NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan fitarsa dariya tasaka tace”matsorancin banxa kawai wallahi zanyi maganinka kaibaga d’an iska ba,

……………………………………

Lameer ya galla mata harara”zaki fad’amin gaskiya ko yanzu saina illataki,kuka tasaka”ni wallahi bansan inda aka kaita ba,

Juyawa yayi yabar gidan,yasan maganinsu,baiso itayensu suji wannan abunba yaso ne kawai ya magance matsalar nan da kansa,yana zuwa ya tadda su Ammi basa nan,tunowa yayi da maganar da sukayi da Ammi da safe inda take cewa”Lameer idan ka d’auko Ummi kuwuce gidan Malam yaucen zamu wuni sai dare zamu dawo,

Juya motarsa yayi sai gidan Kakar tasu,

Iskesu yayi suna da hira cikin raha,ganin yanayin da ya shugo yasa Ammi tace”Lameer lafiya kuwa?,Umma ta dafe k’irjinta tace”wani abu yasami Ummi ko?tun safe gabana ke fad’uwa abu kad’an saita fad’omin arai,

Zama yayi,baice musu komaiba saida ya kira Abbu da Baba,domin yasan halin mata yanzun samayar da gidan na mutuwa????,

Bayan yasanar kuwa ilai nan Kaka Ammi da Umma sukahau kuka,damansu mata raunine garesu duk girman mace kuma duk tsufanrta haka duk yarintarta raunine da ita,

Abbu ya Mik’e ransa 6ace yace “wllh sai nayi maganin Alh Kamalu zai gane ruwa ba sa’an kwando bane,siyasarshi ta banxa nikeda ‘yan siyasa duk da banayi zai gane ya ta6o ‘yar gata…….

My Mumcyna Ameenat Ibrahim Meenat ina miki fatan alkhairi tare da addu’ar Allah ya baki lafiya ya raya mana Hassana da Hussaini Ameen,

Muje zuwa????

Ummu Affan✍️✍️✍️

❤❤❤❤
????????????????

      *NI DA YAYA LAMEER*

             ❤❤❤❤
              ????????????????

GAJERAN LABARI

Story and written

By

Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍????✍????
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now????

NI DA YAYA LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144

Diditated to Fans

Special gift to Anty Hauwa

Masu cewa na turo musu daga farko har k’arshe don Allah suyi hak’uri na fad’a muku wnn book d’in sabo ne sai nayi typing snn nake turowa don Allah kuyi hkr ni bakina har ya gaji da wnn mgnr,idan na kammalasa duk meso xan turo masa amma yanzu nake typing d’insa da ftn masu tambaya zasumin hkr hakan harna kammala

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

????️25↪️26

Fita Abbu yayi yana waya,dame girma gwamna domin babban abokinsa ne,tare sukayi karatu,

Duk wanda ya dace yasanar mawa,zuwa wani lakaci,jahar Kaduna ta d’auka gidajen tv da redio cewa Senator Alh Kamalu ya saci ‘yar wajen,Babban d’an kasuwarnan Alh Ibrahim Halilu babba,

Zuwa wani lokaci matune sunfi d’ari sun taru a k’ofar gidansa suna “bamayi”bamayi,a fiddo mana da yarinya,

Hankalin Alh Kamalu yayi mugun tashi haka Hjy Luba,Khairat kuka kawai take,Dad d’inta yace”Khairat idan ke kika d’aukar musu ‘ya ki rufamin asiri ki fiddota kafin wnn mutanen su shugo sumana duka,

Tace”Dad yanzu me kake nufi kana nufin bazaka bani Lameer ba kasan shine frn cikina,idan har baka bani shiba wllh xan kashe kaina babu abinda nata6a saka kayimin bakayimin ba sai wnn karon duk wani abinda nakeso ko ba naka bane sai kayi yarda kayi na samesa me yasa ka kasa samomin soyayyar LAMEER?,

Numfashi yaja yace”tunda har kinsan kome kika nema ina iya bakin k’ok’arina na samar miki to kiwa Allah ki fito musu da ‘yarsu wllh abin nan yana iyasa na rasa muk’amina,ni danake nema nan gaba na zama gwamna kinga wnn abun zaisa na rasa,

Kuka sosai tasaka “ni wllh sai na auri Lameer ko kuwa na kashe kaina,Hjy Luba ta rik’e d’iya tata tace”Khairat kiyi hkr ni zan miki abinda ubanki ya kasa miki ko zanyi yawo tsirara sai na nemo miki soyayyar Lameer,

Kallonsu yayi cike da takaici yace”Luba baki da hankali meye kike cewa haka baki tunanin yadda rayuwarmu zata koma idan narasa muk’amin nan,kinsan bani dashi ban ajeba ban ba wani ajiya ba,duk kud’in gwamnati dashi muke komai wllh ranar da asirinmu zai tunu muna cikin garari,

Tsaki taja mtsuuuww “kaidai tunda ka kasa ni zanyi ta kama hannun Khairat sukayi ciki,

Shi kuwa ya kasa futa sai tunani yake kar su k’ona masa gida,

******************

A hankali ya lalla6o duk a tunaninsa Zainab barci take sai sakin murmushi yake,ya hayo kan katifar a hankali,ya fara shafa bayanta yana lashe le6e da had’iyar yawu,

Cikin barcinta wanda ba sosai ya d’auketa ba takejin kamar ana shafata a furgice ta tashi tana salati,turesa tayi tantan k’arfinta kunsan abinku ga sauran sigari ba wani k’arfine dashiba,nan ya wuntsila,

Mik’ewa tayi tace”waikai wanne irin maye ne?,me jikina ya maka?wllh zan kassaraka yanzun nan,

Rarume-rarume ta kama kamar wata mahaukaciya sabon kamu,kome ta samu ta jefa masa,

Shima a fusace ya mik’e yace “wllh duk haukanki yau nima zan nuna miki mahaukacin kaina ne yau duk tsiyarki sai nasami abinda nakeso a jikinki,tace”chaffff wllh ni dakai shege ka fasa d’an halak sai yanka,kujimin katon banza mahaukaci d’an shaye-shaye anya kuwa iyayenka basu cemaka jeka ka gani ba?,

Yace”maganarki hakkun haka take hakan yasa dole yau na san abinda ya yaga ajikinki,tace”to zo gani sai kayi mugani,

Yadda kawai take kallonsa abin sai ya baka mamaki,hakan yasa ya juya yace”zamu had’u ne,

Bayan fitarsa jagab ta zauna kankatifa tare da rik’e kanta,meke shirin faruwa da rayuwarta?hawaye ne kebin fuskarta daman haka rayuwarnan ta koma,sai taji jikinta duk yayi sanyi Yaya Lameer Umma Baba,Abbu Ammi da Kaka kawai take tunani,

Snn makaranta ta fad’o mata yadda take rayuwa da kowa,K’awayenta Hafsa da Maryam,malamanta da ta raina ta mayar dasu kamar wasu abokanan wasanta,

Hawaye yazubo mata ta share “Allah sarki yayanah me sona dason nayi karatu,gashi yanzu inason nayi karatun babu hali,yayanah kazo ka tafi dani kar mutumin nan ya kassara rayuwata,ta fashe da wani kuka mai ban tausai,

Daidai lokacin fitowar Yaya Lameer kenan daga masallaci,tunda abon nan ya faru ko aiki ya dena zuwa kullum tunaninsa Zainab d’insa,

Kwantawa yayi saman bed d’insu dasuke kwana shida Zeey d’insa ya k’amk’ame zanin gadon yana shinshinar k’amshin zeey d’insa yanzu shi kad’ai yake kwana bayajin d’umin jikinta hawaye suka xubo masa,da sauri ya mik’e key ya d’auka bai zame ko inaba sai gidansu Khairat rashin sa’ar da yataka yana zuwa me gadi yasanar masa ba kowa gidan sun fita,

Juyawa yai cike da 6acin rai,ransa na suya,

…………………………………………………

Zainab ce shuru tana tunanin me yadace tayi,wani tunani ne ya fad’o mata,alwala tayi bayan ta idar da sallah ta cire hijabin makarantar daman kullum dashi take wuni dashi take sallah,batayin wanka sai ta tabbatar boss yafita tunda akwai toilet d’akin da take kuma akwai fanfo,

Ko tayi wankan kayan jikinta na mkrnt take mayarwa,wnn tunanin ya fad’o mata yasa tace”ko wacce mace da irin kissarta nasan maganinka insha Allahu yau sai na koma gurin ahlina,

Zaune ta iskesa a farlour,da sauri ya mik’e ganin yadda ta taho gabansa tana wani rausaya da girgiza……..

????????????
Shin me Zee zatayi?kai nimafa zanso nasha kallo????????

Nasan Ummu Inteesar nacen na tunanin tome kishiyarta zatayi hhhhhhhhhhhhh

Mu had’e a page na gaba donjin ya zataci gaba da kayawa acikin littafin nan nidai burina kuci gaba da biyoni sannu a hankali har ku fahimci abinda nake son isarwa

MUJE ZUWA

Ummu Affan takuce masoyana nah✍️✍️✍️
❤❤❤❤
????????????????

      *NI DA YAYA LAMEER*

             ❤❤❤❤
              ????????????????

GAJERAN LABARI

Story and written

By

Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button