
Lamyah bata samu matsala ba a kwana hudun da tai a gidan mai gari, sai dai abu biyu kr damun ta, har yanzu ba’a hada ta da dangin mahaifiyar ta ta ba, balle kakar ta, sannan wannan dan mai garin fa na takura mata, da nacin kallo da magana, yauma zaune take tana shan Tea, ita da Mubarak, ya shigo, ” A’a qanwata, me kk ci haka, ba gayya , miqa hannu yai ya karbi cup din hannun ta, ya daidaici inda ta saka baki, ya sha, tare da lumahe ido, a ranshi yana ayyana wataran fa bakin ta zan ji a nawa, da sauri ya bude idon shi, dan gudun. Kar ai abin kunya, sai yaji ma kamar ta gane me yace, kauda kai yaga tayi, cike da kunya tace, ” Yah Musaddiq, ragowa ta fa ka shanye, kuma ni ai ban qoshi ba,” ta qarashe cikin shagwaba, daidai nan Inno ta shigo ta same su, wani kallo tai wa Lamyah ta kauda kai, ta shige daki, kwalawa musaddiq kira tai, ya miqe yana cewa Lamya ta bashi 2mnts, kada kai tai tana mamakin yanda yake rawar qafa akan ta, ” kaii me nake gani a can, wanan yarinyar mai kama da ‘yar tsana tana yi maka,” hade fuska yai sosai, dan yasan in yai lakwa2 wannan karon ma ba yarda za tai da zabin shi ba, a kullum tana mata biyayya amma bata gani, sai tai ta manna mai jikar qawar ta, Delu, Saddiqa, har wani kirari suke mata na Saddiqa amanar Musaddiq, ita kuma tai ta yanga tana rawar kai, ‘yace a wajen Hamza, wanda ba abinda ya sani sai lalata yaran mutane, qanana, shi dayan tsabar shaye2 bama a san in da yake ba yanzu, kwata2 Saddiqa bata ji, bin mazan unguwar su kuwa kamar karya, ciki ta zubda shi yafi a qirga, ga ta ba arabi ba boko, in musaddiq na wannan complain din, Inno na ce mai nima ban arabin ba ban bikon ba kuma na haife ka, ya kanyi mata kuka akan ta barshi da zabin yammatan da yake kawowa na mutunci amma sam haka zata qeqasa qasa taqi, ga shi mai garin ma shi kanshi shakkarta yake ji, ” da kai nake magana ka hade gira, ko kaima kanzama dan zamanin ne?” ” ni dai a gaskiya wannan karon Inno dole a barni na zabi abinda nake so, dan wannan ma ba kamar sauran bace, inna hakura a bayan wannan karon ba zai yu ba,” ya miqe cike da fushi ya bar dakin, kama baki tai, amma shakkar dakatar da yaron ta shige ta, dan ta san shi yaro ne mai biyayya, amma yau akan mave gashi yana neman juya mata baya, a haka ta ji ta tsani Lamyah, tsana mai tsanani. Yau ne da yamma Mai gari ya sa aka kira mai delu da Hamza, dan su shaida dawowar Yar uwar su dan sauran qannen mahaifin ta wasu sun riga mu gidan gaskiya,masu taurin kan ne ke da rai, take suka ce ai su sun ma manta da waye Muhammadu bare zuri’ar shi, Malam Abubakar ne ya zo shima idon shi yai ja alamar yai kuka sosai, kukan tinawa da Aminin shi, sun halarta a wajen, in da mai gari ya masu bayani, Musaddiq na gefe, amma hankalin shi na kan Lamyah, wannan ne yasa daga Hamza har Delu sukaji ko suna da niyyar karbar ta sun fasa, dan da ganin wannan kallon na so ne, yanda Musaddiq yaqi diyar su da can, yanzu tsanar ta zai, duk ko da kyaun da Allah ya mata itan ma, haka su ma suka nuna to dangij uban ta na haqiqa sun qi karbar jikar su balle ita, meye hadin su, dan ta kuma ba yanda zai ya dau wannan balagaggiyar ta kai gidan shi, kuka kam Lamyah tin da aka ce Bappanayen mahaifiyar ta sun qita ta fara shi, Malam Abubakar kam yai kukan rashin aminin shi, sannan yai masu barka da zuwa sosai, ya karbe su hannu bibbiyu, haka aka tashi taro Lamyah bata da madafar dangin uba.
Niger
” Haba Ameenullah, kaifa na kasa gane alqiblar ka, kwanaki har ka amince zaka auri yarinyar nan amma yanzu sam kace a’a akan me, to bari kaji, ka sauya tinani,san ba zamu zama qananan mutane ba, Lamyah ko ko yau ta bayyana na maka al’qawarin aura maka ita, amma wannan yarinyar nan da wata biyu kamar yanda mukai alqawari za a aura maka ita, Naufaliyya ya rinyar kirki ce, kusan ni dai ban taba jin ance ga matsalar ta ba, dan haka kai hakuri ai wannan al’amarin,” tinda Baaba ya fara magana bai ce komai ba, haka Momma ta dora da nata,itama bai tanka ba, ba abinda yake hangowa face kukan Lamyah dake taba ran shi,kalaman da ya mata yasan basui daidai ba koda karuwa ce, balle Faisal ya gaya mai ko wanne daga halayen ta, amma tsananin kishin da yake halittar shi ne ya hana ya kasa daina hango ta tana tiqar rawa a gaban qatti, wani ma yasan in ya je gida da tinanin ta yake bacci, yana tina hakan yaisaurin daga kai cikin tsananin kishi yace,” Baaba ni ku auran koma wace, amma dan Allah ku nemo man Lamyah itace cikon rayuwa ta,” ya qarasa cikin hawaye, dan ko so da kishin waccen YAR RAWAN zai kashe shi ba zai aure ta ba, ba zai taba zama inuwa daya da ita ba……….
Readers i am so sorry for the late update, those that ar worried about not seeing my post here i come???????? thank u so so so very much for the love, i have been busy this past 2 days, but inshaa Allah, i will try as much as i can to update it for u, thank u so much again. HAERMEEN HAERMMAERH NA SON KU XX❤
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘ YAR RAWA ????????
BY HAERMEEBRAERH
page 17:
Jitai an ja ta baya, dubawa tai taga Musaddiq ne, saka yatsan shi yai a kan lips din ta, idon shi taf hawaye, ” da gaske kk baki so na? Son yaya da qanwa kk min? Kin amince na auri Saddiqa? Ko da bana son ta? Ki duba wannan lamarin fa ki gani ba a min adalci ba kwata2, in aka hada ni da wannan yarinyar sauran mazan qauyennan, ni na san nayi ‘yan mata kala2, kuma soyayyar da ake gudanar wa ta zamanin nan na taba a baya, amma daga baya da ilimi ya shigeni na tuba, dan Allah ki yarda na aure ki,” ” Yah Musaddiq ba macen da zata ce bakai mata ba, amma ni matsalar da aka samu zuciyata cike take da rudani, ka tausaya min nima kar ka qaran akan na da, ka barni na koma inda ake mutunta ni, kaima ka fada ka taba soyayyar zamani amma ka tuba, to itama in ka aure ta da ilimin da kk da shi zaka ribace ta ka daidaita mata rayuwar ta, ka taimaka min ka ceci ‘yar uwata, ka tina ita daya nake da ita a dangin mahaifiya ta da nake saka ran zan iya hada kai da ita, in ta shiryu, mu na sada zumunci a tsakanin mu, wannan jihadi zakai, tinda in kyau ne itama ba a baya take ba, kusan da kadan zan fita, halaye ne kawai bata da su masu kyau kai kuma zaka iya taimaka mata, plssss for me?” Wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, idon shi ya kada yai jawur, ga qirjin shi dake dagawa saboda tashin hankali, ji sukai an saka ihu, da gudu suka fita, Farha suka gani ta shaqe Inno, tana dima mata duka, ” an gaya maki jaka ce ita da zaki mata abinda kk ga dama, meye hadin ki da ita da kk da ‘yancin ci mata mutunci haka, tinda nake da ita nasha ganin kukan ta ban taba jin irin na dazu ba, jakar ki ce da zaki sata a wancan madafin baqiqqirin, sai ko yau kin shiga na rufe ki in yaso iya azabar da kk ji wataqila kin gane Lamyah tana jin fiye da haka, tinda ko risho bata taba kunnawa ba,” kakari kawai Inno take, da kyar ta furta,” ‘Yannan daga ina kk diro kamar aljana kk dukana, in mutan boye ne kui min rai ba zan qara ba, dama da ganin yarinyar nan jinsun su ce, na dade da zargin hakan, dan kyaun ta ya fi gaban namu mutane, ku taimaka kui min rai,” Musaddiq ne ya isa da gudu ya kwaci Inno da kyar, dariya a cikin shi dan jin kalaman ta kamar ta kashe shi,amma yasan bai isa yin su ba,Lamyah kuwa wajen Farha tai dake ta masifa tana yarfa hannaye, fadawa jikin ta Lamyah tai, tana kuka, ran Farha qara baci yai ta banbare ta kuma yunqurawa kan Inno da sauri Lamyah ta riqe ta tana girgiza mata kai, ” Farha ya isa mana, Main tek hain, mu je gida, ku dauke ni a nan garin, kui nesa dani, bana son qara dawowa in da ba su qaunata, ina son zuwa neman Yah Amee, in na samu Yah Amee rayuwata zatai dadi, komai na zai daidaita, Bala ku zo mu tafi pls,” kamo hannun Mubarak tai dake taya ta kuka, fita zasui Farha tai dan zburar nan a gaban Inno, tako kurma ihu tana a ceceta, Farha ta dan sa yatsan ta babba ta shafe hanci da shi, tana wani baubbudawa, gaba daya Inno ta tsorata da lamarin wannan yarinya, wajen mai gari Lamyah ta so zuwa ta mai sallama, amma sam Farha tace ba za a ba, da dake mata iskanci ba yazama mijin tace ba bai hana ba me zasu je mai? Da kyar Lamyah ta shawo kan ta sukai mai sallama, ya basu hakuri sosai, Malam Abubakar ma sin yi sallama, a take a gaban Lamyah Misaddiq yace a sanar da su Delu ya amince zai auri Saddiqa, nannda wata daya, kowa yai murna amma ban da shi, zuciyar shi kamar garwashin wuta haka yake jin ta, haka suka tafi bayan musayar lambar waya, duk da Lamyah taci alwashin ba zata qara sati a Nijeria ba Nijer ta nufa.