NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

El- mustapha Sadauki, wani shahararren mutumi ne wanda yake da arziqi da taimakon gidan marayu,da islamiyyoyi, yau qungiyar su ta baro qasar su dake Niger, ta taho Nigeria, domin taimakawa, islamiyyar da malam Muhammad ke jagoranci, ya samu labarin qoqarin shi ne, ta bakin wani mai masa hidima, a nan Nigeria, dan yana da masu nemo masa rahotanni a qasashe don ya samu damar taimakawa.

El-mustapha yana da nasaba da kuma jinin larabawan Dake da mazauni a Dubai, garin tainakon shi ne yasa ya baro qasar shi ya kafa gidauniya anan Niger, wanda da dawowar shi da komai bai fi shekara biyar ba kenan, ya samu tsananin qiyayya daga ‘yan uwan shi na can, wadan da ba su qaunar shi ko kadan sakamakon son talakawa da yake da, rayuwar shi daban da tasu, ta dalilin haka ne ya tattaro ya dawo, iyayen sun rasu. Dawowar shi nan bai sa ya yanke alaqar shi da su ba, yana zuwa a kai akai, dan sada zumunci, gaba daya hakan da yake yi ji suke kamar su kashe shi su gaje dukiyar shi, tinda yaqi auren ‘yayan kowa a qasar yace bai ga wadda ta mai ba, yana son yarinyar da zai aura ta kasance daga gidan tarbiyya, da mutunci, amma fa talaka, wannan kalmar qarshen ta baqanta ma yan uwan shi ba kadan ba, a haka suke har yau da yashirya zasu so Nigeria, sannan Unguwar Rimin Gata, kuna gidan Malam Muhammad mai Islamiyya……

Hello guys, can u pls do me a favor? Ku dan aje wannan page a wani wajen, yanda koda nai nisa kunji sha’awar bi na sai ku lalubo ku karanta,ba sai nai nisa kuna tambaya ba, wayata yar qwaya ce,lols???? ta yi nauyi da yawa, saboda abubuwan da take dauke da shi, ba zai yu na dinga sendin abu mai yawa ba ba tare da tana riqewa ba, so pls ku na adanawa, Thank u
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘ YAR RAWA ????????

           BY HAERMEEBRAERH

page 2:

   Sun iso a gajiye, inda suka fara isa gidan mai garin, suka gabatar da kansu da dikkan bayanan abinda ya kawo su, nan take mai gari ya aika a kira Malam Muhammad, domin bangaren shi ne, isowar shi keda wuya, suka gaisa sannan aka qara kora mai jawabin komai, godiya ya musi mai tarin yawa, sannan ya nemi izinin tafiya da su masauqin da yakan aje baqi in sun zo, tashi sukai suka isa gidan Malam din, daidai lokacin Ameenee ta fito wanka tana shiryawa, kiran ta Malam yai ta je tare da durqusawa, " Abba gani" " Ameenee je ki dauko mazubin ruwa mai kyau da tsafta ki debo ruwan sha mai sanyi na randar gefen madafi ki kai wa baqi a dakin baqi, sai ki dawo a kai masu abinci kinji?" Amsawa tai da " To Abba" sannan ta miqe ta tafi ta qarasa saka riga da skirt din ta na atampa, ta dora hijab din ta akai, saboda Allah ya mata halitta mai kyau da diri, wannan dalilin ne yasa bata ta'ammili da mayafi. Sallama tai cikin muryar ta mai sanyi, kanshi a duqe yake a hankali ya dago dan ganin mamallakiyar wannan daddadar muryar, kallon ta ya tsaya yana yi kawai yana mamakin samun yarinya mai kyau a cikin Africa kuma a Nigeria, Nigerian ma a kano, lumshe idanun shi yai da suke madaidaita da cikar kyau ya amsa sallamar ta, ruwan ta miqa mai ya karba ta gaida su, cikin hausar shi da ba wani ji yake ba sosai, ya amsa, miqewa tai ta tafi ciki ta qara dawowa dauke da abincin da ita ta dafa, taliya ce mai mai da yaji, sai maggi da aka bada mata? Irin taliyar murjinnan ce, amma tai wara2 kamar ba ta murji ba, sannan Malam ya siyo  kifi manya aka dora musu akai, a da da aka kai El-mustapha sadauki ya fara ganin anya zai iya ci? Kawai a dakko mai abincin shi a mota ya ci, sai kuma zuciyar shi ta raya mai ya tambaye ta. " Yaya sunan ki?" Murmushi tai dan jin hausar shi, ta amsa mai da" Suna na Ameenaa" " Malama Ameena ana zuwa makaranta kuwa?" " Eh ina zuwa, dan na sauke alqu'ani da shekara goma, da sauran littafan addini, yanzu ma ina taya Abbana koyar wa a wasu daga cikin ajujuwan da suka rage ba malamai" " Masha Allah" shine abinda ya fada cike da jin dadin tabbas abinda yake ayyanawa zai tabbata da yardar Allah, " Malama Ameenaa kin iya girki ne?" Ya tambaye ta da alamar zolaya, amma ti be honest yana son jin wa yai girkin ne, cikin jin kunya da. Sadda kanta qasa ta amsa mai da" Eh, ni nake girki dama" godiya ya mata yace ta je, miqewa tai ta fita, ya hango yanda jikin ya ke ta cikin hijab, ya tabbatar an yi halitta a wajen, dakko kwanon yau ya fara ci ba sai ga El-mustapha ya tashi da taliya da manja ba????fadi yake lallai, Bahaushe akwai hikima......

( Ana kiran shi da Sadauki ne saboda jajrcewar shi wajen taimakon al’umma duk rintsi duk wuya, sannan duk nisan gari da surquqin qauye zai shige shi, amma asalin sunan shi shine El-mustapha Ahmad Nabeel.)

Sun kammala dukkan abinda ya kawo su, a cikin kwanakin nan ba qaramin shaquwa da sabo ne ya shiga tsakanin shi da Ameenee ba, duk da cewar, bqi taba furta mata kalmar so ba, amma soyayyar ta ta gama da dukkan jiki da ruhin shi, ita kuma a nata bangaren bata san me ne ne take ji game da shi ba, all she know is that in ya tafi she will miss him alot, and she don’t even want him to go. Samun kan ta tai da shiga damuwa a duk sanda ta tina sallamar da sukai daran jiya, Delu kuwa hankalin ta ya fara kwanciya dan jin za su tafi, dan ta kula da take2n El-mustapha, wanda taci alwashin ko zata mutu bazata bari ya aure ta ba. Shi da malam ne suke ban kwana a dakin da aka sauke su, anan yake shaida ma Malam manufar shi, Malam yayi farin ciki sosai, inda yace ai wannan magana ya kamata mai gari ya jita, dunguma sukai can wajen mai garin, a gaban su ya rabbatar ko bayan ran shi suka dawo batun auren Ameenee a aura mai ita, godiya yai mai yawa suka wuce Nijer.

Tafiyar shi da kwanaki ne malam ya hau rashin lafiya a tsattsaye, wata rana ya tashi ya tafi fadar mai gari ya same shi daga shi sai mai garin yace mai ” ranka ya dade ina neman wata alfarma, ina son ko bayan raina in yaron nan ya dawo ku taimaka, ku bashi auren Ameenee, dan na yi alqawari bana son na mutu ban cika ba kuma ba a cika min ba, na sanar da Abubakar amini na shima hakan,” ” Hab Malam Muhammadu, ai ciwo ba mutuwa bne, in Allah ya so da kan ka zaka aurar da Ameenatou” kada kai malam yai yace ” Kayya ranka shi dade ni na san me nake ji kawai a zuciyar nan tawa, na kasa cire tinanin margayiya a raina, da zan iya da nayi na huta, amma zuciyata kamar ta rabe gida biyu nake ji” ya qatasa yayin da wata qwalla ke bin fuskar shi, gogewa yai, a lokacin da mai gari ke ta kwantar mai da hankali tare da mata addua, godiya yai ya tafi gida, ba ai sati ba Allab yai ma Malam Muhammad cikawa, sakamakon ciwon zuciyar da ke damun shi, Ameenee tai kuka sosai kamar ranta zai fita, in da Delu kam da yaran ta sun yi kuka na ranar daga baya suka shiga harkokin su, jira kawai take ai arba’in a raba gado.

Bayan an dan kwan biyu ne ya tattara ya tafi Dubai don sanar da ‘yan uwan shi batun auren shi, sannan da gayyatar su zuwa auren nashi,fafir suka mai rashin mutunci,suka nuna su fa ba zasu tako qafafun su garin takakawa ba, masu qaramin qarfi, ya buga ya raya, amma fir suka qi aminta, yai kuka yai kuka har yaji ba dadi, take kewar mahaifan shi ta addabe shi, tabbas da suna da rai da hakan bata kasance ba, ya sani ko mahaukaciya ya nuna zai aura ba zasu qi ba,balle mahaddciyar qur’anul kareem, share hawayen shi yai ya aje masi doguwar takadda da wasu daga dukiyar da Allah ya bashi, yai umarnin su raba a tsakanin si, sannan ya tafi ya koma Niger, bayan ya iso ne ya samu wani daga abokin shi, da suka zama kamar yan uwa, wani hamshaqin mai kudi ne shima a nan qasar, ya roqi arziqin zuwa ya zama waliyyin shi, a haka suka iso Nigeria. Tana gaban murhu tai budu2 da hayaqi ne taji Sallamar shi, tabbas ba zata taba rasa gane muryar shi ba, hijab din ta ta dauka ta fita da sauri, tana ganin shine, ta durqusa a wajen tana kuka, ita kanta bazata ce kukan meye ba ne, kukan maraicin daya mamaye ta ne da shekaru qananan da ba zata wuce sha uku sha hudu ba a yanzu? Aa ko kukan murnar ganin shi ne? Itama ba zata tantance ba, durqusawa yai gaban ta shima, ya qurawa zara2n gashin idon ta da suke a lumshe idoj na zubar da hawaye ido, ” Meenaa, me ya faru, ko baki son ganina ne na koma” da sauri ta daga kai ta girgiza kanta, ” Abbana ya rasu bayan tafiyat ka” cike da tashin hankali ya miqe yana baya, idon shi nan da nan suka kada sukai jawur, ” Ameenee saboda tsabat iskanci da tsagwaron tijara na saki aiki ki aje ki tafi yawon iskanci, dan najiyo muryar maza, wane ne yazo?” Tana tozali da shi tashin hankali qarara a fuskar ta, to in ma ta bar wannan ya zo ya dauke mata Ameenee gadon ta da ta lissafa za ta sake kayan daki da sho uban wa zai bata? Sannan wa zai ci gaba da mata ayyukan gidan? ” ke dawo baya wannan dan rainin ne yazo, ba sallama da manya kawai sai kazo ka tasa yarinya qarama a gaba da zance? Kai kuma na gefe waye kai, ka tsaya ka tsare ni da ido?” Duqawa El-mustapha yai har qasa idon shi na hawaye, dan tunawa da nagartar Malam Muhammad da yai, ya gaida ta ya mata ta’aziyya, shima haka abokin shi mus’ab yai, a kaikaice ta amsa tana kada qafa, ” ke ! Wuce ciki ki qarasan abinda kk yi tin fari” miqewa tai tana waiwayen shi, kada mata kai yai alamar karta damu yana nan ba inda zai je, wani dadi ne ya lullube ta tai ciki da gudu, ta je nan da nan ta hau girkin ta gama, tai wanka ta shirya cikin doguwar rigar atampa, bunjimemiya, ta dora hijab, ta zauna tana bitar katatun ta, ita kuma iya masifa ta kasa zaune ta kasa tsaye, sawa tai yaran ta suka kira bappanin su, tace tana son magana da su, nan da nan ko suka taru.
Shi ko yana tashi wajen mai gari ya nufa,ya sanar da shi ya dawo kuma a yau da yamman yake son a daura masu aure gobe ya wuce da matat shi, dan yanda ya tadda ita ya tabbatar tana cikn wahalar matar uban ta, mai gari bayan ya amsa gaisuwar da ya masa ya tabbatar masa da cewar za ai yanda yake so din da zarar an dawo daga sallar la’asar dan sauran mintina kadan a yi ta, aikawa yai yace a gaya ma bappanin ta in an yi sallah su hallara auren Ameenee…….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button