Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

Ad

_____

Saleem yace”na sani ni daman bance ka rakani ba bari na wuce don a yau insha Allahu nakeson dawowa,

Har bakin motarsa ya raka sa yamasa fatan alkhairi snn ya juya,girgiza kai Saleem yayi cike da tausayin aminin nasa snn ya ja motarsa ya wuce,

To akan hanyar dawowar Saleem daga Jos,tundaga nesa ya hango ta tana d’agawa moto hannu har zuwa lokacin da ta zube tana kuka,bai ta6a kawowa Zainab bace har ya wuce ya dawo don tabasa tausai besan meyasa tayi hakamba don hk ya dawo da niyyar temaka mata yasakar mata hun,

Shinefa ta d’ago agigice a tunaninta boss ne,ganin ba motar boss bace yasa ta taso da gudu ta bud’e tace don Allah bawan Allah ka temakamin Kaduna zani,

Jin kamar muryar zainab yasa yace”Ummi,a d’an gigice,da sauri ta d’ago ganin Saleem ta fashe da kuka tace”Yaya Saleem mubar gurin nan wllh xai biyomu,ai da sauri ya tada motar ya fuzgeta,

Suna tashi Boss ya zo gurin,sai dube dube yake ransa a jagule amma bai gantaba,yace”wllh zaki gane ne koda na barki Khairat tunda tayi niyyar kasheki to saita kasheki wawiyar yarinya,ai bai gama rufe baki ba,wata babbar mota dake ta aikin danna masa hune don ya tsaya bisa hanya tayi ciki da motarsa domin me babban motar yakasa sarrafa burkinsa,aikuwa motar boss tayi ta wuntsilele luwa a daji zuwa cen ta kama da mota,shi kansa me babban motar da sauran mutane biyun dake ciki da k’yar aka curosu d’aya cikinsu ya rasu,boss kuwa ai tuni ya gama k’onewa haka ‘yan kwana-kwana suka ciroshi da kyar aka nufi asibiti dashi da sauran biyun waccen motar,suka hau kashe wutar,

Kuka kawai Zainab keyi hakan yasa Saleem bai iya cewa komai ba har suka isa Kaduna kai tsaye gidan malam babba ya nufa da ita tunda acen sukayi sallama da Lameer,

Ai tun kafin ya gama parking,ta fita a guje tana “yayah Lameer Ummana Babbana Abbuna Ammina Kakaaaaaa!,

Da sauri dukansu suka mik’e dukansu sukayi waje da sauri ai tana ganinsu ta ruk’umk’ume Ammi tana kuka,suma duka suka saka kuka,suka ciki suna tambayarta ta kasa bada amsa sai kuka,

Shi kuwa Saleem jin ana sallahr magrib shiga yayi masallacin k’ofar gidan,bayan sun fito ne ya yaga sun fito gaba d’aya tare da su Abbu Baba da Lameer,nan ya gaishesu,suka amsa cikin fara’a,

Lameer yace”kadawo kenan,yace”aikuwa,ya d’aura da cewa mushiga kaga abinda xaka gani yau har tukwici sai ka bani,

Da sauri ya kallesa tare da murmushin yak’e yace”aini yanxu ba abinda ke burgeni idan ba Zainab zaka dawomin da itaba,yace”kaidai abokina mushiga ka gani,haka suka shiga gidan suma su Abbu suna addu’ar Allah yasa suga alkhairi……

Nace muku banjin dad’i kuyi hak’uri da wnn,wad’anda sukamin addu’a na gode sosai ana mugun tare🤝😍

Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓

      *NI DA YAYA LAMEER*

             ❤❤❤❤
              🧡🧡🧡💓

GAJERAN LABARI

Story and written

By

Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇

NI DA YAYA LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144

Diditated to ATK

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Wad’anda sukemin addu’a nagode sosai ana mugun tare Alhamdulillah naji sauki nagode da addu’o’inku gare ni ana mugun tare

🅿️31↪️32

Shiga sukayi ciki haka nan Lameer yaji gabansa na fad’uwa,da sallama suka shiga farlourn Kaka,

Duk hijabaine jikinsu da alama suma basu dad’e da idar da sallah ba,

Zainab kuwa na jikin Ammi har zuwa lokacin kuka take don gani take kamar boss zai sake zuwa ya tafi da ita,

Tajin sallamarsu ta mik’e da gudu ta ruga ta k’amk’ame Lameer,ai shi suman tsaye yayi bai ta6a tunanin Zainab d’insa zai gani ba,kasa magana yayi sai rik’eta sosai da yayi ajikinsa yana sauke ajiyar zuciya,

Abbu da Baba,kuwa Alhamdulillah kawai suke maimaitawa,Abbu ya d’aga hannu yace”godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai Allah kaine abin godiya mun gode maka,gaba d’aya gurin sukayi salatin Annabi,

Bayan duk sun zauna,Saleem ya musu bayanin komai yace”bayan na dawo Jos daidai k’auyen nan Fanbeguwa anan naganta tana tsaida mota ba motar da ta tsaya har na wuce sai tabani tausayi ban d’auka Zainab bace saida tashugo,

Kallonta sukai idanuwansu cike da alamar tambaya,cikin kuka ta sanar musu duk abinda ya faru har zuwa yau da ta gudu,

Ai wani mek’ewa da Lameer yayi kowa saida ya dubesa,idanuwan nan nasa tuni suka cenza launi zuciyar ‘yan maza ta tashi cikin wata irin murya me had’e da kishi yace”maxa kitashi muje ki nunamin inda mutumin nan yake wllh yau sainaga bayansa,

Saleem ne ya kamashi ganin yadda yake fuzgar hannun Zainab yana”ki tashi muje nace,yace”haba abokina wnn duk ba naka bane tunda Allah ya ku6utar da ita daga hannunsa ai sai mugodewa Allah snn Allah zai mata sakayya ita da sauran mutanan da yacuta har yakashe don hakkin rai ai babba ne,

Baba yace”wnn haka yake karka damu d’ana Allah zaiyi ikonsa akansa,da k’yar ya zauna donji yake da zaiga mutumin nan zai iya kashesa sbd 6acin rai,

Kallon Zainab yayi yace”to ke bakiji yace wani yasashi ya d’aukekiba,shuru tayi tana tunani zuwa cen tace”eh naji dai yana yawan ambaton wata wai cewa tayi akasheni,gaba d’aya suka d’au salati yace”bai fad’i sunanta ba,tace”ko Khairat yace kome?,da sauri ya mik’e yace”Khairat ko daman na dad’e ina zargin dasa hannunta a 6atanki yau zata gane kuranta,

Da sauri ya fice,suna kiransa amma ina xuciyarsa ayi zafi,

………………………………………………

Acen gidan Alh Kamalu kuwa,rigima ake sosai domin an amshe Senator da aka basa daman ba mutane ne suka za6esa ba murd’iya ce,to asiri ya tuno don haka gwamna me adalci ya amshe anbawa wani ruk’on k’warya kafin ayi za6e,nan fa hankalinsa yatshi inda ake ta d’auki ba d’ai d’ai domin gidan Redio yaje yana ta zagin gwamna,

A hanyarsa ta dawowa dunduzun matasa suka taresa sukai masa tsinannan duka,snn suka kona motarsa,nan suka barsa kwance rai a hannun Allah,

Da k’yar wasu masu tawakkali suka kaisa asibiti,lokacin da aka sanar da Hjy luba da Khairat tsaki sukaja,sukace babu ruwansu aisaida sukace kar yaje snn yaje dama kashesa sukayi,

Cikin dare kuwa gidansu ya kama da wuta domin d’akin da dodonsa yake ya faraci,zuwacen gidan ma ya faraci,sosai suke ihu suna neman temako,kafin ‘yan kwana-kwana suzo ai tuni sun galabaita,

Mutanan unguwa aka taru domin ihun da akeji a gidan yayi yawa,wani d’aki da aka bud’e anan akaga kawunan mutane da gangar jikin mutane,nanfa aka dunga tsine masa da Allah wadai,’yan jarida tuni suka hallara da ‘yan gidajen tv kai abinfa ba kyan gani,

A wnn halin Lameer yazo,ganin abinda ke faruwa yasa jikinsa sanyi da Allah wadarai da halin Alh kamalu,

Su Khairat kuwa anji jiki,Hjy luba tuni ta amsa kiran Allah,khairat kuwa duk ta k’one ta cenza kamannin babu kyawun gani,abin da abin tausayi,

Haka Lameer ya koma gida yasanar da iyayensa nan suga dunga Allah wadai da wnn abu,

Alh Kamalu kuwa ai asibiti ihu ya dungayi yana fad’ar mugayen abunda yayi harda uwarsa da k’annansa da yabawa dodonsa da duk wasu da yakama,

Zuwa wani lokaci akaga cikinsa yayi girma sosai irin naban mamakin nan,uhmm kai abin fa babu kyawun gani da haka yarasu yana ihuuu,(Ya Allah kasa muyi kyakkyawar mutuwa kagara halayenmu ka hanamu aikata alfasha,don Allah yanzun ina amfanin bad’i ba rai Allah ya kyauta),

Alh kamalu dai an tafi cikin wani mayuwacin hali,ya Allah ka shirya masu hali irin nasa amin,

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button