NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

            BY HAERMEEBRAERH

page 18:

“El-mustaphaaa?” Shine abinda bawan Allahn nan ya furta kawai, da sauri ya hau jujjuya Mus’ab yana kallon shi, ganin haka ne yasa Farha miqa mai hannu akan ya bata Mubarak, gaba daya ta tsorata da ganin canjin mutumin a lokaci daya, ga shi ya fara zubda hawaye sosai, a firgive tace,” Malam bani qanina mu tafi meye haka, ko an fada maka nan wajen makoki ne?” Fizge Mubarak tai wanda shima a yanzu ya fara tsorata da mutumin, tabba Baaba Mus’ab ya san wannan yaro jinin abokin shi ne, to amma ina Lamyah, dan wannan ba ita bace, ya san Lamyah ta hanyar hotuna, da kuma zuwan da sukan yi Dubai lokaci zuwa lokaci, anan ne sukai mata alqawarin boye wa Ameenullah ita har sai yaje da kan shi ya ganta ko kuma ita taje Nijer, ” hukumullahu laa ajabun, wannan yaro tabbas dan Aminina ne, baiwar Allah ki taimaken ki sanar da ni ina zan ga AISHAA LAMYAH,,” jin ya ambaci haka ne, Farha ta matsa kusa da shi sosai tace,” kaiiii malam dakata kaji, ni fa da kk ganina hakan nan kar ka nemi kawon raini, ko wani 419, karrr nake ganin mutanen duniya yanzu, in ma wani tuggun ka ke son hadawa to bari na fada maka ka kiyayen, dan in daki qato ni ba wani abu bane waje na, a ido ne zan maka kamar va zan iya aikata hakan ba, amma duk wanda zai taba Lamyah a shirye nake dana sadaukar da rayuwata dan kare ta ta,” ” tabbas kin cika masoyiyar gaskiya, amma baiwar Allah ki taimake ni ki taimaki Lam…….” wata murya mai zaqi suka ji daga bayan su, an kwala kira da ” Baabaa” juyawa suka qarayi dukkan su ,Farha tin kan ta juya ta san mamallakiyar muryar, Baabaa Mus’ab da gudu2 ya aje Mubarak itama da gudu sosai ta isa gare shi ta fada jikin shi tana kuka sosai, kuka suke ba qaqqautawa, Mutuwar aminin shi ta dawo mai sabuwa fil, ita ma mussing Abii din ta take, da Ammii sannan ga farin cikin ganin Baaban ta, tabbas tasan a yau ta gama ganin Yah Amee din ta, sannan ta san Allah baya bacci, Allah yana amsa addu’ar bawan sa da ya yarda shi Allah ne, ya yarda da ya roqe shi akan komai ya kwantar da hankalin shi ya jira sakamako daga mai dika, Lamyah imanin ta ya qaru akan na da, domin tai wa Allah godiya a wannan lokaci yafi a qirga, Farha ce ta je ta kama hannun ta,” can u guys pls tell me what is going on here?” Murmushi Baaba yai dan ya san wannan tabbas ba a taba Lamyah gaban ta mutum ya sha, kuma a yanda ya kula tana da kusanci da Lamyah in ko haka ne to tabbas yasan ta san ko shi waye,” ‘yata ni ne mahaifin Ameenullah, Yah Amee din Aishaa Lamyah, ” ai ko wani tsalle ta daka ta dane Lamyah, tana murna, sai ga hawayen taya Lamyah farin ciki na bin fuskar ta, tare da hawayen tinanin tabbas rabuwa da qawar ta kuma ‘yar uwar ta yazo, kukan ta qaruwa yai da kyar Suka samu tai shiru, Faisal ne ya qaraso da kudin Lamyah,” to ni da kk bar min kudin me zan da su, kin san yau kin fi burge kowa wajen nan dan haka ne kudin suka fi na kullum kar…..” maganar shi maqalewa tai ya duqa qasa yana sosa kai,” Baaba barka da zuwa,” qasan zuciyar shi yana mamakin ganin Lamyah a jikin Baaban abokin shi, ga Mubarak da farha a gefe idon farha ta sha kuka, shima haka da Lamyah, ,” kudin meye kk ba ‘yata Faisal?” In ina Lamayah ta fara, ta amshe kudin tai wa Faisal sai da safe, a haka Baabaa yace ba zai bar Lamyah tafiya ba tare da yasan inda take ba, nan take yai ma drivern shi waya yazo ya shiga motar shi da Mubarak da Lamyah ita kuma farha suka tafi da Bala, tun da suka shiga motar Farha ke kuka, ba irin lallashin da Bala bai ba amma taqi shiru, hankalin ta ya tashi matuqa, dan tasan tabbas rabuwar ta da wani bangare na jikin ta ya sake zuwa mata, nan take kan ta ya dau ciwo, zazzabi ya rufe ta, Bala ma hankalin shi a tashe yake ga masoyiyar shi ba lfy, kuma komai kan idon shi ya faru, ya tabbata rabuwar shi da uwar dakin shi yazo, haka suka isa gidan kowa da abinda yake saqawa, bayan sun shiga ne, suka nufi ciki, inda Baaba ya kira Baba mai gadi, bayan sallama da yai ya sanar da su yana son nan da kwana sha daya zasu tafi da Lamyah, nan take wajen ya kaure da koke2 Baba mai gadi kan shi hawaye yake,anan Baaba ya fuskanci lallai Lamyah yarinyar kirki ce, tai halin iyayen ta, ” kar ki tafi ki barni ‘yar uwa ta,in kk tafi za sake komawa cikin maraici ne, ki tausaya min , ko aure na baki gani ba zaki tafi kwanakin sun mana kadan Baaba,” kuka take sosai Lamyah ma kukan take, sun manne juna kamar wadan da aka ce tafiyar yau dinne, ,” ku dakata, wannan kukan da kuje ba magani bane ba fa, ke an kusa auren naki ne? Waye manemin naki, na roqa a kusanto da auren, dan kuwa tabbas zan tafi da ‘yata da dana, ba zan bar su anan ba ba su da kowa, ko me ake. Buqata a auren ki na dau nauyu, ke koda mijin ne bai shirya ba, domin ke masoyiyar diyata ce komai zan iya maki,” Baba mai gadi ne ya nuna mai Bala a matsayin mai neman auren ta, ya sanar da shi matsayin karatun Bala, da aikin da yake a gidan, yaji dadin hakan sosai, yace to ai abu yai kyau duk gida ne ma, dan haka a na sauran kwana goma zasu tafi za a daura auren, ta tare a randa zasu tafi, in yaso sai su zauna a cikin gidan kawai, sun yi murna da hakan sosai, amma fa banda Farha, dan ita yanzu ba ta da sauran murna sai tashin hankalin rabuwa da Lamyahn ta, ko daga kai batai ba, Baaba ya fuskanci hakan ya sa yace,” to ku naga sai murna kuke anaryar ma naji tace ta fasa a ba wa Bala wata ya aura,” da sauri Farha ta daga kai tace,” yaushe mukai haka da kai,” cike da zaro ido, aiko nan take wajen ya kaure da dariya,kunya ta kama ta ta miqe daki da gudu, Lamyah ma bin ta tai, sukai ta dariya, tare suka dawo, kitchen suka shiga suka debo mai abinci da kayan motsa baki kala2, dama bai ci abinci ba nan take ko ya ci ya qoshi, sannan sukai sallama akan gobe zai dawo, bayan ya tafi ne suka zauna suna ta tattauna yanayin yanda komai zai tafi, Bala ne ya fara hamma yai masu sai da safe, kafin Lamyah tace,” to amarya aiki ya samen ya kamata na fara gyara ki kamar Yanda Juwaireren mama na ga tana gyaran jiki kema haka zan din ga maki,” miqewa Farha tai ta shige daki tana qunquni, ” ba sai ki gyara nin ba tinda ni daya ce amaryar? Kema kina zuwa za sui ramm da ke a ba Yah Amee din ki, kunqara ta can,” ” Farha me kk cewa ne, kin san ban son kina magana qasa2 dan na san halin ki sai ki zage ni tass ta haka ina nan baki bude,” Farha bata ankara ba taji duka a baya, dama a wuya take, kuma tafi Lamyah qarfi, kokawa suka fara cikin daren Mubarak da yau idon shi ya soye ya fara dariya yana ” Yauwa qashi da rai, cika mata aiki, ke kuna kumburin buredi zaune ta,” suna jin haka suka saki juna sukai kan shi, yana ganin sun yo kan shi ya zare ido ya dora hannu aka yai hanyar fita da gudu, sai dakin shi, kan su isa ya sa key, yana dariya, yana qara tsokanar su, kowa a cikin su ta tsani sunan da yake kiran ta da shi, a haka suka je sukai wanka sukai addu’a suka kwanta.

Shirye2n biki sosai Lamyah tai wa Farha, qawayen su na wajen RAWA suka gayyata, harda yan baqin cikin su, sai da suka gayyata, su kuma suka ci alwashin zuwa ko dan suga dame yaran ke taqama su ke nuna su wasu ne. Farha ta sha gyara wajen Tani da Lamyah, Lamyah kullum sai ta kwadan ta mata zogale danye da manyan timatir, da kuli , ai ko nan da nan Farha hips din ta ya fara fitowa, ita kuma Lamyah ta dage da gyara belly din ta dan so take a bikin Farha ta cashe rawar da bata taba yi ba, hakan ne yasa take shan gwalba wadda ake hadawa da nono amma bata sa nonoj haka take jiqa ta ta murje kwallayen tana sha bayan duk wanu cin abinci, nan da nan kuwa tumbin ta yai qasa, ya dada shigewa yai flat yai kyau, ita kuma Farha sai Lamyah ke bata kwalbar bayan ta saka mata madara a ciki, na musamman ta sa aka yo mata dakan hannu na busasshiyar aya da kayan qamshi a ciki, da minannas, sai dabino busasshe, da madarar shanu da zuma Lamyah ke hada ma Farha ta sha, amma wajen shan kullun sai an kokawa, dan Lamyah ma cewa take sai ta sha,” yacin kk sha kema sai an miki auren,ke za a aurar ko ni, ni ban gane ba , in aka zo ci ko shan me dadi kina gaba, in aka zo masu daci da bauri ki noqe, kaji min yarinya , ni gaskiya Tani na min wariya,” dariya suke sakawa sosai, aiki duk randa aka ma Farha hadin tsumi masu bauri baurin nan, sai ta danne Lamyah ta dura mata, in taqi taita soka mata guiwar hannun ta a cinya, ita kuma abun dariya yake bata, kamar cakulkuli, a dariyar nan zata samu ta dura mata, sai ta gama sha tai allah ya saka mata, ” zai saka miki mana da alkairi randa Yah Amee ya same ki a matsayin mata,” ai ko da taji haka farin ciki na kamata sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button