NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
????????????????
*NI DA YAYA LAMEER*
❤❤❤❤
????????????????
GAJERAN LABARI
Story and written
By
Fateemah Sununi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
MARUBUCIYAR ✍????✍????
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now????
NI DA YAYA LAMEER!
WhatsAPP no 08104335144
Diditated to ATK
Special gift to Anty Hauwa
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
????️11↪️12
Saboda rashin k’ok’arinta yasa aka dungawa Zainab rufitin,sam ko sunanta bata iya rubutawa,hankalin Lameer ya tashi ya dawo da kansa yake mata lessin a gida,ya fadage koya mata amma ta kasa domin haka Allah ya halicceta ita bamai gane karatu bace,
Wataran ya bugeta kai har yadawo suka dena shiri,don baisan rashin mayar da hankalin da batayi,
Da k’yar aka samu aka yarda har ta zana jarabawar fita Primary ganin irin takurar da Lameer kewa Zainab akan karatu yasa ta had’a yaranta ta kalli Alh Ibrahim tace”inaso ku tara mutane ku d’aurawa Lameer da Zainab aure don nagaji da wannan takurar da yakewa jikata,
Muryarshi akaji kamar daga sama dawowarsa asibiti kenan zai shugo yaji maganar da Kaka take,yace”wllh da ma hakan yafi aini nasan yadda zan sata gaba sai tayi ilmi ba abinda zai zaunar damu gidan nan balle kice na rabu da ita,
Iyayensa ruk’e baki sukayi,Abbu yace”Lameer rashin kunyarka har takai nan uwar tamu kake fad’awa haka,Kaka tc”rabu da shak’iyin ai shiyasa nace amasa aure ko ya rage,
Murmushi yayi yace”Abbu afuwan nifa ba rashin kunya nayi ba,Baba yayi mrmsh yace”Yaya kawai amasu auran nan hakan zaifi,girgiza kai yayi yace”shekarun Ummi goma fa taya za’a musu aure yarda yake rawar jikin nan ai sai ya illa yarinya,
Ai gaba d’aya Abbu kunya ya basa da sauri yayi k’asa da kansa ya rasa da wacce zaiyi wani abu Zainab haba shima Abbu da wani zance,
Kaka tc”kaga ni banson jin wata mgn auran nan sai anyisa inaso da raina naga auransu kuma mucika wasiyyar Malam,
Haka suka amsa don yadda sukejin mgnr Gwoggon tasu basason 6acin ranta,sad’af-sad’af Lameer ya fice cike da jin kunyar abinda Abbu yace,yaji frn cikin zai auri k’anwar tasa aransa yasa zai kula da ita sosai sai iyayensu sunyi frn cikin had’in da sukayi,
Biki sosai akayi aka gayyaci ‘yan uwa da abokanan arziki,Inda ranar wata asabar dumban jama’a suka shaida auran Lameer Ibrahim Halilu da amaryarsa Zainab Ahmad Halilu anyi biki sosai inda Zainab batasan komai ba itadai sai murna take ana bikin Yaya Lameer d’inta,
Bayan bikin basu tare ba domin saida Abbu ya gama gidin da ya musu part biyu babban gida na nunawa tsara,saidai shima Lameer yana gininsa had’ad’d’e saidai Abbu cewa yayi bazasu tare yanzuba sai Zainab ta mallaki hankalin kanta inda yace su tare nan gidansa da yamusu,
Lameer baiji komai ba haka suka tare inda aka shiryawa Zainab part d’inta sak na amare,saika rantse wata k’ayuwar mata ce za’a kawo,
Khairat ta kalli Lameer wacce ke zaune kujerar dake fuskantarsa a office nasa,mrmsh tayi tace”bazan 6oye maka ba Lameer na dad’e ina k’aunarka ganin lkcn karatu muke yasa nak’i sanar maka,
Shima mrmshn yayi yace”Khairat kenan kuma gashi kin makaro dumin a satin nan aka d’auramin aure,da sauri ta mik’e “aure kuma Lameer waka aura?,”wacce nakeso,ya bata amsa,
Ckn fusata tc”yayi kyau amma inason kasani ni Khairat ban ta6a neman abu na rasaba kuma kaima banajin zan rasaka ta halin k’ak’a sai na aureka,
Wani shu’umin mrmsh yai yace”Inaso daga kaina ki gane ba komai mutum ke nema yasamu ba,muzuba mugani,
Wani kallo ta masa kafin ta fita a matuk’ar fusata,
Da farko Part d’in su Ammi Zainab take kwana,daga baya kuma ta dawo gurin Lameer domin idan Ammi tasa ta kawo masa abinci sai ya rik’eta da hira har tayi barci don saurin barci gareta,tun Ammi na zuwa ta tafi da ita har ta gaji da wnn abu na ‘ya’yan zamani????,
Amma sosai suka sa masu ido don kar ya illata yarinya shekara goma meta isa,da sukaga rawar kan nasa yayi yawa Abbu da Ammi suka zaunar dashi akan karya kuskura wani abu ya had’asa da Zainab,shi wllh kunyama suka basa yace”wai Abbu me yasa kuke tada hankali haka ni ba abunda zan mata,nan dai sukaja kunnansa(ni kuwa nace kai Abbu shida matarsa????loll)
Haka shuk’uwa me yawa taci gaba da wakana tsakaninsu,inda dakansa yake mata lessin,harta fara gane wasu abubuwan snn ya kaita junior secondry school,
To ko’acen ba wani maida hnkl take ba,sai shegen surutu da k’awaye,malamai har kawowa Lameer k’ara suke akan tsokanar mutane da take a skul har malamai bata ‘yaleba,
Yayi mata fad’an har nasiha da rarrashi amma Zainab bataji,
Khairat ce gaban iyayenta tana zuba shagwa6a ckn kuka tace”dad an mum idan har baku yi yarda kukayi na auri Lameer ba wllh guduwa zanyi,nan takefa hankalinsu ya tashi suka fara lallashinta Dad yc”ki kwantar da hnklnki ‘yata shiko d’an gidan uban waye sai ya aureki,Mum tace”duk yarda zanyi zan samo miki farin cikinki ‘yata ba wani abu a duniya da zakiso ya gagaremu ki kwantar da hnklnki…
Tofa fans kunji wata sabuwa wai inji ‘yan chacha,muje zuwa????
Wanna littafin ya koma na kud’i duk wacce ko wanda hakan baiwa dad’i ba ina bai basu hak’uri wasu ke jawa wasu ga duk wanda/wacce ke son saya zata iya Transfer ta wannan acc d’in,Talatu Amadu Zaria 30719716460 First bank,ko katin layin MTN ta wnn number 08104335144 akan 200 kachal ????
Kar ku mance duk wacce ta turo ta sanarmin ta wannan number dake sama????ta fatan wanda yaji haushi zaiyi hak’uri????
Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
????????????????
*NI DA YAYA LAMEER*
❤❤❤❤
????????????????
GAJERAN LABARI
Story and written
By
Fateemah Sununi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
MARUBUCIYAR ✍????✍????
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now????
NI DA YAYA LAMEER!
WhatsAPP no 08104335144
Diditated to ATK
Special gift to Anty Hauwa
Fans kuyi hak’ur da abinda ya faru,Wannan littafi ya koma na kud’i ga duk wacce/wanda zai iya saya zaya turo 200 kachal ta wnn acc Talatu Amadu Zaria 30719716460 First Bank ko katin layin MTN ta wnn number 08104335144 karku mance kuturo min alama idan kuntura duk ta wnn number????domin nasaka ku sabon group d’in wnn book idan ma baki karanta ba zan turo miki tundaga farko,
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
????️13↪️14
Tashi tayi a juciye kamar ba iyayenta ba ta nufi bedroom nata,su kuwa duk sukabi suka damu,Dad ya kalli Mum yace”wai Hjy wanne yaro ne take mgn,numfashi taja tace”wani yaro ne dasukayi karatu tare tun lokacin take sanar mini nayi zaton yadda take kyakkyawar nan shi dakansa zaice yana sonta amma tunda ta furta masa ya watsa mata k’asa a ido zaisha mamaki bai san wacece Hjy Sa’a ba jina yake,
Cikin fushi Dad yace”uban waye ubansa a k’asar nan da har zai 6atawa ‘yata rai wllh tallahi na rantse sai naci mutim cinsa sai ya gane ya ta6o d’iyar Alh Kamalu yasan waye ni kuwa a garin nan da k’asar nan to wllh ya ta6owa kansa,
Tashi yayi kamar zai tashi sama ya sa6a malin malin d’insa yayi gaba bedroom d’in Khairat ya nufa,
Zaune ya isketa tana kumburi idanuwan nan nata k’ek’ashe,kwalaben syrup me zube da alama su tasha don rage zafi,idanuwanta jawul sosai,
Zama yayi tare da kamo hannuwanta,da sauri ta fuzge tace”ba abunda zakamin na saurareka idan ba soyayyar Lameer zaka samomin ba,
Cikin sanyin murya kamar shine d’iyar ita uban yace”kiyi hakuri ‘yata wllh nayi alkawari saikin auri wnn yaron badai kina sonsa ba gyad’a kai nayi alamar eh,