidai ku nema masa aure Agadez kawai” Insha Allah zai nemo Mata da kanshi, Nima babu wadda ya zaba min dakaina nazaba Kuma inaji ajikina zai kawo matar sa komai lokaci ne” Allah yasa Alhaji, Nima zanyi farin ciki da haka, tuni nake rokon Allah yabashi matar da zata iya hakuri da juriya da halinshi, ma’ana Allah ya Saba halayen su, bashidai da fada, amman yakafe Kan abu ya kafe kenan, wlh har tsoro abun ke bani, koni saiya nuna bazai saurara ba, kaga idan ya samu mara hakuri akwai matsala, shiyasa nai farin ciki sosai da nafahimci akwai wani abu tsakanin Sagir da Munirah, kaga alhaji, Allah yayi Munirah da masifa, masifaffiyar yariya ce, gata kuma matsiwaciya, shikuma Sagir akwai sanyin hali ya iya zama da ita duk masifsrta saiga idan yayi fushi ta bashi hakuri, sannan shima ya iya zama da ita” Toh alhamdulillah daman bamu taba hadawa ba, shima malam yamin zancen Munirah da korafin halinta irin wadda kikayi nan *Kujeransu kusa dana juna yayin da duk kamshin turaren sa ya isah Munirah, tunda ta zauna bata kalli gefensa ba, illa kamshinsa daya addabeta ya hanata suke ni” Bata saba zama kusa dashiba’ Dan haka takejinta duk atakure inama kusa da Anass aka zaunar da ita, gaba daya tagama sawa ranta wannan tafiyar Sam bazata mata Dadi ba inda an taho da Sagir tare da Lubbunah da Aliya da bakaramin dadi tafiyar zatayi ba tsintan kanta tayi dajan taki wadda taji gabanta yafadi sabodajin fitan shi batare data shirya ba saidai ko motse beyi ba, bare tasa ran zai waigo ya kalle ta, dan haka tacigaba da kallon gefen da Anass ke zaune sosai bakin ta ke kaika yi, ganin bashi da niyar waigowa yasata make muryarta cikin sirantata tace” Anass???? beji ba harsaida ta kira sau uku sannan ya waigo” Idonsa akanta fuskar sa dauke da murmushi yake kallonta tare da mata alamar meye?? Nagaji” Dariya Anass yayi har hakuransa suka bayyana, sannan yace dan ba’a mota ma zakijeba ashe da kin gayawa me garin ku, duk cikin buzanci sukayi mgnr saidai yawancin mutanan gurin ma buzaye ne waddan da ba buzayen bama basu da yawa, dan haka duk suka juyo suka kalleta tare da murmushi” Kuna min dariya, bantaba zuwa ba toh, duk agidan mu nikadai ce bantaba zuwa ba, ni naga nisan shi gaskiya” Wasune suka fara bata lbrn yadda tafiya amota take da nisan yayin da tashiga zaro Ido tare da fadin aikuwa wlh da bazani ba, dariya sukaita mata yayin da Munirah ke burgesu yadda bata da wuyar sabo nan tafiyar tai masu dadi kusan har suka isa hira suke da jama’a da dama wadda ma basusa baki ba suna murmusawa, tuni Munirah ta manta da waye akusa da ita, Anass kuwa sai kwasan dariyar Munirah yake domin shima mutum ne ma’abocin fara’a” Yadda abokan tafiyan tata sukayi ta hira da ita yasa taji dadi sosai Kuma ta karo da tafiyar sosai domin tasan wasu abubuwan da inda tayi shiru da Bata samu ba” Lokacin da suka isoma hasken fitolu kawai take hangowa sannu ahankali akafara sauka acikin jirgin yayin da taita tsayawa jiran Anass saidai shi Anass kokarin zuwa gurin me gidansa yake yi” Tuni suka sauka yayin da take binsu abaya tana cigaba da hiranta da Mutane” Bayan sun sauka mutane ne da dama suka tsaya domin son tabasu number wayarta” Amsa wayar taitayi tana basu yayin da Suma suke Bata nasu, zuwa can taga Anass yadawo gurinta ya tsaya da alama jiranta yake, cikin fara’a da dagawa juna hannu ta rabu da kowa maza da mata kusan acikin jirgin Sadiq ne kawai batai mgn dashi ba” Bayan duk sun wuce ya rage daga ita sai Anass awajen yace” Munirah baki da dama fah, ji tafiyar da batafi da awa biyu ba kin Saba da mutum sama da 50″ Kaga laifina Anass ai mutum rahama ne, Dan me Allah ya tsaga min bakin?, Sai kuma in kunshe saikace wata kurma, ai ban godewa Allah kenan ba daga ni’imar dayai min” Wurin ta kallah taga duk mutanen sun fara watsewa tace Anass Ina motar da zata dauki mu sanyi fah nake ji” Basu karaso ba tukuna tafiyar ce da dan nisa” Gaskiya akwai sanyi amman ka tsaya muhau mota daya tare dakai banson nahau da wannan mutumin Ina yake nema Wai?? Murmushi Anass yayi sannan yace gashi can ya zauna” Sai yanzun ta hange shi nesa dasu sosai cikin katuwar rigar sanyi me hola yayin da hannunsa ke zube cikin aljihun rigar sanyin kafarsa daya kan daya idon sa sanye da bakin gilashi ko kallon inda suke biye” Sauke idonta tayi tare da fadin nasha ma ya bace ne” Dariya sosai Anass yayi me gidan ne zai bace anan?, Saidai ya battar dake” Ahakan? Au tambayata ma kike, bazaki gane ba Munirah sai mun shiga ingal, wai meyasa ke bakiyin shakkar me gida?, gaban sa fah kike ta surfa surutu saikace akku nasan tabbas bazai so ba kuma kema kila taraki yake Bangane tarani ba?, saikace kayan wanki toh Yaya zai dani? Anass haka Allah yayi ni” Dariya Anass yaitayi shidai sosai Munirah ke bashi dariya” Anass Wai Ina ya samu rigar sanyi” Saya yayi inaga Munirah” Gaskiya sanyi nakeji wlh Toh mukarasa mu zauna can kila kema ya saya miki” Allah ya kauta, wlh bazan amsa ba, gara nazama kankara, shima bazai fara Suna kokarin karasawa gurin suka hangeshi yana Shan Madara har yanzun kafarsa daya kan daya, gora ahannun sa yayin da yake rike da waya da dayan hannun” Zama Munirah tayi kujerar dake kallon tasa Anass na kokarin zama kusa da ita yaji Sadiq ya kirashi, mikewa yayi ya isa gurin yana fadin” Ranka ya dade” Goron hannun sa ya rufe bayan yasha rabin madarar Mika masa yayi gashi kabawa Tamudiriccin, kace mata saura kadan su karaso” Amsawa yayi sannan ya juya ya koma yana isah ya mika mata gashi” Yatsuna fuska tayi Allah ya kauta insha bakin wani, Ina kallo fah waddda ya gama lallashewa ne ya rufe, toni ko sabo yabani bazan shaba wlh A’a toh meye aciki? Wlh bansha, shanye kawai, indai zakasha” Yabaki fah dan kada wunya ta dameki” Anass gara hanjina ya tattare wlh” Zama yayi goran ahannun sa yana me Mamakin halin Munirah gata da fara’a sakin fuska ga kowa amman Bata shiri da Babban yayanta, ko kadan Bata iya boye kiyayarta gareshi” **Motoci ne suka faka agurin manya manya guda biyu, Cikin sauri suka fito daga cikin motar maza ne su biyu yayin da suka nufi rufar da sauri” Tuni Anass ya mike ya isa gurin motar hakama Sadiq, ganin haka itama Munirah ta mike, tun kafin ta karasa ta hangi Sadiq rungu jikin mutum biyun da sukazo daukan su sai yanzun ta hangi murmushi akan fuskarsa yayin da ya shiga gaban motar farko, shikuwa Anass ta biyun ya shiga shima gaba ya zauna yayin dataga an bude Mata bayan motar da Sadiq ke ciki” Ni can zan zauna ta fada tare da wucewa” Bayan motar da Anass ke ciki ta zauna yayin da suka dauki hanya har yanzun hasken fitulun take gani sai abun daya haska yayin da Munirah ta fara tambayan nan Ina ne” Nan suka shiga sanar da ita yayin da wasu guraren take cewa a tsaya tagani har ta cire takalmi ta taka kasan gurin, yayin da wasu guraren da dama take mikawa Anass wayarta tace ya dauketa hoto, tuni motar su Sadiq ta wuce tasu yayin data bata lokaci sosai ahanyar hutuna ko ta dauka babu adadi” Zuwa can Anass ya yaji sanyin ya karo cikin sauri yace asuba ta gabato fah yakamata ace yanzun mun dauki hanyar ingal kar ran megida ya bacci fa nasan zuwa yanzun sun jima da isa” Cikin sauri driver dake Jan motar Ibrahim ya nufi motar da saurin sa yana fadin muje cikin yaren su” Motar ta shiga ta zauna yayin da suka kama hanya tafiya sosai sukayi sannan suka fara hango rakuma kwankwance cikin kasa nesa dasu sosai tare da Mutane atsai tsaiye tare da manyan motoci” Wanni irin farin ciki Munira taji tare da nishadi mara misaltuwa sosai ta kosa ta isa kusa da rakuman balakin so take taga amalen tsoho sabo da yadda Su Aliya ke bata lbrn rakumin tsohu yasa bata da buri illah ta ganshi yadda ta kosa taga rakumin koshi kanshi tsohun bata daukin ganin shi haka” Ji take kamar tai tsalle ta dira waje,n cikin fara’a sosai tace Ibrahim acan gurin akwai rakumin tsohu? Eh Akwai, ba’a fitowa dashi sai tsohu zai fita, amman ana fitowa dashi ne idan Sadiq nagari” Wani rin sirrataccen murmushi tayi wadda ita kadai tasan ma’anar sa” Suna karasawa gurin jama’ar gurin suka taho tare dayi mata Barka da zuwa amsawa take cikin fara’a da Sakin fuska tare da kokarin wucesu ta isa gurin rakumin” Sadiq ta hanga saman wata mota ransa hade sosa,i yayin data kura masa Ido, ta cikin gilashin sa ta hange ya rufe idonsa daya yana kallonta da daya kallo na kurullah sosai” Sakkowa yayi yayin daya ya mikawa wani wayarsa lokacin garin ya fara haske, wuceta yayi ya isa gaban wani rakumi ya tsaya yayin da wani yazo kusa dashi yana me meshi nade irin na buzaye” Munirah ko wanni Dattijo take bi abaya koda batasan waye ba tasan jininta ne domin kama suke da Abbanin ta sosai, Baba Ina rakumin tsoho” Cikin buzance yace taho ki ganshi, cikin farin cik take bin bayansa sai dai suna zuwa taga Sadiq gaban rakumin” Jamar’ar da sukazo taryansu kuwa kowanne ya hau kan nasa ragumin babu wadda yai saura saina tsohu wadda ga dukkan alama Sadiq Shirin hawa yake yi” Duk da gani shi tsaye agurin be hanata tsogunawa ta shafi jikin rakumin ba tare da sun batan sa takefe gurin cikin sa” Wannan Dattijo ne cikin fara’a yace ‘yata muje ki shiga mota dan kusamu kuje ku huta….. Baba ni bazani amota ba, a Nigeria na hau mota anan ma nahau mota” Daga nesa mutumin yayi Umarni cikin buzanci saidai gani tayi ana tahowa da jaki yayin da aka taidashi gabanta” Kallon jakin tayi sama da kasa sannan ta juya ta kalle Amalen dake gaban Sadiq, Baba me za’ayi da jakin? Kicne bazaki amota ba” Turbune fuska tayi, ni sainahau jaki??? Eh Munirah al’dace ta Ingall Mata jaki suke hawa” Maza Kuma suhau Amale? Eh” Baba? Na’am Munirah Gaskiya ni baxan hau jaki ba, rakumin tsohu zan hau nadade da burin haka” Dariya akayi agurin Banda Sadiq daya dago ya kalleta sau daya ya maida kansa can gefe tare da fadin” Baba? Na’am Sadiq Ku tambayeta ta taba hawan rakumi? Tunkafin ma akai ga tambayanta tace ni yau zan fara” Dariya aka sake yi agurin cikin rarrashi mutumin yace kinaji ko yariyata, tafiyace me tsayo zamuyita yanzun bazaki iyata ba, kibari idan munshiga gari saiki hau ahankali saiki koya” Cikin yanayin bacin rai tace yanzun kenan Kuma duk amotar zamu tafi? A’a wasu zatafi aragumi wasu amota kinsan mu munfi sabo da Amale sabo da kasan mu nada laushi ba kowacce irin mota iya wucewa nan gurin ba gudune ake bana wasa ba, bance bazaki iya ba Amman ki Bari ki Saba, wannan rakumin anxo dashi ne domin Sadiq” Kanta ta sunkuyar kasa yayin da hawaye suka zubo Mata, hannu tasa ta share sannan tace ni gaskiya arakumin zani, tun Ina gida nake da burin haka idan har banhau Amalen tsohu ba bazanyi fsrinci da zuwa ba, naso ace nice ta biyu ahawansa Cikin sauri Sadiq ya kalleta gilashin dake sanye a idon sa ya cire tare da dawowa kusa da jakin ya tsaya, cikin kausasarsiyar murya yace” Kubarta tahau” Jimmmm kowa ya tsaya yayi yayin da Sadiq ya sake cewa baba muje, kafarsa ya daga ya daura ata Munirah dake sanyi cikin dogon takalmi ya mutsuke batare da kowa ya luraba” Runtse idonta tayi saboda wanni irin azaba dataji sosai taji zafin daman sanyi ya gama ratsa kafa,r dagawa yayi yana me kallon cikin idon ta da dandanan ya kala yai jawur, itama kallon shi tayi yayin dataga idonsa daya rufe daya Kuma abude ahankali ya bude bakin sa yace Tamudiriccin hau nabar miki” Daman rakumin kwance yake dan haka ta nufa inda take ganin ana zama ta zauna yayin da duk sauran suka fara tafiya ya rage daga motar da Sadiq yake ciki sai Rakumin da Munirah ke Kai” Ganin yashige motar tarasa yadda za’ayi rakumin ya mike, saidai motar su Sadiq natashi kamar jira rakumin yake shima ya mike” Subuhanallahi, Munirah ta fada afili, domin kuwa ji tayi kamar zai mikata sama ta farko, hannunta kuwa rasa inda zatayi dasu tayi dan haka ta dafa bayan rakumin kawai” Sosai wani abu ke rawa acikinta idan ta hangi yadda Rakuman gabanta ke kwarara gudu tunda uwarta ta haifeta Bata taba gani ba” Anya kuwa zan iya?, Narantse tsoro jiri ma nake gani, wani irin tafiya rakumin yake da ita saidai motar su Sadiq na kwasa da Gudu taji Analen yayi Mata wannni irin fizga, innalillahi, gaba daya rasa a inda take tayi yayin data shiga zunduma ihu ta dawo karshe ta dawo gefe tana ta tangal tangal wadda takejinsa tamkar amafarki, zuwa can jinta kawai tayi cikin kasa yayin da takejin mgnr mutane da yawa saman kanta” sauri tashi zaune tayi tana kallon gefen da takejin motsin mutane Sadiq ne ta hango zaune cikin motar yayin daya bude kofar ya zuro kafarsa Banda murmushi ba abun da yake yi, zafin dataji kafarta nayi shiya ya dauke Mata hankali daga kallon shi, kuka tasa saboda wani irin radadi da takeji akafar zaiyi wuya idan ba karaya bace” Dagota akayi tsaye yayin data kasa taka kafar cikin kuka take fadin, wayyo kafata kafata, wayyo Annanin ” Sannu suke Mata tare da sakata cikin mota sannan suka aje Mata takalminta agefen ta, Sadiq kuwa rakumin ya nufa ya hau, gyara zaman sa sosai akan rakumin sannan ya kwashi ragumin aguje yana me waiwayen motar yadda Munirah ta saki baki tana ta kallon sa, kasa daina kallonsa tayi yayin da tsoro da fargaba ya shiga ranta yadda ya burara Amalen nan ba makawa ya fado mutuwa zaiyi ko kallon gabansa bayayi, cikin ranta tace toni idan ya fado ya mutu anan yaya zanyi na koma gida, gaba daya gerin ya fitan min arai, Idan ma mutuwa zaiyi yabari ya mayar dani gida” Shikuwa Sadiq sosai yake nuna kwarewarsa wannan fannin yana me mata kallon zaki sani tare da cin burakan koyawa Munirah hankali dazaran sun isa Ingall, hukunce nafarko kenan ya fara yi mata wadda shine laifinta na karshe awannan tafiyan, …….Mmn Yazeed???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? *SAWUN BAYA* ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ Page 15 to 17 Typing……..????️ Idon Munirah nakan Sadiq takasa daukewa shikuwa duk da cewa ba gabansa yake kallo ba bata iya cewa motar tasu yake kallo” Tafiya sosai sukayi har yanzun hawaye bebar idonta ba, kuka kawai take yi tare da zuba masa Ido” Tafiyan kusan awa daya sukayi sannan ta fara hango gine ginen su daga can nesa, raba hankalinta tayi gida biyu tana kallon Rakumin Sadiq dake karta gudu tare da kallon gine ginen” Sosai hankalinta ya tashi ganin irin Saharan da suka keta, cikin ranta take fadin inda nasan haka garin yake banzuwa da kowa sai Annanin na” Suna isa suka samu cin cirondon mutane tun kafin motarsu ta tsaya Sadiq ya diro akan rakumin sa saidai wannan karon be ko kalli inda take ba, fuskarsa ya goge tare da kafar wandon sa sannan ya nufi inda mutanen suke yayin da yake mika musu hannun, wasu Kuma suna runguman junah” Kokarin sauka take amman takasa taka kafarta Saida taimakon wasu ‘yan mata da sukaxo gurin su Uku ta samu ta fito, biyu ke rike da ita yayin da dayar ke rike da takalman Munirah” Wanni banban falo suka shiga inda ta hango Sadiq zaune dafda wani tsoho, nan ta tabbatarwa kanta kakansu ne tsoho duk da cewa hutun shi da take gani gidan su bekai haka tsofa ba Amman ta shaida tsoho ne” Zama tayi tana fadin wash Allah na” Zonan, yaki, karaso Muniratu” Bana iya tafiya tsoho, kafata ta karye ahanya” Subuhanallahi, juyawa yayi ya kalli Sadiq yace” Abubakar garin Yaya?? Kallon kakan nasu yayi sannan ya maida kallon sa ga munirah yana fadin, akasa kawai naganta” Subuhanallahi, lallai ya kamata aduba gurin, da alama yana ciwo sosai tunda har take tunanin karaya ce” Ibrahim daya tsinkayi mgnr ne yace, daga Kan Amale ta fado baba” Juyawa yayi ya sake kallon Sadiq sannan yace waye ganin daurata a Amalen? Ibrahim ne yasake cewa ita ta matsa saita hau” Ganin inda Sadiq ya dauke kansa yasa tsoho ya kalli Ibrahim yace ka leka nan waje ka Kira min Sule wanzami” Juyawa Ibrahim yayi cikin sauri, yayin da Sadiq ya sake gyara zaman shi ya daura kafa daya Kan daya sannan yaciro gilashinsa ya maida” Bajima ba Ibrahim ya dawo da Sule kamar yadda tsoho ya bukata, nan ya fada masa bukatarsa yayin da ya juya ya kalli Munirah yace Mugani” Hannunsa yasa ya rike kafar riko mekau tunda ya rika be sakiba yayin da Munirah ta shiga kwala ihu tare da Kiran mutanen gidan su Annanin da Abbanin Umma da Sagir, tsone ke Mata sannu yayin da Ibrahim ma ke Mata sannu” Saida ya gama daidaita kafar sannan ya saki lokacin Munirah ta hada zufah sosai” Wannan ‘yan matan ne dai na dazon suka sake shigowa saidai wannan karon su biyu ne kama Munirah sukayi suka shiga da ita ciki” Nan taga Babban gida saidai yanayin duk yana canza mata, jinta take kamar awata duniya daban komai bayya Mata dadi” Wani daki sukashi yayin da matar dakin ta fara fara’a tana me zubawa Munirah Ido” Alhamdulillah Masha yau gani ga Muniratu” Munirah babu vakin mgn gurin kwanciya kawai take nima, kasa taso kwanciya Saida tsohuwar tai saurin tarewa cikin fadin” Yau naga raguwa menene haka? Mammmah nagaji kwanciya kawai nake so” Toh kidaure kiyi wanka mana” Badan ranta yasoba aka hada Mata ruwan wanka Sannan aka Mata jagora zuwa bayin” Wankan tayi yayin da tana dawowa dakin ta samu akwatin ta Kan gado, goggoge Jikinta tayi sannan tafito da mai ta shafa doguwar riga tasa kawai sannan tagabar sa Sallah ta kwanta” ** Misalin Karfe biyu narana ta tashi zaune, gaba daya gabobin jikinta ciwo suke Mata, yayin da kewan gida ya fara damunta lallai gidan mu aljannar duniyace tafada cikin zuciyarta, tunani tashigayi tare dayin zurfi cikinsa, nayi nisa da gida sosai, babu wadda nasani wadda Sai Sadiq anan dagani sai shi, hawaye ta share sannan ta mike ta nufi tsakar gida” Mammah kawai tagani tare da yan matan nan guda biyu sai aikace aikace sukeyi acikin gidan sanna ta musu yayin da suke binta da kallo” Buta ta dauka tai al’awala sannan ta sake komawa dakin, Sallah kawai tayi ta sake komawa gadon ta kwanta tana mecifaba da zubar da kwallah” Tsowar ce ta shigo dauke da kwano abinci ta tashita tana fadin tashi kici abinci” Hawaye ta share tare da fadin” Nakoshi” A’a, menene haka Munirah, toh fada abun da kike so akawo miki” Kanta ta girgiza alamar babu komai” Wani iri tsohuwar tayi zuwa can takalawa wata Kira tare da fadin kawo min kwanon” Cikin sauri ta fita tadawo da kwano cike da naman zabi gaban Munirah tajashi ta ce to ci wannan idan Kuma Madara kikeso kema aje a anso miki? Kaita sake girgizawa tare da fadin nakoshi” Kallo tsohuwa ta sake tsareta dakyau sannan tace, ke nan ba gurin bakunta bane, nan da kika gani anan dakin ubanki ya girma, kinzo musan juna Kuma kamar kin shigo cikin bare? Dauke Kai Munirah tayi cikin turo baki, yayin da tsohuwar ta fice tabarta awajen” ****** Sadiq ne kwace awani wakeken gado, yayin daya yasar da wayarsa acan karshen gado” Dagashi sai gajeren wando yayin kafarsa take Kan daya, bacci yake sosai wadda daganin yanayin kwanciyarsa kasan yanajin dadin baccin sa” Wani irin duka yaji ankai masa agefen marar sa, runtse Ido yayi daya dafe gurin, wani dukan ya sakeji adayan gefen dan haka yaja tsaki batare daya bude idoba yace” Muhammad banson iskanci” Toh katashi tsoho na mgn” Tashi yayi zaune tare da tura hannunsa cikin gashin kansa yace” Ina tsohon?? Aikoni yayi, Wai Munirah takicin komai, yace kaxo kusa da ita komai aka Bata bataci, tunda tashigo gari batasa komai abakinta ba kuka kawai take” Kallo yabi mutumin dashi sannan ya sake shafa gashin kansa tare da fadin” Toh takicin abinci zan dannetane inbata? A’a Wai kaje kusa da ita dai inji tsohu fah bani ba” Kawar dakai yayi koma waye ya Aiko ka mezan Mata?? Tabe baki Muhammad yayi tare da mikewa shikuwa Sadiq komawa yayi ya kwanta rigingine tare da fadin” Kasan menene?? Batare da Muhammad ya juyoba yace saika fada” Awanni daki aka sauketa? Wacece? Tamudiriccin Munirah” Tana dakin Mammah” Jimmmm, Sadiq yayi, sannan yace, kace masu su ware mata daki, subarta ita daya, komai nadakin Kuma ya kasance fari ne tass???? Cikin mamakin Muhammed yace bangane ba?? Nima bangane ba, amman haka naga kamar an mata agida, Aliya da Lubbunah suna kwanciya guri daya, Amman ita daya dakinta daban, komai farine adakin ta, farin kaya, farin zanin gado, ta kwanta tsakiyar gado, haka naga suna mata, kuje ku mata hakan wata kila taci abincin tunda kun matso saitaci” Ban gane mun matsu saitaci ba? Kun matso mana, ida rashin cin abincinta be dameku ba bazakazo nan gurin sabo da itaba kawai, wacece ita?, Ko taci abinci ko kartaci ni ba matsalata bace” Murmushi kawai Muhammad yayi ya fice dakin, shikuwa Sadiq wanka yayi sannan ya wuce masallaci sallar la’asar” *****Misalin hudu na yamman Munirah taji Kara wayarta wadda sai ayanzun ta tuna da ita, cikin sauri ta jefa hannunta cikin Jakarta ta fiddota, Kallon dakinta tayi tana fadin” Allah yasama waya na aiki awanan garin, Sagir ne cikin sauri ta dauka tana ajiyan zuciya tare da fadin Amukarnin” Na’am, Munee, Yaya akayi Kun isa shine ko ki kirani” Amukarnin mancewa nayi da waya, sannan bana tunanin waya zatayi aiki anan gurin???? Murmushi yayi yana fadin, kardai kuka kike gaya min menene? Hannu tasa ta share hawayenta sannan tace Amukarnin garin ba Dadi Sam, jina nake kamar Ina bangon duniya, jikina ciwo yake min sanan Kuma rakumin tsoho ya kadani Saida aka min gyara muna sauka” Toh ke banda abinki daga zuwa saiki kama hawan rakumi, basai kibari ki huta ba” Toh ai su sukazo daukan mu tare da rakuma Kuma ai tun agida nace maka zan hau rakumi” Ikon Allah, yanzun kina nufin cikin garin Zaki shiga arakumi?? Labarin yadda akayi ta gaya masa tsaf jin ya kwashe da dariya yasa ta tsaya cak tana sauraron sa” Me isarsa yayi sannan yace” Muneee? Shiru tayi cikin Jin haushin shi” Kinajina Munirah mgn nake fah? Ai dariya kake min” Nabari, kinajina? Ummm” Toh Ina dau’uwana fah? Dan uwanka bansan inda yake ba, ai yasan bazan iya hawa Amalen ba yace yabarmin Ashe tsabar munafunci ne” Dariya Sagir ya sake yi sannan yace kinaji Munee, ba haka bane, taurin kanki yasa yabar miki, kinga nafarko beson aga yana jayayya dake vayan kina matsayin kanwarsa, abu na biyu kuma yana son ya gaya miki shi ba sa’anki bane, Kuma na tabbatar yanzun kin gane ba’anki bane” Ni daman can nasan ba sa’ana bane, daman waye zaiso yai sa’a dashi” Dariya Sagir ya sakeyi sannan yace to kinsan meye ne yanzun?, Sharawa zan baki, kitashi ki mike kici abinci, Ina me baki shawara idan har Sadiq yaga kin firgice haka hmmmm bazan gaya miki abun da zai faru ba, tayaya mutum zaije asalin sa ya firgice haka? Toh ni Amukarnin bansan kowa bafa anan saishi Kuma ya gudu yabarni tunda mukazo banganshi” Idan kin ganshi me zai miki?, Kinga shidai bazai rarrasheki ba, Kuma bazaije ko Ina dake ba, sannan bazai Bari kije koda kusa dashi ba bare Kuma ya kalleki” Kuma fah hakane wannnan sai Aliya” Ashe dai kin gane, yanxun Zaki saki jikin ki ga kowa ko kuwa? Zan sake, shiyasa naso ace dakai nsyi tafiya gashi ma duk gidan kaine kafara kirana, yauwa Amukarnin rannan Umma tace Wai nida Kai soyayya muke? Me kikace Mata to? Cewa nayi barin tambayo ka” Lumshe idonsa yayi da kinsani kince mata Eh, ko baki sona? Runtse Ido tayi kamar tana gaban sa, rasa abun cewa yasa tai sauri kashe wayar yayin databi wayar da kallo tana murmushi, ayanzun ta manta komai har tama manta inda take, ahankali nutsuwa ya dinga shiganta har ta fara dawowa cikin hankalinta saidai hankalin nata har yanzun yana gurin Sagir domin fuskarsa kawai take gani koda Bata gabasan tana iyasta yadda fuskansa yake ayanzun tasan yana nan cikin farin ciki, aunau sa tayi sanda ya sauke waya banyan sun gama wayar, sosai Sagir din ke burgeta fiye da tunani, Karan wayar data sakeji yasata kallon wayar Sagir din ne dai murmushi tayi sannan ta dauka” Munee munyi waya da Sadiq ya gayamin akwai bikin da za’ayi anjima, zan rokeki wani abu dan Allah ki taimake ni” Inajin ka” Munirah kada kiyi rawa dan Allah” Ai bazan ma iya rawaba Amukarnin kafata ciwo take har yanzun sannan jikina ciwo yake min, ni inaga bazan fita ba ma” Idan baki fitaba bazasuji Dadi ba kije Amman kada kiyi rawa, sannan Kuma banda hira da maza idan kin dawo zan gaya miki wata mgn” A’a nidai ka gaya yanzun kawai” Nafison sanda zan fada gani gaki, kina kallon idona Ina kallon naki” Cikin kukan shagwaba tace Amukarnin ni ko yanzun ji nake kamar Ina kallon ka, kasan tunda mukayi waya dazon?, har ka sake bugo wayar ban daina ganin fuskarka ba” Dan Allah fah Munirah? Wlh Amukarnin har wani murmushi nake gani Kan fuskar taka” Kara fadada murmushinsa yayi sannan yace kamar kin shiga zuciyata fah” Inajinka toh Gaya min” Kinaji Munirah, mgn ce me girma ba irin mgnr da mukasabayi bace, idan kin dawo zan gaya miki” Kukan shagwaba tasa mishi yayin daya shiga murmushi tare da fadin” Ya isah ya isah, kinaji ko, daman cewa zanyi gidan yamin fadi da bakyanan sann……. Kukan takarasa sakawa wlh bawannan mgnr bace” Dariya yayi sosai sannan yace to shikenan yi shiru naji zan fada miki, kin shirya? Eh Ki Kara shiryawa dai” Amukarnin ni ashirye nake” Toh rufe idon ki” Kaima ka rufe naka” Narufe to, kinajina nafara? Eh Zuciyata takamu da ciwon son ki, daren jiya banyi bacciba bayan tafiyan ku, gani cewa ban bayyanar miki da soyayyata ba, inajin tsoron kar wani yayi maki tayin tasa ki amsa, ajiyan zuciya yayi sannan yace Munirah Zaki yadda ki aureni?? Lumshe idonta tayi yayin da take karajin amon sautin sa yana Mata wannan dai tambayar kashewa tayi da sauri sannan ta bude idon ta kalli wayar cikin sauri ta daga filon ta tura kanta ciki Sagir ma kallon wayar yayi tare da murmushi kadan” *Misalin Karfe 8:00pm kofar gidan Baba tsoho cike yake makil da jama’a” Banda kide kide da bushe bushen babu abun dake tashi” Wuri yayi guri, tuni baki ya kankama Sadiq na hanga kusa da tsoho tare da wasu Samari guda biyu sai Sai Mammah tare da wasu yan Mata biyu itama agefenta dagacan gefe kuwa Kannen Alhaji jafar ne Mata su Uku zaune da yaran su, iyalan Bava tsoho kenan sai Kuma baki dakecan gefe yayin da iyalan Baba tsohu suka fara taka rawa” Sadiq kallon rawan kawai yake tare dabin ‘yan matan da kallo daya bayan daya yana kallon yadda suke tasu girgizan saidai nasu ba irin nata bane yafada cikin ransa, Amman duk da haka ya kasa dauke idonsa akan su” Sosai yan uwa da jam’ar arziki ke son ganin Munirah Amman Sam taki fitowa acewarta jikinta ciwo yake mata dan haka aka barta sadai duk wadda ya tambayeta saidai agaya masa inda aka sauketa” Ita kuwa Munirah kusan awa biyu kenan tanajin kida natashi, sosai Busan ke tsumata yawanci saidai ta kunna taji yau ga busa muraratan natashi wannan yasata zuwa yin wanka batare data shirya ba” Cikin sauri tayi wanka shiryawan ma cikin sauri sauri tayishi, sannan ta dauko kayan da aunty Khadija ta saya mata, wandon tasa sannan ta dauki doguwar rigar ta tabude daga kasa ta Sanya, ita dakanta ajikin ta take tabbatar da tayi kyau bana wasaba” Dan kunne da sarka tasa tare da awarwaraye sanna ta Kara gyara gashin kanta afili tace yau ba zan sa lafaya ba, dogon takalmin da aka bata tare da kayan ta sanya sannan ta fesa turare ako Ina najikinta” Gaban madubi ta tsaya tana me fadin masha Allah nayi kau saidai makiyi” Inda takejin kidan natashi take nufa yayin da take tafiya kidan na dada tsomota tare dajin dadin yanayin, kamshin garin da komaima ayanzun burgeta yake yi” Tana fitowa ta hangi matan dake rawa afili cikin sauri tsowar ta mike tana fadin, ko ke fa Muniratu ki shiga cikin yan uwan ki kowa yasanki yafi ai ko” Toh Mammah gashi ai na fito Amman ni kibar cemin Muniratu kar wani yaji yakama” Nikuma shina iya fada yaya zakiyi dani? Nidai gaskiya banso” Hannunta tsowar taja suka zauna kusa da yanmatan yayin da kallo yadawo gun Munirah sosai kyaunta ke daukan hankalin jama’ar gurin duk da cewa akwai kyawawa agurin Amman daganin Munirah da shigarta kasan bakuwa ce” kamar yadda shigan Sadiq ma ya nuna hakan’ **Tun fitowan Munirah Sadiq yamaida gilashin sa tare da daura kafarsa daya kan daya” Mawakin da take yawan kunna wakokinsa ne yafara tasa, yayin da kida ketashi kota Ina tare da bushe bushe, sosai Munirah ta tsomu fiye da tunanin me karatu yayin da har tafara rawa daga zaune ganin be gamsar da itaba ta mike tundaga inda take zaune ta fara rawa dan haka da rawa ta isa filin yayin da gurin ya dauki tafi da ihu hakan ya karawa rawar tata armashi” Bayan ta tsaya tsakiyar filin kuwa wani irin girgiza tafara yayin da tabbatarwa jama’ar Ingall iyalan tsohu basu yada al’ada ba” Mikewa Sadiq yayi daga inda yake zaune cikin kasaita yake takawa harya isa gaban Munirah ya tsaya” Ita ko Munirah wannan lokacin ta tsomu iya tsumuwa rawa take tare da gigiza kirjinta” Idonsa cikin gilashi yake kallonta cikin sauri ya zura hannunsa a alihun wadonsa nabaya, bandir din kudin can ya fito dashi yayin da ya fara yi Mata liki akirjinta, be tsayaba Saida ya karar dashi sannan ya maida hannunsa yasake dauko wani adayan aljihun dai dake bayan sa, likamata yake yayin da Munirah tai nisa busa yai mata dadi rawa kawai take” Ihu gurin ya dauka tare da tafi, abune wadda ba’a Saba gani ba Sadiq betaba shiga fili yayiwa wani likiba, itako Munirah tana kallon yadda kudi ke sauka akirjinta saidai batasan waye ke manna su ba” Ganin abun yaki karewa ta daga idonta sama dan ganin waye da wannan aikin…….. Mmn Yazeed???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? *SAWUN BAYA* ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/Page 18- 20 Typing…..????️Bayan sa kawai take iya hangowa cikin sauri yake takawa, cikin Mamaki tace” Sadiq? Kasa kasa ta fada dan haka babu mejinta harya koma gurin zamansa ya zauna tana kallon sa” Muhammed da yake daf da Sadiq ne ya tabashi, Sadiq abun Mamaki yau kaine dayi likin sannan likin ma karasa wadda zakamawa sai Munirah? Ni banyiwa Tamudiriccin likiba Allah ya kiyaye ni” Wani irin Murmushi Muhammed yayi sannan yace” Idan ma idonka gizo yake maka ka maza ka dawo hankalin ka wacece waccen tsakiyar fili” Munirah ce” Toh ita kama liki ai” Eh nayi liki Amman ni Sam ba ita naiwa ba” Tsaki Muhammed yaja sannan yabar zancen” Munirah ko Mamakine ya kamata idan har ta fahimta Sadiq ne ya Mata liki???? Bata sake rawar ba gefe ta koma ta zauna jikinta asanyaye har akayi aka gama, sai yanzun ta fahimci wannan yan matan guda biyu abokan wasanta ne, domin sai janta suke da wasa hakama Muhammed yajata da wasa” Yadda Kannen Babanta Mata suka kula da ita yasa da aka tashi gurin tabi daya wadda taga kamar tafi sakin fuska” Gidan ta bashi da nisa da gidan tsoho, sai dai abun Mamaki suna shiga falon sukayi Ido biyu da Sadiq” Sannu yan matan suka masa yayin da suka wuce shi itako Munirah dauke idonta tayi” Daki daya aka ware mata dan karami kusa dana Mamma Aysha, katifa ce dindimemiya adakin, yayin da aka laikayeshi da zanin gado me kyau, Dadi taji sosai bayan ta kallah dakin sannan tai Shirin kwanciya ta kwanta, sai ayanzun tafarajin zafin kafarta” Kwanciya tayi yayin da bacci yaki daukanta dan haka ta kashe wutar dakin, sannan ta koma ta kwanta” Kwanciyarta befi da minti 30 ba tafarajin motsi” Ahankali ta bude idonta tare da fadin” waye? Cigaba dajin kamar ana tahuwa yasa ta mike zaune da sauri tare da kokarin sauka agadon tana neman makunnin wuta, cikin shirin fashewa da kuka” Haskene ya bayyana adakin yayin da sukayi Ido biyo da Sadiq dake tsaye gefen gadonta” Komawa tayi ta jingina da jikin bango tare da fadin” Ann???? Hannunta tasa da sauri ta rike wuyar rigarta dalilin tuna yadda yai mata wancen lokacin” Zonan, taji yafada Cikin yanayin dake nuna tsoron ya shigeta tace mena maka toh? Kizo nace ko?? Nidai kai hakuri inda nasan nai maka wani abu da nazo ai” Cire gilashin sa yayi idonsa suka bayyana yayin dataga ya kafeta da Ido” Itama cikin idon nasa ta take kallo tare da cewa ni me nayi, inda nasan nayi wani abu ai zanzo” Ganin ta kafeshi da Ido ya lumshe nasa, yanzun fah?, bazakizo ba kenan? Idonta anashi tace toh me namaka?? Ki matso kusa nace ko? Aini ban maka komai ba, Kuma saikazo min daki Ina bacci, haka wancen ranar ma kamin duka har yanzun kirjina bebar ciwo ba???? Kawar da kanshi gefe yayi, ni ban tambayeki wannan ba, ciwa ya warke ko be warke ba ba abun da ya dameni bane, cewa nayi kizo nan ni bana wasa dake” Ganin inda ya hade fuska ta fara takowa ahankali tana me yarfa hannuwanta, gani toh” Kikara mataowa ” Kara matsawa tayi daf dashi kamar yadda ya nuna Mata da hannunsa sannan yace kisa min guiwarki akasa” Cikin sauri ta zube tayi kamar yadda yace” Kallo yabita dashi yayin da yaga itama ta tsura masa idonta” Cikin ransa yace meyasa yariyar nan har take iya tsuramin idone, yariya Ido atsaitsaye, afili kuwa cewa yayi daina kallo na” Kawar da idonta tayi yayin daya cigaba da binta da kallo” Cikin siririyar murya yace nataba wasa sake?? A’a????, Ko ni abukin wasan ki ne?? A’a Meye alakata dake… Ni gidan mu daya” Lumshi idonsa yasake sannan ya bude tare da fadin, gidan mu daya??? Eh Kujeran dake gefen gadon ya jawo ya zauna sannan yace” Ina nufin meye matsayina agurin ki? Gidan mu daya ai” Okay Sagir fah? Jimmmm tayi, sannan ta dago ta kalleshi Amukarnin na ne” Yawu ya hadiye, sannan yace shikenan naji, ni gidanmu daya, amman dan ubanki kinsan ba ayaki aka ciwoni ba ko? Eh” Masha Allah, kuma kinsan zan iya baki kashi duk da ciwa zaman gida daya ne ya hadamu?? Ai Abbanin yace kada wadda ya tabani….. Dukan dataji yakai mata abaki yasa tai saurin rike bakin tare da tsiyayar hawaye???? Ni zakiwa iskanci?, ai bansan ke cikakkiyar mara kunya bace saiyau, kisamin guiwarki akasa sosai ki rufe idonki sannan ki daga hannun ki sama” Cikin idonsa ta kallah adaidai lokacin dayake daura kafarsa daya Kan daya” Kamar yadda yace haka tayi yayin da hawaye ke zubowa cikin idonta” Kusan minti talatin ta dauka ahaka yanzun ya tabbatar da tayi laushi dole ta aje taurin kanta yamata hukunci yadda ya dace dan haka yace” Meyesa kika min surutu ajirgi?? Ainaga ba daukan karutu ake aciki ba, sannan kuma Ina tsoron kar bakina yayi wari, Kuma ni bansan bakaso ba da bazanyi ba” Lumshe Ido yayi sannan ya bude akanta, idonta arufe yace Oya to bani hakuri akan daukan alhakina da kikayi kikaita min ihu a kunne” Kayi hakuri toh” Ba haka nakeso ba, bude idonki ki gani” Budewa tayi yayin data bishi da kallo idonta yai jawur” Ki tsuguna ki hada hannunki waje daya sannan kice ka kafarceni bazan sake maimai hankan ma, idan Kuma nasake kayi min abun da kaga dama” Tana kuka sosai ta yi yadda yace yanzun bukatarta kawai yafice yabarta ta kwanta kawai” Toh naji, zauna dakau” Gyara zaman tayi gabanshi tana me jiran abun da zai sake fadin” Ke wacce irin ballagaza ce da zaki yadda kina bawa duniya number wayan ki?, daga haduwa da Mutane da bekai na awa biyu ba kita raba number wayarki, saboda ke kina da arha kamar kayan gwanjo ko??” Su sukace in basu ai” Duka yakai Mata da kafar sa yayin datai saurin mikewa ta matsa tana fadin, kayi hakuri toh” Jimmmm yayi sannan yace, sannan Kuma naga kinsa kayan Aliya dazon, waya baki izinin ki taho mata da kaya?? Ni? ???????????????????? Eh Kayan da kisa dazon kayan Aliya ne” Mikewa tayi nibansa kayan Aliyaba Kuma tunda nake bantaba saka kayan wani ajiki na, Abbanin da Annanin Aunty Khadija sai Amukarnin Sagir kadai ke saya min kaya na saka” Murmushi Sadiq yayi sannan ya daure fuska kayan da kikasa dazon nina sayawa Aliya matsayin tukuicin wani rawa datayi ya burgeni, naso in ga kayan ajikinta banso in gansu jikin ki ba” Runtse Ido Munirah tayi cikin tarin bakin ciki irin wadda bata tabajinsa ba, ganinta kawai tayi gaban akwatin ta kaman a iska, tafara fito da kayan sannan ta wuce ta juye kayan dake cikin wata leda atsakiya gadon ta zuba kayan acikin tazo gabansa ta ajiye” Murmushi Sadiq yayi sannan ya daga ledan ya cillah mata agoshi yana fadin, Allah ya kauta tasa kayan da kikariga kika shafa musu warin jikin ki” Sosai ran Munirah ya baci in badan tana tsoronsa ba yau saita rufeshj da doka Allah yasoshi ba mace bane shi, ganin inda take ta haki ransa yai fari karr mikewa yayi tare da fadin” Na Aiko miki da Madara kinkisha saboda nasa bakina agoran kika barwa Anass, sai gashi kin sunbaci ragumin tsoho nikuma nahau kansa bayan na mutsuke bakin ki da kafata, wannan ya isa yasa ki tabbatar kullum Ina gabanki” Mikewa yayi yana zabga mata harara yafice yabar dakin yayin da Munirah ta fada gadon cikin matsanancin kuka, kuka tasa sosai me tayar da hankalin me sauraro cikin yanayin Bacci Mamma Aysha tajiyo kukanta yayin data shigo dakin aburkice” Munirah lafiya? Kuka kawai take dan haka Mamma Aysha ta zauna tare da rungumeta ajikinta meyene ya faru Munirah?? Tana me share hawaye tare da tsagaitawa da kukanta take fadin babu komai” Babu komai kike kuka cikin dare? ko garin namu ne be miki dadi ba? A’a Kina kewan iyayen ki ne? A’a toh me ya faru?? Bakomai Mamma ni mafarki na yi” Mafarki?, Kinyi addu’a kafin ki kwanta? Eh” Jimmm Mamma Aysha tayi sannan tace toh je kiwo alwala kizo ki kwanta, ko Zarah ta dawo nan ku kwana tare? Tsintan kanta tayi da cewo eh” Fitan Mamma bajimawa saiga Zarah ta shigo, Zarah ‘yace ga mamma Aysha cikin yanayin tausayawa take kallon Munirah ahankali ta zauna abakin gadon tare da zubawa Munirah Ido” Itako Munirah zama tayi ta mike kafarta akan gadon yayin da hawaye yacigaba da ziraro Mata Kan kumatunta” Tsayon awa biyu ta dauka ahaka dan haka Zarah tace” Munirah kidaina saka tunanin wannan banzan mutumin aranki ki kwanta kiyi baccin ki” Sosai kalamin Zarah yabawa Munirah Mamaki cikin tsananin Mamaki tace kinsan abun da yamin ne?? Koma dai menene nasan bazai wuce girman kansaba tare da jijida kai, shi arayuwarshi kowa ba komai bane, musamman idan ya lura mutum be damu dashi ba al’amarin sa baya burgesa toh shi Kuma lokacin yafi maida hankalin sa akan ka, maida hankali bana arziki ba shi adole saiya kaskantar dakai” Ni bazai kaskantar Dani ba Zarah har abada, natsane shi fiye da tunanin ki, wlh wlh da zan iya kashe mutum dashi zan fara, Zarah kina nufin kinsan irin abun da yake min ne?? Himmm bansani ba, Kuma zan iya cewa nasani, amman ki sausauta kalamanki akanshi kada Hasat tajiki” Wacece Hafsat” Hafsat yaya tace, Kuma soyayya suke ita da Amukarnin Sadiq batason taji ana mgn akansa yanzun zakiga ranta ya bacci wani lokacin har fada muke” A’a, toh ai acan gida ma son Aliya yake, buni buni yana nanike da ita” Zaron Ido Zarah tayi cikin Mamaki sosai sannan tace” Toh kodai su biyun zai hada? Hawaye Munirah ta share, sannan tace ni kinga ba wannan ba, ni koma me zaiyi yaje can ya karata amman wlh saina rama wulakanci da yai min, kwashe komai tayi ta bata lbr” Dariya Zarah tayi sannan tace dan wannan kike kuka, lallaima ke cenan kika barshi, bari gobe da safe muje mu aje masa akofa yana fitowa yaci tuntube dashi” Idan yaci tuntube ni ai ban burge ba, agoshi nake son na buga mishi dan nima haka yai min” ???????????????? Kina son yaci ubanmu kenan ko, Amukarnin Sadiq din zamu jefa?, toh wlh idan kikayi haka Tsoho yaji labri sai yaji kaman ya jefeki da ranki, indai kin yarda gobe mu aika Yaro yakai masa ko muje da kanmu mu” Jimmm Munirah tayi zuwa can tace Muje da safen toh” Ko Kuma kibari Mamma Hauwa tazo ki hadata dashi wlh masifaffiya ce har hakuri saiya bak ** Nace maka banje inda take ba ko? Haba Sadiq yanzun Kai meye amfanin ka, anta kiranta ai bata dauki wayar ba” Toh kaje can ka nemeta ni karka dameni” Dan Allah ka taimaka min ka bata waya” Bangane in taimaka maka ba?, cikin yamutsu fuska yake jiran Jin abun da Sagir zai fadi” Toh katainaka min mana Ina son Jin muryarta ne wlh” Runtse Ido Sadiq yayi da sauri zuwa can ya bude tare da fadin” Sagir abun haryakai haka?, Kodai abun da Mubarak ya fada kwanaki gaskiya ne?? Gaskiya ne mana Sadiq, ai zance boye boye ya kare tunda harma na gaya Mata” Runtse idon sa ya sakeyi akaro na biyu batare daya bude idon nasaba yace ka Gaya Mata ita wa?? Munirah mana” Wanni mummunan faduwan gabane ya sameshi yayin da har yanzun ya kasa bude idonsa Kuma ya kasa cewa komai” Sadiq!!! yanaji kayi shiru daman nasan Kai kadaine zaka nuna rashin Jin dadin ka saboda baka shiri da ita” Daker ya iya bude baki yace ba haka bane Sagir, yanzun Kai dan Allah yaya zakayi da Tamudiriccin?? Lallabata zanta yi, zan diga mata abun da ranta keso har tazo tayi hankali” Sosai jikin Sadiq yai sanyi cikin wata irin murya yace da gaske dai kake kenan?? Wlh Sadiq da gaske nake yi, zan mata fada akanka sosai yanzun Kai sirikinta ne girmamaka zata dinga yi sannan dan Allah Amukarnin kadaina hararanta???? kaji dan Allah na rokeka????” Ajiyan zuciya kawai yayi tare da fadin naji” katse Kiran yayi sannan ya kwanta yai rufda ciki lokaci bayan lokaci yana sakin ajiyan zuciya” **** Zarah keda Munirah ku karasa girkin nan, idan har Kun kammala bandawo ba kuraba” Mamma Ina Zaki da Yamma? Yarona yau tun sabe be shigo ba Muhammad yace Wai yana kwance bashi da lafiya, gashi jibin bikin dayazo domin sa, inason inje inga yanayin jikin ne” Saita dawo suka mata bayan data fice Munirah tace” Waye yaron nata? Sadiq ne” Au shine babu lfyr? dariya sosai Munira ta fashe dashi yayin da Zarah ta tayata” Kinsan menene Zarah? Inajin ki? Idan na koma gida saina hadasu fada da Aliya, gaya mata zanyi yana da budurwa ita me rawar kafa akansa gara ta bari karya cuceta” * Sadiq meke damun ka? Sanyi nakeji Mamma Subuhanallahi tunda ka girma bantaba ganin ka kwanta ciwo ba, lfy lau fa ka shigo garin nan” Hannu tasa ta birkitoshi daga rufda cikin da yayi tare da daura hannunta akan goshin sa wayyo Sadiq kanka kamar garwaashin wuta dubi idonka inda yai jawur Sadiq Ina da Ina ke maka ciwo? Kaina ne kawai Mamma Sannu barin je in gayawa Baba tsoho ya turo akaika Asibiti” Bazani ba mamma, jibi bayan an gama bikin da daddare zan koma Nigeria” A’a dole kaje asibiti Sadiq saikace ana korar ku jibi jibin nan?” Tashi yayi ya zauna barin yi wanka nasan idan na watsa ruwa zanji dadi” Jiran shi tayi har yayi wankan ya fito ya goge jikinsa sannan yasa kaya yayin data shiga gyara gadon nan ya wuce masallaci yabarta Nan tai alwala tai Sallah sannan ta zauna har yadawo daga masallaci, sosai jikinsa yayi kau sai Jan da idonsa yayi” Barin tashi intafi tunda naga kaji Dadi, nabarsu Munirah da aiki, au na manta ban gaya maka ba, Jiya munirah tata kuka da daddare wai dana matsa Mata da tambaya sai tace min mafarki tayi……. Mamma kibarmin zancenta, ita ta sani” Kallon shi mamma tayi yayin da tai saurin ficewa adakin” Washegari baki ne keta turu ruwan zuwa zuwa gidan Baba tsohu dalilin bikin al’adar da za’ayi gobe, sallah kadai ke fita dashi dan har yanzun karfin hali kawai yake yi saidai duk abun da ake yanaji” Washegari masalin 6:30am yaga shigowan Muhammed da sauri, yana zaune Kan sallaya da qur’ani ahannun shi dagowa yayi yace lafiya” Me meyasa yariyar nan Munirah batajin mgn ne? Meya faru? Karaka takai gun Mamma hauwa yanzun tace tana Kiran ka” Mikewa yayi ya aje qur’ani sannan yace babu inda zani” Kasan idan bakazo ba ita zatazo harnan kadai san halinta ko? Toh Ina jiranta, ina iya yanke alaka da Tamudiriccin har abada, amman bazan bawa kowa hakuri ba” A’a abun bekai hakama Sadiq” Zama yayi Kan kujerar dake gefen gadon sa ya daura kafa daya kan daya tare da fadin, lallai yariyar nan ta raina ni da yawa, ai tariga takaini Kara, ko bata kaini karaba bazan sake shiga harkarta ba har abada, Muhammad natsana Munirah ko ganinta banson nasake yi arayuwata Karuta ka ajiye nacireta alisafina , Kuma ni yau zan Kuma gida komai dare……..???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? *SAWUN BAYA* ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ Page 21- 22 Typing……????️ Duk abun bekai hakaba Sadiq, idan kace yau zaka wuce ita Munirah fah? Ba abun daya dameni bane, sai Susan inda zasuyi da ita, rashin kunyanta ya isheni, nine zatakai Kara? Shigowan Mamma Hauwa yasa su yin tsin yayin da Sadiq ya dauke idonsa agurin” Cike da masifa ta shigo Kai sakona be sameka ba?? Naji Mamma banjin dadi shiyasa banzo ba” Bakajin Dadi?? Meya hadaka da Munirah ahanya ka daurata Amale ta fado?, Yanzun inda ta karye fah?, Waikai meyasa baka kaunar Kannen ka, haka kwanaki kasawa Zarah Ido Saida nayi da gaske, toh yanzun ma akan Munirah ka fita daga idona in rufe tun muna shaida juna, yariya zuwanta kenan kabarmu muganta rass sai muganta tana dingisa kafa?, Ko badakai nake mgn bane ? Inajin ki ai mamma, kaina ne yake ciwo” Allah ya sauwaka, amman kafita hanyarta inba zallici ba meye naka na daurata a amale?, Sannan Kuma kazo kabata hakuri” Hakuri Kuma?? Eh wani abu ne Dan kabata hakurin? Jimmm yayi zuwa can yace” Mamma badai kince nafita hanyarta ba?, toh nafita amman ni bazan bata wani hakuri ba” Au bazaki bata hakuri ba? Mikewa Sadiq yayi cikin yamutsa fuska yace, Mamma ita ta matsa saitahau, Kuma da kanta tahau, bani nasayata ba, amman dan Bata da kunya tace nine na daurata sannan Kuma kice in bata hakuri ni babu ruwana da ita” Jimmmm mamma tayi, ta tsaya tai shiru daga masifar data kwaso sannan tace” Haba dan Allah Sadiq, ka dinga rarrashin ta ka daina zarewa kannenka ido, duk garin nan kaita sani tare kukazo saika bige da mata mugunta? Ai shikenan an wuce gurin, nabari bazan Kara shiga duk wani shirgi nataba bare damin rashin kunya” Toh sannu ya jikin naka? Cikin kawar dakai yace naji sauki” Mutanen gidan fah duk suna kalau” Sunce agaishe ku” Muna amsawa, yan uwan nakafa Mubarak Sagir Lubbunah da Khadija? Suna lafiya mamma” Toh yayi kau, juyawa take kokarin yi tare da kallon fuskan Sadiq” Toh ka saki ran mana” Kawar dakai ya sake yi sannan yace bani da lafiya tun jiya ni yauma zan wuce” Cikin yaren buzanci tace haba wanni irin yau, sati biyu kakeyi yau ko ai kwanan ku uku” Ni daman wannan bikin nazo Kuma ana gamawa anjima tafiya zan yi” Toh Allah ya kiyaye hanya, Munirah fah? Idan ta gama saita taho” Shiru Mamma tayi sannan ta juya ta fice” Tana fita Muhammad dake tsaye can gefe yace yau ba masifar sosai” Tsaki Sadiq yaja sannan ya mike cikin Jan tsaki ya nufi toilet, wanka yayi ya shirya cikin manyan kaya sannan ya nada rawanin kamar yadda buzaye ke yi sosai yayi kyau, jikinsa ya fesawa turare sannan ya fito hannunsa rike da wayoyin sa” Shirye shirye kawai ake ahabar gidan tsoho wucewa Sadiq yake yana kallon yadda aka shirya gurin, cikin gidan tsoho ya nufa kusa da Mammah ya zauna wato mahaifiyar su Baban su, kwanciya yayi Kan cinyarta yayin data zame rawanin ta shafa kansa tana fadin” Meke damun ka Sadiq? Bani da lafiya mamma sannan ana nema na agurin aiki ayau” Lumshe Ido tayi sannan tace yanzun Yaya kenan megidan” Dole zan tafi ayau Mammah” A’a ai ako Ina ana uzuri, kasanar dasu baka da lafiya wannan doguwar tafiyar bazakayita kana cikin jinya ba” Nidai Mamma tafiya zanyi, nima inason naje din akwai abun da zan yi” Himmm Sadiq akwai dai abun da yake damun ka Gaya min meye shi? Inda akwai wani abu ai bazan boye ba, nidai da daddare zanwuce yanzun gidan su Annanin zani” Jikin kakartasu asanyaye tace toh Allah ya nuna mana anjiman, Munirah fah? Idan nakoma zakuyi mgn da Abbanin duk yadda yace shikenan” Mikewa yayi ya fice yayin da Mamma tabi Sadiq da kallo ko tantama bata yi, wani abun ne ya bata mishi rai, indai tafiyan shi zai Samar masa da kwanciyar hankali Allah ya kaishi lafiya” ****** Ganin fitowan Sadiq rike da wayoyin sa yasa Anass yai saurin dauko mota yayin da wani Kuma ya riko rakumi kafin ya isa gurin sun ajeshi gaban sa Dan haka yana karasowa gurin yaiwa Anass alama da hannu cewa ragumin zaihau dan haka ya koma da motar” Tafe yake cikin garin na Ingall Kan ragumi yayin da komai bayya masa dadi Mutane da dama ke miko gaisuwa daga hannu kawai yake batare dayasam suwaye ba” Misalin sha biyu na rana ya isa daman tuni suna da lbrn zuwan sa, wasu kanana yara ne guda biyu suka fito duk Mata, yayin dayai saurin bude musu hannun sa sukuwa aguje suka hayeshi shima rungume su yayi” Kananan yarane da bazasu wuce shekara goma ba, rike da hannun su ya shiga cikin gidan yayin da wata Dattijuwa kecewa lala Barka da zuwa” Amsawa yake fuskanshi babu walwala dan haka kakar tashi tai saurin shin fida masa tabarma tare da fadin” Yaya dai Sadiq da alama kana da damuwa sosai” Bakomai Hajiya nasameku lafiya? Lafiya Alhamdulillah Duk suna gaisheku kowa yace agaidaku” Muna amsawa, ai ban tsanmaci zuwanka ayau ba, nadauka sai zuwa gobe ko jibi ganin yaune bikin gidan naku” Eh Nima haka naso Amman Kiran gaggawa yasameni anjima zan tafi shiyasa nace barin zo karkuji nakoma kawai” Yau?, Yau yau mu din nan? Lafiya ko? Eh lafiya lau yanayin aiki ne” Shiru tayi, tana nazari zuwa can yace toh kanwar takafah ya bakazo mana da ita ba? Ita tana nan, zatazo kafin ta wuce” Amman sai naga kamar wanni abu na damun ka” Kansa ya shafa sannan yace jiya nayi fama da zazzabi” Kallo tabishi dashi, yayin daya mike yana fadin Ina bilkisu fah” Tana nan dakin ta inajin batasan da zuwan ka ba” Hajiya kice Mata takawo min shayi zan dan kwanta in huta kona awa daya ne” Bayan fitan shi befi da minti biyar ba yaji tahowowan Bilkisu tana fadin” Amukarnin ni daneke Shirin zuwan ka gobe kofar yaran dazon suka bude Mata ta shiga, yayin da daya yariyar take dauke da tire dayar kuwa budurwar yariya take budewa hanya, sosai fara sol da ita hannu ta take dagawa sama dalilin Jan lallen data kunsa” Tiren yaran suka aje sannan suka fice Sadiq kuwa yana kwance awani dan siririn gado dayasha shin fida” Yariyar kuwa zama tayi abakin gadon tana me zuba masa Ido” Idon shi alumshe yace meye wannan ahannun ki?? Lalle ne na yi” Kije ki wanke banso” Ya mutsa fuska tayi, dan beriga ya kama bane ka gani idan ya kama zai burgeka” Nace banso ko? Mikewa tayi da sauri ta fice cikin buga kafarta akasa, zuwa can ta dawo tana goge hannunta yayin dashi Kuma yai saurin tashi zaune” Zunburo baki take har yanzun, yayin shikuma take binta da harara kokarin sakin fuska tafara dan tasan halinsa sarai dan haka tai saurin zuwa kusa dashi ta zauna ahankali ta mika hannunta ta kwance rawanin sa yayin data ajeshi agefe, kasa ta sauka ta zauna asaitin kafarsa tare da daukan kafar duk da takalmin nasa ta daura akan cinyanta sannan ta zame takalmin dayar ma haka tayi sannan ta zame safar yayin data rike kafar guda daya ta bita da kallo” Abubuwa da dama take kiyastawa cikin ranta ganin duk be mataba ta dago daya kafar ta sunbata yayin da Sadiq yai saurin lumshe Ido tare da dago dayar kafan ya mika Mata, aje waccen tayi kamar ta aje kwai sannan ta kama wadda ya miko Mata ayanzun itama sun batan sa tayi yayin da Sadiq ya mike da saurin sa ya dagota ya rungumeta ajikin shi tare da sunbatan goshin ta yana fadin nagode” Kallo juna sukayi tsayon minti 5 sannan Sadiq ya wuce bakin Dan karamin window dake dakin ya bude labulen ya tsaya agurin” Binsa da kallo Bilkisu tayi ahankali ta fara takawa harta isa bayan shi ta tsaya, wasu irin gauron numfashi taja har sau biyu sannan ta Mika hannu ta ta rungumeshi ta baya” Lumshi Ido Sadiq yayi tare da ajiyan zuciya ahankali ya rike hannun nata sannan ya juyo yana me kallonta idonsa ciki da wani farin ruwa, kallon juna sukayi na tsayon lokaci sannan yayi Mata wani irin wawan runguma daya sata sakin ajiyan zuciya batare data shirya ba” Sosai suka rungume juna tsayon lokaci ganin duk hakan be masa ba ya dauketa cak ya ajeta tsakiyar Dan karamin gadon sannan ya balle butirin hannun rigarsa tare da cire na wuyan sannan ya cire rigar yai wurgi da ita gefe, lokaci daya ya hau kanta tare da rungumeta sosai ta yadda har suke iya Jin bugun zuciyoyin junan su” Yadda yake goga kirjinsa sosai anata yasa gaba daya Bilkisu ta fice cikin hankalinta yayin da take Kara rungumeshi, adaidai wannan lokacin bazata iya hanawa ba, ko wani yinkuri sosai yanayin ke mata dadi dan ma kirjinta narage mata dadin dalilin radadin da suke Mata saboda yawan gurza kirjinsa da yake agurin sosai radadin ke damun ta Hannunsa yake kokarin turawa cikin rigarta taji yaja dogun tsaki tare da janye hannun nasa yana fadin” Astagfirullah ya rabbi” Gefe ya koma sannan ya sauke kafarsa cikin sauri ya nufi toilet din dake cikin dakin” Yafi karfin awa sannan ya fito yana goge jikinsa tare da kallon Bilkisu dake gyara gadon yace baki tafi ba?? Cikin Jin kunya tace a’a inajiran kasha shayin saina wuce da kayan” Tahowa yayi ya zauna bakin gadon ya karbi kofin data miko masa yana fadin” Jeki abinki nagode” Juyawa tayi tana tafe tana waiwayen sa shikuwa tana juya baya ya dauke idonsa akanta lokaci daya ya shanye shayin sannan ya mike ya fara shiri dan yasan yanzun an riga da an fara shagulgula” Cikin sauri ya fito yayin daya dan saki ransa kadan fiye da sanda yazo” Sallama yayi da Dattijowar kakan shi mahaifiyar mamanshi yayin dataita sa masa albarka yana amsawa da ameen Har yahau ragumin sa Bilkusu tana tsaye idonta cike da hawaye, murmushi yayi sannan yasa hannunsa ya ciro kudi ya mika Mata yana fadin saina sake dawowa” Yaushe?, Tayi tambayan kamar zatai kuka” Kibari zamuyi waya” Karyar dakai tayi tare da fadin nagode” Har yai nisa tana tsaye har Saida ya bacewa ganin ta” *Lokacin dayai zo anyi nisa da shagali dan haka wanka kawai yaje yayo sannan ya sake fitowa akaro na biyu Cikin shiga ta alfarma” Sakin jiki yayi aka gabatar da komai tare dashi duk da dai shi ba rawa yake ba amman yayi rawani Kuma yayi busa irin Busan da Munirah ke so sosai Kuma take taka rawar ta” Duk da tsanar da tai masa Saida ta saurara har yagama sannan ta kalli Zarah tace, tir yau dai su Zarah basaban ba” Dariya Zarah ta kwashe dashi tare da fadin Munirah uwar fadin rai , wai yaushe zakibar fadin rai dacin buri tsiya? Kyalkyalewa da dariya Munirah tayi sai randa kasa ta cika bakin sa, da hancinsa tare da idanun sa, sannan burinsa zai cika” Lalala Munirah kice min ranar kwanan sa nafarko akabarin shi” Dariya suka Kuma kwashewa dashi Saida sukayi ma ishi sannan sukashiga fili sukayi rawar su sosai ” Saidai ayau Sadiq naganin Munirah ta dosu gurin ya maida hankalin sa Kan baba tsoho yayin da yake Jan sa da hira” Ana Kiran Sallar mangariba taron ya tashi yayin da baki sukayita wucewa na gida kuwa cikin gida suka shiga” Munirah da Zarah ne zaune Kan sallaya sun ida Sallah ta jawo Jakarta ta lalubo wayar ta data aje tun safe” 8 missed call tagani duk daga Sagir, yayin dataga sako guda daya” Budewa tayi sosai yau take cikin nisha di ganin sakon Sagir ta farin ciki ya Kara mamayeta, cikin nutsuwa ta shiga karanta guntun sakon data gani” Nakira baki dauka ba, da gaske Wai Sadiq zai taho gida ayau ke Kuma ya barki can?…..Mmn Yazeed07014197556???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/Page 23- 24Typing……????️Mikewa tayi tsaye da saurin ta, tare da fadin, a’a tare zamu dawo” Yau din?, Sagir ya tambayeta” Shima ai bayau zai dawo ba” Moh’d ya gaya min cewa kinkai Karan Sadiq gun Mamma Hauwa harma ta rufeshi da fada anyi haka??? Jimmmm tayi zuwa can tace eh” Himmm, ainagaya miki ki nutsu kishiga hankalin ki, Wai mesa bakijin magana, shikenan saiki shirya zaman Ingall dan yau dinan Sadiq zai baro Ingall” Tsuntan kanta tayi tana zubar da hawaye tare da fadin, wayyo Amukarnin Sagir, wlh banson ya tafi ya bar ni, dan Allah ka kirashi ka lallabashi yabari mu tafi tare, idan ma har yau din xai tafi na yarda zan bishi wlh akan yabarni anan???? Kingama mishi rashin kunyan Kuma saina kirashi nabashi hakuri?, Shikenan nina goyi da bayan ki dinga mishi rashin kunya kenan?, Yayana ne fa, ni Ina burin in aureki ace kuma baki da abokin fada sai yayana??? Nabari toh Amukarnin, dan Allah kabashi hakuri kaji, nidai kawai yayi hakuri ya maidani gida dan Allah kaji????????” Shikenan Ina zuwa” ****** Ance yau zaka dawo? En Ina shiryawa yanzun haka” Munirah fah??? Idan ta gama kwanakin nata kana iya zuwa ku tafi tare, ko daga nan asata ahanya” Nidai dan Allah alfarma nake nema, kayi hakuri ka tahomin da ita dan Allah Tsaki Sadiq yaja sannan yace ninasan cewa daman yariyar nan bata da kunya shiyasa banso aka hadani wannan tafiyar da itaba, rashin kunyanta ya wuce misali, nasan mutane da yawa na shakkan kallon idona amman saboda rashin kunyarta can cikin idona take kallo banason alkarka da ita Sagir, banson mutum mara kunya” Zata Bari Amukarnin dan Allah kayi hakuri itama tace in baka hakuri batason ka tafi ka barta” Karya kakeyi Sagir bazatace hakaba, ai ita yanzun taga guri sunata jida ita, sannan Kuma ta hadu da daya Mara kunyan” Nidai Kai hakuri kataho da ita” Kasan Allah Sadiq, yau zan taho, Kuma wlh wlh kaji narantse ko Tamudiriccin zata mutu bazan jerah hanya da ita ba, tana abu kamar ballagazar mace, mgn ajirgi hira da maza da matan da bata sansu ba, wasu da dama sun shiga jikinta tayi pic dasu sannan Kuma da tabada sadakar number wayarta wa kowa, daga murya yake yayin da yake mgnr cikin daga murya tare da nunawa da hannunsa kamar Sagir din da yake mgn dashi yana gaban shi, idonshi jawur yayi gawani ruwa ruwa kwance acikin idonshi, yayin da jiyoyin shi nakai ke radowa” Shima Sagir gaba daya ransa yagama bacci daga halin Munirah da Sadiq ya zayyano, Kuma kowanne ciki yasan zata aika, sosai kishi ya kamashi yayin dayai kasa da muryan domin daker yake iya mgn yace” Sadiq tunda tai haka kana tare da ita idan babu Kai Kuma yaya zata yi??, Dan Allah kayi hakuri kasawota agaba” Katse Kiran yayi tare da kashe wayar gaba daya dan shiyasan yadda yakejin haushin Munirah, haushinta yakeji ba kadan ba” Shima Sagir yana sauke wayar ya sake Kira yayi jinta kashe yasa ransa ya Kara bacci cikin fushi ya nemi number Munirah, cikin fada ya zayyana Mata abubuwan da tayi kamar yadda Sadiq ya gaya masa, bayan ya gama be jira jin wani zance daga karetaba ya kqshe wayarsa gaba daya” Itama Munirah hankalinta sosai ya tashi kukan da take kunshewa ta fito dashi fili” Lokacin ita kadaice adakin ganin kukan bazai masa ba ta yanke shawaran zuwa kawai tabawa Sadiq hakuri” Mikewa tayi ta fito bayan ta share hawayen ta sosai saidai duk wadda yaganta yana iya gane taci kuka” Zarah kizo ki rakani inda Sadiq yake” Cikin Mamaki tace wanni Sadiq din? Sadiq dinmu, Wai Shirin tafiya yake yabarni anan fah” Toh sai mene Dan yabarki anan, da zakozo goyaki yayi?? A’a koda be goyaniba dai nafison yadda mukazo tare mukoma tare” Wanni irin kallo Zarah ta Mata sannan tace bantaba sanin baki da wayauba sai yau kawai dan yayi barazanar tafiya yabarki saiki wani birkice har kibashi hakuri” Zarah nidai ki nuna min hanyar da zan bi inje inda yake dan Allah” Cikin tabe baki Zarah ta nuna Mata hanyar yayin data mike ta nufi gurin hasken fitulun kawai take gani kasancewar dare yayi” Tunkafin ta isa gurin ya ta tabbatar ta part dinsa dan haka ahankali ta dinga takawa har ta isa gaban part din” Turo kofar tayi ahankali yayin data shiga falon cikin sanda dan tunda take bata taba shiga part din Sadiq ba ko can gida” Afalon ta tsaya ta dinga kwada sallama Amman ba’amsa ba, duk da cewa falon ya burgeta amman Bata da lokacin tsayawa ta kalli gurin” Saida tayi sallama kusan sau goma sannan taji ance waye ne?? Jikinta ne ya fara rawa dalilin rashin sabo da yanayin cikin rawa faki tace nice” Shiru taji zuwa can tajishi cikin kasaita yace wa kenan?? Munirah ta fada ahankali” Bata sakejin muryarnsa ba har tsayon minti 20 har kafafunta sun fara gajiya da tsayowa, hanya data jiyo muryan sa ta zubawa ido tun dazon Amman har yanzun shiru” Karan motoci tafaraji waje tare da kukan rakuma hakan ya tabbatar Mata da Sadiq da gaske tafiyan zaiyi sosai hankalinta ya tashi cikin sauri ta fara takawa har ta shiga cikin dakin baccin nasa batare data sani ba” Zaune yake cikin shirinsa tsaf na tafiya, kananan kayane acikinsa cikin irin shirinsa da yayi ranar da zasu taho ya daura kafa daya kan daya ” Dagowa yayi ya kalleta yayin dayai saurin daukan gilashin shi dake gefe yasaka tare da gyaran murya” Itako Munirah tsaye tayi tana wasa da hannunta tare da Satan kallon shi tana kokarin yin kuka” Shima dagowa yayi ya kalleta sau daya sannan ya maida hankalin sa ga wayanshi fuskansa ko kadan babu walwala” Yadda take wasa da hannunta kamar zata karya su da alama batama sanin abun da take yi” Daker ta iya bude baki cikin siririyar muryarta tace” Wai yau zaka gida?? Dagowa yayi cikin sauri ya kalleta sannan ya sake maida kansa gefe tunda yake da ita bata taba masa mgn cikin taushin raiba sai yau, dagowa yasake yi ya kalleta yadda take lankwasa hannunta kamar zata karya yasashi ya fara fahimtan halin da take ciki dan haka yace, eh yau zan wuce wani abu ne?? Kaita girgiza alamar a’a Toh meya kawo ki, me kikazo yi anan?? Batare data kalleshiba tace bakomai” Cikin kada hannunsa yace maza kibar nan gurin toh ni ba sa’anki bane” Hawaye ta matso ya sakko kumatunta sannan tace ni idan katafi kabarni ni Yaya zanyi naje gida???????????????? ” Batare daya kalleta ba yace, duk ma yadda zakiyi ni ba matsalata ce” Fashewa tayi da kuka tare da zaman durshe akasa idonta akanshj irin kukunan nan dake nuna magiya nake Amman yai banza da ita Tirtirje kafa take tare da shashekar kuka , kukan rakuman data sakeji yasa hankalinta ya Kara tashi sosai ” Hankalinta bekara tashiba Saida taga ya mike yayin da Anass ya shigo ya dauki akwatin Sadiq ya fita dashi Ganin Sadiq ya mike ya dauki wayoyinsa ya zagayata ya wuce yasa ta mike da sauri tabi bayan shi, yayin da yana cire kafa tana jefa nata cikin kuka sosai, ganin tana miko hannu da niyar rike rigarsa yai saurin Kara gaba” Jama’a ne burjik wajen ciki harda Baba tsoho da Mammha tare da Kannen babansu dukka kusan duk dangin babansu na gurin dalilin yaune akayi bikin al’adar gidan Baba Tsoho” Kukan da Munirah take hankalin mutane ya koma gunta, ganin yana shirin isa kusa da ragumin tai saurin mika hannunta ta rike rigarshi cikin kuka tace Amukarnin dan Allah karka tafi ka barni” Rigar tasa ya riki yana fadin, sakeni dallah, bige hannun nata yayi yayin data sake rarumoshi cikin daga murya yake fadin karku barta ta tabani ke kina da hankali kuwa” Duk yadda su Mamma da Zarah ke kokarin rike Munirah sai kubcewa take, tanayin kan Sadiq dan haka ya fara kakkauce mata cikin gudu gudu harda tsalke yayin dayai caraf ya haye ragumin” Yadda yake gudu tana binsa yabawa mutanen gurin dariya, bakowa sukewa dariyar ba sai Munirah domin kowa ya kula kuka take yayanta zai wuce yabarta” Jin ransa yake fari karrr ayau, yana saman ragumin ya kalleta, inda tasa saddan hannunta daya afuskanta tana shashekar kuka, dariya ne keson kwace masa yaji muryan tsho na fadin” Shasha kawai, ko kunya bakiji kinawa sirinki kuka?? Cikin dariya Mama Ayaha tace siriki kodai yayanta? Baba tsoho ne ya sake cewa sirike mana baki da labarin Sagir da Munirar sun shirya kansu?? Hamdalah akaitayi agurin yayin da kowa yake dauke da fara’a har yanzun ba’abar yiwa Munirah dariya ba kuka harda majina yayin da akacigaba da tatttauna zancen Munirah da Sagir, dake duk sun San Sagir kowa fadi yake aikuwa sun dace da juna su” Sosai Sadiq yaji Mamakin yadda har su kasan da wannan mgnr, kenan yanzun acan Nigeria kowa ma Yasani kenan???? Sunkuyar dakai yayi cikin sanyin jiki sannan yace ni zan tafi lokaci na kurewa” Mammah ce tace niko Sadiq dakayi hakuri ka Kara ko kwana biyu ne ka wuce da ita dan idan kabarmu da yariyar nan ka barmu da aiki” Ni yatafi Dani kawai yanzun, baba bazan zauna ba” Tsaki Sadiq yaja sannan ya kwashi ragumin nasa aguje, kamar jira take itama ta kwasa da Gudu tare da shiga gabanshi” Daker ya iya tsayar da rakumin yayin dayaga Munirah tsugune akasa tana fadin Amukarnin Sadiq dan Allah kayi hakuri ka gafarceni katafi dani dan Allah???? Shiru yayi yana kallonta tare da ajiyan zuciya sannan ya sakko akan rakumin lokaci daya, yana goge hannunsa yace naji Amman sai in kin tsuguna nan gurin, gaban kowa kin kama kafata kince na yafe miki daga sharri da kika min….. Bekai ga rufe bakiba ta tsuguna ta rike kafar sannan tace kayafemin nabari bazan Kara makaba sharri” Zame kafarsa yayi, yayin dayai saurin komawa cikin gidan” Mikewa Munirah tayi tabi bayan shi yayin da mutanen keta Mata dariya dayawa fadin suke lallai yariyar nan shagwababbiya ce” Afalo ya zauna tare da sauke ajiyan zuciya ajejjere, ganin shigowan Munirah yasa shi dauke kansa, tomeye Kuma Zaki biyoni nan?? Ni tsoro nakeji kar intafi ka gudu” Ganin shigowan Baba tsoho yace Baba zan nemi alfarman akara min kwana biyu acikin kwana biyu taje ta gaida yan uwan mamanta sai mu wuce” Cikin murmushi Baba tsohu yace hakan yayi Abubakar, tunda tana da kawazuccin gida gara ta wuce, idan anyi bikin nasu saitazo tare da Sagir din duk anuna mata dangi tasan Kuma kowa” Lumshe Ido kawai Sadiq yayi ya kosa subarshi shi kadai yasha magani domin ji yake zazzabi na neman rufe shi” Munirah tagaba tayi, bayan taji Sadiq yabar tafiyan, saidai tana fita harabar part din nasa tafara maganganu cikin murmurguda baki saidai bamejin abun da take fadi” Shikuwa Sadiq bayan fitan Baba tsoho gado ya fada vatare daya cire ko takalmin saba, afili yake fadin” Mgn ta watso Sagir da Tamudiriccin sun daidaita, shikenan kowa ya sani, kansa ya shafa yayin da idonsa yai jah, iska ya fesar sannan yace shikenan kowa cewa yake sun dace da junan su, Ina wani dacewa agurin mara kunya?, Ya fada sannan ya daki gadon da karfi ya Kuma shafa kansa shikenan tunda kowa yace sun dace ni ma dole nace sun dace, yana mgnr yana nunawa da hannun shi cikin fada fada kamar meyi da wani” Mikewa yayi yaje ya sha ruwa me sanyi sannan ya dawo ya zauna number Sagir ya Kira kamar jira yake ya dauka cikin ladabi yagaidashi” Amsawa yayi cikin fara’ar daya kirkirota yanzun nan sannan yace” Yanxun na huce saboda nasata dole tabani hakuri, zamu taho jibi, sabo dakai duk nayi hakan, nasan idan nadawo bata bazakaji dadiba, kuma tunda yanzun takace bazan barta tayi wani abu dabe dace ba ahanya, ka kuma gaya mata yanzun matsayi biyu nake dashi agurinta, Yaya da Kuma siriki, bana son raini” Wani irin Murmushi Sagir yayi ganin dan uwan nasa ya dauki girnan shi cikin farin ciki yake gode mishi tare da tabbatar mishi insha Allahu girmamawa ne tsakanin shi da Munirah” Bayan sun gama wayar hannu Sadiq yasa ya share fuskanshi yayin da yaga ruwa ahannun sa hakan yasashi saurin kwanciya agadon tare da daukan filo ya danne kanshi dashi” Washegari tun da sassafe Munirah tawuce gurin dangin mamanta cikin rakiyar Zarah” *Da misalin 11:00am Sadiq ya shiga cikin gida gurin kakar tasu zaune take tana cin dumamen tuwo da ke dashin kamshin man shanu” Zama yayi gefenta yayin da yake mika gaisuwa amsawa tayi tare da mika masa ruwa ungu wanko hannun ka kazo muci” Amsan ruwan yayi ya ajiye agefe sannan ya cire gilashin idonsa yana fadin banajin yunwa” Cak ta tsaya bakinta cike da lumar tuwan datakai bakin ta, tana kallon fuskanrsa” Sadiq meya sameka haka, Wai meke damun kane, nakasa ganewa, idonka kamar garwashi sannan sun kankance kamar zasu rufe, harjini ya kwanta daga kasa, sannan gaba daya gefen idon ka yayi bakin Kirin, ga hancin ka yayi jah sosai, baka kalli madubi bane ka fito?? Mikewa yayi ya taka ya isah bakin kofar, daga labulen dakin yayi ya leka tsakargidan sannan ya dawo ya zauna yana lashe lebensa tare da daura kansa akar kirjita, hannu shi ya tura acikin nata na hagu ya runtse tare da lumshe idonsa……. Mmn Yazeed???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ GAISUWA TA MISAMMAN GARE KU Beauty Khadija Uthman maruciyar MATSALARMU Salmah Sadiya Mohammad Hafsat yusuf Maman Kairy Ummy afrah Zainab Bayaro Fatima Billiya Mmn Musaddik & Maman humairah Ina ganin Comments dinku akoda yaushi???????????????????????????? Page 25- 27 Typing…….????️Sayin dataji akan kirjinta yasa ta kalli fuskan shi” Subuhanallahi, Sadiq meke damun haka? Hannunta ya Kara runtsewa cikin nasa tare da fadin Mamah Sagir nason Munirah sosai fah, sun shirya dashi da ita zasu yi aure Wai a tsakanin su” Runtse idon tayi cikin nazarin kalaman shi, zuciyarta ce ta tsinke gaba daya, yayin da bata bude idontaba Saida hawaye yazobo Mata, tsintan kanta tayi da tura hannunta cikin gashin kansa tana yamutsa gashin cikin sigar lallashi take fadin” Toh ai kaga abun da nauyin bakinka yajawo maka ko? Gaba kake da Sagir, shekara 6 ne tsakanin ka dashi, ya akayi kabari harya furta kai ka kasa? Nidai yanzun Mamman ba wannan ba, abun da ya faru ya riga ya wuce, saidai narasa yadda zanyi Kuma, Yaya zanyi ne Mammah” Sunkuyar da kanta tayi sannan ta dago ta kalleshi tace” Sadiq ka nutsu ka dawo cikin hankalin ka kawai, karkayi abun kunya, kanin ka ya ruga ya furta, Kuma yariyar ta amince, dan haka kaga zancen kama be taso ba” Hakane, Nima nasan haka mammah, Nina barta har abada, ni yanzun bansan meke damuna bane kawai” Kansa tacigaba da shafawa tare da fadin” Allah ya kwantar maka da zuciyarka Sadiq sannan zanta addu’a Allah ya baka wacce ta fita, ka Kuma sota fiye da yadda kaso Munirah, dan Allah bayan tafiyan ku karnaji wata mgn Kuma, hakan na iya jawo kiyayya dagaba wacce bamusan iyakarta ba, karika da ka aikata kuskure” Ni babu zancen dazai taso daga gareni insha Allahu, nafi kowa kin hakan koma koda Tamudiriccin ta rage ita daya kwal aduniya babu aure tsakanina da ita, idan na wuce guri bana sake waiwayen sa” Kadaiyi shiru Sadiq….. Eh mana Mammah, ni bana waiwaye, ko kintaba ganin Ina tafiya na waiga bayana??, Munirah tana bayana Mammah na wuceta har Kuma abada, bazan sake waiwayenta da waccen fuskar ba” Da Ido Mamah ta bishi tana me fadin Allah yasa hakan shine yafi alheri” Ameen ya fada tare da mikewa ya haye gadon Mamah, rufda ciki yayi, yayin da Mamah ta bishi da kallo, tunda ya kwanta agurin Sallah kawai ke tadashi, nan dakin mama yake sannan yakoma gadon ya kwanta, kallon sa kawai Mammah take Bata mai tayin abincin dan tasan bazaici ba, ranan adakin Mammah ya kwana da abune yaje masallaci ya dawo ya sake kwanciya” Misalin sha daya na rana Munirah da Zarah suka dawo ganin Sadiq kwance dakin Mammah abun ya basu mamaki, zama sukayi nan suna hira da kakarsu, yayin da Munirah ta shiga tattara kayanta tana hadawa cikin akwati, ganin ya tashi zaune duk suka sunkuyar da kansu, yayin da Mamman ta kalleshi tace toh tafiyar taku ta dare ce ko ta yamma”?? Kaina naciwo sosai Mammah inaga sai gobe da safe tafiyan yanzun zan shirya Anass zaizo mu fita” Toh Allah yakaimu goben” Mikewa yayi ya fita, yayin da Munirah tace Mammah Wai bashi da lafiya ne naga kamar idonshi sun kunburah?, Kuma naji yace kanshi na ciwo???? Eh Bayajin Dadi tun jiya, nan dakin ma ya kwana” Lallai kina da mukami matar tsoho, tunda har wannan dan fadin ran yaga gurin kwanciya anan” Cikin dariya Zarah tace Mama halan har kukan shagwaba yai miki Naga idonsa yayi jah” Ciwon Ido ke damun shi, kinsan ciwon Ido akwai saukar da ciwon kai…… Allah ya sauwaka Amman, amman fah alhakina ne najiya, daman nasan sai Allah ya saka min, dan nariga na tsine tun agida” Kika tsine me?, Mammah ta tambaya” Nifah bana shiri dashi Mama, yaki jinina tun tuni, aduk gidan ya tsaneni ni daya kuma Kicere aranki Muniratu babu tsanarki aranshi” Wlh matar tsoho ya tsane ni, yana mgn da Lubbunah da Aliya amman ni daya budi baki sai yace banda kunya, ni fitsararriya ce sannan dayaji muguntan sa ya biyoni har daki ya dakan, ranan nan garin doka saura kadan ya fasa min nonona shiyasa na tsane shi fiye da misali” Dariya sosai Zarah ta fashe dashi har tana rike ciki, bayan ta sarara tace a wannan ai iskanci ne, in banda iskanci Ina ruwanshi da nonon ki???? Shidai ya sani, dan nidai nariga na tsine wlh ko ba dade ko bajima duk saddan yaimun zallici Allah ya isa kawai” Tabe baki Mammah tayi tana kokarin mikewa tace kwayi kwa gama, shidai Sadiq yafi karfin ku saidai gani sai harara daga nesa, ai karyar rashin kunya kike tunda shekaran jiya bakin ki mutuwa yayi Aini kawai wayyo nayi minshi yakaini gida, gashi dan tsabar gulma yaje ya hadani da Amukarnin Sagir yaki daukan wayata, ashe muna tafe yana samin Ido, duk wani numfashin na saina ya kirga ya gaya mishi, kina ganin shi haka kamar be iya mgn ba himmm” Sosai Mammah ta rike baki tana kallon dan mitsilin bakin Munirah, sannan tace, Himmm lallai???? haka kike daman, Ashe keda Zarah zanice ta tadda mujemu, ai danasan haka kike da shekaran jiyan nan ce masa zanyi ya take ki da da Amale….. Sai na roko Tsoho ya take mu tare” Dariya Zarah ta Kuma sawa cikin dariyar take fadin wayyo ni sister Ina sonki zan barki, wayaga idon Mammah tsoho yatafi yabarta… Kinsan kuwa rakumin natakasa mutuwa zaiyi….. Mikewa Mammah tayi tana fadin Wai, barin baku waje, kungama da Sadiq din ne Kuma kuka gangaro Kan Mijin naku” Ficewa tayi tana fadin, Wai akwai aiki, wannan ai daidaita Sagir din” * Agajiye ya koma part dinsa yana cike da Jin gajiya yana kokarin fadawa gadon nasa yaji alamar Kira ya shigo wayar sa” Ciro wayar ya kallah” Aliya yagani nan danan murmushi ya bayyana afuskanrsa” Ganin da yayi Video call ta kirasa yasa ya nemi guri ya zauna sannan ya amsa” Ganinta yayi Zaune tana dada gyara lafyarta cikin fara’a sosai tace” Amukarnin yau 1week da tafiyan ku amman ko dan Kira babu” Lumshe idonsa yayi aike yakamata ki kirani kiji saukan na Amman ai bakiyi hakan ba” Sunkuyar dakai tayi tare da murmushi ai tsoro nakeji kar in dameka…. Bakya cikin mutanen da suke damuna Tamudiriccin, ki daina shakkar kirana ko fadan wata mgn daban” Dagowa tayi cikin murmushi ta kalleshi yayin da tai saurin sauke kanta kasa dalilin idon da suka hada” Kallonta yaitayi kamar yadda ya Saba idonta akasa saidai cikin jikinta takejin kallonta yake yi, dagowa tayi ahankali, Ido suka sake hadawa dan haka tai saurin saka tafukan hannunta ta rufe fuskarta cikin yanayin dake nuna taji kunya” Take yaji yanayin da bayaso ya sameshi cikin mutuwan jiki sosai yace” Meyasa kika rufe fuskan ki?? Kaine kake kallo na” Bakyason in kalle ki? Ahankali tace eh” Toh meyasa kika kirani video call? Ni so nake in ganka kawai” Kawar da kansa yayi cikin murmushi sannan ya juyo yana kallonta yana fadin to ai gani ki ganni” Ganin zasu hada Ido tai saurin kawar da idonta tana fadin ai naganka” Wani irin Murmushi yayi tare da fadin himmm ai nasan bazaki iya ba Aliya, bakaramin jarumi bane yake iya hada Ido dani, sannan kuma zakiga bamu cika shiri ba ni dashi” Amukarnin niba jaruma bace kenan? Murmushi yayi yana kallonta kasa kasa yace” Zadai kizama jarumar idan muna tare, yanzun gobe zan dawo tunda baki bani tsara ba ni ki fada min tsarabar mene zan kawo miki?? Cikin wasa da hannunta tana me kallon hannun nata tace nafison ka kawo min zabin ka banawa ba” Kashe idonshi yayi cikin murmushi yace dakau Tamudiriccin shiyasa kike burge ni” Idonta ta lumshe cikin murmushi sannan tace Nima me zan shirya maka matsayin tarba?? Murmushin shi ya Kara fadadawa ni ganin ki ma kawai ya wadatar dani” Nidai a’a yanzun fah kace da zaka tafi ban baka komai ba” Shikenan ki tanadar min Madara, inason Madara sosai” Da haka sukayi sallama yayin da Aliya take cike da farin ciki hakama Sadiq wani irin sanyi yaji aransa yayin da ya aje wayar neman ciwon kansa yayi ya rasa wanka yayi ya shirya cikin shiga irinta buzaye sannan ya fito, Anass ne ya taho da mota suka shiga saidai wannan lokacin tafiyan tasu canza akala tayi daga zuwa Asibiti ya bige dazuwa yiwa Aliya sayayya” Kasuwa suka shiga yayin da yaita zaban ma Aliya kaya har kala biyar, tare da takallama kafa uku, sosai zabin sa ya burge Mata dake gurin, yayin da akaita binsa da kallo yana dauka yana ajewa saiya zaba ya darje yake ajewa agefe, matan gurin kuwa kuskus sukeyi cewa duk wadda akayiwa wannan siyayyar yar gata ce gurin sa, bayan tagama ne yazabi sarkar gwal ya hada da ita, fitowa sukayi Anass na rike da ledojin” * Lubbunah!! Kina Ina?? Gani nan Umma” Yauwa dan Allah ki Kira Aliya kutafi cefanan dan tun yau zamu fara aikin wannan karon fitowan safe zasuyi bana dare ba” Toh Umma Inna Zaki toh” Part din Sadiq zani na gyara mishi” Umma da kanki?? Toh ai kinsan halinsa Lubbunah, bayason kowa ya shigar masa shashin sa musamman idan baya ciki, Kuma na tabbatar Kona tura wani saiya gane bani bane na gyara” Wlh Umma ki daina biye mishi, bara nakira Aliya muje mugyara” A’a gwara na gyara yanzun ma ai ba aiki nake ba na motsa jiki” Daga haka ficewa tayi, acan part dinsu Aliya kuwa yau tun da Sassafe ta tashi da gyaran dakin Munirah sai dai tanayin gyaran cikin ranta take fadin, Ina aikin da baza agode min ba, da wuya muyi dadin awa uku nasani, shirri zataitawa Amukarnin Sadiq nasan, yanzun laburuka na nan cike da bakinta, na tabbatar yanzun bakin Munirah yana zuba kaikayi, dariya tayi ita kadai adakin, sannan tace Allah yadawo mana daku lafiya duk da rigimarki sai gidan yayi shiru da Bata” Ingall Nifa nagama hada kayana waccen ishashshen kawai nake jirah” Kallon ta tsohowar kakar tasu tayi sannan tace” Kida bi ahankali, duk kinbi kin dami bawan Allah abun da ke damunsa daban dan Allah ki rabu dashi” Toh Mammah shine fa saiyaita yanga harya zarta mace, yana mgn daker, nifa natsana ya kallen hararata kawai yake” Tabe baki tsohuwa tayi sannan tace yadaifi karfin ki shiyasa halinsa duk yabi ya dame ki, shikuwa kinga dake da Kashi duk daya, sai kiyi tayi shi besan kinayi ba” Cikin fushi sosai Munirah tace, ai daman nakula dake duk garin nan kece kadai kike nuna kinfi son Sadiq akaina, dan haka Nima ban damu dake ba, shiyasa kikaga bana zama gurin ki” Ai daman wadan da kike zama gurin nasu suna iyayanki bani ba kita zama can din…… Shikuma Sadiq din ai ke kika haifeshi shiyasa bezuwa gurin kowa yana manne kusa dake ai” Dariya kawai tsuwar tayi tare da mikewa tana kokarin barin dakin” Ganin Haka Munirah data kule sosai tace” Ni bansan kina son Saba saikin daukeshi kinsashi acinyan ki kin bashi nono” Dariya sosai tsohuwar tasake yi, tsohon zance kenan, idan kin koma ki tambayi ubanki yabaki lbr na nawa Kuma, tun sadda aka kawoshi yaye yake wannan, Saida hankali ya fara shigan shi tukun yabari…… Ashe nono be isheshiba aka yaye shi” Koma dai mazakice kin dade bakice ba, kuji min yariya da dan banzan kishi, ficewa tayi tabar Munirah adakin” Washegari Munirah tashi maza ki shirya, yanzun Sadiq ya sanar dani amota zaku tafi” Subuhanallahi nashiga ukuna” Meye na shiga uku Kuma” Amface tafiya amota akwai wahala sosai” Nidai ki tashi ki shirya idan ya fito baki shirya ba ranshi baci zaiyi” Mikewa tayi cike dajin haushin Mamma yayin data fara tunanin anya kuwa ba Gaya masa zancen jiya tayi ba” Wanka tayo ta shirya, tunda tazo garin saiyau ta nada lafayanta cikin sauri sauri ta karasa shiryawa” Anass da Moh’d ne suka shigo suka dauki akwatin ta yayin da suke fadin yace kiyi sauri” Cikin rakiyan gaba daya mutanen gidan suka fito saidai ko alamar sa bata ganiba agurin” Motar tashiga ta zauna, yayin da Anass ya zauna amazaunin driver ganin har yanzun babu alamar sa yasata waiga ta kalli part dinsa kofar rofe take dan haka ta maida hankalinta Kan window dakin, hangosa tayi da Hafsat bakinsu june kowanne idonsa lumshe, cikin sauri ta dauke idonta tare da fadin, nashiga uku, Allah natuba kayafan sosai jikinta yahau bari take kalaman sa suka shiga mata yawo akai, bata ankaraba ta hango fitowan shi hannunsu cikin na juna shi da Hafsat din dai Wanni irin haushi taji Hafsat din ta bata, shikuwa tahowa yayi cikin tafiyansa nan wadda yasaba koda yaushe, bayan motar ya zauna kusa da Munirah bayan an rufe motar ya sake mika hannunsa ya riko hannun Hafsat ta window mgn yake Mata kasa kasa Bata iya Jin abun da yake cewa, sannan ya saki hannun tare da gyara zaman sa sosai” Juyawa tayi ta kalleshi kananan kaya ne jikinsa sun matse shi sosai, bayan sa ya kwantar jikin kujeran motar tare da Sakin ajiyan zuciya yana me lumshe idonsa da alama yana cikin mawuyacin hali” Har Anass ya tada motar idonsa arufe yake, duk irin sallama da aka dinga masa yana amsawa ne idonsa rufe da alama akwai wani Babban al’amari dake damunsa” Tsohuwa har hawaye tafara ganin tafiyan nasu yayin da kowa ke fadin sai munzo biki, itako Aliya cikin fara’a take amsawa har sukayi nisa tana daga masu hannu Saida ta daina hangosu sannan ta maida hankalinta cikin motar yayin da ta sake kallon sa Idonsa rufe yake har yanzun dan haka ta kare masa kallo da kyau, acikin zuciyarta tace, meye amfanin hakan toh, mutumin dayasan shari’a, yana karantawa koda yaushe, amman yake kama bakin mace ya tsotse, wlh saina gayawa enisilim, juyawa tayi ta sake kallonsa wannan karon yana dafe da mararsa da duk hannunsa biyun wani irin dogon tsaki taja batare data shirya ba……..???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ Page 28- 30 Typing…….????️ Cikin bacin rai sosai ta juyar da kanta can gefe yayin da jefi jefi take waigowa ta kalli Sadiq din dake dafe da marar sa” Duk abun dake faruwa Anass yana kallonta ta madubin dake gaban sa sai abun ke bashi dariya domin shidai tuni ya Saba da yanayin me gidan nashi” Sun dauki hanya sosai suna kwarara gudu cikin Saharah, motar su kadai ahanyar, sabanin wancen tafiyan da sukayita da raguma tare da motoci” Anass abude min widows dukka zafi ya dameni” Me gida iska kasa zai shigofa” Cikin tsawa yace abude nace zafi” Budewa yayi gaba daya yayin da kasa tace samualaikuma cikin sauri Munirah ta sunkuyar da kanta hawaye ta fara matsuwa tana sharewa sosai takejin wani irin daci cikin ranta shi kanshi Anass kasar ta dame shi ganin haka yayi tunanin ya tsaya da motar kawai” Tsayawa yayi sannan ya bude motar ya fita, ganin haka Munirah ma ta bude ta fice yayin da talli Sadiq tana cike dajin haushin sa har yanzun idonsa arufe yake kamar yadda yake dazon” Anass bude kofofin motar yayi sannan ya wuce saman motar ya zauna yayin da Munirah ta mike hanya” Nisa tayi tayi sosai ganin haka Anass ya kwala Mata Kira yana fadin Ina Zaki? Tafiya kawai take dan haka ya mike yabi bayanta Saida ya hada da gudu yacin mata, fuskanta ya kallah Munirah meye haka Ina Zaki?? Haushi yake bani Anass, shiyasa bana son tafiyar dashi, sanda yaje ya tsotse bakin Hafsat besan da beda lafiya ba saida muka kamo hanya, jibi jikina Anass duk ya bacci inda shine zai yadda ne in mishi haka?? Munirah ai hakuri zakiyi, ko ke bakisan lalura ba?, Baki ganin cikin sa ke masa ciwo” Dacan besan da ciwon cikin ba saida ya gama iskancin shi? Shiru Anass yayi yana nazari zuwa can yace, kiyi hakuri kizo mukoma, kafin mukoma ya sakeshi insha Allahu sai mu wuce” Kafin mukoma, kasani ne toh? Aini wannan ba bakon abu abu bane agurina Munirah, yanayin abun da yafi haka ma, wannan kadan ne kika gani, Munirah me gidana abun tausayi ne, yakamata kema kiji tausayin sa” Wlh bebani tausayi ba, ko yanzun da zaiga Hafsat mikewa zaiyi ciwon rashinta ne” Ba haka bane Sam Munirah, akwai wani sirri daya dade karkashin zuciyata, akan me gidana, nasan me gida sosai fiye da tunannin ki, matsalarsa daya bayya barin kowa yasan damuwarshi ko Kuma yasan cikinsa, wannan dalilin yasa baka iya taran me gida kabashi shawara, yana cika Ido sosai, idan nagayawa wani Kuma bansan irin matakin da zai daukaba, zaiyi tunanin Ina zaune dashi inacin dunduniyarsa, Amman azahiri banajin dadin yadda yake tafiyar da rayuwarsa” Sosai Munirah tabashi hankalinta Dan ta fahimci yasan wani abu akansa” Shikuwa juyawa yayi ya kalli motar dake tsakiyar Sahara sannan ya juya ya kalli Munirah yace” Duk gidan ku, dake kadai nake hira, ko banyi mgn dake ba ke zakimin, kuma Me gida dan uwanki ne, nasan bazakiso mutuncinsa ya zubeba kamar yadda Nima vana so” Cikin sauri tace eh Ina jinka Anass” Munirah me gida yana da karfin sha’awa sosai, Ina nufin sha’awa irin ta ‘ya mace mu’amala irin na auratayya…… Idan hakane me yake jira, yayi aure mana” Kema kinsan bazai bude baki yace zaiyi aure ba, idan kuwa ya bude to ta Yaya zai nemi yariyar?? Himmm ta yadda yayi har Hafsat ta yadda yake tsotse Mata baki” Wannan ai ita takai kanta, barin baki misali, yanzun misali ki samu mayen kafen ki sabo dal, gangariya, ki ajeshi aguri na musamman killatacce, misali ace ni Ina da wani abu daya danganci karfe Kuma Ina matukar sonshi in tambayeki zan kaiahi kusa da Mayen karfe ne?, ai dayaje rikeshi zai yi, dan me Hafsat zataje kebantaccen gurin da yake, ba Hafsat kadai ba harda Bilkisu” Cikin rikicewa Munirah tace wacece Bilkisu??????? Bilkisu kanwace garai can bangaren Maman shi, ita wannan abun da sukeyi ma ya kazanta Babban abun Mamakin ma itace ke shige mishi”Me gida nasan aure sosai Amman bazai bude baki yafada ba, iya sa sanina dashi becika son yin mgn ba, yanzun ne ma nake ganin yana danyin mgn” Hmmm Amman ni Anass misalin da kakawo wannan ai ba hujjah bace, tun da aishi ba mayen karfe bane mutum ne kamar kowa, Kuma ni wlh koshi mayen karfe ne yayi kadan yajani” Murmushi Anass yayi, bazaki gane ba, daman ba Ina nufin shi mayen karfe bane, Amman dai mutum ne lafiyayyen namiji meji da lafiya, Kuma idan mace da namiji suka kebe na na ukun su shedan ne” Amman aidai yana da zunubi gurin Allah ko?, dan yana da lafiya sai akace mishi duk yariya da yagani ya taba? Yanada shima mana sosai ma, Amman nafi ganin laifin yariyar da take daukar kafarta takai, sannan harda gudum mawan iyaye, domin da sanin su suke barin yaran su na kebewa da baligin namiji” Cikin yamutsa fuska tace ba laifin iyayen mu bane, su gani suke sun bashi tarbiya, Kuma duk mu Kannen sa ne, sun yadda dashi suna ganin bazai cutar damuba, duk gidan yafi kowa kokari gurin karatu bangaren addini dana zamani, shiyasa sukeji dashi, tamkar yafi kowa agidan, an yadda dashi Kuma saiya dinga munafunta mutane?? Himmm, Munirah bazaki gane ba, idan akace addini be yadda da abu ba kiyayeshi shine mafi a’alah, a addinance mace da dana miji suka kebe waje daya na Ukun su shaidai ne dan haka yadda ba hujja bace” Jimmmm, Munirah tayi zuwa can tace kumafah haka ne anass, daga yanzun Aliya bazata sake zuwa part dinsa ba, yasan bashi da gaskiya shiyasa ya ware kanshi agefe” Shiru ta sakeyi zuwa can ta kurawa Anass Ido sannan tace, toh kaima kana da lafiyar ne kamar sa?? Murmushi yayi aini nama zartashi domin shekarata 19 nayi aure” Kuma shine yanzun nan nima na kefe dakai??? Eh ai……..Ganin da yayi ta tsuguna tana cire takalminta yasa shi binta da kallo, tare da kasayin mgrn dake bakinsa” Akirjinta ta rungume takalman sannan ta kwasa aguje cikin ihu tare da waiwayen bayanta” Motar ta nufa tana guje tana kwala ihu acikin saharah ba gida gaba babu gida baya” Fashewa Anass yayi da dariya harda rike cikinsa yayin daya biyota aguje” Ganin datayi ya fiyota aguje ya Kara figitata takara kwallara Kara tare da watsar da takalman hannunta” Dariya taki Tsayawa Anass harda hawaye” ** Zufa Sadiq ke sharewa daidai lokacin daya farajin ihon Munirah, fitowa daga cikin motar yayi, yana hango inda take cin uban gudu daga nesa, saman motar yahau ya zauna yana cigaba da share zufah” Munirah kuwa har takusa zuwa gurin motar ta hango Sadiq zaune saman motar cak ta tsaya yayin data hango Anass abayan ta, innalillahi wa Inna ilaihir raju’un tafada sannan tayi gefe aguje tana Kara kwallara Kara” Sosai Anass ya gaji Dan haka ya tsaya cikin kama kwankwason shi yana haki sosai” Da kallo kawai Sadiq yake binsu inda Munirah tabi yamma tai nisa shima Anass yake haki” Saida hakin ya sarara masa sannan ya karaso gurin da Sadiq yake” Goran ruwa Sadiq ya daga ya kurba sannan yace” Meye yake faruwa?? Me gida, nidai Ina tunanin firgicene ta firgita ne kawai” Ruwan ya sake kurba tare da hade fuska yace meya firgitata har haka?, Wani abu ta gani??? Bansani ba me gida ganinta kawai nayi tasa gudu” Tsaki Sadiq yaja sannan ya sauka ya yazuna a mazaunin driver yayin da Anass ya zauna agefen sa” Figar motar yayi aguje sosai yayin da duk nisan da tayi sai gashi sunsha gabanta” Kwance suka sameta cikin kasa sai haki take, saukowa Sadiq yayi da goran ruwa ahannunsa yanacigaba da kurba ya iso gabanta, tuni al’amarin yafara bawa Anass tsoro yadda yaga munjrah ta firgita” Cikin ihu take fadin karku tabani????????????????, Tsaki Sadiq yayi sannan yace, mike da uwarki” Haki take sosai kamar Numfashinta zai dauke Amman fadi take karka tabani????????????” Saitin kanta ya tsuna yana tsirara Mata ruwa tana saurin kurbewa Dan gudun karta kware” Ganin tana kurbewa yasa Sadiq fadin rigimammiya kawai Zaki Kashi kanki abanza meye ya same ki toh” Tashi tayi zaune nidai karka tabani” Tashi muje yafada yana mikewa tsaye” Ni kuje abin ku wlh bazanje daku ba” Tsaki Sadiq yaja tare da gaura Mata mari” Mikewa tayi tana kuka tana binshi, cikin fadin ni karka tabani banso bazan bikuba” Abun ne yafara bawa Sadiq Mamaki dan haka ya Kira number Malam” Enisilim toh ga Tamudiriccin Munirah nan sai wahalar damu take a ahanya akarshema cewa tayi mubarta anan bazata bimu ba” Kuna Ina yanzun?? Bamu fita daga Ingall ba muna cikin Sahara ? Kuma take cewa kubarta?, Ko tayi gamo ne? Shine ai, Sadiq ya fada yana zafga Mata harara” Kabata wayar” Anass ya mikawa wayar yayin daya Mika Mata jikinta narawa ta amsa tasa akunnenta” Abbanin? Na’am Munirah meyake faruwa?? Ni kazo ka taffin dani banson tafiya da maza” Wani abu ya faru ne?? A’a???? Toh maza ki tashi kar dare yai maku ahanya, gashi nan kowa jiran isowan ku yakeyi idan sunbarki anan yaya zakiyi, Zaki iya komawa Ingall da kafa ne?? A’a Toh ko nan kigan zakizo akafa ne?? A’a Toh tashi maza kuje Ina jiran ku wannni abu nabaki tsoro?? Cikin share hawaye tace a’a Toh tashi maza inajin ku har ku tada motar” Tashi tayi tabi bayan su” Bayan motar ya zauna yayin data shiga kaban motar ta zauna har yanzun tana rike da wayar tana Jin muryan Abbanin” Saida suka dauki hanya sosai tukun ya kashe wayar yayin data mikawa Anass shima yana amsa ya mikawa Sadiq” Tafe suke shkru babu me cewa kala illah Anass dake kallon Munirah lokaci bayan lokaci yana dariya” Lokacin data kula kallonta yake dauke kanta tayi cikin turo baki, duk ciye ciyen da sukayi kin amsa tayi, tunda take bata taba ganin Sadiq na ciye ciye ba saiyau dan haka taita satan kallon sa” Nunawa yake besan Allah yayota agurin ba Duk baccin da takeji kinyi dayi, ga tarin gajiya kafarta har zafi suka mata, tun tana kallon hanya harta gaji ta Bari yayin da bacci ya dauketa batare daya nemi shawaranta ba” Hayaniya takeji sama sama hakan yasa ta bude idonta” Ganin Sagir tayi yana rungume da Sadiq yayin da Aliya ke tsaye bayan Sagir” Ganin hasken fitolu ya tabbatar mata da lallai tazo gida, kamshin Nigeria ma dabam take, budewa tayi ta sakko yayin da Aliya da Lubbunah suka rungumeta” Turesu take tare da kokarin wucewa Part dinsu” Jin Sagir ya kirata yasa ta waigo, nan ta hange hannun Aliya cikin na Sadiq, daure fuska tayi sosai sannan ta wuce part dinsu kamar zata tashi Sama” Annanin!!! Na’am auta” Ki godewa Allah da kika gannin nadawo daraina” Allah shine abun godiya Munirah meya faru? Kwanciya tayi jikinta baku bane kuka hadani tafiya da kartai” Toh kin fara ko? Toh ai…… Rufemin baki daga dawowanki Zaki fara korafi Kuma duk ba akan kowa bane akan Sadiq, Sadiq din ne kartai?, Wuce kije kiyi wanka” Dakinta ta nufa, itako Aliya tana part din Hajiya Fatima watoh mahaifiyar Munirah can suka hadu gaba daya hsrda mahaifin Munirah” Sai misalin shabiyu na dare sannan Aliya suka taho ita da babanta koda ta leka Munirah tayi bacci dan haka ta wuce dakinsu ta kwanta” Lubbunah idan kin ida Sallah ki sameni dakin Munirah” Dakai Lubbunah ta amsa Aliya na shiga dakin ta same Munirah tana shafa addu’a” Yauwa daman gunku zani yanzun, jiya baku dawo ba harnsi bacvi Allah yasa ba part din Sadiq kika tsarya ba? Muna gurin Umma gaba daya har enisilim” Mikewa tayi tana nuke sallayar take fadin, Wai Aliya Sadiq cewa yayi son ki yake ne?? Meya kawo wannan mgnr? A’a nidai naga kamar soyayya kuke” Oho nidai kawai muna shiri Amman ba soyayya atsakanin mu” Toh Shirin me?, Shirin tabe tabe?? Wanni irin tabe tabe bangane ba? Eh mana nasha ganinsa yana rike miki hannu bayan kunsan hakan babu kyau daga ke harshi, Kuma nasan ko Malam bazaiyi tunanin shi zaiyi hakaba haka kema” Ajiyan zuciya Aliya tayi sannan tace toh ai rike hannu na da yakeyi gaban kowane ba aboye ba, kema kince kingani ai” Dan muna gani ai bashi zai hana yaji Dadi ba, ki daina bari yana tavaki kawai” Cikin sanyi sosai Aliya tace hakane kuma Munirah gaskiya ne San be dace ba, zan Kuma gyara” Ni so nake ki daina shiga part dinsa kwata kwata” A’a, Wai meyasa kike irin wannan mgnr Munirah baki yadda Dani bane Wai?? Shine ban yadda dashi ba Aliya, Sadiq dan iska ne, neman Mata yake, ya taba wancen ya rungume waccen, Kuma duk acikin dangi, ki daina biye mishi wlh yana da Budurwa a Ingall” Runtse Ido Aliya tayi, Munirah sai yaushe ne zakiyi hankali ki daina fadin mgn Mara dadi akan Amukarnin Sadiq?, Inason inga ranar da Zaki yabe shi sannan ki fada mgn me Dadi akanshi ke akoda yaushe baki fadan Alheri akansa” Ki tsaya kiji Aliya ” Bazanji banso karki Kara min irin wannan mgnr, mikewa Aliya tayi ta fice ta inda take shiga batanan take fitaba” * Sadiq ne zaune awani Babban Falo yayin da kan kujerun iyayensa ne guda uku, hira suke da Sadiq tare da masa tambayoyin akan garin nasu, shikuma yana basu amsa” Munirah tayi sallama ta shigo ta zauna akasa nesa dashi tana me gajda iyayenta cikin girmamawa” Janta da hira suka yi tayi yayin da ta kasa sakin jikinta agurin, mikewa Sadiq yayi ya fita” Bayansa tabi da kallo sannan ta Kara matsawa tsakiyar su tanacigaba da kallon sa” Alhaji Abubakar ne yace yaya dai keda Yayan naki?? Hannun ta daga alamar suyi shiru dan haka sukayi dariya gaba dayan su suna fadin Munirah akwai wayau” Bayan taga fitan shi kallonta ta maida kansu Abbanin sai Amukarnin Sadiq bashi da kirki…… Cikin tsayawa mahaifinta yace ki rufe mana baki rashin kunyan ce Kuma yau har nan” A’a ba’a haka, idan Yaro yazo da mgn karka tari numfashin sa kabari ta fada saika nunar da ita a inda kuskuren yake, ke Ina Jin ki? Mahaifin Sadiq ne yake wannan mgnr tare ta gyara zaman sa” Yadda mahaifinta ke hararanta yasa tai kamar zatai kuka tare da kasa yin mgnr gaba daya” Mikewa Alhaji Mustapha yayi ya mikawa Munirah hannunsa suka fita yana kallon fuskanta da tai kasa da kanta yace” Ina jinki Munirah gaya min me yake faruwa?? Bakomai” A’a banason haka, ninace ki fada ai” Bakomai” Ashe kuwa zamu samu matsala dake, Ina jinki yayan ku Sadiq bashi da kirki nima nasan bashi dashi Munirah Gaya min ko abun da nake zato ne?? Mata yake tabawa Abbanin???? Yamutsa fuska yayi tare da sake kallonta dakau yace subuhallahi, kin tabbata? Eh nagani Abbanin da idona?? Wacce yariyar yake tabawa Munirah” Hafsat” Hafsat?, Shiru yayi yana kallon kasa, zuwa can yaja tsaki shikenan zanyi maganin abun, idan yana sonta ya aureta mana” Abbanin ai ba ita kadai bace, harda ma wata Bilkisu acen Arlit yake tabawa” Kansa ya dafa, cikin tarin takaici yace kin tabbata?? Eh, Kuma anan ma Naga kamar yana kula Aliya….. Cikin lumshe Ido yace naji shikenan jeki abun ki, Allah yai miki albarka” Ameen tace sannan ta wuce ranta fari karr” Jikin Alhaji Mustapha har rawa yake lokacin da yake kokarin Kiran Sadiq kadawo Ina son ganin ka kawai ya fada sannan ya kashe wayar cikin fushi ya wuce falon cikin yan uwan sa ya zauna” Yanayin yadda yaji Kiran yaji tsoro saidai shi baya tunanin akwai wani abun dazai hadashi da iyayen nashi” Shigowa yayi cikin nutsuwa ya zauna, wani irin kallo Alhaji Mustapha ke masa me cike da tsana yayin da yan uwan nasa ke binsa da kollo” Meye tsakanin ka da Hafsat?? Wani irin faduwan gaba ne ya samesa irin wadda be taba jinsa ba” Dakai nake mgn??? Ni babu komai tsakanin mu” Bilkisu fah??Jimmm yayi sannan yace ba komai” Ba komai kake lalube su??? Kara runtse idonsa yayi cikin rasa abun yi tare da rasa inda akayi zancen yazo nan” Cikin tsananin Mamaki Alhaji yace Subuhallahi” Alhaji jafar ko cewa yayi ni banso ka saurari Munirah ba kwata kwata bata da hankali” Aita fishi hankali tunda ta iya banbace Mara kyau damekau shi kuwa fah? Kaji kunya girmanka ya zube a idonta kayi asara, shekaran ka 35 yariyar da take da 18 Kai abun kunya agaban idonta tir dakai karatun ka ya zama na banza tunda baka aiki da abun da ka karanta” Idonshi jawur daker ya iya bude baki yace Abbanin ni karya tamin Kuma…… Zaka iya rantsewa da qur’ani cewa Munirah sharri take maka??? Kansa ya sake mayarwa kasa jinsa yake kamar ya nutse, wani irin tsanar Munirah yaji lokaci daya tun da tamai irin wannan lallai kiyayyarta akansa Babba ne, wata zuciyar ce tace zata iya kashe ka tunda ta zabi ta kunyatar dakai cikin bainar jama’a” Ganin yakasa cewa kala ya yasa Alhaji Abubakar fadin muma harda laifin mu, yakamata ace tuntuni mun matsa mishi yai aure Amman mun zauna mun zubawa yaro Ido Gaskiya ne wannan aishi ba dutse bane shekara 35 yanzun ya isa ya aje yara, yanzun cikin su ya zabi daya sai ahada dana Sagir da Munirah, cewan mahaifin Munirah yake fadi cike da kwarin guiwa” Cike dajin haushin mahaifin Sadiq yace su biyun zai hada kuna nufin ya taba banza kenan” A’a Uzuri za’ayi masa, ya dai zabi daya din cikin su, Sadiq wacce kake so” Idonsa alumshe batare daya bude ba yace Aliya” Wani irin kallo mahaifin nasa yai masa yayin da Alhaji Abubakar yace” Aliya Kuma ai Bata cikin waddan da aka lissafa” Mahaifin su Munirah ne yace, a’a indai Aliya ce an bashi” Mgn Alhaji Mustapha da Alhaji Abubakar ke kokarin yi yayin da Malam Jafar yace dan Allah karkuce komai, Aliya yace, muyi addu’a kawai, Kai Sadiq jeka abun ka” Daker Sadiq ya iya mikewa cikin sanyin jiki sosai yabar gurin, idan ransa sunkai dubu to yau sun baci daker yakai kanshi daki yayin daya fada gadonsa yana rike da kanshi” Bayan kusan awa daya kwanciyarsa mahaifiyarsa ta kirasa, fada ta shiga masa cikin shashekar kuka ta inda take shiga batan take fita ba, kusan zai iya cewa tunda yake bata taba masa fada irin hakaba, ayau gashi gashi hartana kuka da idonta Sauke wayar yayi yayin da hawaye ya wanke masa fuska Wani Kiran ne ya sake shigowa sharewa yaso yi saidai yana dubawa yaga Mammah ce dan haka ya dauka yana me share hawaye Sadiq meyasa zakace Aliya kake so??, ai dasai kazaba can wani guri daban Sadiq????Hawaye ya share, sannan yace” Sabo dame Mammah? Sadiq Aliya da Munirah fah uwa daya uba daya suke…….. Yanzun aka fara???? ku biyoni mushiga cikin labarin???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ Page 31- 32Typing….????️Bakomai Mammah karki damu”Nidai banji dadiba Sadiq, Kuma banason ka da Aliya kwata kwata, badan bata cikaba saidan kusancin ta da muneerah” Dan tana da kusanci da Tamudiriccin sai in karbi abun da ko kusa bana ra’ayi, Hafsat ko Bilkisu fah akace, Mammah karki damu Aliya nada kirki sosai, duk tafi yaran family mu nutsuwa” Himmm, shikenan tunda kace haka Sadiq Kana nufin ita Munirah Bata da nutsuwa? Kibar min zancen wannan yariyar Mammah, kema kinsan nutsuwa be shigetaba har yanzun, shiysa nake yawan ganin laifin zuciyata” Toh shikenan, Allah ya tabbatar mana da abun da yafi alheri, dan Allah ka kwantar da hankalin ka yanzun duk ka zama wani iri” Zanyi yadda kikace Mammah Amman yanzun wannan lbrn har yaje Ingall?? Ran mahaifinka ya bacci sosai Sadiq shiya Kira tsoho ya sanar masa ” Shikenan Mammah zan kwanta na huta akwai gajiya ajikina” Sallama sukayi sannan ya koma ya kwanta, ayanzun kunya tafi damun sa fiya da kowacce damuwa da yake da ita, kunyan iyayen nasa yakeji sosai” Misalin shabiyu na rana cikin baccin sa yaji kida na tashi, ko ba’a fada ba yasan Muneerah ce ayau tsintan kansa yayi da Kara runtse idonsa bashi ya budeba Saida ya tabbatar dabar gurin ta hanyar daina Jin kidanta” Zaune ya tashi yana nazari, gaba daya gidan ya isheshi domin gaba daya gidan fushi suke dashi dan, yau babu wadda yaxo inda yake ko tayin breakfast babu wadda yai masa” Mikewa yayi ya sakko da akwatin shi ahankali ya shiga fito da kayan shi yana zubawa aciki, akwati biyu ya cika da kaya manya manya tare da daukan duk wani abu dake da hamimanci arayuwarsa, Anass ya Kira ya fitar masa da kayan, wanka ya nufah yi kome ya tuna Kuma saiya fasa” Wayoyinsa ya debo yace da Anass muje kawai” Sosai yanayin Anass ya canza ganin me gidan sa cikin damuwa” Cikin bashi umarnin hanyar da zaibi har suka isa wani katoh gida, sosai gurin ya burge Anass” Me gadin gidan ne ya leko cikin sauri ya koma ya bude gate din suka shiga” Sauka Sadiq yayi yasa hannun cikin aljihu ya ciro key sannan ya nufi cikin gidan yana cewa Anass kawo min kayan” Falon ya kwanta yayin dayasa Anass ya shigar masa da kayan dakin bacci” Shikuwa afalon ya sake kwanciya jikin shi babu kwari zuciyar sa ma babu dadi” Misalin Karfe 8 na dare Munirah da Aliya ne zaune afalon su, hira suke sama sama, suna tsaka da hirar Mahaifin su ya shigo, cikin girmamawa suka gaidashi, zama yayi nan falon fuskarshi babu walwala yace” Munirah Kira min Maman ku” Kiranta tayi Amman ita sai takasa dawowa gurin, balakin tsoron Abbanin ta takeji” Annnanin nazuwa yace Ina Munirah fah? Kira ta kwala Mata yayin da ta amsa kamar Munafuka” Fitowa tayi ta zauna kusa da Aliya” Cikin rashin walwala yace watau Munirah kedai kunnenki nakashi ne ko? Kanta ta girgiza alamar a’a Eh mana, baki da kunya, meyasa ni baki tareni nikadai da zancen ba, kinje har gaban mahaifin shi kika Gaya, shikenan yanzun hankalin ki ya kwanta kin hadashi da iyayen shi shikenan sai hankalin ki kwata, ni bansan irin wannan bakar zuciyar taki ba da baki gwadata akan kowa sai Kan Sadiq” Abbanin nifah ba haka bane, Naga abun da yake bedace bane???????? Meyasa ni baki min mgnr ba in fahimtar dasu cikin hikima??? Cikin kuka sosai tace toh kayi hakuri enisilim bazan karaba” Shiru yayi zuwa can yace dan Allah ki daina irin wannan dabi’ar bansonta” Juyawa yayi yace sai mgnr da zanyi na karshe ko ince Umarni ne zan bada ba neman shawara ko ra’ayin wani nake bukata ba” Mun gama shawara akan zamu hada auren Sagir da Munirah da Sadiq da Aliya lokaci daya” Dagowa mahaifiyarsu tayi da sauri, bangane kunyi shawara ba, nasan zancen Munirah da Sagir Amman bantabajin zancen so ko wani abu tsakanin Sadiq da Aliya ba, karku hada rigima idan Aliya za’a iya tankwarata Sadiq fah? Shi Sadiq da bakin shi yace Aliya ai, Toh da sauki, yanzun Sadiq din ne yace Aliya yake so????? juyawa tayi ta kalli Aliya sai yanzun take tuna wasu abubuwa tabbas Aliya na kula lamarin Sadiq, haka shima yana kula nata cikin Sakin fuska tace” Au ashe da wata akasa shiyasa buni buni kice Amukarnin Sadiq kaza” Mikewa Aliya tayi da saurin ta tabar gurin tana me boye fuskanta” Murmushi iyayen nasu sukayi yayin Munirah tabi bayan Aliya fuskanta daure” Yanzun ke Kuma saikace wadda basiran ta ya bace, ya kasa bude baki yace yana son ki saidai da akace wa kake so yace Aliya, narantse in nice bazan kulashiba saiya fada da bakinshi wlh” Zama Aliya tayi abakin gadon da Lubbuna ke kwance tayi yayin da Lubbunah tace lafiya??? Kinji Wai Sadiq ne aka turkeshi wa yake so yace Aliya, wlh inda nice cewa zanyi banson shi ” Toh aini daman tuni nasan son Aliya yake yi wlh daman jirah nake ta fashe, Ashe ta fashe Ina kwance, tashi tayi zaune, Kai abu yayi kau wlh, gaskiya nima baxan yadda kubarni agida ba, cewa zanyi da Sani ance ya turo” Kyalkyalewa sukayi da dariya gaba dayan su zuwa can Munirah ta mike tana fadin” Nidai wlh nayi bakin cikin wannan hadin Aliya da Sadiq, abun ko tsari babu, indai zancen nan ya tabbata bakiyi dacen miji ba, bazan dinga zuwa gidan ki ba, haba wani Kaya ne Kuma Sadiq ?? Lumshe Ido Aliya tayi sannan tace kinga Munirah ki Bari banso” Tabe baki Munirah tayi sannan ta mike tana fadin lallai Allah ya kyauta” Annanin Sadiq yayi tafiya ne?? Me ka gani?? A’a ban ganshi bane kawai” Cikin kawar da Fuska tace yana nan part din sa” Baya nan fah Annanin, tun jiya nake zarya zuwa neman sa, be dawo ba Sam sannan Kuma ma ai babu motar shi gaba daya” Babu motar sa yanzun Haka?? Ai be kwana gidan nan ba fah” Jimmm tayi zuwa can tace, toh Ina yaje?, Kodan an masa fada jiya? Fada? Yayi wani abu ne?? Eh Sagir, jiya Baban ku ya samu wani lbr akansa ranmu yabaci gaba daya” Mike tsyi tana gyara kayan ta Sagir yace wanni irin lbr ne Annanin?? Munirah ta kawo karansa ta kamashi da mata yana abun dabe dace ba dasu” Runtse idonsa yayi sannan ya mike da sauri yabar dakin” * Yakamata muci uban yariyar nan, iskancin ta yana yawa sannan in ta tasa mutum agaba ya shiga uku, yanzun dan Allah koni natara Su Abba da irin wanan mgnr?? Himmm ni inaga muje gurinsa kawai shi yafi, sakkowa Mubarak yayi daga Saman motar suka nufi gidan da bakin da yake aiki karkashin sa suka bashi, saidai suna zuwa akace musu ya tafi aiki” Me gadi kawai suka samu agidan Dan haka suka fice da nufin da Yamma zasu dawo, haka kuwa akayi misalin Karfe 8 nadare suka sake komawa” Kai tsaye suka shiga falon, babu kowa dan haka suka nufi dakin baccin sa suna me kwala mai Kira” Yanajin muryoyin su yaji wani sanyi ya ziyarce shi, lumshi idonsa yayi sannan ya tashi ya zauna yana me share gefen idonsa da hawaye ya kwanta” Gaba dayan su zama sukayi bakin gadon yayin da suka saka Sadiq a tsakiyar su suna fadin Ashe abun da Munirah tayi kenan??? Himmm bakomai ai, waye ya gaya muku?? Mubarak ne yace ni dazon Sagir ke Gaya min wlh, juyawa yayi ya kalli Sagir yace Annanin tana fushi Dani ko?? Zata sakko ai karka damu, Munirah ce ta jawo komai zanyi maganin ta Kuma” Murmushi yayi yana me tsurawa kafarsa Ido yace a’a karku tabata laifina ne ai” Cikin fada Mubarak yace yazama dole a hukunta yariyar nan idan ba hakaba nan gaba mun shiga uku, yariya duk abun da aka gaya Mata saita bada amsa, kamar jira take, nifa tuni take bani haushi, kallon Sagir yayi kaima da kake sha’awan aurenta saikayi da gaske idan ba hakaba banza zata maida ka…… Cikin Sanyin jiki Sadiq yace kungane ne ku rabu da ita, kada wadda yace zaiyi Mata hukunci ko wani abu, ninasan yariyar nan daman ta tsaneni, shikenan nina amince nakuma ji tayi nasara akaina, dan haka ku rabu da ita, idan dan Ina shiga harkarta ne take kallona amatsayin abokin gabanta to nabari, yar uwata ce nasani har abada wannan bazai goge ba, amman ni babu abun da nake nema agurinta bakuma na fatan Allah yasa in nemi wani abu gurinta, dan haka idan taga dama ta gaidani idan Kuma taga dama karta gaidani wannan ruwanta ne, nidai idan ta gaidani zan amsa abun da nasani kenan” Amma fah ya kamata a zane ta” Nagaya maku karku tabada, ni yanzun ni me laifine agida, indai ra’ayina zakubi ku barta kawai” Sagir ne yace toh Amman meyasa ka dawo nan bayan da aka baka ciwa kayi bazaka iya zama ba” Ton ba dole nadawo nan ba Sagir, na lura indai yariyar nan tana ganina bazata barni in zauna kalau ba” Kenan Saboda Munirah ka dawo nan?? A’a kawai naga su Abbanin suna fushi danine ” Shiru Sagir yayi ciki yanayin tunani sannan yace, toh katashi muje gida” Kuje zanzo idan na gama hutawa” Kazo muje gida kawai Sadiq Sunbar zancen yanzun, kokarin tsayar da ranar bikin suke rana daya da nawa za’ayi” Lumshe Ido Sadiq yayi tare da fadin yayi kau Amma kuje gobe zan dawo da Yamma bayan na taso office” Badan ransu yasoba suka mike shima Sadiq mikewa yayi yana fadin Ina zuwa, wani dan karamin akwati ya dauko yace gashi kubawa Aliya” Murmushi sukayi gaba dayansu yayin da sannan Mubarak yace, nidai gaskiya ka dawo gida Ina son inga naka salon” Murmushi Sadiq yayi sannan yacewa Sagir kacewa Annanin bazan dawoba sai in tabar fushi Dani” Cikin murmushi yace zan gaya Mata” Aliya ce ke kokarin bude akwatin yayin da take zuba murmushi, Lubbuna da Munirah na zaune suna bin akwatin da kallo, yayin da Lubbunah takosa tasan meye aciki Munirah ko sai harara take zubawa akwatin” Aliya da Lubbunah lokaci daya suka bude akwatin cikin nuna komai ya burgesu suna ihu suke jawo kayan riguna ne irin dai waddan ce saidai kowanne zubinsa daban yayin da wannan n yake wane waccen” Iho suke, sabo da yadda rigunan suka hadu kowanne da takalmin sa” Munirah kuwa ganin rigunan ta saki baki gurin kallon su, ai waccen bola ce akan waddan nan lallai ya iya zame duk kinsa da take dole ta yaba zabin sa ayau dan haka tace” Gaskiya Aliya kayan sun hadu saura haduwan ki dame kayan” Bangane saura haduwata dame kayan ba? Toh tunda yana son ya lalube miki jiki ba dole ba, dole yaje ya ware Ido ya zabo karshen kyau ba, halan ke baki bari an tsotseki bane shiyasa yace ke zai aura” Runtse Ido Aliya tayi sannan tace kinga Munirah bana son irin wannan mgnr, zan hadaki da Abbanin ni ba ‘yar isaka bace banson iskanci” Nima ba ‘yar iska bace tun da bantaba bari wani bazza ya taba hannu na ba” Yawu Aliya ta hadiye sannan tace ai saikiyi tayi mahaukaciya” Kara atsawa gaban akwati tayi tana fadin, mahaukata dai, hannunta ta mika ta dauko wani leda tana fadin meye wannan? Lubbunah ce tace gyale ne” Au nazata bra ce” Lubbuna ce ta kwashe da dariya yayin da Aliya tayi murmushi tana fadin munafuka” Mikewa Aliya tayi dan gwada rigar bayan ta cire ta jikinta tasa waccan, abun Mamaki wannan karon ma gaba daya kayan kin shiga sukayi hakama takalmin, Munirah ce ta shiga dariya sosai yayin da Aliya ta cika fam idonta na Shirin kawo ruwa” Mikewa Munirah tayi cikin dariya idonta cike da hawayen mugunta take kiran Annanin!!! zo ki gani” Dawowa tayi tare da Annanin tana me Bata lbrn” Murmushi itama tayi sannan tace wai Munirah yaushe Aliya ta zama abokiyar wasan ki, shidai Sadiq yana son sayan mike kaya Amman baya gane size dinki” Jefan Munirah Aliya tayi da kayan tana fadin gashinan shegjya nabar miki ke zasu miki” Rungume kayan Munirah tayi tana fadin wlh sawa kuwa zanyi kodan mesu yaji haushi” Takalman Aliya ta sake watsa mata tana matukar dariya take cabewa” Dankunne da sarkar kawai ne Aliya ta dauka sai gyale da turare ta maidasu cikin akwati yayin da taji Munirah na fadin” Kinga wannan hawayen da kike zubarwa, danice Sagir yaiwa haka, tasashi zanyi gaba naita kuka har sai ya sawo min Size dinna, kinga keko ba fuska, daurewa zaiyi kaman konnanen kosai yace, ke, ni abokin wasan ki ne?, Tana mgnr ne tana dariya tare da kwatanta yadda yake mgn, dan haka Aliya ta sake kulewa” Tsintan kanta tayi da Kiran Sadiq cikin ikon Allah bugu biyu ya dauka yayin data bude muryan kowa naji bayan tayi Sallama ya amsa tayi shiru ahankali taji yace” Aliya yaya dai ? Bakomai ta fada cikin turo baki” Jimmm yayi sannan yace, akwai mgn abakin ki gaya min inajin ki” Kayan fah gaba daya sun min kadan har takalmin???? Kash, banji dadi ba, yanzun ina kayan?? Nabawa Munirah” Harya bude baki zaiyi mgn kome ya tuna sai Kuma ya fasa ahankali yace shikenan, yanzun me kike so?? Toh haka fah na kwanaki ma sukaki shigata yanzun ma wannan haka, gashinan Munirah sai dariya take min wai bakasan size dina ba” Jimmm yayi cikin tunani zuwa can yace shikenan nagane, ki shirya zanzo na dauke ki muje tare” Tam” Yauwa sai anjima, amman ki gayawa enisilim zamu fita tare anjima” Tana sauke wayar Munjrah tace zan biku” Sadiq kuwa bayan ya sauke wayar tsaki yaja tare da buga wayar da bango yana fadin meyasa?……..???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ Page 33- 35 Typing…????️ Tsaki yake ta faman jah babu kaukautawa, cikin tsabar bakin ciki da takaici” *Annanin nayi mgn bakice komai ba? Kaga Sagir idan kana da abun yi kaje kayi kawai karya dawo din yaita zama acan” Shiru Sagir din yayi yana kallon mahaifiyarshi zuwa can yace yanzun Munirah tarabaki da danki kenan?? Eh taraba mu” Ai kuwa bazan aure taba” Cikin sauri ta kalleshi, sannan tace sabo dame karka ma soma irin wannan mgnr, koda wasa banson ta” Annanin ta yaya zanga farinta, bayan nasan ta dalilinta kike fushi da Sadiq, shima Kuma ya Sani, duk ita ce ta hada komai, wlh ji nake kamar in mata duka, sa’anta ne shi?, Ina ruwan ta? Bangane Ina ruwanta ba?, ai abun da Munirah tayi abune wadda ya dace sosai, yanzun badan tayi mgn anyi mishi tsawaba komai na iya faruwa, Bilikisu ninasha nono nabarwa uwarta, hakama Hafsat mahaifin kune ya ragewa uwarta nono, shi mahaukacin Ina ne ?? Annanin kimai uzuri, wlh Sadiq mgn na mishi wuya, sai dai idan yaudaren shi suke yi” Wani irin murmushi mahaifiyar tasu tayi, sannan tace, eh, sosai, dayake laifi tudune, dole ka take naku ka hango nawani, amman in banda rashin son gaskiya har macece zata yaudara namiji, Sadiq fah ba yaro bane?, koko kana nufin sai muji irin wannan Babban laifin nasa muyi shiru, sabo da ba ‘ya’yanmu bane yake tabewa ko?, ni tsoron da nakejima kar ace me aukuwa ta auku” Kashh, Annanin dan Allah kibari, babu wani abun da yafaru, itafah Munirah ko rike mace taga yayi a haukanta zata iya fadin haka, Kuma Sadiq yana da wannan labi’ar tun bayan daya dawo karatu” Sosai nutsuwa ta shiga Annanin, wani sanyi taji cikin ranta, afili tace toh Allah yasa va abun da yafaru, amman kabar ganin laifin Munirah dan Allah” Annanin saina hukuntata Allah, aiba sa’anta bane shidin yayanane, meyasa ni Bata Gaya min ba, wannan ai rashin kunya ne da zataje tara Abbanin dakansa ta fada mishi, inda wata nake nema awaje tayi haka Ku ma sai kunce bata da kunya” Wannan Kuma daban Sagir, dakai da Sadiq din da Munirah duk dayane, kuna da kusanci sosai Kuma bata kallon Sadiq amatsayin yayan wadda zata aura har yanzun, kallon yayanta take mishi, hakama Baban naku, ai Babanta ne, har gobe tana da damar da zata tareshi tayi ta Gaya masa matsalarta, wannan ba laifi bane ubanta ne, kuma kalmar rashin kunya ka ajeta annan, banso wani yajita abakinka, zama muke fatan kuyi nahar abada, ba wasan yara ba, shikuma Sadiq aiba koransa akayi ba, bikon sa kakeson naje ko me? Toh idan takama kije basai kije ba, danki ne ai Kuma kema nasan daurewa kawai kike, kin damu dashi, wlh idan zaki dauko daki kije ki dauko shi, cikin turbune fuska yake mgnr dan haka tayi murmushi sannan tace” Daukoshi zanyi ma?, toh dauko min zani ne in goyo shi” Wucewa yayi gaban akwatin ta ya bude ya dauko zani, yana mika mata tare da fadin gashi” Toh muje ka rakani barin dauko mayafi” Wucewa yayi fuskanshi har yanzun daure, tare da daura zanin akanshi, bayanshi tabi da kallo yayin da cikin ranta take karajin tsanin son yayanta guda biyu rak da Allah ya Bata, Sagir nada baki sosai, Kuma sosai yake sakin jikinsa da mahaifiyarsa kamar wata kawarshi, sabanin Sadiq da beson mgn, koda mahaifiyar tasa ma mawuyacin abu ne kaji yana hira saidai mgn sama sama, cikin gidan ma becika shigaba, so da yawa saidai ita ta nemeshi idan taso ganin shi, saidai duk da haka tanajin shi sosai cikin ranta” Bayan ta gama shiryawa wayarta ta dauka ta Danna sannan ta Kara akunnenta, bajimawa ta fara mgn” Ranka ya dade Ina neman izzini ne gurin ka” Cikin murmushi yace inajin ki” Zamu fita da Sagir yanzun” Zuwa Ina?? Sagir ne ya matsamin sai munje bikon Sadiq” Wata ‘yar dariya yayi sannan yace adawo lafiya” Godiya tayi sannan ta kashe wayar tana me gyara zaman lafayanta, Hajiya Fatima kenan kyakyawan mata fara tass da ita” A farfajiyan gidan ta hangi Sagir zaune cikin motarsa har yanzun zanin na bisa kansa, bayan ta shiga ta zauna ya data motar yayin da suka shiga hira har suka isa gidan” Dadi sosai Sagir yajj dayaga motar Sadiq betaba tunanin za’a sameshi ba kawai dai yabari suzone ko bayanan yaji lbrn tazo zaiji Dadi, ganin sa ko agida abun yasashj farin ciki sosai” Saukowa sukayi suka nufa ciki tare da Sallama, yayin da sukaji Sadiq na amsawa daga can ciki” Cikin suka nufa Sadiq gaban madubi yana caje gashin kansa ya juyo ya kallesu, ganin Annanin sa yai saurin sakin Murmushi” Karasawa take, yayin da Sagir ke warware zanin har suka isa gaban shi” Bayanta ta juya masa, tare da fadin nazo biko zo kahau” Sagir ma bayan Sadiq ya wuce ya bode zanin yana fadin yau goyo za’ayi, maza ka hau” Kallo bayan Annanin Sadiq yayi tare da fashewa da dariya, hannunsa ya mika ya dafa kafadarta yayin daya rungumota jikinsa yana fadin nagode Annanin” Cikin murmushi tace bakomai Allah yama albarka” Ameen Annanin, Kara rungumeta Sadiq yayi yayin da tsayon shi ya karewa nata, haka Sagir kusan tsayin su daya da Sadiq sai kauri da Sadiq zai gwada masa, dan haka sai mahaifiyar tasu tayi can kasa, dan yaran nata tubar kalla, dogaye ne” Sagir ne ya taba Sadiq yana me nuna masa zanin hannunsa tare da nuna bayan Annanin” Murmushi Sadiq yayi sannan ya girgiza Kai Alamar a’a” Annanin kinji Wai bazai hauba, wlh danine hawa zan yi” Toh hau mana nabarmaka, cewan Sadiq daya fada idonsa cikin na Annanin sa” Bayan Annanin ya koma tare da fadin duka” Dukawa tayi yayin da Sadiq ya ansa zanin hannun Sagir yana me cike da murmushi ya bude kamar yadda Sagir ke yi” Hawa bayan nata Sagir yayi, yayin da Annanin fuskanta ke cike da murmushi” Zanin Sadiq ya rufa abayan Sagir yayin da Annanin ta kama tana kokarin daurewa tana fadin wannan zanin ko zai rutsamu?, Sadiq kadai ce kabar masa ko? Jin yadda take mgnr cikin nishi Sadiq yace Ummm tare da fashe da dariya” Kokarin mikewa tayi tana rike da sama yayin da Sagir yake fadin ya zaki mike baki daure kansa bafah” Ai saman ma ban daureba Sagir, Bari dai mu mike tukuna” Dariya kawai Sadiq keyi harda hawaye yayin da Annanin keta nishi cikin kokarin mikewa” Wayyo Allah na tafara fadi yayin da cikin matsananciyar dariya Sadiq yafara fadin Sagir sauka” Kara kwantar da kanshi yayi yana fadin ni a’a saita goya ni” Yaye zanin Sadiq yayi, cikin tsawa tare da dariya yace zan nausheka fah” Ni a’a Ka sauka Allah zan nausheka????, dungule hannunsa yayi yayin da Sagir ya tashi aguje ya nufi kofa” Zaman dirshen Annanin tayi akasa tana maida numfashi tare da fadin wayyo kamar an daura min dala da gauron dutse abayana” Cikin dariya sosai Sadiq yace Sannu” Sagir kuwa yana daga bakin kofa yake fadin Dan ma bashi bane hau” Har yanzun dariya Sadiq keyi, saiya kalli Sagir ya kalli Annanin yayi dariya” Kura masa Ido Annanin tayi sannan tace su Sadiq anga mugunta, to tashi muje” Annanin Office zani, idan na tashi sai nayo gida” A’a Sam kazo muje kawai, da munje saika wuce abunka” Sagir ne ya kama akwatunan su ya fice dasu gaba yayi amotarsa ko kafin su fito ya wuce, Suma tahowa sukayi suna hira Sama sama” Bayan sun isa gida gaba dayan su a part din Hajiya Fatima suka hadu kitchen ta wuce ba jimawa sai gata da dumamen tuwa inda ta dire gaban Sadiq da Sagir ku wanko hannu kuzo muci abinci yau mutuna da da” Cikin sauri Sagir ya mike yayin da Sadiq ya yamutsa fuska gaskiya ni banci” Saikaci Allah Annanin ta fada tare da sake cewa maza ka wanko hannu” Mikewa yayi har yanzun danne danne yake yake ciki wayarsa bayan ya wanke hannun ya dawowa ya samu Sagur aban tuwon zama yayi har yanzun wayar sa yake kallo” Hannu Annanin ta mike ta amshe wayar sannan tace ci abinci Malam” Hannu yasa badan ransa yaso ba, yayin da suka saka Annanin a tsakiyan su” Saidai yana fara cin tuwan yaji wani dadi ya ratsashi rabon shi dashi tun yana karamin yaro, ganin inda yakecin tuwan Sagir ya tuna da lokacin yarinta dan haka ya tura hannunsa cikin na Sadiq ya kwakuke tuwon daya gutsuro, dagowa Sadiq yayi ya kalleshi meye haka?? Tsayawa Sagir yayi cak yana kallon kofar da tuwo cike abakin shi, yan Mata uku ne suka shigo Lubbunah Aliya da Munirah, shigowan su yayi daidai da lokacin da Sadiq yake zabgawa Sagir harara” Annanin suka gaida bayan ta amsa tai masu tayin abincin saidai kinci sukayi yayin da suka maida hankalin su gurin su Sagir da suketa kici kici da tuwo” Adaidai lokacin Annanin ta dawo da hankalin ta wajen su, ganin yadda duk suka yi Sagir sai tsokanan Sadiq yake cikin kwace lomarsa daya gutsuro tace” Toh fah, sannun ku da aiki” Dariya Aliya ta fara yayin da ta kurawa Sadiq Ido, Lubbuna kuwa kanta ta boye cikin dariya yayin da Munirah ta musu kerr cikin Harare harare” Sagir kabari banso fah” Zafine Amukarnin ban iya gutsurowa” Cikin tsawa yace aikuwa ka Kara zan nausheka” Karawan yayi yanin da Sadiq din yakai masa naushi da hannunsa da yakecin tuwu, rike hannun yayi bayan ya isa cikinsa duk ya bata mishi riga ta miya Aliya keta faman dariya yayin da Annanin ta mike tana fadin ni karku takani lafiyace ta isheku” Aguje Sagir ya fice yayin da Sadiq ya mike idonsa ya hadu Dana Aliya da taketa faman dariya, hade fuskan sa yayi sannan ya wuce yana fadin ke zo nan” Harya fice Munirah hararan bayanshi take yi, bayan ya wanko hannun ya dawo ya yana kallon Aliya cikin hade Fuska yace bacewa nayi ki biyoni ba? Cikin murmushi race toh ai zuwan zanyi ka dawo” Atsaye suke dafda juna yayin da Lubbunah ke gyara wajen da suka gama cin abincin” Wa kikewa dariya?? Hannunta tasa biyu ta rufe fuskanta yayin da Munirah ke kallon su kamar ta samu tv cikin Harare harare” Hajiya Fatima ce tace ku takema dariya taga kartai na shirme” Ido ya zuba Mata sosai kasa kallonsa tayi ta durkusar da kanta kasa cikin murmushi” Shima wani irin Murmushi yayi yayin da duk dakin aka bisu da kallo” Kara matsawa yayi dafda ita a hankali ya mika hannun shi ya kamo kasan rikarta wadda ya sauka Kan siket dinta kadan, hannunsa na dama daya wanko yanzun yasa aciki bayan ya tattaro rigar ya shiga gogewa” Cikin tsayawa Annanin tace meye haka Sadiq?? Tas ya goge hannun yayin daya fizgo dan kwalin atamfar dayake daure akanta ya goge fuskansa yana fadin dariya tamin Annanin” Sakin baki tayi tana kallon shi lakacin da yake fadin, zanje indawo ki shirya kinji, juyawa yayi ya fice yayin da Munirah ta kannne idonta daya tana ganin Fitanshi tace” Kan balaki????, cabdijam, lallai, himmmm” Aliya kuwa tare dan kwalin nata tayi wadda ya jaho Mata fuskanta sannan ta fice tana fadin wanka yazama dole” Annanin kuwa fadi take, nabani ni Fatima halin Sadiq saishi” Lubbunah dariya take tana fadin salon soyayyarsa kenan ko Umma?, dan yana sonta ya goge hannun arigarta yazo ya goge anawa mana” Tsaki Aliya taja tare da fadin” Umma wlh inda nice saidai ya tafi wanka Nima in tafi, bazanyi ni dayaba, wannan ai wulakanci ne” Aina Sani Munirah basai kin fada ba, ai halin Sadiq sai Aliyar” Lubbunah ce tace toh jarabarbiya” Bawani jaraba, mikewa tayi tana kokarin fita tana cigaba da maganganu” Asaman mota ta hangi Sagir zaune gurinsa ta nufi zuwa yayin da yana ganin ta nufosa ya daure fuska” Amukarnin Wai har yanzun fushin kake Dani? Eh Ina fushin dake Munirah banajin dadin yadda kike min” Jimmm tayi sannan ta dada matsawa gabanshi shikenan Amukarnin tunda har wani zai hadani dakai, ni ban iya inzauna shiru ba gaskiya shiyasa naita mgn da Mutane Kuma aishine yake mgn dani to dawa zanyi mgn amman tun da kaji haushi kayi hakuri” Ina zuwa Munirah, Sadiq sa’anki ne shi da zakice dole saikinyi mgn dashi…… A’a, Amman ai kaima ba sa’ana bane Kuma ai muna mgn shi saiya dinga wanni daurewa” Tsaya Munirah, tsakanina dake daban tsakanin sa dake daban karki Kara hadawa, ni auren ki nake son yi shi Kuma Yaya nane wannan nake son kisa cikin ranki” Cikin turo baki tace ai nasan yayanka ne basai kamin goriba, bance daman inason ya zama Dan uwana ba, me zai tsinanamin to” Shikenan wuce kiban guri tunda rashin kunya kikazo dashi” Hawaye tafara sharewa shikenan tunda ya hadamu daman ai yaki jinina, juyawa tayi kamar zata tashi sama” Zo, dawo nan” Juyowa tayi tana kallon sa” Kikace Sadiq ya hadamu?? Eh mana” Keda kika hadashi da iyayen shi fah….. Ba sharri namaiba ai, Kuma ramawa nayi, tsurkun da yama nima narama” Dariya Sagir yayi cikin ransa afili kuwa cewa yayi, kinyi nafarko kinyi na karshe idan kika kara zamu samu matsala” Cikin kawar dakai tace naji din” Kawar dakai tayi can gefe yayin da Sagir yayi ajiyan zuciya tare da fadin to meye labari?? Juyowa tayi ta dallara masa harara tare da sake juyar da fuskanta can gefe” Murmushi yayi sannan yace, bansan kina hararata sai naga idon ya fado kasa Murmushi tayi kadan ai kasan bazai fadoba shiya ka fada, dazon naga wasu kamar kananan yara suna dambe akan abinci” Cikin sauri ya dauke kansa can gefe cikin nuna alamar fushi yake” Toh fushi Kuma kakeyi Wai? Ummm badole inyi fushiba bakijin mgnta” Naface nabsri”. Yadda ta tsareshi da Ido yai murmushi tare da cewa Allah yasa da gaske ne muje in rakaki ” Banso” Toh shikenan sai anjima” Saman motar ya koma ya zauna yana me kallon ta har takusa shiga part dinsu ta tsaya” Amukarnin Sagir zo kaji!!! Shima bude murya yayi yace bazanzo ba idan kin matso ki dawo” Juyawa tayi tana fadin kada kazo din” Yana kallonta harta shiga part dinsu yayin da yana kokarin barin wajen sakonta ya shigo wayarsa” Amukarnin Sagir gobe zan koma makaranta” Allah ya kaimu ya tura Mata sannan ya tashi yabar gidan” *Misalin 4 na yamma Aliya tagama shiryawa tsaf, ganin Aliya na shiryawa Munirah tahau shiri, cikin kayan da Aliya tabata ta zabi daya wannada take ganin yafi kowanne kyau ta saka, sosai tai kyau” Lubbunah ce tace ke Kuma Ina Zaki?? Binsu zan yi wlh” Binsu?, Amman wlh Munirah baki da hankali” Hankali sarai, kallo kawai zanyi wlh” Toh Allah ya shirye ki” Ya shiryemu dai, ni babu abun da Zaki nuna min” Cikin fushi Lubbunah tace wlh kikace zakimin iskanci ubanki zanci niba Aliya bace” Wlh kika Kara zagin ubana bazan yadda ba, Aliya ma abun da yasa nake barinta ubanmu daya ta zagini kanta ta zaga Amman wlh duk wadda ya zagi ubana ubanshi zan zaga” Cikin fushi Lubbunah ta bake Mata baki yayin da suka shiga dambe gaba dayansu haki suke duk da wuyar da Aliya Kesha Bata saduda ba Kara shigewa Lubbunah take, Annanin tashiga kwalawa Kira yayin da tana rama dukan tana fadin Allah ya isa itako Lubbunah Kara mata take” Annanin ce ta shigo ta raba fadan inda ta tambayi dalili” Lubbunah ce tagaya mata inda Annanin tace toh Banda abunki Lubbunah daga cewa zata rakasu ai ba laifi bane, ke Kuma Munirah dan Allah ki daina rashin kunya, juyawa tayi tana rike da hannun Munirah dake kuka yayin da dake cewa bazata fita adakin ba saidai Lubbunah ta fita, janta Annanin ta dingayi ganin tana cijewa ta tsinketa da Marin da babu shiri tabi bayanta” * Ta window ta hango zuwan Sadiq tabe baki tayi waishi nan adole zai fita da budurwa” Falon ta dawo ta zauna kusa da Annanin tana kallo Aliya tayi sallama ta fita harta saki kofar ta dawo tace, Munirah zo muje” Kamar jira take ta mike fuskan ta kunbure saboda kukan dataci” Sakowa Sadiq yayi ya zauna bayan motar dalilin hango Munirah” Kusan atare suka iso yayin da ya kali Aliya yace kinyi kau, shiga muje, sakowa yayi ya zauna cikin motar bayan Aliya ta zauna yaga Munirah na kokarin bude baya yace, ita Kuma wannan ina zata? Tare zamu? Umarni ne kenan?? A’a nag…… Toh ban amince ba” Kallon Munirah tayi tace Munirah bari muje mu dawo” Juyawa Munirah tayi tana wula karamar Jakarta sama cikin wani irin tafiya harta shiga gida” Yamutsa fuska yayi cikin binta da kallo harta kuke sannan ya data motar” Juya hancin mitar yake yaji an Kira sunan sa cikin tsawa” Cak ya tsaya tare da kallon wawakeken farfajiyar gidan nasu” Mahaifinsa ya hango kafarsa babu takalmi haka kansa babu hula jarida ahannun yana kallon motar tare da Kiran sunan sa” Sakkowa yayi da sauri tare da sunkuyar dakai” Daga can nesa yace Ina zakaje mana da yariya??? Kansa ya shafa sannan yace Abbanin zamuje ta zabi kaya ne” Cemaka tayi Bata dasu?? A’a” Cikin fada yace ke Aliya sakko!!!!” Saukowa tayi yayin da Abbanin ya nuna Sadiq da yatsa karka sake ka fidda yariyar nan daga cikin gidan nan idan ba daura muku aure akayi ba, kaji ko bakaji ba” Naji” Cikin sauri Sadiq ya shiga motar yayin da Aliya ta nufi part dinsu, Enisilim ne ya fito cikin Munrmushi yace ya haka?? Fita zaiyi da ita nace ban amince ba” Murmushin sa ya fada sannan yace ai nasan da tafiyan tasu ga Munirah ma zata musu rakiya” Ajiyan zuciya Abbanin yayi sannan yace shikenan” Aliya da Munirah yaga sun sake fitowa tare, duk su malam na gurin har Aliya tashiga gaban motar ta zauna, Munirah kuwa baya ta shiga cikin sannan wayarta bayan ya tada motar kafarta daya ta dauka ta daura Kan daya tana karkadawa……???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ Page 36-37 Typing……????️???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ Page 36-37 Typing……????️ Cikin fushi sosai Sadiq ya fike motar tafiya yake azuciye kamar zai tashi sama” Cingam Munirah ta ciro cikin Jakarta ta wurga abakin ta tana taunawa yana bada Kara kasss” Cak ya tsaya domin tabbatarwa kansa abun da yakeji” Karass yasake ji cikin sauri ya faka ya bude motar ya zagayo ya bude gefenta tare da gaura Mata mari” Dafe wajen tayi cikin kokarin danne hawayenta dan karyaga kukanta” Bani abun dake bakin ki” Hannunta tasa ta ciro ta Mika masa yana haranrata ya karba yai jifa dashi tare da fadin karyar rashin kunya kike, barinki nake bawai kinfi karfina bane, tara ki nake Kuma duk ranar da kika Bari na rikeki saina nannaushi ki, hanyar da nabi ba bazaki yadda kibita ba doluwar yariya kawai” Ko dagowa Munirah batayi ba Dan ita kadai tasan zafin da taji, zagayawa yayi ya shiga motar yayin daya maida fadanshi Kan Aliya ke Kuma daga yau karki Kara min haka daga cewa zan fita dake kin tashi kinyo min kwashe kwashe” Cikin sauri Aliya ta kalleshi Munirah ce kwashe kwashe?? Eh wacece ita?? Kanwata ce” Okay kina gayamin kanwarkice Amman kina kallo take min fitsarar dataga dama ahaka zamuyi auren? Kuka Aliya tafara ganin inda yake fada” Fakawa ya sakeyi akaro na biyu ya bude motar ya fice yana fadin ni banson kuka, idan kin gama ki min mgn” Tsallawa yayi can gefen titi ya zauna yayin da Aliya ta shiga share hawaye” Tashi ki bishi” In bishi Ina? Bayace beson kuka ba binshi zaki yi” A’a Yaya za’ayi in bishi dan Allah jeki kice mishi yazo muje” Cafdijan wlh bazani ba, ai in niceke binshi zanyi in tsaya gabanshi inta tsalle harsai natara mishi jama’a, yanzun nan ke barin kukan zakiyi? Tsaki Aliya taja tashi dan Allah kije’ Wlh bazani ba kibar ma Bata bakin ki, nidai yau Naga wulakanci kamar wata mayya, Kuma fah duk wannan masifar saboda ni yakeyi duk ya haukace kamar wani tababbe”Murfin mutar Aliya ta bude ta fira cikin kallon motocin ta tsallaka titin har ta isa gaban shi, ahankali tace, muje toh” Badai ni kikema kuka ba akan waccen wayiyar kanwar taki” Kayi hakuri ba kanwata bace ni daya kaima kanwarkace Kuma kalmarce tamin kama da cin fuska kaga tana gurin” Wacece ita, hakan Zaki aureni kina fifita wata can akaina, ni agabaki takemin iskanci ai” Ina Mata fada Enisilim ma yamata kasan kowa da halin sa” Karki gaya min zancen banza, ni babu ruwana da yariyar nan, Kuma karki sake fadan sunana gaban yariyar nan balle hartaji wani lbr akaina” Shikenan naji muje toh, ganin bashi da niyar tashi ta mika hannun ta roko rigarsa ta gefen cikin sa mikewa yayi cikin zuba Mata ido, ahankali suka fara tahowa har suka tsallako titin, motar ya shiga ya zauna sannan itama ta bude ta zauna ganin yaki tada motar tace muje” Kallonta yayi sau daya ya kawar dakai tare da fadin ki gyra mayafin ki” Cikin sauri Aliya ta gyara lafayanta yayin da Munirah ta durkusan dakai cikin wata yar karamar dariya” Suna isah Sadiq ne ya fara sauka, yayin da suka jera da Aliya, itako Munirah bin bayansu take tare da kare masu kallo, acikin ranta tace Dan Allah jebeshi har yafi mace yanga, ji inda yake kamar mejin wari” Gyalenta ta cire akafada ta rikeshi ahannu suna shiga itama tana saka kafarta” Wani tabire ya samu ya daura hannunsa yana fadin kije ki zaba abun da kike so Ina nan” Bin bayan Aliya Munirah tayi tana dauka tana neman shawaran Munirah, cikin tsiwanta tace” Nice zan zaban miki, dafa masoyin ki kike tafiya, wucewa tayi can ta samu wani guri ta tsaya” Ganin Munirah tabar kusa da Aliya Sadiq ya taho hannunsa duk cikin aljihun sa yake fadin mugani” Daga kayan tayi kala biyu data zama tana nuna masa” Lumshe Ido yayi tare da fadin ba laifi, kin fison irin wannan ne?? Eh toh Kai wanne irin kake so? Tafiya ya fara yana dubawa yayin da Munirah ta hangoshi tai saurin zuwa gurin daidai ya nuna wata” Kama rigar Aliya tayi takura mata Ido sannan tace” Wannan bazata min ba saidai mu duba wadda tadan fita” Gaba suka karayi cikin sauri Munirah ta roko hannun Aliya tai kasa da murya tana fadin kice yazabar miki” Lumshi Ido Aliya tayi adaidai lokacin ya sake taba wata” Amukarnin wannan girmansu daya da waccen fah, wani saurayi ya Kira cikin masu kula da gurin yace muna neman size din daya danfi wannan kadan….. Ayya ranka ya dade, irin wannan kayan wannan shine Babban number da yake zuwa duk inda zakaje bazaka samu wadda ya fita ba” Hannunsa ya ciro a aljihu ya shafa keyarsa sannan yace ba damuwa jeka barin duba wasu” Hannun biyu Aliya tasa afuska tana dariya tare da rufe fuskanta” Gurin ya karede tass be samo ko daya ba dan haka yace Aliya ki dauki abun da kike so kawai” Batare da Aliya taji wani abu ba tazaba abun da ranta keso ta matso kusa dashi tana fadin nagama” Kudin yaje ya biya suna kukarin fita yace Ina wannan yariyar ne? Juyawa Aliya tayi bayanta cikin duba Munirah ganin babu ita yasa ta dawo da baya tana me kwala Mata Kira” Jin Bata amsa ba yasa ta dawo da baya da niyar ta fada masa, saidai shima babu shi agurin, cikin sauri ta nufo hanyar, yayin da tana karwa kwana ta hangeshi hannunsa cikin aljihu ya wuce Munirah dake tsaye da wasu Samari guda biyu suna ta kashe hotuna” Tahowa tayi itama ta wucesu tana fadin muje” Bayan Aliya Munirah ta biyo suna tafe take cewa narantse da Allah Sadiq din nan sai ahankali, nidaman so nake nagani shi yake zaba koko wasu yake sawa su zabar masa, Kuma nabawa idona abinci idan kinyi aure ko banje gidan kuba nasan wani irin zama zaku yi, bakinciki zaita tura miki Kuma baki isa kiyi mgn ba, ya dakeki yakuma hanaki kuka, ai kingani dazon ko rarrashin ki beyiba saidai ke kika rarrasoshi, ku kuke ganin kamar bani da wayau Kuma ni da wayauna sarai, ni bakeba ma Sadiq dinma sai in saidashi, wlh nabaki shawara karki yadda ki aureshi idan ba hakaba Kuma zakice nagaya miki wlh wlh wannan ba mace da zataji dadin zama dashi, kuka kawai zaita saka ki” Isan su wajen motarsa yasa Munirah tai shiru tare da bude bayan motar ta zauna” Itama Aliya gaba ta zauna saidai jij gabanta tayi yayi wani mummunan faduwa saka makon kallon fuskar Sadiq” Wani irin baccin raine wadda bashi boyowa, idonshi jawur, yayin da ya tsurawa guri daya Ido hannunsa Aliya ta taba muje gatanan ai” Afusace ya waigo ya kalleta ya juyo ya kalli Aliya kamar zai daketa, matsawa tayi tare da runtse idonta, Jin Karan bude motar yasata bude idonta bayan shi ta hango afusace yake kokarin komawa gurin da suka fito yanzun nan, afusace yake tafiya” Sakin baki Munirah tayi Aliya Ina zashi?????????? Idon Aliya akanshi tace bazai wuce gurin yaran da yaganku tare ba” ???????????? Tabdi Aiko bazan tsayawa ba sai mun hadu agida” Bude motar tayi ta fita yayin da Aliya ke kiranta tana fadin inazaki toh?? Wucewa tayi batare data saurari Aliyaba bat ta bace agurin” Aliya kadai sai raba Ido take zuwa can taga wasu maza sun fito rirrike da Sadiq tsoro masifar Sadiq tafara bata ganin tahowan sa yasa ta gyara mayafin ta, shiga yayi ya zuna batare data kalli bayan motar ba yace Ina take?? Tafita Wai mu hadu agida” Kansa yashafa lokaci daya ya bode motar ya fita gabasss yayi cikin dube dube sannan ya dawo yai Yamma cikin rike kwankwaso” Dawowa yayi bayan ya tabbatar babu ko kyallinta, zama yayi amotar acikkn ransa yake tambayan kansa wannan wacce irin yariyar ce afili kuwa cewa yayi kema harda laifinki meyasa Zaki Bari ta tafi, aguje ya kwasa motar yana tafe yana dube dube har suka isa gida, ganin gyalenta afarfajiyar gidan ya tabbatar masu da ta dawo gida” Sauka yayi ya wuce batare dayacewa Aliya komai ba, jikin Aliya asanyaye sosai ta shiga gida” ****** Misalin Karfe 8 nadare Sadiq da Sagir zaune gaban iyayen su maza da Mata” Har yanzun fuskar Sadiq babu wata walwala” Gyaran Murya enisilim yayi sannan yace kungama shawara nan dacen Ingall, inda muka tsaida ranar daurin auren ku wata biyu masu zuwa dan haka nace gara asanar daku ku fara shiri” Shiru kowa yayi yayin da Enisilim yace kuce wani abu mana hakan yayi maku??? Cikin sosa Kai Sagir yace yayi Malam” Dariya sukayi sannan Alhaji Mustapha yace daman nasan Kai zakayi mgn, Sadiq ko bazaice komaiba Kuma yazama lallai yau yayi mgn inason Jin ra’ayin sa” Cikin kawar dakai yace karatun su fah?? Zasu karasa adakin su, ko me kace?? Cikin sauri Sagir yace yayi Sadiq kusa cewa yayi ni gaskiya gara abari tagama?? Gaba daya Ido suka zuba mishi yayi da mahaifinsa ya hade fuska yace dalili?? Kasa kasa yace banada ra’ayin ne Abbanin” Jimmm sukayi sannan zuwa can Alhaji Abubakar yace kenan bazakarta aiki ba?? Shiru yayi harsaida aka sake tambayan shi sannan yace bana da ra’ayi ne” Himmm shikenan zamu tambayi yariyar idan ta amince shikenan” Cikin kasa kasa da murya yace abani dama na tambayeta da kaina” Nan danan mahaifin sa ya saki murmushi dan da ya zata zukewa yake son yi, an baka daman, kace dai zaka mata wayau, kowa na aiki ita ahanata shikenan idan ta amince ai” Daga haka aka sallame su yayin da Kai tsaye part din su Aliya ya wuce falon ya zauna sannan ya tura Lubbuna ta kirata” Tahowa take ahankali yayin da yai saurin lumshe idonsa shi kanshi wani lokacin yana rasa gane kansa zama tayi nesa dashi yayin da ya tashi ya matsa dafda ita, ganin zaman be dace ba gashi acikin falon su wadda koda yaushe wani na iya shigowa” Lumshe idonsa yayi tare da Kara matsawa daf da ita ganin zata Kuma matsawa yai saurin roko kwankwasonta yana fadin meye haka?? Hannunsa ta rike tana fadin Amukarnin wani zai iya shigowa fah” Bakomai Aliya, fitulun basu da haske, Kuma Ina cikin tsananin damuwan da nake rasa inda zansaka raina, nasan ke kanwata ce Kuma kina tausayi na dan haka kullum nake Kara sonki cikin zuciyata” Cikin sanyi sosai tace Amukarnin idan fitulun basu da haske ai Allah yana ganin mu” Cikin sauri ya zare hannun sa tare da fadin, hakane, shiru yayi cikin yanayin tunani” Ganin Haka yasa tace Amukarnin idan nabata maka rai kai hakuri kajj” Wani irin Murmushi yayi bakomai Aliya, yanzun daga gurin su Enisilim nake suce sun tsaida rana wata biyu kina da labri?? Eh Yayi kau, saidai ni ban amince da karatu ba agidana, nagaya masu sunce sai anji ra’ayin ki, nakuma roki subani daban tambayan ki sunkuma bani, abun da nake son ki gane anan shine daga ranar da aka daura aure aljanar ki tana karkashin kafar mijin ki, ni kenan, idan kin faranta min raine kadai zansa miki albarka har ki sameta, boko rudin duniya ce sannan Kuma ni Ina da kishi sosai, ban yadda da aiki ba, kibar waccen wawiyar tayi karatun, daman ita batasan ciwon kantaba, shashanci tasa agaba, ki dubi abun da take yi dazon ni bazan yadda matana taje makarantaba kodan saboda irin haka, tunda Sagir ya amince kibarsu kinemi aljanna kawai” Sosai Aliya taji ta gamsu da bayanin sa koba komai tana son Sadiq sosai, amsa tayi cewa ta amince cikin sauri ya riko hannunta idonsa cike da kwalla yace nagode Tamudiriccin, yanzun banda wata Tamudiriccin saike daya, sunbatan ta yayi akunatu yayin da take fadin” Nikadai ce kanwarka?, Idan baka shiri da Munirah Lubbunah fah?? Mikewa yayi tare da dagota tsaye naki nadavan ne, ki daina hada kanki dasu, ke saura kadan ki zama tawa” Murmushi tayi idonsa akansa yace zan wuce me zan samu?? Me kake so?? Kirjinta ya nuna idonsa akansu” Cikin sauri ta dada gyara mayafinta tare da kauda idonta” Bazaki bani ba?? Turo baki tayi tare da juya baya, cikin sauri ya rungumeta tabaya tare da sunbatan wuyanta bakomai hakan ma nagode zakizo hannu ranar zaki gane baki da wayau” Zamewa tayi cikin sauri ta wuce Saida ta leka dakin Munirah ta tabbatar da tai bacci sannan hankalinta ya kwanta” Sagir kuwa be samu ganin Munirah ba Saida safe kin fitowa tayi saboda tsoron kar Sadiq ya bigeta” Meyasa jiya kikaki fitowa??? Amukarnin Sadiq nake tsoro? Yaushe kika fara tsoron sa? Ni ai yanzun baruwana dashi tunda idan Ina zancen shi haushi kakeji” Yafi hakan kin kauta” Amukarnin indan tambaye ka mana? Inajin ki, yanzun ace saurayi ne kulllum yaje saya ma masoyiyarsa abu baya gane size dinta Kuma ko sau daya betaba sa’a ba…… Kafin ta kaj karshe yace be damu da ita bane” Toh haka yayanka yake yi” Hade fuska yayi wanne ?? Amukarnin Sadiq haka yakema Aliya” Yanzun fah kiga macewa baruwanki dashi, Wai Munirah meke damun ki ne? ???????? Allah yabaka hakuri mantawa nayi” Kansa ya kawar gefe cikin nuna fushi cikin sauri ta mika hannunta ta kama dan karamin gemon shi kamar tanawa yaro wasa” Dariya yayi batare daya shirya ba sannan yace daga yau sai yau ki adana wannan wasan naki sainan da wata biyu indai ba kinason asamu matsala ba” Wacce irin matsala?? Ki Kara tabamin gemo kika irinta, mikewa tayi da saurinta ta matsa gefe yayin yake cewa rawan Kai ya kusa karewa yariya, idan nabarki ni, aure bazai barki ba, duk wannan abun da kike samun guri ne, wata rana da kudi aka hadaki bazakiyi ba” Cikin dariya tace banga amun dazai hanani mgn ba wlh, ko mugunta aka min sainayi mgn enisilim ma yace lafiya garan” Dariya yayi zako ki hado dame lafiyan, ke lafiya ni lafiya saimu hadu muyita rawar kai……. Motar yan sandan data suka shigo har guda biyu yasa su barin dariyar da suke yi, yayin da suke bisu da Ido” Enisilim ne ya fito da sauri adaidai lokacin da police din ke dirowa Daga nesa Sagir ke hango Enisilim yana magana dasu zuwa cen Alhaji Mustapha da Alhaji Abubakar suka fito, matsawa Sagir yayi yayin da Munirah ta shige gida” Idan ya dawo anjima zamu zo tare insha Allahu” Cikin motar suka koma yayin da Sagir ke tambayan Su me yafaru ne” A’a jeka abun ka babu komai” Cikin rashin kwarin jiki yabar gurin yana tafe yana waiwayen su yayin dayaga jikinsu yayi sanyi” ** Tun jiya nake tambayan ka meke damun kake ta fama da Jan Ido kanace min babu komai, magana nake maka kamin shiru karyar rashin mgn kake zamma rashin mutuci wlh Maya hadaka dasu??? Tashi yayi zaune cikin Jan Ido yace” Daukan hoto sukayi da Tamudiriccin?? Lumshe Ido Annanin tayi cikin tsananin Mamaki wacece haka, Aliya ko Lubbunah??? Kawar dakai yayi tare da fadin a’a Toh inajin ka wacece??????????????? Tamudiriccin……….. Muneerah Idan anga kuskure ai hakuri dashi nasamu matsala ne???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ Page 38-40Typing……..????️Rufe Ido Annanin tayi sannan ta sake budesu akan sa, yadda yake mutsu mutsu agadon take kallo ya kasa kwanciya guri daya duk da cewa tana tsaye akan sa” Har yanzun Bata dauke idonta akansa ba, shima bebar abun da yake ba, ahankali ta karasa bakin gadon ta zauna yayin data juya mishi baya cikin taushin murya tace tashi ka zauna” Annanin bani da lafiya sanyi nakeji..… Katashi nace banson musu” Tashi yayi cikin sauri ya zauna yayin data tsareshi da ido, inajin ka kace mene??? Cewa nayi Muneerah” Suka yi hoto da ita??? Kanshi akasa yace eh” Ido takara lumshewa sannan tace” Shine ka zage ka musu dukan mutuwa ko?? Ganin bazata samu amsaba ta sake cewa toh ita Muneerah meka Mata??? Kawar dakai yayi batare da yace komai ba kallon sa Annanin take tana karantan sa zuwa can ta mike cikin tsananin firgici da tashin hankali tace Sadiq toh Wai meyene tsakanin ka da Munirah haka?? Cikin sauri yace bakomai mikewa yayi, zan yi wanka Annanin ana jirana awaje…… Karya kakeyi Sadiq dawo ka zauna” Zaman yayi sannan tace inajin ka naji ajikina akwai wani Babban al’amari da kake boyewa meyeshi ka gaya min” Annanin babu komai ba, rainane yabaci kawai har nai hakan” Ba wannan na tambayeka ba cewa nayi meye tsakanin ka da Munirah….. Bakomai” Kirjinta ta nuna tare da fadin, ni kakeyiwa boye boye? Waye zaiyi maka maganin damuwar ka duk duniyar nan? Idan kuma har kana ganin sirri ne waye zai iya boye maka sirrin ka duk duniyan nan sama Dani, kafin son kaita zama da damuwa har wani ciwon yazo ya kamaka” Ni fah Annanin Banda wata damuwa inda akwai wani abu zan gaya miki ai” Murmushi tayi sannan tace shikenan Sadiq nikuma yau zan nuna maka Nina haifeka, kuma tun kana tsuma nake kokarin sanin damuwarka, lokacin bakasan inda yake maka cewoba, amman saboda tsananin kulawan uwa akan danta nake sanin inda ke maka ciwo, awannan lokacin baka iya mgn ba Sam dan haka har yanzun ma bana tunanin zata canza zani, Sadiq kana son Munirah” Wani irin mummunan faduwan gaba ne ya sameshi, take yaji zufah na keto masa, cikin sauri ya zame kasa batare daya shirya ba, kafarta ya rike Annanin dan Allah ki rufamin asiri kibar wannan mgn acikin ki” Meyasa tuntuni baka fada ba?? Annanin abun da ya faru ya riga da ya faru dan Allah abar zancen” Shiru tayi yayin data kurawa guri daya Ido sannan tace” Nikaina zanso abar wannan mgnr Sadiq, domin Sagir ma yajima yana son Munirah ni nadade da fahimtan haka tun kafi ma ya fadi kowa yaji, fitowan wannan mgnr yanzun tamkar yayyafa ruwan gaba ne atsakanin ku, baya ga hakama da ace kaine zaka aureta saidaga baya aka gane Sagir nasonta har haka, zaka iyacin girma ka bar masa, wannan kuwa kaine Babba abun kunya ne wannan zancen ya fita, zanfi kowa son alillufe zancen” Nima Ina matukar son haka Annanin, shiyasa ma na zabi Aliya, domin in cire Munirah cikin raina Kuma ma nacireta” Baka ciretaba, inda kacireta da bakayi abun da kayi jiya ba, Kuma ni mgn ta gaskiya nafison ka da Aliya, naji Dadi sosai nayi farin cikin fiye da inda baka zato danaji ka zabi Aliya, yariyar tana da hankali sosai, barin gaya maka abun da bantaba gayawa kowa ba, bana son auren Sagir da Munirah ko kadan, nayi shiru ne sabo da naga yana sonta tana son shi, sannan ya iya hakuri da rashin kunyanta, inda kaine kace kanason ta tunfarko bazan taba yadda ba Sam, baka dace da itaba, Aliya tafita nutsuwa, kaima Kuma in banda sharri zuciya mezakayi da ita, yariyar da bakinta baya fadin alheri akan ka” Nasani Annanin tuni nacire tunanin aurenta cikin raina” Jimmm Annanin tayi zuwa can tace inason kamin wani alkawari guda biyu zuwa uku, nafarko katashi cikin dare karoki Allah yacire maka ita azuciyar ka, sannan ka saki jikin ka kadawo kamar da, abu nakarshen Ina son kayiwa Munirah irin kallon da kakayiwa Lubbunah, bazance har Aliya ba sabo da ita kana shirin aurenta ne, amman Lubbunah kanwarka ce hakama ma Munjrah, idan naga kana hararanta ko kinyin mgn da ita zance akwai wata akasa” Dagowa yayi idonsa ya Kara jah sosai yace, duk zanyi yadda kikace, Amman Banda mgn da Munirah, ni ba ruwana da ita, dama can bawasa nake da yara ba, amman duk da hakan be hana tamin rashin kunya ba, gaisuwa ce kawai, Kuma ninake gaba da ita idan tagaidani zan amsa bayaga haka banda wata mgn da ita” Gamsuwa Annanin tayi da zancen sa sannan tace shikenan, dama su Alhaji cewa sukayi in Kira musu Kai, amman yanzun zan koma ince bakajin dadi, sun ruga sun kashe rigimar daman bayan sun biya kudin da asibitin suka bukata, innaje zance Ina tunanin rigimar taku akan Aliya ne” Har cikin ransa yaji son mahaifiyansa ya Kara shiganshi” * Sagir da Sadiq ne zune kasa kusa da mahaifiyar su, hira suke sosai yayin da sagir keta dariya Annanin natayashi shikuwa Sadiq murmushi kawai yake, zuwa can Sadiq yace waikai baka gajiya da mgn ne” A’a bashi yayi, lokaci ne wata rana nan zanzauna shiru babu me tayani hira Dan kai ba magana kake ba, koda yake kaima din tafiya zaka yi” Murmushi Sagir yayi Dan ya dago inda ta dosa cikin shakiyanci yace Annanin har kewa ta fara damun ki? Toh idan kuka shige dakin matan ku wazan gani?, Musamman Kai Sagir ai inaga saidai ka leko kace min Hi✋ natafi office, idan ka dawo Kuma kace Hi✋Munirah najirana agida, Ina ga abinci kana abinci najirana agida” Fashewa sukayi da dariya har har Sadiq bayan Sagir ya tsaigaita yace habadai Annanin saikace Mijin tace” Kawar dakai Sadiq yayi tare da fadin gaskiya ta fadi zaka aika” Hararansa Sagir yayi sannan yace toh kin fada dawa, saura nashi” Kallonshi Annanin tayi ta cikin murmushi yayin dayai saurin kawar da kanshi gefe” Shi Sadiq zai iya kwashe sati biyu ma be lekoba, idan ya tashi zuwa kuwa zakaga yana cincin magani sannan yace, tace agaishe ki” Fashewa Sagir yayi da dariya, yayin da Sadiq yace Annanin kibari banso” Toh Annanin idan Office ya dawo fah?, Sagir ya sake tambaya Cikin yar dariya tace kaima kasan cewa zaiyi barin je gida nagaji da yawa, yana dandaure fuska bayan can gidan ba haka zai rika yi ba” Dariya Sagir keta yi yayin da Sadiq ke fadin nace banso fah, ni haka nake, bawata yariyar da zata canza ni” Dallah tafi can jebeshi, aina godema Allah daya hadaka da Aliya ko ita dima bazataji dadin zama dakaiba, idan baka rage tamtamke fuskar nan ba, Kai ai baki ma tsoron zuwa gidan ka zasu rinka yi” Mikewa yayi ya yana Shirin barin dakin cikin kunkunai” Sagir kuwa babu abun da yake sai dariya haryanzun” *** Lubbunah da Aliya kwance akan gadansu lbr irin rashin mutumcin da Munirah kewa Sadiq Aliya kebawa Lubbunah yayin da Lubbunah ke fadin” Kema ai kina ban haushi, kece fah yayar Munirah ba ita bace Babba ba, Amman sai ki dinga barin tana miki abun data ga dama” Toh Yaya zanyi da ita Lubbunah?, Itafah ko baka shiga harkarta ba saita shiga taka” Tsaki Lubbunah taja ai inajin ki jiya dazaku fita da Amukarnin kika kirata bayan tafita ya korota kuma Dan tsabar iskanci takira Babamu tace gashi can zai fita dake, ni inda nice ke cire rana daya zanyi in mata duka wlh, sosai yanzun Munirah take ban haushi, Amman ba laifinta bane, laifin mu ne da muka Bari tun farko tana shiga cikin mu aiba tsarar mu bace” Hmmmm kwata kwata banson halin Munirah Lubbuna, gashi tasa Amukarnin Sadiq agaba Nima tace batason alakata dashi, bakiji abun da take fada ba bakinta babu alheri acikin sa” Kwashewa Lubbunah tayi da dariya sannan tace itafa Munirah kin gane nufin ta?, Ita fah balakin haushin Amukarnin Sadiq takeji, ita kullum kokarinta taga ammai fada ko Kuma ace bashi da kirki, ta tsana taji ance yana da kirki ko Kuma komai ace Amukarnin Sadiq, gani take duk gidan anfi sonta Kuma ta lura shima suna sonshi sosai” Niko bana ganin Haka Lubbunah meye kikace haka?? Lallai ai hakane ma, yanzun fah ta hadashi da baban mu har gunsa taje tace Masa Amukarnin Sadiq yana neman mata” ????????????????, Munirah batajin mgn ……. Shigowan Munirah yasa duk suka juyo suka kalleta, wuce su tayi tahau can karshen gadon ta kwanta cikin kawar dakai Lubbunah ta fara danna wayarta, yayin da Aliya tafara tarkata takardunta data baxa agurin” Tunda akayi gumm, munafunci na ake yi” Yi sukayi kamar basu jitaba, yayin da fara kokarin sauka agadon tana cigaba da fadin” Inba tsoroba afada agabana” Ke Munirah ki shiga hankalin ki wa kikaji yayi zancen ki? Barta anyi zancen naki dan ubanki kiyi zo kiyi abun da zaki yi” Ni, Allah ya kauta in hada kashina daku, ku shafa min warin kashi, saidai in sa muku bulala” Sakowa Lubbunah tayi tana fadin Aliya mukoyawa yariyar nan hankali” Tanajin haka takwasa da Gudu Suma aguje suka bita, ficewa tayi a part din yayin data nufi part din Hajiya Fatima Suma rufa Mata baya” Karo taci da wani abu gummm taji ta bigi dan haka tafara fadin wlh duk wadda ya tabani saina hadashi enisilim kankame jinta tayi tana jiran Jin saukan duka” Ji tayi har yanzun bataji saukan dukan ba yayin da wani daddadan kamshi ya ziyarci hancinta, cikin nutsuwa take shakan kamshi ahankali tafara tuna kamshin waye wannan” Tunawa da tayi damishi yasata saurin dago kanta sama ta kalleshi adaidai lokacin da yake kokarin rabata da jikinsa cikin sauri yasa hannunsa ya dafa kasan cikinsa yana fadin meta muku haka?? Cewa tayi zata zane mu” Juyawa yayi yaima Munirah wani irin kallo sannan ya juya ya kalli Aliya hardake zata zane din?? Haka tace Amukarnin ita intazo guri idan bayi fadaba batajin dadi” Munirah ya sake kallo yana rike da hannunta daya yayin da daya hannun yake Kan mararsa Wai haka kince zaki dake su? Eh, sune suka zauna sukayi tacin namata” Danye ko gashshe?? Danye” Juyawa yayi ya kalli Aliya da Lubbunah yace to kukuma meyasa kukaci namanta?? Dariya Aliya tayi Amurkanin aimu ba mayu bane” A’a, yazama dole ta hukuntaku ni gurin zan maku tayi maganin ku anan guri” Tahuwa Lubbunah tayi tana fadin Yauwa hakan yafi kaje mu kabarmu da ita” Toh kujirani inci abinci indawo man Sakin hannunta yayi yayin datai saurin wucewa ciki falon Hajiya Fatima” Lubbunah kuwa cewa tayi baxafah ta dawo ba” Murmushi yayi sannan ya kalli hanyar databi ta wuce yace aina sani wadda zaiyi zana inashi Ina gudu, tsiwace tai mata yawa kawai ba wani abu ba, haka zayita hakuri da ita masamman ma ke Aliya koba kanwarki bace??? Kaima ai kanwarka ce”Lumshe Ido yayi ya bude cikin faduwan gaba kinfara mayarmin da mgn ne kema?? Sunkuyar dakai tayi sannan tace a’a” Cikin sauri Lubbunah ta wuce ciki, Sadiq ma ficewa yayi batare daya kalli Aliyaba ganin fitan shi Aliya ma ta shige ciki” *** Ke!!! matsa karki karya ni, waike bakijin kunyata sai kizo ki dare min jiki??? Umma sosamin kaina zaki yi” Dankwalinta ta zame tare da tura yatsunta cikin gashin Munirah tana fadin” Idan kin tafi gidan mijin ki maji Sakatt acikin gidan nan, ko jiya Saida najiyo ihunki tundaga part dun ku, zan sayawa Sagir durina me baki buyu idan baki nutsuba ya miki hukunci da ita” Rufe idonta tayi tana fadin ai wlh nasan bazai dakeni ba, saidai yayi fushi, Kuma idan yayi fushin nasan abun da zanmai yayi dariya” Baki Hajiya Fatima ta bude sannan ta ture Kan Munirah tana fadin tashi min ajiki Mara kunya, wato ko irin dan kunyar nan babu, inason inga ranar da zakiyi hankali Munirah, yanzun fah sai danki yayi rashin ji kice zakiyi mai fada ko???????? Cikin sauri ta rufe idonta sannan ta tashi zaune tana me nuna taji kunya” Daidai lokacin su Aliya suka shigo yayin da Munirah ta bude idonta tana me hararan su tana fadin” Waini za’ama wayau, in tsaya a jibgeni, ni jikin karfe garan, ku tambayeshi tsakanin shi da Allah ya Gaya, beji zafi ba Dana fada cikin shi?, indai zai fadi gaskiya harsaidaya rufe idonshi sannan ya dafa cikin shi” Hajiya Fatima narike da baki tace waye din” Lubbunah ce tace da Amukarnin Sadiq take” Nashigesu ni Fatima???????? Munirah Sadiq din kikecewa in zai fadi gaskiya? Toh Umma shine fa ya rike masu ni zai basu su dakeni, Kuma ban musu komaiba, dan dai ni komai sai ace ni, komai ace ni, kuka tafara hawaye wani nakorar wani cikin sauri Lubbunah ta juya ta fice cikin mamakin Munirah” Umma kuwa jawota tayi jikinta tana share Mata hawayen take fadin” Gaskiya Aliya kubar yi Mata irin haka, idan Kuma itace karamarku bekamata ku taru ku dinga kuntata Mata ba” Cikin kukan Munirah ta sake cewa, Kuma kowa na laifi agidan nan Amman nawa ake gani shiyasa wata rana nake cewa dama duk su mace in huta” Ton nidai ya isheni banson wannan haukan naki tashi kije…… Shigowan Sagir yasa suka maida hankali su gurin shi kallon Munirah yayi yai murmushi sannan yace waya tabamin ke?? Turo baki karayi yayin da Hajiya Fatima tace gasu nan Lubbunah da Aliya sai Kuma Sadiq nake tunani tafarayin bakar addu’an tata, nifa inaga yariyar nan sai an hada Mata da rokon Allah” Dariya yayi sannan yace wlh Bari zatayi Annanin bari Kuma ki gani, ni harna hangota ta nutsuma wlh, watarana ma sabo da nutsuwar da zatayi saita baki tausa yi” Toh Allah yasa, Amman dakamar wuya fah” Juyawa Sagir yayi ya kalleta sannan yace ni ahakan ma son aba take yi” Murmushi ne ya kwacewa Munirah yayin data mike aguje tabar part din” Kallon hanyar Annanin tayi sannan tace akwai aiki sosai fah agaba ka, idan kayi sake zakasha muguwar wahala ba fata take maka ba, Munirah bata shiru kowacce magana tana da amsan ta” Annanin kiyi mana addu’a kawai, yaritace ba wani abu ba Kuma ni Ina sonta sosai Kuma inaji ajikina zata Bari insha Allahu daga ranar da aka daura auren mu komai zai canza insha Allahu, ninasan ni kadai ne zan iya zama da Munjrah cikin kwanciyar hankali, sannan Kuma aure zai iya canzata Annanin ki kwantar da hankali ki, saura kadan ne zakiga Munirah ta gyaru insha Allahu harma kiyi alfari da kasancewar ta surukarki” Toh Sagir Allah ya nuna min wannan ranar nadai kula bakaramin so kakeyiwa Munirah nan ba” Ina sonta sosai Annanin” Toh Allah yakara daidaitaku yakuma tabbatar mana da alherin sa” Amsawa yayi da ameen” **”Amukarnin Sadiq kaji me Munirah take cewa?? Aje wayarsa yayi agefe, ina jinki?? Wai jikin karfe gareta, kaima data fada jikinka Saida ka rufe idonka ka rike gurin sabo da radadin da kaji” Wani irin dariya yayi har hakuransa suka bayyana ganin beji haushi ba ta sake cewa har tana cewa Wai a tambaye ka indai zaka fadi gaskiya” Wani dariya taji ya Kuma yi tare da gyara zaman shi sosai ya rufe idonsa acikin ransa yake fadin” Allah ka aramin dama inci uban yariyar nan, idan ta tafi ahaka ta cuceni, bude idonsa yayi ya kalli Lubbunah, kinaji ko Lubbuna ku daina biyewa yariyar nan, dan Allah, kusata alayin mahaukata inhar kuka biye mata kukai ta guje guje a tsakar gida toh kuma Kun zama mahaukata irinta, jeki abun ki idan kinje ki turo min Aliya” Koda Lubbuna ta juya haushi ne ya kamata taso yaci uban Munirah ne” ** Kishigo ciki mana” Nan ma ya isah Amukarnin” Kodai an hanaki shigowa part dina” Kanta aka tace eh Babanmu yace beson haka” Shiru yayi zuwa can ya dago ya kalleta, Ina cikin matsala ne Aliya, inason ki taimake ni” Toh Allah yasa befi karfina ba” Matsowa ya karayi dafda ita bani da lafiya inason ki taimaka min inason indan taba jikin ki” Cikin sauri ta sunkuyar da kanta kasa” Tsayon lokaci yana kallonta sannan yace karkiji tsoro, kinsan va yaudaren ki zanyi ba, ni dan uwanki ne babu yadda za’ayi in cutar dake, ni zan aureki, Kuma nasan kina sona, dan Allah karki barni in kwana da wahala bayan zakiya min maganin ta” Haryanzun Aliya Bata dago kanta ba dan haka yacigaba da cewa” Kije kicewa Mama zan kaiki gidan Khadija, nasan bazata hanaba saiki sameni awaje……..???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ Page 41-43Typing…..????️Haryanxun batace komai ba, idonta kasa, takasa kallon shi illah wasa da hannunta da take” Kije mana, kiyi sauri Ina jiran ki” Juyawa kawai tayi jikinta asanyaye yayin da Sadiq ya dauki agogonsa ya daura ahannun sa sannan ya fesawa jikinsa turaruka ya fice” ** Annanin su ta samu zaune afalo tare da Munirah azaune, cikin sanyin jiki sosai Aliya tace Annanin Amukarnin Sadiq yace inzo muje gidan Aunty Khadija” Cikin sauri Munirah ta dago ta kalleta murmushi kawai tayi ta dauke kanta yayin da Annanin ke fadin lafiya ko? Lafiya haka dai yace zamuje can” Toh kudawo lafiya Amman karku dade” Juyawa Aliya tayi ta kalli Munirah tace Munirah muje………. Cikin harara tace bazani ba” Haba Munee dan Allah tashi muje” Wlh bazani ba, kibarma Bata bakin ki, inda nai niyar zuwa ko ba’aso sai naje” Annanin ce tace rakata mana Munirah” Ni Annanin bazani gaskiya, wayo suke son suyi min adakan” Bawani wayau rakani fah nace kiyi? Ai sai kiyi tayi, wlh bazani ba, shima yana ganina zai fara masifa kamar wani tababbe” Aliya tunda tace bazataba wuce ku tafi” Juyawa Aliya tayi badan ranta yaso ba, gidan Khadija suka fara zuwa ita kadai ta shiga yayin da yace mata karta wuce minti 5, ba jimawa kuwa suka fito tare da Khadija gaidashi tayi yayin daya amsa cikin tsare gida, har motarsu ta tashi tana tsaye duk da cewa basu dade ba taji Dadi sosai” Kai tsaye gidansa ya wuce da ita yayin da suna shiga falon ya fara warware lafayanta cikin suri ta rike hannun sa, tare da kallon fuskansa, irinkallon da yake Mata yasa tai saurin dukar da kanta, warware lafiya ya farayi tare da ajiyan zuciya sama sama” Bayan ya wareshi ya aje agefe tare da zuba Mata tsayon lokaci sannan ya koma bayanta ya bude zip din rigar yayin da ya rike rigar ta wajen kirjin ta yana kokarin fizzge rigar tai saurin rikewa” Yana daga bayanta yasa hannun shi akan kirjinta yace dan Allah ki taimake ni karki hanani” Hawayene suka fara zubo mata, yayin daya shiga shafa jikinta tare da shishina ta yana sauke wani irin numfashi tsayon minti 20 cikin shakakkiyar muryarsa yace zaki barni in dan tsotsa kirjin ki?? Cikin sauri ta girkiza kanta” Meya sa?? Inajin toron kar wani abu ya faro alhalin bamuyi aure ba” Ba abun da zai faru, bazan wuce nan din ba, Kuma koma na wuce ni zan aureki Aiko?, Meye abun tsoro?? Shiru yaji tayi dan haka ya juyo da ita suka fuskanci juna, hawayen daya gani a idon sa yasashi saurin sakinta, kuka kika yi?? Shiru tayi tare da share hawaye” Kindai San banson kuka ko?, Komawa yayi saman kujera ya zauna idan kin gama kukan kimin mgn” Hawayen ta share dakau sannan tace nagama Amukarnin Kai hakuri” Dan nadan taba jinki ki kike kuka?, Ni zakima rowa? Bahaka bane Amukarnin, ni tsoron Allah nakeji nasan yana ganin mu” Kash, yafada tare da Jan tsaki yayin dayai shiru tsayon wani lokaci, sannan ya wuce yana fadin, mayar da kayan ki, cikin sauri ta shiga mayarwa saidai takasa mayar da zip din idonsa akanta tana ta ciki ciki tsayon lokaci daker ta samu ta maida yayin data dauko lafiya yanta tana kokarin nadawa yace kinyi kau” Ahankali tace nagode” Murmushi yayi sannan yace idan kin gama kimin rawa sai mu wuce gida” Rawa Kuma?? Eh ko bazakiyi ba shima? Cikin sanyin jiki sosai tace Amukarnin muje gida mana” Kafarsa ya daura daya Kan daya gaskiya Ina son kimin rawa” Wasa tafara da hannunta acikin zuciyarta ta tace Sam bazan iya rawaba anan wajen, nasan kur zaimin yaita kallo na bazan iya ba Sam” Ganin inda tayi yasashi ya mike ya fice, bayan sa ta biyo da sauri yayin daya shiga motar itama saurin shiga tayi ya figi motar” Har sukaje gida bece komai ba, tana kokarin bude motar yace shikenan kije ki kwanta kiyi baccin ki ni Kuma kibarni nakwana da wahala” Jimmmm tayi cikin rashin walwala sannan ta bude motar ta fita” Ke zonan!!! Dawowa tayi ta tsaya yayin daya kureta da idon yana fadin” Ni kikama rowa ko?, Wucewa yayi batare daya jira amsan taba, itama ciki ta shiga cikin rashin kuzari” Part dinsa ya shiga yana me shafa kansa hankalinsa tashi yake sosai, dan haka ya rasa nutsuwarsa wannan girgizan data Saba yin sa ne yake ta dawo masa cikin sauri ya lumshe idonsa tare da gyara zamansa sosai” Har yanzun dai bebar hango abun cikin idonsa ba, dan haka ya mike ya nufi window inda ya Saba tsayawa nan ya leka yaga bata” Sakin labulen yayi ya koma gadon yayi rufda cikin na tsayon wani lokaci Amman ya kasa dawowa daidai” Kwanciyar kusan awa biyu yayi gurin sannan yaji busan nata shi” Runtse idon sa yayi daker ya tashi zaune tare da kallon agogon hannun sa” 5:01pm ya gani dan haka yai saurin mikewa ya koma bakin window ya yaye labulen” Ji yayi tamkar anbude masa kofofin gashin jikin sa saboda wani iska dayaji tana shigarsa kota ita” Lumshe idonsa yayi sannan yasake budesu akan kirjinta, wannan wani irin rawa ne yariyar nan keyi, a ina ta koya? tambayan da yaketiyiwa kansa kenan tare da Kara sakin jikin sa da maida duk wani hankalin sa kanta, tsayon minti 25 yayi yana kallon rawan nata sannan ya rufe idonsa tare da wani irin tande bakin sa kamar wadda ya lashi wani abu me zakin gaske, tsayon lokaci yana lumshe da idonsa, Jin yabarjin kidan yai saurin bude idonsa ganin Bata agurin ya saki labulen, cikin sauri ya nufi toilet saboda zufar dake keto masa” Bayan wani lokaci ya fito yana goge jikin sa Tare da sauki ajiyan zuciya, jinsa yake tamkar ya dawo wani sabo babu nauyin komai, duniyar ma wani irin sanyin dadi take badawa, shiryawa yayi cikin jallabiya tare da daura farar hula sannan yai nadin irin na buzayen Ingall” Fitowa yayi rike da carbi ahannun sa ya nufi massallaci lokacin sai kiraye kirayen sallan mangariba ake” Amasallacin suka hadu da Mubarak dan haka suka rankayo gida tare bayan an ida Sallah isha’i” *** Daga Ina kike haka kiketa nishi?? Rawa naje naci wlh, lafayan ta shiga warewa tana fadin wayyo wazai fifitani inason rawa arayuwata wlh” Ainaga alama idan kina rawan tamkar bakijin nauyin jikin ki” Kinga laifina?, yaushe kuka dawo, inata jiran dawowan ku naji shiru shine na wuce part din Umma” Ni tundazon nadawo” Da Ina da Ina kukaje?? Wani irin kallo Aliya tai Mata sannan tace Ina ruwan ki? Himmm, nasan wlh bawani gidan Khadija dazashi, Kuma ki rantse da Allah gidan Aunty Khadija kukaje” Munirah banson iskanci me kike nufi toh??? A’a ni ba abun da nake nufi karki jawo min jaraba” Daurewa Aliya tayi yayin da fara dannan wayarta itakuwa Munirah kwanciya tayi zuwa can tace” Inajin kamshi kala biyu” Sosai gaban Munirah ya fadi saidai dakewa tayi yayin dataki dagowa” Zuyawa can taga Munirah ta juya baya addu’a ta shigayi Allah yasa bacci ya dauketa, jinta shuru yasa tai tunanin ko batayi bacci ba tana daf dayi, ji tayi kamar tana karanta addu’a bacci, yayin data kasa kunne sannan ta tabbatar da me take cewa” Cikin kira’a take kamar wadda ke karatun qur’ani, ni inajin kamshi kala biyu cikin hancina, Abubakar Sadiq wa Aliya” Mummunan faduwan gabane yasake samu Aliya akaro nabiyu saidai taki Bari Munirah tagane ta fahimci da ita take Tajima tanayi Aliya Bata kulataba, illah gabanta dake tsananta bugawa cikin tsoro da firgici” Daga can taga Munirah ta mike tana cigaba da karatun harta wuce Aliya ta dawo da baya ta daba wuyan Aliya tana fadin Aunty Aliya wane ya shafa miki janbaki awuya” Cikin kulewa Aliya tace Ubanki ne? Kafada Munjrah ta dage, kin zagi kanki wlh ko ajikina” Ficewa tayi yayin da Aliya tabitada kallo dan ta tabbatar da fitatan ta” Wayar Sadid ta shiga Kira saidai har tamai Kira uku be daga ba, daren nan kasa bacci tayi” Washegari da Sassafe ta sake Kiran shi sai ana biyu ya dauka menene kika daman da Kira” Kayi hakuri, inason muyi mgn ne” Ina jinki” Kwashe duk yadda sukayi da Munirah daren jiya tayi ta Gaya masa cikin sauri ya dafe kansa sannan yace bansan abun da yariyar nan ke nufi Dani ba wlh, amman duk yadda zakiyi karki yadda kiyi fada da ita ki rabu da ita, idan kika biye Mata mgnr zata iya kaiku har gurin enisilim ita ba hankali gareta ba, ki lallabata kawai” Amman da nasu ka Bata hakuri” Ni, aini bana bawa mace hakuri, inbanda Annanin na, kisan yadda zakiyi tabar mgnr koda kudine kuyi ciniki zan biya” Lumshe ido Aliya tayi cikin ranta take cewa ince zan Bata kudi taje ta gaya ace na zama Babba ba karama ba ni baruwana” Kwanciya tayi ta fara kuka tundaga lokacin Bata bari su hadu da Munirah sai da aka dauki tsayon lokaci” *“”Abubuwa nata tafiya yayin da kwanakin biki ke tahowa har ya rage saura sati daya bikin” Ayanzun wannan katafaren family babu abun da suke banda Shirin biki” Hakama Mutanen Ingall kowa burinsa yazo biki musamman ma da sukaji hardana Sadiq dinsu Dan sosai yan uwa nacen Ingall sukeji dashi” Hafsat da Bilkisu sun samu lbrn auren Sadiq Kuma sunji baccin rai sosai bakadan ba saidai kowacce acikinsu bazata iya kiranshi tamai korafi ba Dan betaba bude baki yace yana son daya ba cikin su, dan haka Shirin zuwa biki kawai sukeyi, hakama zarah tafi kowa zumudin zuwa Nigeria badan komai ba saidan kawai taga Munirah” Aliya da Munirah kuwa kullum cikin masu shirye ake gyaran jiki sosai ake masu dan haka da sun giftaka zakaji kamshi natashi, inda Aliya tafi maida hankali akan Munjrah, duk wani maganin da aka Bata tashanye shi yayin da Munirah ta kwashe masu zakin tasha sauran kuwa saidai ta faki Ido ta zubda” Sannan dazaran lokacin makaranta yayi zata shirya ta wuce bata wasa da karatu ta kwata kwata, itako Aliya tunda aka shiga watan bikin su Sadiq ya hanata zuwa” Shikuwa Sadiq ayanzun baya shiga harkar Munirah daya ganta yake canza guri itama tarege sukarsa ayanzun, saidai duk abun da take kota ganshi Bata bari, shima baya kulata saidai idan ya gaji dagani ya tashi yabar gurin” Annanin ma tana kokarin hada kayan auren yaranta maza guda biyu yayin da takejin wani farin ciki musamman idan ta tuna shakara daya me zuwa idan Allah ya yarda zata iya samun jikoki biyu” Yauma Annanin ce ke zaune ita da yaranta yayin da Sadiq ke zaune kafarsa daya Kan daya yana matsa wayarsa, Sagir kuwa yana zaune daf da Annanin sai janta yake da hira” Annanin? Na’am Sagir da mgn ne? Cewa nayi yaushe zamuje mu nida Sadiq mu hada Balecc” Au kana son ka hada da kanka ne?, Aini nariga nafara maku shiri” A’a ni gaskiya dakaina zan hada” Alhamdulillah Kun hutasheni, juyawa tayi ta kalli Sadiq tace kaifa?? Bani da zabi Annanin kizaba kawai” Hmmn kaji gulma, Wai bani da zabi Annanin kinsan meyasa yace kizamar masa?, Baya iya gane size din da zai dauko Mata” Dariya Annanin tayi sannan tace akwai aiki Sadiq kasan halin shi baya maida hankali, Allah yasa ma yasamu yariyar me hankali, nasan Aliya bazata sawa kanta damuwar halin sa” Batare dayabar Danna wayar ba yake fadin, Annanin banso fah” Karkaso, halin mutum ai dole afada, idan ka hade ranka ko dariya baka son yi” Annanin ki bari fah” Saika bigemin baki, Ina mace zataji dadi ka kana kunbure kunbure matar mutum dai kabarin sa Banda haka ai Aliya baxata soka ba” Dariya Sadir yaita fashewa dashi yana kallon Sadiq yayin da Sadiq din yasha mur ganin Annanin taki barin zancen ya mike kamar zaiyi kuka ya fice” Yana fitowa yaga wata mota na kokarin barin gidan, ganin motar bata gidan bace yasa shi yai tunanin ko ko baki ne akayi” Hannunsa gaba daya yasa cikin aljihu har ya isa inda su Anass ke zaune cikin girmamawa suke Mika gaisuwa batare daya amsa ba yace wacce motar ce tabar gidan nan yanzun nan” Hajiya Khadija ce tazo” Okay ta wuce kenan” A’a zuwan ta kenan ta shiga ciki” Shiru yayi yana nazari sannan ya juya da sauri ya nufi part din su Lubbunah” Rabon da ya shiga part din ya dade sosai, cike ya samu falon mahaifiyar su Lubbunah sai Aliya Munirah Lubbunah duk suna tsaye curko curko cikin tausayawa yayin da Khadija kekan kirjin mahaifiyar su Lubbunah tana kuka” Hannunsa yakara turawa cikin aljihu yayin da duk suka bishi da kallo hade fuska yayi sosai sannan yace me kikazo yi yanzun ??? Gabanta taji yayi mummunan faduwan yayin data Kara kwantar da kanta jikin mama” Khadija!!! Me kikazo yi da daddare?? Cikin kuka tace nazo gurin su Enisilim” Kara hade fuska yayi sannan yace wani abu ne?? Hararan shi Munirah ta fara kome ya tuna saiyai saurin waigawa yace masu Kai duk kubar nan, cikin sauri suka wuce saidai Munira labewa tayi” Ina jinki??? Nagaji da zaman ne Amukarnin ni gaskiya bana Jin dadin zama dashi” Kallo yabita dashi sannan yace” Yana dukan ki ne?? A’a Zagi fan? A’a Akwai wani hakki naki daya danne ne?? Ni fah Amukarnin ba…… Cikin tsawa yace eh ko a’a kawai” Cikin firgici tace a’a Wani irin kallo yai Mata bayan tsayon lokaci yace tashi ki wuce gida ko in nannaushe ki” Sakin Mama tayi da sauri tare da fashewa da kuka itako Munirah tana daga labe take fadin tabdijam” Tafiya Khadija ta fara tana kuka yayin da tausayin ta yakama mama cikin taushin murya mama ke fadin Sadiq lallashi ake yi ba fada ba” Waye zai lallasheta Mama aure taje yi taje can tawa mijinta biyayya, in kuna biye Mata ta dinga kawo maku iskanci kenan” Bayan Khadija ya biyo yayin da mama kebin bayan shi tana fadin daka bari babbanin ku su dawo” Khadija kuwa fadi take ni wlh banajin dadi zaman dashi kwata kwat……. Idan kika sake mgn zakiga abun da zan miki” Motarsa ya dauko ta shiga tana me zubar da hawaye yayin daya figi motar yabar gidan” Fitowa Munirah tayi idonta cike da hawaye matsosu tayi suka zubo Kan fuskarta sannan tace Amman mutumin nan mugune wlh bashi da tausayi ko kadan hawaye taita sharewa batasan iya wani lokaci ta dauka awajen ba hasken fitilan motar yasata mikewa saidai kafin takai ga barin wajen Sadiq da Sagir suka taho atare” Fuskanta tai saurin sharewa tare da kirkiro murmushi, yadda Sadiq ke tafiya ta kallah sannan ta kalla tafiyan Sagir take tausayin Aliya ya kamata sauran Sati daya rak bikin su kuma wai da gaske Aliya Sadiq zata aura sosai takejin takaicin haka nan taji wani masifar tausayin Aliya ya sakko Mata dan haka koda suka iso gurin gani sukayi hawaye na sakko Mata…….???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? SAWUN BAYA ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ Page 44- 47 Typing…….????️A’A Munee waya taba min ke? Hannunta tasa ta share hawayen sannan tace babu komai” Wanni irin kallo Sadiq ke mata yayin da hannun sa duk suke cikin aljihu yana mata kallo kasa kasa” Nasan akwai wani Abu waye ya tabaki? Goge fuskanta tayi tass nace ai babu komai inda akwai ai zan gaya” Wani irin kallo Sadiq yaiwa Munirah mekama da harara sannan ya shige cikin gida ya barsu agurin” Juyawa tayi ta tana kallon shi harya shige gida sannan tace” Wai daman haka akeyi?, Aunty Khadija tazo kawo Karan mijinta ya wani koreta, tanason tayi mgn ya hanata saboda zalinc……. Bana son haka Munirah, koda baki Kira suna ba, nasan da Sadiq kike, nasha gaya miki ba sa’anki bane shi, banajin dadin wannan abun sosai, barin gaya miki wani abu kome zakiyimin aduniyan nan banjin zafin sa kamar inda in kikawa Sadiq ko Yaya ne nakejin abun, wai meyasa hakan ke faruwa ne idan wani abu yayi miki narokeki amadadin sa kiyafe mishi???? Nifah Amukarnin ba abun da yamin tsanarshi kawai nayi” Wani iron kallo yai mata shikenan tunda kin tsane shi tashi kiban waje” Wani irin shan mur yayi dayasa Munira tayi dariya tare da kama gemon sa cikin son yai dariya” Duk yadda dariya keson kamasa kinyi yayi yayin da Munirah tagaji har ta fara magiya cikin bashi hakuri” Ganin inda take bashi hakuri yace naji zan hakura Amman har sai in kin yadda muje kibawa Sadiq hakuri” Turo baki tayi ni gaskiya bazani ba, bana bawa kowa hakuri bayan iyayena sai kai, wlh ko Aliya bantaba bata hakuri ba” Toh tashi kije” Mikewa tayi muje ka rakani” Bazani ba” Kwalkwal tayi da Ido to Wai Kai haka akeyi saboda wani yayan ka saikaita ma mutum masifa, haka akeyi baka rarrashina baka shagwabani…… Ya isah Munirah, wanni irin rarrashi kike son indiga miki Banda Wanda nake miki ayanzun, jikina ya rage kawai na dauraki, shine kawai banyi ba, sabo da keba muharramata bace Amman da ace inada wannan daman danayi indai zuciyarki zata miki sanyi akan Sadiq dan Allah Aliya na rokeki kirage kiyayyar Sadiq azuciyar ki abun yafara bani tsoro” Shikenan naji nabari, Toh tashi Muje Mikewa yayi yana gaba tana binsa abaya har suka shiga falon Umma Suna shiga falon ta zauna ahannun kujer da Sagir ke Kai yayin take kallon Sadiq tace” Amukarnin Sadiq kayi hakuri” Dagowa yayi ya kalleta sannan ya dauke Kai” Cikin wasa Sagir yace Amurnin mu ana mgn fah???????????????? Dagowa yayi ya kalli Sagir cikin sauri ya nuna masa Munirah yayin da munarah tasake fadin” Kai hakuri Amukarnin Sadiq” Daker ya iya bude baki yace naji” Haba Babban Yaya kaida zakace nayi hakuri kanwata, Allah yai miki albarka Murmushi Sadiq yayi sannan yace, ni bana fushi da ita Sagir, Allah ya zaunar daku lafiya” Ameen Babban Yaya Annanin dake gefen sai dariya take ganin Sagir ya tursasa Munirah tabawa Sadiq hakuri hakan yai Mata Dadi sosai” Sadiq kuwa ayau wani irin nutsuwa yaji yana shigansa domin ya dage da addu’a Kuma yanajin saukin abun, kullum sukayi waya da Mammah cewa take ya ringa addu’a dan haka yanzun yasamu nutsuwa sosai Kuma abun da yakeji game da Munirah raguwa yaketayi, kullum yanajin saukin azuciyarsa fiye Dana jiya dan haka yadan murje yai kiba, ayanzun abun daya ne ke yawan damun sa ciwon maran da yake kullum, sai kusan asuba yake samun bacci” Ba yadda beyi ba Aliya tabari yadan tabata, Amman taki, ayanzun sosai yakejin aliyar acikin ransa inda yake danganta hakan da addu’ar mahaifiyar sa akan sa dan yaga canji sosai” Ana saura kwana uku biki baki suka fara sauka, saidai Aliya duk jikinta ya mace itako Munirah ko alamar firgici babu a tattare da ita” Aliya ce zaune tayi tagumi tare da tsurawa waje daya Ido” Munirah ce ta kalleta tace Wai zuru zuru kenan Wai tunanin me kike?? Tabe baki Aliya tayi sannan tace himmm wlh gabana faduwa yake idan na tuna bazan Kara sati daya ba agidan nan” Kwashewa Munirah tayi da dariya meye aciki tunda ba lahira zani ba, ni babu abun da ya daman koda yake na mance kefa gidan Sadiq zaki gidan sa ko banbanci sa lahira kadan ne” Lubbunah ce ta kalli Munirah ta tabe baki sannan ta kalli Aliya tace” Kewan gida da iyaye dole ne Aliya domin Sabo wani abu ne, ki godewa Allah ma zaki tafi gidan mijinki suna sa miki albarka, sai Kuma ki roki Allah yabaki ikon yiwa mijinki biyayya, koda lahira cema idan ka dace baka da matsala” Nikuma ai kinsan tsine min sukeyi ko? Cikin Sauri Lubbunah tace kinji nakira sunan ki??, Au yanzun kinga Sadiq yafi karfin ki ni Kuma kin dawo da rashin kunyan ki kaina ko” Sadiq din Banza da wufi, wayeshi bare wani ke” Kidaiyi hankali da bakin ki inba hakaba Zaki gidan miji da tabo narantse da Allah” Wani irin Murmushi Munirah tayi sannan tashiga Danna wayar ta ta kara akunne” Amukarnin? Yadda tai mgnr yagane tabota akayi Dan haka ciki kasalaliyar murya yace” Na’am, waya taba min ke? Sosai take Jin dadin wannan kalmar Dan haka ta lumshe Ido tare da maimaitawa cikin ranta waya tabamin ke, murmushi tayi afili sannan takara shagwargwabewa tace” Lubbunah nace take cewa Wai in ban iya bakina ba sainaje gidan ka da tabo” Lumshe Ido yayi saboda yadda tai maganar sannan yace, kiba Lubbunah wayar” Nidai bazan baso phone dina ba” Shikenan barin kirata anata” Kashe wayar tayi sannan sannan ta dauki kafa ta daura Kan daya yayin da taji wayar Lubbunah tadau Kara” Duk abun da take suna kallonta Lubbunah najin Karan wayarta tasan Sagir ne cikin sauri ta dauka tare da gaidashi” Bazan amsa ba, me Munirah ta miki??? Rashin kunya take min Amukarnin” Karki sake ki taba min mata, ke bakisan Amarya tsautsaiyi gareta ba??, har kike cewa zatazomin da tabo?, to ko kwarzane karna gani jikinta, kebama kwarzane ba kirki sake Bari ranta ya baci matar Amukarnin ce fah” Kuka me hade da dariya Lubbunah tayi Amukarnin saitaita mana rashin kunya kuma? Lubbunah kudinga hakuri da Munirah dan Allah, itace karama cikin ku Babba Kuma da hakuri aka sanshi, Aliya nakusa daku ne? Eh Bata wayar”Mikawa Aliya tayi bayan sun gaisa yace har dake za’ajiwa Munirah ciwo?? A’a ni bandani Amukarnin” Yauwa, ku Kara hakuri da ita takusa tabari dan Allah ku yafe Mata” Nifah daman Amukarnin Sagir bansashi kaina ba, da anbar gurin nake yafe Mata” Yauwa Aunty mu, yanzun Ina take” Cikin murmushi Aliya tace gatacen tanata mana yanga ta daura kama daya Kan daya Wai ita adole mijinta nasonta” Dariya Sagir yayi yayin da Aliyama tayi dariya adaidai lokacin da yake fadin” Kinga laifina ta?? A’a Amukarnin Amarya ai bata laifi” Cikin dariya ya kashe wayar yayin da Lubbunah da Aliya ke kallon Munirah suna dariya” Ina zuwa haka?? Makaranta zani” Makaranta?, Yaufa baki na hanya Ingall ta hado gayyarta gaba daya” In ba tsohu bane zaizo banga abun da zai hanani zuwa makaranta ba” Lubbunah ce tace toh wlh har da tsoho aka taho, ai tunda akace miki Ingall ta taho kema ki gane” Eh lallai kuce dai saboda auren wancen dan cin burin tsohu ya tattaro tsufan shi ya taho” Kaman kinsa saboda shi kuwa wlh” Tsaki Aliya tayi Nina tafi idan Zarah ta iso ga dakina nan ita daya kar kowa yashigar min wlh” Tam kawai suka ce mata sannan ta fice saidai tana fitowa harabar gidan taga babu mota ko daya saita Sadiq da Anass yake gogewa da alama fita za’ayi da ita” Cikin sauri ta karasa Anass Ina motocin gidan ne” Duk an tafi kwaso baki dasu, fita zakiyi ne? Eh makaranta zani” Ki roki megida mu saukeki tunda hanyarsa ce” Ni daya zaka Kai, kadawo ka daukeshi ko tare dashi zamu jera?? A’a mufita dai gaba daya sauri yake fah” Bazani ba toh, wucewa tayi harta fita gidan sannan Sadiq ya fito ya shiga bayan motar ya zauna” Anass ne yaja motar yayin da tundaga nesa Sadiq ya ango Munirah” Anass wacece waccen?? Munirah ce” Tamudiriccin??? Eh” Ina zata haka??? MaKaranta tace zata Kuma babu mota agidan” Makaranta??, Murmushi yayi sannan yace ka dauketa Anass” Shan gabanta yayi sannan yace megida yace ki shiga asauke ki” Babu yadda zatayi domin tunda Sagir yasa tabashi hakuri ta daina masa rashin kunya saidai bayan idon su dan haka ta daga Ido ta gaidashi yayin daya amsa ba tare daya kalletaba, gaba ta shiga har sukayi tafiya me tsayo babu me cewa kala, ganin akan kusa makarantar taiwa Anass mgn Amman sai taji Sadiq yace kafara sauke ni” Kallon Sadiq taitayi tanaji tana gani aka wuce makarantar tasu sosai taji ranta ya bacci tafiya me tsayo akayi sannan taga sun shiga wani katon banki” Sosai Bank din ya burgeta yayin da take ganin sunan sa rubuce ajikin ginin, gurin ya burgeta sosai tana kallon gurin har suka isa daidai kofar da zata Sadaka da cikin Banki, saidai abun da yabata mamaki wata zarkadediyar budurwa taga tafito daga cikin Banki cikin riga da wando da sukayi matukar matseta tam, kanta dayasha Karin gashi yai kinkimeme ta kalla sannan ta gangaro fuskarta” Kyakyawan ce sosai doguwar fuska tare da dogon hanci saidai bacc bata da haske, Kuma alamu sun nuna ba musulma bace, motar ta nufo Kai tsaye inda ta bude gefen Sadiq cikin sauri ya zura kafafun shi ya sauka yayin da yariyar tai saurin shiga jikin sa, hannunsa yasa yadan shafa bayanta sannan ya sauke hannun nasa zuwa kugun ta yana me ciro wayoyin sa a aljihun sa ya mika Mata Sanan suka rabo da juna cikin sauri ta shiga gaban sa yayin da yake binta abaya kamar wani Bosss” Himmmmm lallai Munirah ta fada lokacin da motar su ke kokarin barin gurin” Har suka isa makarantar takasa daina Mamakin Sadiq domin ta tabbatar su Enisilim bazasu taba zatan ai aikata hakan ba, kallon wani dan ustazu suke mishi ada” Misalin 4 na yamma Munirah ke kokarin komawa gida balakin so take taga Zaharah ayanzun dan haka duk jinta take kamar tai tsuntau ta tashi sama” Tunda driver yazo daukanta ta tabbatar da isowan bakin su yayin da tace mishi muyi sauri dan Allah” Suna shiga gate din gidan su tafarajin kida da busa natashi, yayin da motuci suka Kara yawa agidan sosai da alam mutanen Ingall sun taho da makaladan su inda wani irin busa me Dadi yake tashi wani irin sanyin jikin Munirah yayi lokaci daya Jin busan, karo nafarko arayuwarta dataji busa me dadi Amman ta kasa yin rawa” Sagir ma daya hango shigowanta jira kawai yake yaga tayi rawan yayin daya tsareta da Ido, shima Sadiq be tsammaci zataki yin rawan ba yayin daya Dan sata kallonta ta gefen ido” Samarin ne gaba daya aharabar gidan na nan Nigeria Dana Ingall, inda dayawan bakin keson ganin Munirah Dan tun saukan su sunga Aliya” Tahowa tayi tagaidasu sannan ta wuce jikinta sanyi sosai yayin da Sagir yabi bayanta tana daf da shiga part din su ya sha gabanta” Muneee, menene?? Kwalkwal tayi kamar zatai kuka” Meya faru?? Bakomai” Banson haka fah” Ajiyan zuciya tayi sannan ta matso hawaye suka zubo kumatuta Ina shiguwa gidan naji gabana ya fadi” Dariya Sagir ya fashe da ita tare da fadin aina gaya miki hankali zai shige ki Munirah, aure kenan, yau saura kana biyu ya rage Ina cikin tsananin farinciki, sannan Ina fatan na gobe insha Allahu saiyafi nayau, na jibi Kuma ya kasance min abun alfahari, ke Kuma hankali ne zaita shigarki daga yau” Hawayene suka sake zobowa ni bazanyi farin cikin ba kenan??? Ai hankalin shine farin cikin, bazaki gane me nake nufi ba yanzun, nidai gavana baya baduwa dama mata tsoron gare su” Hawayen tai saurin sharewa ni bana tsoron ka? Eh nasani amman kina tsoron aure, in ba haka ba meye na faduwan gaba? Tunawa da tayi da Zarah yasa tace Nina tafi zanje inga Zarah” Toh sai anjima” *Cikin ihu suka tarbi juna yayin da suka kankame juna tayon wani lokaci ita da Zarah sannan Zarah ta kalleta tace” Kiba kikayi Munirah, amare na rama ke kina kiba? Mezai daman Zarah, Sagir na mugun sona wadda ma zata auri kumurci bata damuba saini” Eh fah can na hangoshi fuskar nan babu rahama haryau din daya kamata ace yana farin ciki, Amman Naga yanata Kiran Aliyan awaya da alama dai yana sonta tun har kiranta yake awaya” Himmm yana sonta fadin raine dai bazai Bari ba, akwai burin tsiya, dazon fah Wai zani makaranta adole sai ya fara sauka dan iskanci, makarantar mu tafi office din nasu kusa Amman sai da nabi abin da ransa keso, hankalin Sadiq bazai taba kwanciya ba sai yaji kasa abakin sa da hancin sa nake gaya miki Zarah” Cikin dariya Zarah tace kifa Bari, yayarki zai aura ko banza dole ki daga masa kafa, sannan ki daina masa fatan mutuwa tunda idan ya mutu yayarki ce zata shiga wani hali” Himmm keni daga Aliyar har Sadiq din baruwana dasu abun da yasama nake dan raga Mata lallabani take” Hira sukaitayi Zarah da Munirah komai tare sukeyi har misalin 11 nadare, ganin Sagir be kirataba tafara kirashi saidai Abun mamaki Sadiq ne ya dauka yace yayi bacci” Washegari ma Kira ta sakeyi Mubarak ne ya Kuma dauka yace Wai ya fita da abokansa” Dan haka ran Munirah ya bacci sosai yayin da take ta ganin Aliya na nata waya da Sadiq tun daren jiya, batasan me suke cewa ba saidai tana ganin kamar Aliyan Bata da walwala, kamar dai Sadiq din fada yake Mata, sannan da safen ma sai kallon wayarta take kamar dai tana tsammanin Kiran sa” Masalin 2 na rana taga Kiran daga Sagir kunbura baki tayi cikin fushi sosai” Allah ya huci zuciyar wannan zukekiyar Amaryar tawa” Turo baki ta sakeyi tare da ajiyan zuciya, tace Ina kashige jiya? Bakine suka mana yawa da nawa dana Sagir Nike kula dasu” Ai yau da Safe ma nakira baka nan” Eh da safe munkai Sadiq Asibiti cikin dare yayi kamar baxai kwana ba ciwon ciki ya murde shi” Yanzun fah??? Mun dawo tun dazon da sauki sosai” Toh ni kazo in ganka’ Yanzun ai gidan cike yake anjima karfe hudu akwai bikin da za’ayi gashinan ana shirya waje” yau zanhau ragumi tare dake, Sadiq Kuma yahau da Aliya, dan Allah kiyi irin zillon nan da kikasoyi a Ingal har kika fado, anzo damasu busa irin wadda kike so” Murmushi tayi sannan tace zanso nayi rawa nayi zillo saidai ni wlh wani iri nakeji” Kamar Yaya?, kinaji kamar baxaki iya rawan ba?? A’a, ko Ina son yi, zanki yi, saboda ni bansan meke damuna ba inajin kamar Banda lafiya” Kinaji ko malama, kiyi zillo zan tareki bazan Bari ki fado ba” Amsawa tayi sannan ta sauke wayar” Misalin hudu na yamma kide kide yafara tashi aunty Khadija ce ta shirya munirah da Aliya cikin shiga irin tasu ta al’ada, hakama zarah Hafsat da Bilkisu da duk sun shirya cikin shigarsu, iyayen su maza da Mata ma ba’a barsu bayaba ba, domin babu baki yau iyaka family ne illah yan bakin da ba’arasa ba irin su abokan Sadiq da Sagir” Tuni aka fara gudanar da bikin ayanzun amaren kawai ake jira” Tuni Sagir da Sadiq suka zaune cikin dakakkiyar shadda tare da nadin buzaye…………..???????????????????????????? ???????????????????? ???????????????? ???????? ???? *SAWUN BAYA* ???? ???????? ???????????? ???????????????????? ???????????????????????????? Na Fadeela LamidoMarubuciyarZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA (heartbeat)KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA and now_SAWUN BAYA_ GARGADI Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba. SADAUKARWA Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su????????✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ® PEN: WRITER’S ASSOCIATION✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ __________________________~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~_________________________——–PAGE——-https://www.facebook.com/110384724043172/——–GROUP——–https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ Page 48- 50 Typing……..????️ Sosai Sagir ya kosa yaga fitowan Munirah, raye raye aka fara, yayin da tuni su Mammah Aysha suke taka rawa ayanzun filin nasu ne na iyaye domin kusan gaba daya iyayen su Mata suna wannan wajen Hajiya Fatima ce kawai Bata wajen” Daga nesa Sadiq ke hango Mammah sosai yakeson ya ganta ko zaiji Dan sauki daga wani irin zugi da zuciyarsa ke masa saidai babu hali” Fitowan su Munirah da Aliya ya dauki hankalin kowa dake wajen, sosai aka shiga kashe masu hutuna har suka isa kusa da mazajen nasu, suka zauna yayin da Munirah na zama ta shiga hira ita da Sagir kamar jira suke cikin fara’a” Aliya kuwa dardar ta dingayi cikin Satan kallon sa yayin daya dauke kansa can gefe” Hutuna aketa daukan su ahakan, dan haka Mubarak ya zagaya kunnen Sadiq yace haba mana meye haka?, kayi kamar wani Bosss ka kallah Sagir mana” Juyawa yayi ya kalli Sagir sai hira suke da Munirah suna ta murmushi, tsaki yaja tare da dauke idon sa” Har yanzun iyayen su ne afilin sai su Zarah da Lubbunah Bilkisu da Hafsat Suma suna tsakiyar filin yayin da Mubarak da Moh’d kecikin filin suna rawa tare damasu liki” Sai ayanzun Sagir ya kula da fuskan Sadiq dan haka yadan zungureshi cikin dariya yace, meye haka??, dan Allah ka saki ranka, saikace Wanda za’ayiwa auren dole” Cikin kawar Kai yace fushi nake da ita” Kayi hakuri, nan ba wajen nuna fushi bane, wajen nuna tsantsan farin ciki, Kuma ka shirya rawa danni rawata zanyi gaskiya” Ai saikaita yi, yafada tare da riko hannun Aliya ya matse cikin hannunsa, kanshi yadawo dashi gefen Aliya yace ni kikewa rowa ko??? Karyar dakai yayi shikenan naji duk abuki dai gobe ne, ayanzun ikon ki ne a gobe Kuma 1:30 Ina tabbatar daga wannan lokacin zan nuna miki kina karkashi na ne, lokacin ne zan gane inda tsoron Allah naki yake” Murmushi tayi cikin gamsuwa tace aina baka hakuri” Bawani hakuri, angaya miki hakuri yana magani ne, da nayi hakurin ai saida aka kaini Asibiti” Kadai yi hakuri” Murmushi yayi sannan yace me wayau, Kiran da akayiwa amaren da angwayen yasa sasu mikewa gaba daya busa ke tashi yayin da agefe daya Mata ke guda hakan yasa Munirah ta fara zubar da hawaye atsakiyar filin, ganin Haka Sagir ya kasa rawar dayai niyayya yayin da ya fara share Mata hawayen fuskar ta dauke da murmushi” Aliya kuwa rawa takeyi ahankali yayin da Sadiq ke Mata liki” Kukan Munirah Kara yawa yake yayin da tafara shashekar kuka dan haka hankalin mutane duk yayo kanta ciki harda Sadiq dayaba da hankalin sa gaba daya kanta” Jawota Sagir yayi Kan kirjin sa cikin sigar rarrashi yayin data tura kanta cikin kirjin sa, kansa ya rankwafu saitin kunnen ta yace menene Munirah?? Gabana faduwa yake sosai Amukarnin” Toh sai Kuma ki dinga kuka?, dazaran kinji irin haka kice innalillahi wa’innalaihir raju’un, yanzun nan zakiji kin dawo cikin nutsuwar ki” Ahakali tafara yadda yace, yayin dayajata suka koma suka zauna har yanzun yana rungume da ita” Sadiq da Aliya kuwa har yanzun suna tsaye afilin yayin da aka rufesu da liki” Haka akacigaba da shagali Sagir da Munirah basu sake tashi ba kallonta kawai yake yana murmushi cikin son kwantar Mata da hankali” Kiran sallan mangariba ya tada taron yayin da maza keta kokarin yin al’wala Tuni Mata duk suka shige cikin gida illah Sagir da Munirah da suke zaune abakin part din su” Amukarnin bazaka masallaci bane? Zani Amman banson in barki gaban ki na faduwa” Ai ya Bari tuni, kaje kayi Sallah saika dawo muyi hira” Indawo Kuma??, Me kikeci na baka nazuba gobe fah za’a kaiki gidana” Nidai bangaji da ganin ka ba, kadawo dan Allah” Tam zanyi kokarin inga nadawo amman dan Allah kiyi hakuri” Bazaka dawo ba kenan? Insha Allahu zan dawo, aini nama fikison dawowan saidai kinsan komai na Allah ne” Turo baki tayi kamar zatai kuka…… Toh kin fara ko?, Dan Allah ki dinga hakuri Munirah ki rage wannan saurin fushin kinji” Ni Ina da saurin fushi ne? Bagashi kin turo bakin ki gaba ba, idan kika yiwa wani haka dukan ki zaiyi fah” Toh aini daman Kai nake mawa” Cikin murmushi tare da lumshe Ido yace ni kimin, Dadi nakeji idan kina min Amman abun da nake son ki dashi hakuri kinji, Munirata Dan Allah ki dinga hakuri banda rashin hakuri kinji? Kai ta daga masa sannan tace jekayi Sallah gashi can za a tada da Allah kadawo anjima” Hannun ya daga Mata cikin murmushi yayin da take tsaye har ya kusa masallacin waigowa yayi yace Munee” Cikin sauri tai murmushi tare da daga masa hannu shima murmushi yayi sannan ya daga Mata hannun ya wuce” Gidan ta shiga tana cike da murmushi yayin da ake ta tsokanar da cewa shagwababbiya kawai kin gama shagwaban? Wucewa tayi abun ta Bata shiga cikin su Lubbunah ba dakinta ta wuce ta rage kayan jikinta sannan tai alwala tada Sallah” Misalin Karfe 9 taga Sagir be kirata ba dan haka ta kirashi bugu biyu ya dauka, Munee kinga banzo ba ko? Dan kukan shagwaba ta saki yayin da yace yi hakuri mana bana gida yanzun haka kinsan muna da baki kiyi hakuri gobe iyanzun insha Allahu muna dakin mu zamu kwana guri guda toh meye abun damuwa Munirata? Bawani nan, nidai kawai kazo, wayau kake min, kazo kaji wata mgn” Jimmm yayi sannan yace gaya min kawai yanzun kinga bamu isa inda zamuba bare mudawo, kilama bazamu kwana gidan ba Gaya miki kawai” Toh idan ka dawo komai dare kazo idan Kuma baka dawo yau ba kana shigowa kazo” Angama ranki ya dade, toh Gaya min abun da kikace zaki gaya min” Ni gemon ka zanja” Dariya yayi sannan yace gobe sai kija muguyar yariya kawai” Dariya tayi tare da kashe wayar, sarai taji zuciyarta wani irin sufa tayi zuwa Kan gadonta saboda tsananin farin cikin dataji” Dawa kake waya bakin ka har yanzun ya kasa rufuwa” Munirah c,e nemana take Wai” Himmm kana shagwaba yariyar nan ba dazon nan kuka rabu ba? Munyi da ita zamu hadu da daddare, taga banje ban,e ta kirani wai nace zan iya yin dare Wai komai daren nadawo inje Kuma kasan me zatayi?? A’a Wai gemona zata jah kawai” Dariya sauran abokan sukayi yayin da Sadiq yaja tsaki tare da fadin iskancin banza iskancin wofi” Dariya Sagir yayi haba mana Sadiq dan Allah idan Kai aure kana barinta tanaja maka gem,o karka hanata, sannan Kuma a dinga hakuri wannan zafin ran banaka bane” Zanci ubanka fah” Shawara ce ai nabaka” Misalin shadayan dare suka dawo gida, yayin da suka nufi part din Hajiya Fatima gaba dayan su su hudun, Sadiq Sagir Mubark da Moh’d yayin da suna shiga sukaji anyo kansu da guda tare da fesa turarewa Sadiq da Sagir sosai ake fesa masu turaren yayin da cikin sauri Sadiq ya zauna tare da dafe kansa, idan ya fahimta irin abun nan na al’ada ake mishi wani irin yanayi ya shig,a Sagir kuwa sai dariya yake ganin Haka Sadiq yai saurin shigewa dakin Annanin” Yana shiga ya danne kofar tare dasa mata key sannan yayi sallama, Amsawa Annanin tayi cikin tsananin farin ciki take kallo shi” Ina Dan uwan ka?? Gashi can afalo” Meyesa Kai ka gudu? Annanin jifah yadda suka Bata min jiki da turaren su nan me karfin tsiya” Ai haka ake dole Kai hakuri” Zama yayi gefenta yayin data kalleshi tace” Toh komai dai Lafitya ko?, ya zuciyarka babu wani damuwa ko??. Bakomai Annanin Ina farin ciki sosai” Buga kofar da Sagir keyi ya dakatar dasu, jeka bude masa” Cikin sauri ya mike tare suka dawo da Sagir yayin data shafa kansu gaba daya tana yi masu addu’a Bayan ta gama mikewa sukayi zasu fita Sagir yace Annanin bakiyi mana nashiha ba” Wacce iri nasiha Sagir ai kullum cikin yinta ake” Eh Amman yana dakau yau ki Karayi mana akan hakuri kice mui hakuri da matan mu Banda saurin fushi sannan Kuma aringa sakin fuska, kare mgnr yayi yana kallon Sadiq da yasha mur” Dariya Sagir da Annanin sukayi sannan tace Allah ya shiryeka Sagir kowa yayi zagi a kasuwa yasan da Wanda yake” Juyawa Sadiq yayi yana fadin Annanin Saida Safe” Yana fita kai tsaye inda aka sauke Mammah ya nufa” Tana zaune tana mamula goronta yayi sallama ya shiga” A’a Abubakar kaine adaren nan” Shafa kansa yiyi, gefen ta ya zauna nine Mammah bakiyi bacci ba? Ina nan Ina tunanin ka tun da muka sauka bamu zauna” Kwantar da kansa yayi Kan cinyarta tare da lumshe idons,a hannunta tasa ta zame rawanin sa tare da fadin Yaya dai Sadiq??, Kana samun saukin zuciya kokuwa? Hannunsa yasa ya share gefen idon sa daya tare da fadin” Nasamu sauki sosai mamman musamman da aka fara hidimar bikin, na tabbatar wa kaina Aliya ce matar aurena, Mamman nakosa hankalina ya kwanta gaba daya, ayanzun abu daya ya rage min” Meye wannan Sadiq?? Ina tunanin saina kusanci Aliya sannan hankalina zai kwata” Hawaye tsohuwar ta share sannan tace Ina rokon Allah ya kwantar maka da hankali baki daya Sadiq Allah yasa haka shine mafi alheri” Kasa amsawa yayi sai acikin zuciyarsa yayin da ya mike ya fice batare da yana ganin gabanshi ba” * Washegari aka tashi da shirye shiryen daurin aure, Munirah kuwa kwance take ta kasa komai jiran isowan Sagir kawai take, dataji wayarta tai Kara zabura take, saita duba taga bashi bane ba” Yadda Aliya taga Munirah na zabura da wayarta tai Kara yasa tayin dariya tare da fadin Munirah kiyi hakuri” Munirah kin kulata tayi yayin da duk sanda Aliya ta buda waya sai Aliya tace Munirah kiyi hakuri” Ganin ta dameta ta mike tana fadin tsokanata kike ni yanzun bani da lokacin ki” Dariya Aliya tayi tanabin Munirah da kallo harta fice” Tun misalin Shabiyu rana harabar gidan ya cika makil da dan mutum wadan da sukazo halartan daurin auren Sagir da Sadiq kowa kagani yayi kwalliya yayin da fara’a kota Ina kowa farin cike yake” Hakama acikin gida kowa yayi kwalliya ta alfarma cikin anko yayin da amaren ma suke sanye da kayansu iri daya komai iri daya ne hakama daidai da zanen lallaen hannjun su iri daya ne, Sosai Munirah takejin wani iri, yake kawai take yayin da Aliya ke yawan kallon Munirah tana dariya” Tun tana share Aliya harta gaji tace kece abun dariya ke dazaki gidan me dauren fuska yau” Gwalo Aliya ta Mata yayin da Munirah tasake mikewa tabar guri tana ni ku rabu Dani banson mgn” Aharabar gidan kowa Shirin tabbatar da saurin auren ake domin kuwa kowa ya hallara yayin da Baba tsohu yake cike da farin ciki musamman Sadiq zai angwance” Adaidai wannan lokacin Sadiq gaba daya kasa banbancewa yakeyi tsakanin karya da gaskiya Wai Sagir ne zai aure Munirah? Kansa ya dafa tare da menan waje ya zauna yana me dafa mutanen dake kusa dashi” Sannu aka shiga masa tare da buda masa Dan ya samu iska domin azaton mutane cunkoso ne yasashi shiga wannan yanayin” Wani irin zafi yakeji yana cikin wannan yanayin ya tsinkayi muryan marokin yana shaida daura auren nasu Sadiq da Aliya sannan Sagir da Munirah” Lumshe Ido yayi be budeba Saida hawaye ya gangaro masa yayin da yai saurin sharewa, jama’a keta miko masa hannun suna gaisawa cikin tayasu murna” Amsawa yake babu wani walwala sai dai shi daman haka fuskar shi take yayin da Sadiq keta washe baki” Sadiq mikewa yayi daga inda take zaune ya nufi motarsa budewa yayi ya zauna kafafun sa awaje tare da dafe kansa” Sadir ne ya matso gurin Yaya dai Sadiq jikin ne?? A’a mutane sunmin yawa banjin iska gaba daya….. Wayar Sagir ce tai Kara hakan ya dauke masa hankali ya dauke wayar” Amukarnin har yanzun fah jiranka nake” Muneerah kiyi hakuri kinji, Ina cikin mutane ni Amman zan kiraki dazaran jama’a sun ragu” Har an daura ne?? Baki saniba?, Toh an daura” Wani iron dan Kara tasa, yeeee???????????????????? Dariya Sagir yayi baki da kunya ko?Kikashe wayar sai nazo” Tam tace tare da kashe wayar” Duk abun da suke Sadiq najin su” Sagir na sauke wayar yaga wasu abokan sa Dan haka hankalin sa ya koma kansu” Banda rawa babu abun da jikin Sadiq keyi, ganin ya rikece yafara nemar ma kansa mafita batare da yana gane abun da yake ba yafara Kiran layin Aliya” Kamar jira take ta dauka Jin muryarsa Saida gabanta ya fadi” Aliya? Na’am Amukarnin” Inason ganin ki” Tam kana Ina? Kisameni abayan part dina” Tam tace tare da mikewa cikin ranta take tunanin duk yadda akayi bashi da lafiya ne” Fita tayi batare da tacema kowa ga inda zataba, daman A part din su Lubbunah take part daya zata wuce saina Sadiq dan haka har ta isa babu wadda ya ganta” Cikin motar ta sameshi zaune, yayin da ya nuna Mata gefen sa, shiga tayi ta zauna ko dar batayi ba, cikin muryansa da Bata fita sosai yace ki rufe min mota” Rufewa tayi yayin da ya figi motar yabar gidan, kallon sa kawai Aliya keyi yadda yake kwarara gudu har suka isa wani gida” Fitowa yayi, yayin daya bude gefenta tare da rike Mata hannu yana janta, key yasa ya bude dakin sannan ya nufi ya shiga da ita, cikin sauri ya ware lafayan jikinta” Binsa da kallo kawai take bata iya cewa komai ba, daukanta yayi cak ya nufi dakin sa da ita yayin da ya cire babba rigarsa ya aje gefe sannan ya nufi Aliya” Ganin yana kokarin zage zip dinta hankalinta yafara tashi tsoro ya bayyana karara afuskanta tanajinsa yayi jifa da rigarta yayin da taisaurin sa hannunta ta kare kirjinta” Rigarsa ya cire sannan ya sake rokota yana fadin, ni mijin kin,e aljanarki tana karkashi kafata, bani da nutsuwa Aliya, ajikin ki kadai nake saka ran samu nutsuwa, dan Allah kirkimin rowa kibarni ko hankalina zai dawo jikina” Yana mgnr ne yana tabata, jikinta rawa yake Amma bazata iya hanashi ba, wani iri tabata yake da karfi yayin da takejin kamar yana fitar da hawaye, wutan dakin ya kashe yayin da ya nufi gado da ita yana jagulata son ransa, wani irin nurfashi yake tare da yin wasu kalaman da bazata iya sanin abun da yake cewa ba, zuwa yanzun gaba daya yarabata da suturan jikinta hawaye tafara domin dai tagaji da irin tsotsan da yake mata yayin da takejin yanayin abun kamar meyin fad,a Jin ya ware kafarta ta fito da idonta waje, Bata ankaraba taji wani azabar radadi ta kasanta Karan da ta kwallah ya tabbatar masa da abun daya aikata” Bayan minti 30 Aliya kidaina kuka kinji??, Wannan ba wani abu bane anriga an daura mana aure Kuma anjima za’a kaiki gidana karki damu kanki kinji?? Kaita daga alamar eh” Sannu, Allah yai miki albarka, yabaki ladan ibadah, Dan Allah karkiji haushina kinji?, Ba laifina bane laifin zuciya tan,e dan Allah kiyi hakuri kinji? Tam tasake fada ahankali sannan yasa hannun sa ya share Mata hawaye yana fadin, kidanji dadi?, Kona sake sa miki ruwan zafin?? A’a tace idonta akasa har yanzun Bata iya hada Ido dashi Nakira number sa akashe, wlh idan aka wuce minti 30 bedawo da Aliya gidan nan ba ransa zaiyi mummunan bacci, aina yaga anayin haka?? Kayi hakuri Abbanin, Ina zuwa barin Kara gwada numbar tasa” Fitowa yayi cikin sauri ya shiga motarsa yabar gidan gudu yake sosai Munirah ta kirashi” Munirah Ina hanya yanzun? Kace Kuma da Mutane sun watse zakazo Kuma ka Kara fita? Ta dole ce fitar” Toh kayi sauri karka dade” Sallama yayi afalon, yayin da yaci karo da lafayan Aliya, tsaye yayi anan yayin da yace, Sadiq!!! Cikin sauri Sadiq ya amsa tare da fitowa yana daure da towel” Haba mana Sadiq menene haka?? Kansa ya shafa sannan yace daga Ina kake? Ran Abbanin ya baci sosai meyasa bakayi hakuri ba a njima za’a kawo maka ita fah” Mika hannu Sadiq yayi ya dauki gyalen Aliya sannan ya koma ciki, tsaye Sagir yayi cikin Jan tsaki zuwa can Saigashi da Aliya sun fito yana rike da hannunta yayin idonta arufe” Duk da cewa Sagir yaji haushi Sadiq Amman sosai suka burgesa dan haka ya juya kawai yayin da Sadiq ya biyosa rike da hannun Aliya” Cikin motar Sagir yasata sannan ya rankwafo yace Sagir ka kula da ita…… Na kula da ita? ni Dana bar tawafa agida wa zai kula min da ita?? Hararan sa Sadiq yayi sannan ya kalli Aliya yace” Sannu, kuje sai nazo ko?, Karkiyi kuka fah Kaita daga yayi yayin da Sadiq ya dagawa Sagir hannun shikuwa Sagir Ido daya ya kashe masa sannan shima ya daga masa hannu” Fitcewa sukayi yayin da Sadiq ya dinga kallon motar harta fice, sannan ya koma cikin gidan” Wayoyin sa ya kunna sannan ya shiga toilet wanka yayi bayan yayi wanka yayi alwala ya fito, shiryawa yayi cikin wasu sabbin kaya yana kokari daura agogon yaji wayarsa nakara ahankali ya isa gareta ya dauka Abbanin yagani cikin sauri ya dauka” Cikin wani irin muryar yace Sadiq kazo gida yanzu nan” Lfy kuwa ?? Kazo gida nace” Lumshe Ido yayi afili yace sai naji kamar muryan Annanin kusa dashi tana kuka, cikin sauri ya fito yana zama cikin motar Mubarak ya sake Kiran sa” Mubarak gani nan zuwa menene meya samu Annanin na take kuka naji kamar tana kuka? Cikin haki tare da hawaye yace kazo kazo gida kawai Sadiq Gaya min mana dan Allah? Sadiq Sagir ya barmu, ya mutu Sagir, yatafi Innalillahi wa’innalaihir raju’un, Yame??, Yamutu kace??????? Ya mutu Sadiq???????? Ina Aliya?, Sagir yana tare da Aliya yanzun nan muka rabu dasu fah”???????? Kayi sauri kawai Sadiq Aliya na Asibiti…. Alhamdulillah Karshen book 1

1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page