NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

Tace”ai zanyi naga sai fad’a kakemin,yace”to Sorry na dena kice ai,gaba d’aya suka saka dariya,ya kama hannunta “zo muje muyi breakfast gurin Ammi mu wuce ko,
Tace”nidai ka goyani,duk’a yayi ta d’are bayansa,sai dariya suke,
Ak’ofar part d’in su Ammi ya direta suka k’ara,akan dinning suka iske Ammin da Abbu yana karyawa shima zai wuce office,
Bayan sun gaishesu suka zauna,suka karya,sannan suka musu sallama,Ammi tace”Ummi a mayar da hnkl a karatu kinji ‘yata,tace”to Ammi,Abbu yace”to adawo lfy,tace”Allah yasa,
LAMEER duk’awa yayi gaban iyayensa yace”to Ammina nima asamin albarka,murmushi tayi kamar yadda suke kullum tasa hannu akansa ta masa addu’a,yace”yauwa Ammina nagode,ya manna mata kiss,yace”Abbu sai mun dawo,sannan ya kama hannunta suka wuce,
Murmishi sukayi gaba d’aya sukabi tilon d’an nasu da kallo cike da k’auna,
Sun fara tafiya ya juyo ya kalleta,ganin yadda tayi shuru,yasan duk sbd zata skul ne ita kuma ta tsani mkrnt,
Har cikin gate d’in mkrntar ya shiga kamar kullum bayan yayi parking,ya kalleta bayan ya ruk’o hannayenta yace”My Wife kiyi karatu sosai ko bakison zama likitar kamar ni,murmushi tayi,”inaso mana,yace”to dole saikinyi karatu sosai kin mayarda hankali,tace”to zanyi,kiss ya manna mata a d’an garamin bakinta yace”oya to sai nazo d’aukarki,fita tayi tana d’aga masa hannu ganin ta wuce ya juya,bayan yawa me gadin mkrntar alheri,
Wani kyakkyawan asibity naga yayi hune da sauri me gadin ya bud’e masa yana masa sannu,gurin da yake parking yakai motarsa sannan ya fito,cikin takun isarsa naga ya nufi ciki,da na d’aga kaina naga anrubuta
LAMZAH speacial hosbital,ganin yadda ya d’aure fuska kamar bashi ba yasa na fara mmk,sai sannu ma’aikatan asibitin ke masa mgn ma ta gagara sai d’aga hannu,wani kyakkyawan Office naga ya shiga,masha Allah kawai nace ganin yadda aka tsara office d’in,zama yayi ya fara dudduba fayil d’in da ke gaban teburin,
Daga bisani ya fara duba marasa lfy,
Waye LAMEER wacece Zainab sai a page nagaba zakuji.
Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
????????????????
*NI DA YAYA LAMEER*
❤❤❤❤
????????????????
GAJERAN LABARI
Story and written
By
Fateemah Sununi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
MARUBUCIYAR ✍????✍????
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now????
NI DA YAYA LAMEER!
WhatsAPP no 08104335144
Wannan page sadaukarwa ne ga Hussen Abu Sameer da Nuradden Shu’aib Light,Ina godiya sosai????
Masoyana ako da yaushe kuna raina ina yinku irin sosai d’in nan,Masu kirana nagode da soyayyar da kuke min masumin magana da pc kuma nagode sosai,NI DA YAYA LAMEER Fans ina godiya sosai da soyayyar da kuke nunamin nagode????
My bestyna Ummu Inteesar marubuciyar ‘YAR GANTALI,Inayinki keda Maman khaleel marubuciyar KISHIYAR ZAMANI,i luv u wujiga-wujiga.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
????️9↪️10
Malam Halilu,wanda aka fi sani da Malam babba babban malamin addini ne,wanda ke zaune a garin Kaduna,tare da matarsa Gwoggo Abu,asalinsu ‘yan jahar katsina ne a wani k’auye me suna,Dukke”dake k’aramar hukumar funtua,
Malam babba karatun addini ne ya kawoshi kaduna inda yazama babban malamin addini na ahlussunna,matarsa Gwoggo Abu duk ‘yan gari d’aya ne,
Yara biyu suka haifa duk maza,Ibrahim ne babba sannan Ahmad,sunyi karatun addini sosai haka harna boko,don ba laifi mahaifinsu na k’ok’ari akansu,
Ibrahim babban d’an kasuwa ne wanda yanzun yayi kud’i sunansa ya shahara shi kuwa Ahmad Babban malami ne dake koyarwa a jami’ar kaduna,
Rana d’aya sukayi aure domin Allah ya d’aura musu k’aunar junansu,Hassana da Husaina suka aura,Ibrahim keda Hassana shi kuma Ahmad Husaina,
Babban gida suka gina nakece raini anan suka saka matansu,kuma suna tare da iyayensu,
Shekara guda da auran matar Ibrahim ta hauhu wato Hassana,ta sami d’a namiji zo kuga murna,gsky sunyi farin ciki da samun k’aruwar nan,nan akayi ta murna da farin ciki ranar suna yaro ya amsa LAMEER Yaro kenan d’an gata gurin iyayensa da kakaninsa haka Ahmad da Hussaina suna k’aunar Lameer part d’insu yake wuni,
Tunda aka haifesa ba ak’ara haihuwa a gidanba,ita dai Hussaina ba lbr da yake suna da ilmin addini sai suka mik’a al amuransu gurin sarki Allah suka dage addu’a,
Shekarun Lameer goma amma ba wani lbr shima iyayensa basu kuma haihuwa ba tundaga kanshi,
Makaranta me tsada yake zuwa,tun yana yaro shi d’in mai hazak’a ne baison wasa da karatu,kyakkyawa dashi ga miskilanci da jan aji kamar wata mace ko a class bai cika mgn ba wasu suna masa kallon mai girman kai shidai haka Allah yayisa baison surutu,
Bayan kammala primary yaje secondry,yana SS3 aka haifi Zainab,wato Ummarsa Hussaina ta haihu kamar yarda yake kiranta,Anyi farin ciki da haihuwar nan bama kamar Lameer,tunda aka haifeta yana tare da ita,haka nan yaji Allah ya d’aura masa k’aunar yarinyar,
Ranar suna taci Zainab,sunan Gwoggo sai iyayen ke kiranta Ummi,Lameer yace Zainab Kaka da Malam babba suce Abulle,
Zainab kenan yarinya mai k’iriniya kamar ba haihuwar gari ba,haka Allah ya halicceta sakaryace ta k’arshe,gaba d’aya halayenta irin na k’auyawa ne kuma ita d’in haihuwar gari ce,
Kaka wato Gwoggo tana tsantsar k’aunar jikar tata musamman da taci sunanta,bayan kammala secondry d’in Yaya Lameer yaci gaba da karatunsa a Kaduna university,mahaifinsa a waje yaso yayi karatu amma yace bazai jeba sbd Zainab,
Wacce sukayi sabo sosai,be bari Umma tawa Zainab komai shi ke mata tundaga kan wanka shafa sa kaya tsifar kai komaidai shi ke bata,
Lokacin da Ta isa shiga makaranta akasata,sai tayi ta kuka ita bazata ba,Kaka tace tayi zamanta,sai ta had’u da yaran unguwa ayi ta shirme,
Lameer duk baisan da hakanba kasantuwar karatunsa da yayi masa zafi kunsan karatun likitoci akwai wahala,
Akwai wata budurwa da suke karatu tare,tana mugun sonsa duk wata hanya da tasan zatabi saida tabi har Lameer ya fara kulata,KHAIRAT tana matuk’ar k’aunar Lameer kaiba ma itaba ‘yan mata da yawa na kai masa hali Amma shi,baya kulasu,
Haka suke binsa kamarme,duk mkrntr Khairat kawai yake kulawa itama don tazomai a mutuniyar arziki ne da sunan karatu kawai zata dunga koya gurinsa,
Zainab bata son karatu sai yawo gidajen k’awaye abin na damun Babanta yasami yayansa sukai mgnr gurin Gwoggo sukaje suka sanar mata nan ta fara bala’in abar yarinya ta sakata ta wala,
Haka sukaci gaba da hakuri da halin Zainab yau taje gobe bata je ba,
Lkcn da Lameer ya gano abinda ke faruwa nan ya fara takurata,suyi fad’a wataran su shirya,
Yadawo da kansa yake kaita skul ganin hakan sai sam bata mayar da hankali tayi abinda ya dace,
Lameer yana matuk’ar k’aunar Zainab da kansa yasanar da Kakansu Malam babba nan take yace ko bayan ransa abawa Lameer auran Zainab,duk abinda Zainab zatayi Lameer baya ganin laifinta ta fannin mkrnt ne kawai suke samun matsala,
Dukkan mai rai mamaci ne Allah ya amshi rayuwar malam babba sunyi kukan rashi sosai,haka mutane domin malam babba mutumin arziki ne yasami yabo saidai fatan Allah ya kyautata makwanci,Gwoggo tayi kukan rashin miji adali,da haka akayi zaman makoki,
Lameer bayan kammala karatunsa,Abbu ya gina masa babban asibiti aka zuba ma’aikata,shi dakansa yasawa asibitinsa suna LAMZAH wato Lameer da Zainab,
Muje zuwa
Karfa kudamu nasan kun k’osa kuji taya akayi wnn auran nasu karda ku damu zakuji????????