NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan kammala cin abincin su ne suna zaune a parlor,suna hira, Lamyah na kan cinyar shi, ta raba qafar ta tana kallon shi, gaba daya ta yamutse mai sumar kan shi, shi kuma idon shi kusan a rufe suke, sun yi jawur, yana amsa ta da kyar, in sun yi hira sun yi hira, sai ta sunkuya tai mai kiss, lips din su gaba daya sun yi red, suna cikin haka Naufaliyyah ta shigo,yanayin da ta gan su yasa ta saki jakar hannun ta da sauri ta dafe qirji, tare da sakin ashar,basu daga kai ba sai da suka yi yanda suka saba, sannan suka saki juna, juyawa yai a hankali yace,” malama ki fita sannan ki jamin qofar ki je gida har sai na neme ki, sannan, kar ki kuskura ku matsamin sai sanda na neme ku da kaina, in ba haka ba, a duk randa kikai yunqurin nemana a bakin auren ki dake kaina,” kurma ihu tai zata shigo ta shaqe Lamyah, da ta rusa mata komai,amma inaaa wani mugun kallo Ameenullah ya mata, wanda ya matuqar tsorata ta, matuqa, bata taba sanin yana da fushi haka ba,Lamyah kanta a hankali ta zame tai gefen shi, ta tsorata ita kanta da ba da ita yake ba, Naufaliyya ce ta kalli jakar hannun ta, yau tin safe take neman maganin da zatai amfani da shi, Ameenullah ya ce ya saki Lamyah da bakin shi, amma yanzu farat daya wannan yarinyar mai zubin mutan boye ta rusa shi, kuka ta duqa ta rushe da shi,miqewa tai a harzuqe yai wajen ta,ai tana gano shi ta kwasa da gudu tai waje, buga qofar yai ya rufe, Lamyah matsiraciya ta saka ihu, tare da fashewa da kuka, ta qanqame waje daya, zuwa yai da sauri ya dago ta jikin ta sau rawa yake, hankalin ta ya tashi, zuciyar ta na ta harbawa, dariya ce ke son kama shi amma ya dake, sai ya rama raina mai hankalin da tai waje. Cin abinci dazu,zawa ya sakar mata mai qarfi,” keeee meyee haka !, ” firgicewa ta yi ta gigice ta saka kuka sosai, tare da kwabe baki, sai ga majina da hawaye na zuba, dariya ce ta kama Ameenullah wannan karon ba zai iya riqe ta ba, ai ko ya fashe da dariya ,yi take kamar an aiko shi, ita ko kuka take tin qarfin ta, miqewa tai da gudu za tai dakin ta,dan ta gane latsa mata hammata guy din keyi, kawai caf ya cafe ta yai dakin shi da ita, sai mutsu2n kwacewa take,amma ta hana, tin a hanya yake romancing din ta, da kyar ta kwace kanta bayan sun shiga, da kyar ta iya furta “Yah Aaaameee lokacinnn sallahhh ne faaa,” tsagaitawa yai yana kallon ta, da idon shi da suka sauya, suka qara lumshewa, dire ta yai, a gado sanan ya wuce toilete yai tsarki yai alwala ya fice masjid, itan ma hakan tai ta koma dakin. Ta tai sallah, tare da aje azkar din ta ba tai ba, yana dawowa ta dakko hisnul muslim ta je wajen shi, addu’o’in yamma ta kwanta a cinyar shi tana yi da qarfi, nan take ya gane me take nufi, so take shima yayi, ai ko tare suka gama.

wayar ta ce ta fara ringing, dagawa tai taga an rubuta Sweetheart F a jiki,dagawa tai ta shiga daki,” Hello Sisto, ya abubuwan ke tafiya, na lallaba Bala da kyar ya barni zuwa amma tace sai jibi zan taho, dan haka kan na zo ki fara takalar fadan shegiya yanda dana zo zan qarasa cin uban ta,” dariya Lamyah tai sosai tace” sannu iya masifa, kin sa kowa na jiran ya ga zuwan ku Nijer, musamman yan Group din BANI NAI KAINA BA, QASAI TATTUN MATA, RIBAR BIYAYYA, ZO KIJI YAR UWA, INA MATAN SUKE, da dai sauran groups, sai ki sha zaman ki” nan ta kwashe duk abin da ya faru daga farko zuwa qarshe ta fada mata, Farha cizin lebe tai da yatsa,” Kashhhhh na si matuqa na zo na dan dirji shegen leben nan nata na qasa daya zazzago, jikin ta yai tsami dan uban ta,ta ji ba wai tsoron ta nake ji ba” dariya Lamyah tai sosai, Ameenullah ne ya shiga bai ce komai ba ya kwanta a kusa da ita, ya janyo ta yana shafa kanta, lumshe ido tai, ya fara mata wasa a kunne, nunfashin ta ne ke sauyawa, maganar farha taji daga sama,” ke meke damun ki?” “Ba komai” itace amsar da ta bata da kyar, a daidai lokacin da farha ke son mata wata tambayar ne Aneenullah ya zura hannun shi a rigar ta,kashe wayar tai da sauri ta juya gare shi, yana ta mata dariya,” ai na zaci zaki iya jure salo…, kan ya qarasa ta kai bakin ta na shi, ina ganin za sui abun manya na fece????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀kar su lalata maku ni????????????……….

Su Lamyah an shahara yanzu Oh ni Haermeen Haermmaerhna???? na fece kan ta bata ma Haermmaerh na ni????????‍♀

I am sorry for any typos coz is unedited
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘YAR RAWA ????????

          BY HAERMEEBRAERH

This page is for u guys
Sis Ramlat
Sis Hajjaju
Baba Larens
Bilkisu zarewa
(GOGGOS)
Fateema Radda
Komai nake kuna raina Me love u XX

Page 27:

Naufaliyyace na hango a zaune a bakin dan qaramin gadon dakin Maman ta, dake malale da ledar daki, sai akwatin kayan ta da ke gefe alamar tin akwatin ta ne na da datana gida, Mamar ta ce ta shigo dauke da flask din abinci da cup a hannun ta,” wai ni ba zaki bar wannan kukan da kk kwana kina yi ba, in sarautar sarkin kuka za a baki ai da tini an nada ki kowa ya huta haba, ko an fada maki kukan zai sa ya maida ki? Ki ci abinci ki sha, sai na fada maki shawarar dana yanke,” tana jin haka ta miqe ta koma kusa da maman nata,” mama sanar dani me zai sa na koma wajen Ameenullah da wuri, Mama bana son abinda zai sa mu rabu da Ameenullah, rayuwata zata wulaqanta, ki duba ku ga irin halin dana shiga a kwana daya, kin sani ina da.matsananciyar buqata, innai sati a gidannan zan koma ruwa, ga aure a kaina, Mama ki taimaka min,” ta qarasa cikin matsanancin kuka, mahaifiyar ta ta tausaya ma gudan jinin nata, ” karki damu Naufaa na, kamar bani ce uwar ki ba? Me zai daga hankalin ki? Bayan muna da boka aikatau, yanzu ya aikata mana aikin komawa Ameenu,” ” haka dai xaku qare, a yawon neman asiri ba, ba xaku zauna kui wa kan ku karatun ta nutsu ba, ki saka ‘yar ki akan turbar gaskiya sai bata, akan shegen yawon asirin nan dubi dakin ki yanda ya koma,komai ya qare ya lalace, ina ce Uwar Ameenullah qawar ki ce? Amma gidan ta, dakin ta, surturar ta, wa zai hada dana ki, ke da sauran qawayen ki ma da basu biye2n bokayen, babban jahilcin ki har yau kin kasa gane su waye bokaye da malaman tsubbu da kk bi, na farko dai dan ni kk fara bin su, amma ko kin min asirin Allah ya bada iko ya kama ni, baki ganin yanda Allah ke warware man da qarfin roqon mai dika? A iya shekarunnn da muke dake, baki ganin cewa roqon Allah yafi roqon boka ko malamn tsubbu? Habaa ki bude idon ki da zuciyar ki ki gani cewar Allah na basu aron likaci ne , yana basu dama da iko akan abinda suka buqata ne domin ya musu talala, ranar gobe qiyama ya kama su da laifukan su, ku sani ke ‘ya ta da kuma mata ta, Allah mai yawan gafara ne, mai karbar tuban bawa ne duk tsananin zunubin shi,har shirka , amma in lokaci bai qurewa mutum ba, kuna da tabbacin ranar da zaku mutu ne? An baku garantin mutuwa lokaci mai tsaho? Ko gajeren lokaci aka baku? Babu daya, dan haka kuji tsoron mutuwar fuji’a mutuwar kwaf daya, ba kusan a ina zaku mutu ba, me kukeyi za a karbi rayuwar ku, ki na aikata zina, kina aikata shan giya, ko kuna kan hanyar ki ta zuwa wajen boka la’anannen Allah? Ko kuwa kina sallah? Ko tasbihi? Ko karatun qur’ani? Ko yiwa iyaye ko miji hidima? Baki san fa lokaci ba,kin dage ke sai kin dora yar da kk haifa a cikin ki, wadda in kukaje lahira sai Allah ya maku hisabi akan komai, har tarbiyyar da kk bata, so kk ta kai qarar ki wajen Allah akan baki bata tarbiyha mai kyau ba? Kuji tsoron Allah, ku zauna ki kame kan ki, ki shiryu, ta dalilin haka Allah zai duba halin da kk ciki ya sa mijin ki ya dawo da ke,kuma batun sha’awa da kk magana akai ai ke kk jawa kan ki ,na farko wannan dure2n magungunan da kuke ke da uwar ki ku hana mutum sakat ai ta abu daya, ku a wahale mutum a wahale, ga na biyu baku banbance haram ke da girman ki kallon iskance2n turawannan kk a waya ko a talabijin, ga maganganun batsa da ba a rasa ku da ita, ke kuma yanzu zamani ya kawo maku wannan wayar ta jaraba,hirar batsa da qawaye maza da mata kina matar aure, ga karanta littafan batsa zalla wani mara tsoron Allahn zai zauna ya rubuta, kema da ba tsoron Allah ne ya cika ki ba ki zauna ki karanta tsaf, sha’awa ta tashi dole ki nemi mafuta, gashi yanzu baku son karanta wa’azin ma da zai amfane ku, sai iskanci, sai kun gama karantawa ku zo kundamu mutane suna zaman zaman su, to in baku gyara wannaj ba, wallahi Allah nesan ta ki zai da Ameenu na fada maku kenan,” Baban Naufaliyyah kenan Alhaj, Rabi’u, tinda ya fara wa’azinnan jikin su ya mutu, zuciyar su ta tsinke sosai kuka suke sosai gaba dayan su, a qasan ran su suna dada tina tabargazar da sukai a rayuwa, kowa na tina rabon data kafa goshin ta a qasa da sunan sallah an dade, ba magana Maman ta ta miqe ta bar dakin, kuka ta kwanta tana yi a zuciyar ta tana istigifari, har dai ta miqe ta fita dan dajra alwala, tana yin alwala tinani ta tsaya yi, to ita ta inama zata fara rama sallolin ta? Kuka ta rushe da shi na tsantsar tsoron Allah, tsoron tinawa da irin azabobin daya tana da domin masu wulaqanta sallah, nan da nan ta fara sallah ba ji ba gani, dan tasan Allah ba dauke mata zai ba, ta bi da istigifari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button