NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

NIJER REPOBLIC

Yau shekara hudu da watanni kenan da Baaba Mus’ab ya san mutuwar Amini kuma aboki sannan dan uwan shi El-mustapha, ran da suka sani dan qaramin hauka ya masu, Ameenullah kuwa, ya suma yafi a qirga, sai da ta kai an mai qarin ruwa tare sa allurar bacci, dan gudun kar wani abu ya same shi, satin shi biyu cif aka sallamo shi, ya rame yai baqi, baya umm baya umm umm, tinanin dake daga mai hankali, da ganin gawar yasan kashe mai Abiii akai, amma an hana su yarda da hakan, domin duk wani shaidar mutuwa yai sakamakon taka bawon Ayaba, da yai an gabatar, in ya mutu ne haka kawai ina Lamyan shi? Ina Mubarak? Sannan ya akai ba a ga komai na dukiyar shi ba? Dakko wayar shi yai ya bude, yana duba messages nan ya ga saqon , da Abiin shi ya turo mai, jiki na rawa yana hawaye ya ke qoqarin bude saqon,
Sallama ce sai gaisuwa, sannan ya fada mai yana cikin hadari, game da ‘yan uwan shi, amma kar ya samu koma mene ne Lamyah da mubarak will be safe inshaa Allah, wasu hawaye ne masu zafi sosai suka zubo mai, “to ina take? Ina zan gan su? Me yasami qanwa ta, amana ta? Wace irin rayuwa suke? Ta ina zan fara neman su?” Tari ne ya sarqe shi, ya fara yi ba tsayawa, Mommaa Aisha ce ta shigo cikin hanzari, fridge din cikin parlorn shi ta bude ta dakko ruwa ta kamo shi jikin ta tana hawaye ta bashi , tare sa shafa bayan shi, a hankali ya samu nutsuwa, ” ka yi hakuri Haerbeebee, ka kwantar da hankalin ka, ka ma Abiin ka addu’a shi da Ammiin ka, ita suke buqata a wajen ka ba kuka da damuwa ba, ba za su so ganin ka a haka ba, sannan ina son ka sa ‘yar uwar ka a addu’ae itama Allah ya bayyana mana ita,” kuka yake sosai kamar qaramin yaro, yana qara mannewa a jikin Momman shi, a hankali tana shafa bayan shi da kan shi yai bacci, gyara mai kwanciya tai cikin tausaya wa dan nata, dan ta san shaquwar dake tsakanij su, haka ta fita tana share kwalla……….

celebrate with me Roumie na and Aisha Bixxisiou, kuna raina always, ku din daban ne, love u da yawa
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘YAR RAWA ????????

         BY HAERMEEBRAERH

WOW ! i must say thanks to this wonderful and amazing people, u guys ar awsome, and i love u so so so very much u made my day so beautiful

My family i love u all❤ My friends ku daban ne na zama ku kun zama ni, Widad Ummu Hafeeza❤ My family freind, and so many others sunayen ku ba zai fadu a dan wannan page ba, amma ina mai tabbatar maku da naji dadin addu’oin ku jiya, Allah ya bar mu tare ya saka maku da alkairi mara yankewa❤

Mamu Novella
Bani nayi kaina ba G
Matsalolin Mata A yau G
Safaa & Marwaa Fans
Tabital fulaku G
Zahrah Surbajo G
Ummyn Yusrah G
Al’ummata G
Sophy And Vc novels
Sawwama Novel G
Matan Gidan Daraja G
Qasaitattun Mata G

Na gode da addu’oin kukuma, sosai naji dadi, Allah ya saka maku da alkairi mara yankewa❤

Page 12:

Sai da Baabaa Mus’ab da Momma Aisha suka sha fama sosai, kafin Ameenullah ya daidaita, ya koma normal, amma ya rage yawan fara’a sosai, sannan ya rage magana, komai akai sai dai yai murmushi, ko ya bada amsa da kai, qasan zuciyar shi cike yake da soj ganin qanwar shi, da yanzu ta tabbatar wa kan shi son ta yake matuqa, so irin na aure ba soyayyar wa da qanwa ba, zuciyar shi na azabtuwa in ya tina har wannaj lokacin ba zai ce ga kamannin ta ba, muryar ta sai ta waya yake ji, abun na matuqar damun shi ba kadan ba, sannan ya zatai ta kula da Mubarak, iya wannan tswon shekarun, yakan yi kuka sosai, ya gode Allah, domin ya san tabbas suma suna cikin kadaicin rashin kowa nasu, cigiya kam a gidan redio da TV tare da jaridu duk sun.bayar, amma shiru kk ji. Yau ne Baaba ya samu Ameenullah, ya ke mai maganar komawar shi Nigeria aiki, don zaman ya isa haka, yana da kyau a ci gaba da kulawa da dukiyar da El-mustapha ya bari ko dan yaran shi, da ci gaba da yin sadaka da kyautukan da ya saba, ba dan Ameenullah yaso ba ya gyada mai kai, bayan ya fita ne ya kwanta yana kallon sama, sai tinani yale kala2, har aka kira sallar magrib, tashi yai yaje yai alwala ya tafi masjid, bayan ya dawo ne, ya fara shirya kayan shi kamar yanda ya saba, kiran abokin shi yai, Faisal,
” Yah Man ya akayi ne? Ina fatan dai gobe zaka zauna gida ba zaka wajen shegiyar rawar nan ta ku da kuka dorawa kan ku ba?” ” yessss gobe zaka zo? Alhamdu lilLAAH, dama ina son ka zo akwai wata haja dana aje maka, wannan karon ko min qin kusantar mace da kk akan dalilin wata da ba ta san kana ma son ta ba, wannan karon sai ka dana, wannan kalar kuce, ta hadu iya haduwa, bata da makusa ko ta ina, matsala daya da za a samu shine, bata kula kowa, sannan bata cika magana ba, dan ina jin tin da muke bai fi sau uku na taba jin maganar ta ba, ita dai kawai ta zo tai rawa ta tafi kuma…….” “Ya Allah, Faisal, me yasa kk min wannan dogon sharhi haka ne? Ni fa ban ce maka ina son kowa ba,hasalima kai kasan bana son hulda da mata, dan Allah ka aje surutun ka a wata ma’adana wataqila zai ma amfani, wanni karon” kit ya kashe wayar ta dayan bangaren Faisal ko da yake shirin shiga hotel din yai dariya kawai dan yasan halin abokin nashi.

Washegari da sassafe ya nufi Nigeria, bayan nasiha da Baaba ya saba mai wannan karon sai da ya qara akan na da, Momma ma haka tai ta mai nasiha tare da kwantar mai da hankali, cikin so da qaunar dan nata tare da kewar shi da ta fara tin kan ya tafi ta kai bakin ta goshin shi ta manna mai kiss, bayan ya tafi ne Baaba mus’ab yace ” To sauran ni, dan na kula gaba daya hankalin ki ya tattara akan dan ki, tin da ya zo kk manta dani” ya qarasa cikin shagwaba kamar wani yaro, kwallar dake idon ta ta mayar nan da nan ta maye gurbin damuwar ta da farin ciki,” Habaa Baaban Lamyah, da girman ka kk shagwaba, to matso ka gani,” matsawa yai ya miqa mata fuskar shi, lips din shi ta kaiwa soft kiss, nan take ya lumshe ido, kan ya bude ta shige bedroom tana dariya, dariya yai shima ya bita yana,” ai sai ki saya ki karbi tukuicin ki kema ko,” ” A’a ni kam na yafe Allah,” dariya sukai cikin nishadi da nunawa junan su so.

Da magrib Lamyah na gani da guntun wando iya cinyar ta, kalar bby pink, sai riga da ta daga hannun ha ana ganin cikin ta, da cibiyar ta, ta daure gashin ta, hannun ta ya sha lalle da qafarta, an mata baqi da ja, sai naga ta dakko tirarukan ta tananta barin su sannan ta shafa powder, tana gamawa ta dora baqar abaya, kusan shigar da Farha tai kenan, Mubarak kuwa manyan kaya suka saka mai, dan shi wataran har kuka yake in an saka mai qananan kaya, sam.basa burge shi,in ba bacci zai ba ya saka na bacci, Farha kan kira shi saurayin qauye kawai, shi kuma ya murguda baki kamar budurwa harda fari da ido, in ta biyo shi ya gudu wajen Mummyn shi, yana mata gwalo,” Lamyah yau gaskiya sai mun fi ruda duk wanda Allah ya sa yai tozali da mu, ni har na fara jin kunya, anya bamui shigar tsiraici da yawa ba?” ” ke malama in zaki gama ki zo mu tafi ki taso, ai dai naga ba sai da jikin namu zamu ba ko, zamu ne dan nishadin mu kawai mu komo,” ” haka ne, to ni dai yanzu gaskiya jibi sai naje kasuwa, dan siyo pant da Bra na acuci maza, qawata Cutie kullum shi take sawa, kan na gano ta ba mai cewa ba nata ba, ni nqi ta tafiya zalau2 ba nama ke kuwa ko ina sai san barka,” maganar ta ba qaramin ba Lamyah dariya tai ba, har tana kama ciki, “kin ga matakar ki dariyar tsiya dilla ni tashi mu tafi, nimq zan qibar ne ai, sai na baki mamaki, har sai kin nema min abun rage ta, kai kuma da kk guntse dariya ka sake kayi ta sai na zaune ka, ta shi kaje kace ma Bala mun gama,” ta fada tana kunburi ita an mata dariyar bata da qiba, aiko sai da mubarak ya kai qofa ya juyo yace ” Farha ni dai kk zaune ni sai na mutu, qashi zaki soka min,” da gudu ya fita yana dariya zata bishi Lamyah ta riqe ta,” haba princess din Bala, ina zaki da gudu haka ai sai Bala yace baki da aji,” ” to laifij waye in an ganni ban da ajin ? Ba ke kk fadan haka a gaban shi ba gashi nan yai hadda, ko batan wasali baya yi? Ni dai gaskiya asan ya za ai dani, ko kuma kema ki fara slimming cinyoyin da qirjin ki su dawo kamar nawa,” ta qarashe maganar cike da shagwaba, Lamyah ce ta shanye dariyar ta ta kamo ta tana buga bayan ta,” kar ki damu yanda kk so haka za ai, tashi mu tafi,” miqewa tai cikin yanga, kamar zata balle, Lamyah ce ta saki tari, mqi hade da.dariya, aiko cikin fushi fuuuuu tai waje, zama tai gefen kujera tana ta tiqar dariyar ta, sai da tai ta qoshi ta gyara fuskar ta suka fita, lokacin tara ta kusa, a hanya ba mai kula kowa, Bala yayi iya qoqarin shi darling din shi tai magana taqi sam,Lamyah ya zabgawa harara ta madubi, daidai sun hada ido,” Whatttt???? Me nai kk hararata,” ” nasan laifin ki ne koma me yasa Farha fushi, ga shi nan kin ja min,” dariya take son yi amma bata son ta bata ma farha rai again,dan yanzu kam tasan tana gab da kuka, kuma tana son ba Bala amsa, haka ta shanye dariyar ta kawai ta koma gefe tana kallon titi, hannu ya sa ya riqo hannun Farha wadda ta zame da sauri, ta na kallon shi, da ma’anoni masu yawa, tsayawar motar a filin da suke parking ne ya janye hankalin ta daga kan shi, da sauri ta kama murfin ta fice, Faisal da Ameenullah su kuma sun fito, suna hira, kawai sai Lamyah ta tsinci kanta da faduwar gaba, like wise Ameenullah, shi ko harda dafe qirjin shi yai, “Man lfy?” ” ba komai haka nan naji qirjina na bugawa da sauri, kuma zuciyata ta tsinke sosai Allah ka jiyar da mu alkairi,” amsawa faisal yai yana kallon gefen su, inda suke takowa cikin yanga da qasaita irin na hadaddun mata……..
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘ YAR RAWA. ????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button