Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

Ad

_____

Fitowa yayi suna tsaye bakin k’ofarsa da alama shugowa sukasoyi,jami’ansa suka hanasu,don gashinan sai ja inja suke,suna ganinsa sukayo kansa,mik’a musu hannu yayi alamar su gaisa,yasakar musu fuska suks gaisa su uku,ne ‘yan sadan,

Yace”ina ftn dai lafiya naji ance kuna nemana,gyad’a kai d’aya daga cikinsu yayi alamar shine babba yace”Eh me girma Alh Kamalu Senoter ne kenemanka a yarda mukayi dashi da munzo kamaka zamuyi amma wllh kamin kwarjini don haka kazo mu wuce hankali kwance,

Wani shu’umin murmushi Lameer ya saki,domin yasan mahaifin Khairat Senoter ne,yace”ok babu damuwa muje,

Bayansu yabi,motarsa ya nufa suka kalleshi,kazo kashiga nan,yace”laifin me nayi da zanshiga motarku,kuyi gaba xan biyoku a baya,

Shuru suka d’anyi sai kuma suka shiga tasu motar sukayi gaba yana binsu,har makeken gidan hutun Alh Kamalu,

A babban falon gidan suka iskesu,bayan sunyi sallama,nan fulisawa suka sara masa kamar wani kwamishi nan d’an sanda,murmushi yayi ya jinjina musu,kai da ka gani kasan irin ‘yan sandan nan ne masu ha’inci da son abin duniya,

Kai tsaye kujerar dake fuskan tarsa LAMER Ya zauna tare da mik’a masa hannu cike da fara’a shima ya mik’a masa nasa,

Lameer yace”ina fatan dai lafiya,Alh Kamalu ya 6a66aka dariya yace”Lafiya k’alau Dr Lameer amma ai nasan kasan Khairat,”eh nasanta lafiya?,ya tambayeshi kai tsaye cikin gadara,

Kallonsa Alh Kamalu yayi snn yasake sakin wata dariyar hhhhhhhhhhhhhhhhhh mutanansa suka tayasa,mik’ewa Lameer yayi yace”idan baka da abin cewa ni zan wuce don muhimman aiyukana na baro,MIk’ewa shima Alh Kamalu yayi yace”Lameer kai yaro ne k’arami bakasan kan duniya ba amma inaso ka auri ‘yata Khairat,

Wani kallon rainin wayau Lameer ya masa yace”daman nasan maganar kenan to inaso kasani ni bazan iya auran ‘yarka ba koda banda mata bare ina da iyali,inaso kajawa ‘yarka kunne ta kiyayeni idan ba hakaba daga kai har ita zakusha mamaki,badai kujerar nan kake tak’ama da ita kakewa kowa abinda kayi niyya ba,uhhm yayi wani d’an murmushi yaci gaba”ni yarone bansan kan duniya ba amma idan ka shugo gonata zakasha mamaki,yana gama fad’ar hakan ya juya cike da izza yana tafiya,

Mutanan Alh Kamalu zasu bisa su kamasa da sauri ya d’aga musu hannu,kur6ar ruwan dake gabansa yayi yasaki cup d’in take ya tarwatse sai kuma yace”uhmmm bakasan waye Alh Kamalu ba,

Shi kuwa Lameer motarsa ya koma ya mata key yabar gurin a matuk’ar fusace wannan rainin hankalin yakai iyaka amma zaiyi mgnin mutumin nan don yana senoter wnn shi ba damuwarsa bace,

Waye Alh Kamalu,shima haifaffen kaduna ne iyayensa ba wasu masu karfi bane,tun yana yaro shid’in irin marasa jin nan ne,su kansu iyayensa basuji dad’insa ba,

Wani kawunsa ne ya talafa masa har yayi ilmi mai zurfi,saidai bin bata da shayeshaye aikinsa ne da haka ya gama karatu sai kuma ya fad’a harkar siyasa,Matarsa Mum sunanta na asali Lubabatu anfi kiranta da Luba,cenda karuwace anan ma suka had’u da Kamalu har ya d’irka mata ciki da yake itama tsaye take bata da kyirki ko kad’an nan sukayi dirama sosai yace ta zubar taki shinefa sukayi aure cikin nada wata biyu lokacin,(kunji jahirci haka suka yi aure da cikin Khairat iyayensa basusan da ciki akayi auren ba),

Haka Khairat ta taso cikin rashin tarbiyya komai takeso sai anmata don iyayenta suna matuk’ar k’aunarta,bata ta6a neman abu tarasa ba a rayuwarta,shiyasa take ganin Lameer ma dole ta samesa,(Allah ka bamu ikon kula da tarbiyyar yaranmu)

Kai kud’inma Alh Kamalu bana Allah bane domin d’an mafiya ne yana shan jini,haka ya bada mahaifiyarsa da k’an nansa har guda biyu,mahaifinsa kuwa yanan dashi da babu d’aya don ba abunda yake masa yana kwance cikin ciwo,to kunji ko waye Alh Kamalu,

……………………………………………

Zaune suke anyi break a mkrntar tasu,Zainab ce sai k’awayenta biyu,Hafsa da Maryam,fira suke don Zainab vadai surutu ba,

Me gadi ne yazo ya samesu cikin fara’a yace”Zainabubuwa Zainabu abu me tagwayen suna kizo Yayanki na kira,da sauri ta mik’e ta kalli su Hafsa tace”ina zuwa,sukace sai kindawo,tace”Baba me gadi muje,kallonta yayi cike da tausayi don sanin abinda aka shirya mata harga Allah badon sunce idan bai kirata sai sunkasheshiba da bazai iya kiranta ba,ganin kamar yana tunani tace”Baba me gadi ina Yaya Lameer d’in,da sauri ya kalleta yace”yana waje yace sauri yake gaisawa zakuyi kidawo,

Shuru tayi na wani lokaci sai taji kamar bata yardaba domin har ciki Yaya Lameer yake zuwa inhar shine ta ta tuno yace mata wai sauri yake sai ta fita da sauri,kallon motar tayi dake waje bakin gate din mkrntrsu,bata ta6a ganin yaya Lameer da wnn motar ba saidai ta k’arasa,

Aiji tayi an shak’a mata wata hoda anyi cikin motar da ita daga lokacin bata sake sanin inda kanta yake ba,

Muje zuwa,Ina sonku masoyana a duk inda kuke,fans d’ina na facebook kuma inayinku irin wujiga wujigan nan ana tare😂🤝

Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓

      *NI DA YAYA LAMEER*

             ❤❤❤❤
              🧡🧡🧡💓

GAJERAN LABARI

Story and written

By

Fateemah Sununi Rabee’u
(Ummu Affan)


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇

NI DA YAYA LAMEER!

WhatsAPP no 08104335144

Diditated to ATK

Special gift to Anty Hauwa

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

🅿️21↪️22

Gudu kawai suke shararawa akan babban titin gaba d’ayama fita sukayi daga cikin garin kaduna,

Wani k’auye suka kaita me suna Fanbeguwa,acen suke da wani gida babba cike suka kaita har zuwa lokacin Zainab batasan meke faruwa ba,

Boss suka kira a waya ya fito daga cikin gidan,kallon yaran nasa yai yasaka dariya hhhhhh ban ta6a baku aiki ba aka sami matsala ina alfahari daku,

Sara masa sukai suka had’a baki,”muma muna alfahari dakai megida,

Murfin bayan motar suka bud’e masa inda Zainab ke kwance kamar meyin barci,murmushi yayi ya d’auketa sak sai cikin gidan,

D’akin dake gidan ya kaita kan wata katuwar katima ya shimfed’eta,murmushi yai yace afili”Zainab bazan kasheki ba kamar yadda Khairat ta buk’ata domin tun ranar da ta nunamin ke naji ina k’aunarki shiyasa na za6i in kawoki nan domin inyi yarda nakeso dake,ke tawa ce har abada ba wanda zai sae jin d’uriyarki,yasaki dariya hhhhhhhhhh sannan ya koma farlour,

Kud’i yabawa yaransa masu yawa sannan ya musu godiya,suka fita daman su Acen Kaduna suke,amma idan yasasu aiki ko inane suna xuwa,

Wajen k’arfi biyu na rana Zainab ta farko,ahankali ta fara bud’e idanuwanta saman d’akin ta kalli ta juya idanuwanta zuwa ko wanne sassa na d’akin,a furgice ta tashi zaune abinda ya faru ne ya fad’o mata,Yayaaaaa Lameerrrrrrrrrr,ta ambata da k’arfi,

Daidai lokacin kuma Lameer ya rik’e saitin zuciyarsa,a hankali ya furta Zainab,sai kuma yaji gabansa na fad’uwa,

Boss ne ya shugo d’akin da sauri,ya gigice ta mik’e tana zare idanu,yace”Zainab lafiya aii daga yau nine na koma Yayanki ki mance da wancen kinji ko kizo muji dad’inmu,gadagadan yayo kanta,

Da sauri taja baya tana hawaye tace”waye kai?don Allah kayi hakuri kamayar dani gurin Yayanah,dariya yasaka yace”ai kuma ke da yayanki kun rabu kenan,kasheki akasa fa nayi amma saboda ina sonki yasa ban kasheki ba,don haka kibani had’in kai,zan mayar dake ‘yar lele muji dad’inmu ko?ya k’arashe maganarsa da tambaya,

Runtse idanuwanta tayi da k’arfi hawaye nabin kuncinta ita bamafa tasan inda mgnrsa ta dosa ba,tace”don Allah kayi hakuri kamar dani cikin ahlina,

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button