
BY HAERMEEBRAERH
page 13:
Tunda suka qaraso da Ameenullah ya hada ido da Lamyah, gaban shi yai wani irin bugawa, wani irin abu yake ji daha qafar shi zuwa kan shi, itan ma hakan take a wajen ta, kallon kallo sukai, kafin su dauke kai ga barin kallon juna, Farha ce tai fari tace,” Hey handsome, ya kk?,” banza yai da ita bayan ya mata kallon tara saura kwata, wayar shi ya zaro yana daddanawa, yana kallon tsohuwar Numbern Lamyah, dan guntun tsaki Farha tai wanda ya sa Ameenullah ya kalle ta da wani irin kallon da yasa ta ja hannun Lamyah tai gaba, tace ma Faisal,” ka same mu a ciki in wannan dan rainin ya barka, ni kwata, bana son yana dawowa gaba daya baida sabo, dan ma ya samu mace kamar ni tana kula shi yake wani basar wa, dadin abun ina da saurayi, ba a kasuwa nake ba ehe,” ta fada lokacin da take kada yan qananun duwais din ta, Lamyah kam yau tana cikin dariya ne sosai, amma wannan karon duk da dariyar da take ji, gaba daya ta kasa yi, saboda yanda take jin mutuwar jiki, bayan sun shiga ne Farha ta kamo hannin ta ta fara cire mata Abayar ta, ,” Gurl me ke damun ki ne? Gaba daya naga jikin ki yai sanyi, ko dai wani abi na miki?” ” A’a ni kam baki man komai ba haka nan naji jikina ya mutu, amma ba komai da naji taken mu zan ware na san,” ta qarasa cikin murmushi, Farha ce ta qarasa mata make up, zata ce Lamyah kenan Faisal ya leqo, sai ta sauya da sunan da tai register da shi wato, Laila, ,” lokaci yayi me kuke yi ne har yanzu?” ” gamu nan zuwa” miqewa sukai a tare suka fito, kida aka baza masu nan da nan Lamyah ta ware, rawa take kamar ba qashi a jikin ta, juyi take kamar wata tarwada, guqun nan kamar zai karye saboda girgiza shi da take, haka ma qirjin ta, ga gashin ta da ta baza in tana rawa yana gaba yana baya, ko ta maoda kai gefe, abun sai wanda ya gani, Ameenullah da ya leqo fadama Faisal zai kwanta ko ya dawo kar ya neme shi ya tsaya kallon ikon Allah, baki ya bude bai ma san yayi ba, kallon ta yake kamar idon shi zasu fado, wani iri zuciyar shi take kamar ya ruga da gudu ya dauke ta ya boye haka yaji, dukan kafadar shi yaji anyi, ” Man ya dai, ko ka gano abinda na hango maka ne?” Faisal ya fada cike da tsokana, daure fuska Ameenullah yai,” malam dama na zo fada maka ne ka wuce dakin ka kar ka damen in ka dawo, bacci nake ji,” kawai ya sa kai ya wuce ” Sunan ta Lailah,” iya abinda Faisal ya fada kenan yai gaba, maimaita sunan Ameenullah yai tayi har ya isa dakin shi, kwantawa yai ringingine yana ayyana abubuwa da yawa a ran shi, ” Lailah, Lailah kin bata sunan ki, na tabbata wannan ba zata wuce sa’ar Lamyah ta ba, Allah sarki Lamyah, duk in da kk Allah yare man ke, ya kiyaye ki daga fadawa halaka,” hawaye ne ya gangaro mai, amma sai me rufe idon da yai hoton Lailah yake kallo, miqewa yai da sauri ya leqa window , aiko yana budewa tana daga kanta, hada ido sukai daidai zata shiga mota, saurin shigewa tai, dan bata zaci zata gan shi ba,saboda gaba daya da tinanin shi ta gama rawar ta, wurga ido take dama taga ina zata sake ganin wannan kyakkyawar fuska? Aiko yana sakewa ya dafe qirji yana murmushi, itama murmushi tai data zauna, Farha ce ta fara zuba kamar kanya, Bala na amsa ta cikin jin dadi, dan dazu ta tsume bai sami damar magana da ita ba, har suka isa gida Lamyah na tina handsome din da ta gani dazu.
A qa’ida kwana biyu suke a tsakani kan su koma rawa, Allah Allah Lamyah take lokacin komawar su yayi tai tozali da wannan kyakkyawa, haka ta bangaren Ameenullah, roqon shi Allah ya bashi ikon daurewa kar ya tambayi wannan sarkin surutun inda zai ga Lailah yake. Bayan ta idar da sallah ne ta yi karatun qur’ani, Farha da Mubarak ne suka zo da nasu qur’anan suka zauna suka tankwashe qafafun su, qari tai masu kamar kullum bayan sun kammala sukai ma iyayen su addu’a, bayan sun idar ne kowa ya miqe yai dakin shi, kwantawa sukai dan su koma bacci, amma kamar daren jiya,haka bacci ya kasa daukar ta, Farha ce ta juyo tace,” Lamyah wai me ke damun ki ne? Gaba daya tin jiya na kula baki da walwala, ko wani abun na miki ne ki sanar dani dan Allah,” ta qarasa idon ta ya cika da kwalla, Lamyah kamo hannun ta tai da sauri tana girgiza mata kai,idon ta cike da hawaye, nan da nan suka fara kwarara,” Farha ban san meke damuna ba, amma ni dai nasan ina missing Abii na da Ammii ga Yah Amee shiru, ba mai nemana, in ma sun neme ni ba zasu ganni ba, zuciyata ta fara raya min na je neman dangin mahaifiyata , dan na samu wasu a kusa da ni da zasu zama majingina a garen ,”kuka take sosai, zuciyar ta na quna sosai, ga shi ba zata iya sanar da Farha me ke damun ta game da wannan Ajnabin da ta gani dazu ba, tabbas zuciyar ta ba wanda take so illa Yah Amee din ta, amma wannan baqon lamarin da take ji game da wannan bawan Allah yana bata tsoro, kukan ta ne ya tsanan ta, Farha sarkin surutu ba baki itama kukan take, haka Tani ta isko su,” me zan gani haka yarannan ku sa juna gaba kuna kuka, ko mai yai zafi maganin shi Allah, ku sauqaqa wa zuqatan ku ko kun samu sauqin ko me ke damun ku,” a tare suka fada jikin ta suna kuka, bubbuga bayan su tai har suka samu sukai shiru, ” to yammatan Tani, ku zo muje a hada abin karyawa,” miqewa sukai, suka bi bayan ta suna goge fuskokin su.
Tanj ta kasance tana koyar da su wasu abubuwan da ya zamana basu iya ba, dan kar au tashi ba su san komai ba, a da Lamyah tana ganin hakan a matsayin aikin wahala, tin da bata saba ba, amma da Farha parrot ta zauna ta mata bayani, a cikin bayanin nata ne, take fada mata a nan in ba ta iya komai ba, wata zata karbe mata miji, ko da Yah Amee din ta ne kuwa, habaaa tana jin haka hankalin ta ya tashi, kishin su na Larabawa ya motsa mata, a ranar ta wahala wajen koyon girki, ta yanke ta qone,amma duk bata ji, burin ta bai wuce ta ga ta iya komai da zai ja mata hankalin Yah Amee din ta, a yanzu tana matakin tsakiya, na koyon abubuwa, Tani kuma ta zage damtse tana koya mata abincin kala2 na qasashe daban daban.
sai nace Lamyah girki adon mace wadda ta iya ta huta, wadda batabiya ba ta sha haushi, mata a dage a iya girki, da sauran abubuwan da suke saka mace ta zama qasaitacciyar mace a wajen miji da ko ina
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘YAR RAWA. ????????
BY HAERMEEBRAERH
page 14:
Yau tin safe Lamyah take cike da farin ciki, zuciyar ta fes, ” Mummy why ar u so excited ? ” ” yeh what’s new?” ” kunji min mutane kawai ku sani gaba da tambaya akan mutum ba zai farin ciki ba kenan?, to nothing new, kawai yau ina jin nishadi ne saboda RAWA, kema kin san ita ke sani nishadi ko?” Farha tabe baki tai tace ” Imm bari kiga na tafi wajen Bala mu sha hirar mu saboda jiya ya wuni school, bamu zanta ba, ina son fada mai how much i love him, ina son na ga kyakkyawar fuskar shi ko hankalina ya kwanta, qawaye na suna ganin a yanda nake bai dace da ni ba, ba zasu gane mene ne so ba, so ba ruwan shi da waye kai, wana matsayi ka taka a rayuwa, wace kala ce fatar ka, ya tsahon ka yake, ko ya jikin ka yake, da ya tashi shiga zuciya baya kwankwasa, fadawa yake cikin zuciya, ba notice,” tabbas Lamyah ta fada tarkon son baqon da bata sani ba, dan na tabbata in da dane wannan cakwaikwaiwar take wannan zuba zamcen sai ta katse ta, ko ta bar wajen , amma wannan karon lumshe ido take tana jin tabbas in haka ake so to itama ta fada tarkon shi a farkon ganin ta da wannan bawan Allah da ko sunan shi bata sani ba, Farha ce ta katse ta, ” Kar dai ki ce man tin da na fita har yanzu haka kk baki motsa ba, naje Bala baya nan Baba ya ake shi,” ta qarashe cikin zumbura baki, kwantar da kan ta tai akan cinyar Lamyah ta juya bayan ta, Lamyah ce ta dora hannun ka akan ta tana shafawa,” Farha me zai hana wani satin Bala ya kaini Rimin Gata? Na matsu na ga dangin Ammii na yanzu ko na gaggauta wucewa Niger neman Yah Amee, saboda Farha my heart us trying to betray me, tana son kuma ta ci amanar Yah Amee, tabbas in abinda nake ji ya tabbata zan shiga uku, Farha zan shiga matsananciyar damuwa, domin zuciya ta bata kasamce daga cikin masu adalci ba,” Farga dake kwance tana lumshe ido jin kalaman Lamyah sai zuciyar ta tai sanyi, gaba daya tausayin ta ya kama Farha, musamman da taji ruwan hawaye a kafadar ta, miqewa tai ta zauna kusa da Lamyah sosai ta jawo ta ta dora kan ta a kafadar ta( duk da dai ba wani tsokar arziqi sai dai ma ta soke wa baiwar Allah kumatu da qashin kafada????) lallashin ta ta yi sosai sai da ta gama kukan ta sannan tace mata ” Lamyah ki sani Allah baya dorawa rai abinda ba zata iya ba, wannan wa’azin ki ne, ina son kamar yanda kk fadakar da mu kullum ya zamana kema kina saka maganganun ki a cikin aiki inshaa Allahu zaki samu komai da sauqi, don Allah ya hore maki sanin daidai da kuma abinda ba daidai ba, sai ki gode mai ta hanyar amfani da su din, ina roqon Allah daya yaye maki damuwar ki Lamyah na,” da Ameen ta amsa, sai taji zuciyar ta wasai, tashi sukai suka shiga daki, Lamyah ta fara fiddo masu da kayan da zasu saka da dare, wasu skirt ne masu hade da dan gajeren wando a ciki, skirt din iyakar shi guiwa, sai rigar da ba ta wuce masu cibiya ba, iri daga multicolor ne kayan, kusan kowacce kala akwai a jiki, amma ya sha adon stones, masu kyalli,n golden a jiki,” wai ban gane ba kin kwanta?” ” to mi zan, dan Allah barni na dan taba bacci kafin daten yayi, yau na gaji haka kawai nake jin gajiya , kewar Bala ta cikan zuciya, rabona da shi tin shekaran jiya fa,” juyi tai ta kwanta abinta, Lamyah ta dakko masu takalman sunda zasu saka nan ma ta aje, sai abayar da zasu dora, tashi tai ta tafi kitchen ta dakko cucumber ta markade bata wani saka ruwa ba amma saida ta yanka qanana sosai, tana fara markaduwa sai ta debo madarar shanu, da zuma sannan ta saka kwai a ciki, sai dan tomeric powder da cinnamon powder da ta zuba, qara markadawa tai saida suka hade tsaf, sannan ta juyo a dan mazubi, dakin su ta koma ta dakko masu zannuwan da suka ware don gyara jikin su, dadawa Farha duka tai a yar cinyar ta da ihu kuwa ta miqe, dariya ta saka , ta miqa mata zanin, harara ta banka mata ” dan cin zali kawai ina kwance har bacci ya fara dibata, ki makan duka a cinya sai kin lotsamin ita,” dariya abun ya ba Lamyah sosai,” me din zan lotsa kamar wata katifa? Ke ai sai dai a karya ba dai lotsawa ba,” Farha ce ta biyo ta akan sai ta rama kuwa tun da abun haka ne, aiko suka fara zagaye dakin, da Lamyah ta samu dama sai ta shafawa Farha wannan hadin , sannan ta kwasa da gudu, a haka har suka gaji suka zube a gado, suna maida ninfashi, bayan sun sha dariyar su ne suka tashi kowa ta shafe jikin ta fea da shi,” wai ni wannan kuma na meye, kusan kullum sai kin fiddo da sabon abu, duk lokacin gyaran jikin mu yai sai naga sabon abu kk fiddowa ina kk koya?” ” a gaskiya a kwa wadan da Ammii na ta koyan, akwai wadan da da kaina na qirqira,” ” gaskiya na gode dan i want to look beautiful for Bala today, sai ya rasa gane wacece wannan, shin canjo ni akai,” sai ta dira wani tsallen murna, Lamyah kada kai kawai tai tana murmushi, dan Farha na bata dariya, ko dake shima Balan ya mato akan ta ba kadan ba,dai dai sun gama ne Mubarak ya shigo, a duniya in yaga su Lamyah sun yi abunnan tsoro ke kama shi, aikk zaro manyan idon shi yai waje ya kama baki, juyawa zai da gudu ya fice aiko abokiyar fadan shi ta cafe shi, shafa mai tai a kuma tu, yana bude ido sika hada ido da fuskar ta da tashi, ya kwalla qara, yana qoqarin sauka, ta hana shi, sai tsorata shi take, Tani ce ta shigo ta karbe shi, ” yaro gobe ma ka qara min rowar chocolate din ka, in ba sai na ma wanda ya fi wannan ba, ko kai kadai kk son yin qibar,” ” to laifi na je da komai kk ci baki qibar,” ya fada cikin kuka sannan ga tsoro ar the same time, ai ko cikin fushi ta zabura zata damqo shi ya kwalla qara yace ” Tani dauke ni kar ta kama ni,” ba Farha ba har Lamyah dake gefe tana sha’anin gaban ta sai da ta sa dariya.