NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A kwana a tashi a sarar mai rai( Allah ka bamu sa’a ka sa mu cika da imani, Allah ka sa mui kyakkyawan qarshe ya rahman) a yau aka daura auren Bala da Farha akan sadaki naira dubu hamsin, wanda Baaba Mus’ab yai ma Farha waliyyi, Baba mai gadi ya karba wa dan shi auren Farha cikin murna da jin dadi, mahaifiyar Bala ta halarci auren, bayan kowa ya watse ne, aka bat Lamyah da Mubarak, da Farha, sai Tani dan itama a gidan zata kwana yau, kuka kowa yake kamar wadan da akai wa mutuwa, yau Mubarak ne jikin Farha lafiya laou ba rikici bate doke2, ya qanqame ta yana ta ta aikin kuka, Tani ce tai jarumtar miqewa tace,” ku mui hakuri,mu zamu ba kan mu hakuri, tafiya ai ba mutuwa bace, za a na gana wa duk sanda aka so, an bamu adireshin ku na can, ga lambar waya, sannan kuma gidannan dai yana nan ba inda zamuje dan zan ci gaba da aiki anan, duk sanda taso ganin munza ta zo gare mu, dan haka kumu tashi mu fara hada kayan nan, ” miqewa sukai jiki a mace suka hau hada kaya, sai da suka gama tass Lamyah ta je inda ta adana jakar da Abee ya bata ta dakko, ta dora kan akwatinan kayan su, wankan kwanciya sukai, kowa taje ta kwanta, ranar farha da Lamyah a manne da juna suka kwana, cikn dare Farha tai ta masifa a cikin bacci wai ba za a tafi mata da qawa ba, Lamyah tai murmushi mai cike da hawaye a idota sauka gadon tai taje tai alwala tai nafil2 tai addu’o’i kamar yanda ta saba yi a duk sanda wani abu zai sameta, sai ta mai addu’ar neman zabin Allah.

Da safe kam an sha kuka da bori wajen farha, da kyar su Lamyah suka bar gidan, Bala ma sai sharce kwalla yake, ga tausayin amaryar shi,ga kuma tausayin su duka, na rasa uwar daki mai adalci.

NIGER REPOBLIC

………………………….????
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘YAR RAWA ????????

             BY HAERMEEBRAERH

Page 19:

Da gudu ta qanqame Momma, a tare suka fashe da kukan farin ciki, kewa, da kuma rashi, Baaba bai hana su ba, sai da suka gaji dan kan su sukai shiru, sake Momma tai ta fara leqa makeken parlon tana kwala ma Yah Amee din ta kira cike da farin ciki da zumudin ganin shi, a sannan ne fa hankulan iyayen biyu ya tashi, dan tabbas in Lamyah taji yai aure ba zaman lfy, to amma ya zama dole su sanar da ita, kamo hannun ta Momma tai tana shafa fuskar ta cikin kulawa,” ‘yata ki ci abinci, ki wanka, ki dan huta mana sai kiji ina Amee din ki yake,” girgiza mata kai ta soma, idon ta cike da kwalla sannan tace,” A’a momma, ni ina son na gan shi yanzu, ina son na fara bashi daddadan labarin da ya dade kunnuwan shi na son su saurara, na gaji da aje wannan sirrin dake raina, abubuwa da dama na yawo akaina,ina cikin rudani, bana son wani matsala ta faru daga bangare na,” a hankali Momma Aishaa ta share hawayen da ya gangaro mata dan tabbas ta san yau akwai daru, sun so just for today, Lamyah ta huta, kafin a bata labarin komai amma inaa……….. ……

Ta bangaren ango da amarya kuwa ana nan ana kan aikin da aka saba, da kyar ya samu ya sulale gefen ta, yana maida nunfashi, kamar wanda yai gudu, zufa kawai yake kamar manomi, ita ko sai wani yauqi take, ta dora kan ta a qirjin shi qafar ta a kan tashi, hannun ta na wasa da gashin qirjin shi, a hankali can qasan maqoshi ya fara magana,” ki shirya na kai ki gidan mu, ku gaisa da su Momma, dan ni nan da kwana hudu zan koma Nigeria, kuma nan gida zan barki, amma in kina so, zaki iya na maida ki gidan mu, ki zauna bangare na har na dawo, dan nan ke daya ba zaki so ba,” wani irin a bu ne ya tokare mata wuya, yanzu duk dadin nan da take kwasa tafiya zai? Ita ya ma za ai ta barshi tafiya shi daya yai watanni baya nan? Ya zata iya sabo da rashin shi bayan ya saba mata da jikin shi? A gaskiya da sake, ko ya tafi da ita ko ya maida ta gidan su, kaiii anya zata iya zama kuwa? Wadannan tambayoyin ne ke mata yawo a kai, sai da taji ya shafo gefen cikin ta, wani dan juyi tai a jikin shi, yana ganin haka ko ya qoqarta miqewa, ya san halin ta so take su koma ruwa,” ki shirya bari na je na shirya a dakina zan jira ki in kin gama ki mun magana,” ai kan tai wani yunquri ya fice, yana shiga dakin shi yai ajiyar zuciya, ya danna key, toilete ya shiga, ya sakar ma kan shi ruwa, zuwa tai qofar dakin shi din ta rufe sannan ga qarar ruwa, tsaki ta ja mai qarfi ta juya ta koma, toilete ta fada itama ta shirya, cikin wani material mai tsada da kyau kalar baqi mai ratsin yellow a jiki, tai kyau daidai ita, ya gama shiryawa kenan suka jero suka dau hanyar gidan su.

……… ” Baaba ku fadan ina Yah Amee na yake pls, i really want to see him,” ta qarashe cikin hawaye masu dumi, sallama suka ji gaba dayan su suka juya, gaba dayan su su biyun ido suka zaro a tare suka nuna juna,” kaiiime kk yi anan?” ” keee me kk yi anan” nan take yace ” ke zan tambaya,” ” ko dai na tambaye ka ba don nan gidan mu ne, ga Baaba na da Momma ta, kai fa me kazo yi?” Wata dariyar rainin wayo ya saki, sannan ya wuce ta ya kamo hannun matar shi sukai ciki suka zauna kan kujeru, qasan zuciyoyin su ba qaramin murnar ganin juna sukai ba,dan zuqatan su sun yi kewar juna sosai, Baaba ne yai ma Momma nuni da suma su zauna, zama sukai Baaba yai gyaran murya, sannan yace” yanzu dai na ga alama kamar kun san juna , amma ba damuwa, komai zai zo da sauqi da ikon Allah, ammmmmm Ameenullah ya iyalin ? Ina fatan kuna nan lfy?,” kan su Lamyah ya kulle sosai, wannan ba abun da za ai shiru bane, a ina Baaban shi ya san wannan tijararriyar? Har take ikirarin su a iyayen ta? Amma zai bi yanda suke so, amsa mai yai, da tana lfy, suka gaisa da Momma da itama abun ya mata daban, kamata yai a zauna ai ma kowa bayanin juna, sannan a warwarw komai amma Baaba ya kawar da zancen, bayan gaishe2 ne da akai, wanda in da sun kula da Naufaliyya zasu ga yanda ta cika tai fammm,dan zuciyar ta ta gama amince wa zama anan in yai tafiya, a da kam tana tantama, amma yanzu ta amince, musamman da taji Baaba na duqunqune zance, wannan mace da kyau kamar ba jinsin mutane ba, ina za ta yarda ta zauna a gidan su mijin ta, salon mijin ta ya na zuwa gaida iyayen shi tin bai son ta ya kyasa? Inaaaa ba da ita ba gada a qabari, sannan ga dikkan alamu sin san juna ma, tabota taji an yi, ta juya sashen shi, taga yana mata nuni da Momma, duqar da kai tai ta gaida ta, itama amsawa tai, idon Lamyah na kan na Ameenullah, shima haka, ko wanne da abin da ke saqawa, shi tashi cike take da farin ciki zullumi, fargaba, da rudani, ita kuma tata cike take da tsananin tsoro, kar dai ace wannan ne Yah Amee din ta, ga shi da mace, lallai da ta mutu, abu biyu sun hadu mata kenan, ga shi shine Yah Amee din ta, sannan kuma mutumin da yai mata satar zuciya ba zato ba tsammani, “Oh yau ya zan yi” shine a bin da ta furta ba ta san ya fito fili ba, kallon ta kowa yai, nan take ta tsume ta dau jakar hannun ta ta koma kusa da Momma, kwantar da kan ta tai kafadar ta tana shagwaba,” Momma zan shiga na watsa ruwa ina ne dakina?” ” Ya kama ta kam tashi mu je na nhna maki,” tafiya suka kama, mamaki ya kashe Ameenullah, na ina suka samu wannan daha zuwa ji uanda take neman kwace mai waje, tabbb inaaa ba zai yu ba,da sake, to shi in ya tashi shagwaba yai a ina, wannan baligar da ta yi a kai ta daki ta cinye mai waje( ni kuma nace kai baka ji kunya ba risheshe da kai kace an cinye ma waje????????)bin su ya tashi zai yi Naifaliyya ta riqe hannun shi tare da murza cikin tafin hannun shi tana wani kashe ido, da lasar lebe, nan take yaji kasala ta rife shi, ya koma ya zauna, Baaba da ya kula da me ya faru ya girgiza kai yai layar zana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button