NI DA YAYA LAMEER COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sauri taja baya tana hawaye tace”waye kai?don Allah kayi hakuri kamayar dani gurin Yayanah,dariya yasaka yace”ai kuma ke da yayanki kun rabu kenan,kasheki akasa fa nayi amma saboda ina sonki yasa ban kasheki ba,don haka kibani had’in kai,zan mayar dake ‘yar lele muji dad’inmu ko?ya k’arashe maganarsa da tambaya,
Runtse idanuwanta tayi da k’arfi hawaye nabin kuncinta ita bamafa tasan inda mgnrsa ta dosa ba,tace”don Allah kayi hakuri kamar dani cikin ahlina,
“Duk irn son da nake miki bazan yarda nayi gangancin nan ba kinsan ma wacece Khairat waye ubanta?,girgiza kai take tace”ni wad’an tambayoyin naka sun girmi kwanyata a makaranta ni banacin jarabawa kaga tambayoyinka zasu iya kassara kwanyata don Allah kayi hakuri kamar dani gurin Yayanah,
Funcikota yayi saigata jikinsa k’arata kwalla da k’arfi,bai damuba yace”wllh tunda nayi sha’awarki to sai na d’and’anaki,kuka sosai Zainab keyi nan fa suka fara danbe,
A 6angaran Lameer daidai lokacin yaga ya mik’e tsaye,a fili ya furta “Zainab duk yadda akayi ba lafiya meke damunki Zainabuna,komawa yayi ya zauna sai kuma yasake mik’ewa,ganin dai hankalinsa ya kasa kwanciya key ya zara ya nufi skul d’insu,
Me gadi na ganinsa gabansa ya buga,ckn fara’a Lameer ya gaishesa kamar kullum harda basa ihsani ‘yar kyautar da yasaba masa,jiki a sanyaye ya amsa,sai yanzu yake da nasanin abinda yawa me kyautata masa a lokacin tunanin ya fad’awa shugabar mkrntr bai zo,masa ba,
Cikin harabar skul d’in Lameer yayi parking kamar yadda yasa ba,da kansa ya fito,don ganinta kawai yakeson yayi yawuce tunda lokacin tashi baiyi ba sai shidda,
Kamar daga sama saiga Hafsa k’awar Zainab tace”lah yaya lameer ina wuni,cikin fara’a ya amsa mata don duk abinda Zainab keso shima yanaso don ta ta6a fad’a masa duk cikin skull bata da kamar Hafsa,
Tace”tun da safe da aka mana break kazo gurin Zainab har yanzu baka dawo da itaba haran wani abunne ya faru,har aka koma class muna zuba ido bamu ganta ba,
Take gabansa ya buga da k’arfi annurin dake fuskarsa ya kau,yace”ni kuma ai duk yau banzo makarantar nan ba,cike da mamaki ta kallesa tace’aikuwa Baba me gadi ne yazo yace kai ke kiranta da sauri ta fita kuma har yanzu bata dawo ba,
A rikice ya juya gate ya nufa,baba me gadi na ganinsa gabansa yasake faduwa cikin yak’e yace”me gida har kafito,”Ina Zainab?abinda ya iya furtawa kenan,nan take jikin me gadi yahau rawa,ganin zai masa inda inda yashak’e wuyansa,Ina Zainab ya sake tambayarsa,
Nan take fa d’alibai da malamai suka fara taruwa,akaje aka sanarwa shugabar makarantar da kanta tafito,har lokacin me gadi ya kasa mgn,itama tambayarsa take abinda ya faru yak’i mgn,
Wata shak’a da Lameer ya masa ai ganin yana niyyar kaisa lahira da sauri ya fad’i abinda ya faru yad’aura dacewa”bindiga da wuk’ak’e suka nunamin shiyasa na tsorata,hawaye ne kawai ke futa fuskar Lameer yayin da kowa dake gurin yayi suranda…….
MUJE ZUWA????????
Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
????????????????
*NI DA YAYA LAMEER*
❤❤❤❤
????????????????
GAJERAN LABARI
Story and written
By
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
MARUBUCIYAR ✍????✍????
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now????
NI DA YAYA LAMEER!
WhatsAPP no 08104335144
Diditated to ATK
Special gift to Anty Hauwa
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
????️23↪️24
Sakin wuyan mei gadi yayi ya nufi motarsa da sauri,key ya mata ya fuzgeta,gudu sosai yake akan titi har Allah ya kaisa gidansu Khairat,
Yanayin yadda yake hun ma kawai ya’isa shaidar isowarsa,da sauri meigadi ya bud’e duk a tunaninsa Khairat ce kartazo ta shuka masa rashin mutumci,
Yana parking ya fito,a fusace yanufi cikin gidan,babu batun ya tsaya a masa iso,
Su kansu suna niyyar fitowa sukayi kici6us dashi domin irin hun d’in da’ake ya basu mamaki,fitowa sukayi suga wanne me tsaurin idon ne,don Khairat tana gida bata fita ba,
Kallon kallo sukawa juna,cikin dakakka zuciya irin tasa da garaje yace”me kake dasuna Alh Kamalu ko me,to inaso kasani wllh idan baka fitomin da mata ba duk wulak’ancin da na maka kai kaja,yinzun nan nakeso ka fito min da mata,
Kallonsa yayi sannan ya kalli Khairat,juya fuska tayi tanaci gaba da taunar cingam,
Gabanta Lameer yazo ya kalleta sama da k’asa sannan ya tofar da yau gefe yace”koda mata sun k’are bazan ta6a dubanki ba balle har nace zan soki natsaneki Khairat banta jin zan iya sonki ba balle na aureki,ku futomin da matata kafin na kassara rayuwarki,
Hawaye ne ke zuba afudskar Khairat tace”Lameer ban ta6a son wani a duniyata ba saikai meyasa katsaneni ni ba mace bace ko ya kad’auke ni,meye ajikin wannan ‘yar ficiciyar yarinyar da kake mgn nidai nasan ba’abinda zata nunamin saidai na nuna mata kum…..
Wani kyakkyawan marin da ya zuba mata yasata yi shuru ta rik’e kunci da sauri,Alh Kamalu yayo kan Lameer d’aga masa hannu yayi yace”karka kuskura kazo kusa dani don kai zan maka abinda yafi na Khairat,chak ya tsaya sai kuma ya fara fad’a,
“Wannan wanne irin cin mutumci ne kaxo har cikin gidan ubanta ka mareta wallahi jami’an tsaro zan kira maka,
Yace”ai hakan nakeso maza ka kirasu,wallahi sunanka yana hanyar 6aci daman kai 6ataccen ne,komai dakakeyi nasan komai wllh sai na tona maka asiri matsafin banza namana da na Matata yafi k’arfin kaci idan ma dodonka kakaiwa Matata maza ka dawomin da mata kafin sunanka yanzu ya fara zagaya gidajen tv radio da jaridu nasan kasan koni waye,tabbas ni likita ne amma ina da abokanai ‘yan jaridu da yanzu idan nabasu kanun labarai zasu yad’ashi duniya taji damansu kullum jira suke su sami kanin sabun labarin dazasu yad’a duniya taji,
Takefa jikin Alh Kamalu ya hau rawa,bai ta6a sanin yaron nan yasan komai gami dashiba,yace”Ni bansan komaiba gami da 6atan matarka wallahi ban sani ba,
Hjy Luba taja tsaki”wai Alh meye haka jikinka yake rawa akan wnn ‘yar barazanar tasa,kallo Lameer tayi tace”idan baka yad’a ba baka haihuba don ubanka,
Kafin ta rufe baki yasakar mata wani zazzafan mari,ai nan take jinta da ganinta ya d’auke na wucin gadi,cen na hango luba ta xube gefe guda,
Duk’awa yayi saitinta yace”ke tsohuwar kilaki nifa wanda baiba kansa girma baija girmansa maganinsa nake,ke har zaki zageni kada ku fitomin da mata kuga abinda zai faru ki kuka dakanki,
Mik’ewa yayi ya kalli Alh Kamalu,”Ina MATATA,rantse-rantse yakama “wallahi tallahi bansan inda take ba,
Kallon Khairat yayi wacce fuskata kumbura tayi jawur sbd marin datasha kunsan meyin bilicin nan take fuskar tayi wani ja,
Yace”tana ina,shuru tayi,matsowa yayi kusa da ita,ganin zai sake marinta tace”nifa ban sani ba,
********
Zainab da Boss sosai suke danbe,ganin yarinyar ta burkice masa kamar me aljanu yasa yarabu da itayace”nabarki yau amma gobe wllh duk tsiyarki sainasha romanki,
Ta murgud’a baki tace”la’ananne d’an iska Allah bazai baja sa’a ba,Kanta yayo “wakike zagi,
Daram ta tsaya tare da rik’e k’ugu tace”an zagekan wallahi ka k’araso gurin nan sai kaga abunda zai faru d’an iska kawai wllh kayi asara dai,
Tsayawa yayi yajasa k’arasawa aransa yace”anya yarinyar nan ita d’ayace,duba da danben dasukasha shi duk yagaji itako ko alamar gaji babu atare da ita gashi yadda take masa magana kai tsaye kamar mai iskokai,
Dariya tasaka tace”uhmm harnaga yadda zan gullisuwa da wani a gurin nan,zakutayani ko?naga tana kallon gefe,tana jujjuya idanuwa,ai da gudu boss ya fita yana al’ajabi wannan yarinyar anya mutum ce,