
Baaba ne da wasu abokan shi biyar, sun taru, shigowa ta qarshen zancen su naji, inda naji Baaba yana ” Alhamdu lilLAAHi, yanzu da ya dawo tinda an daura, sai a kai mai amaryar shi,” sauran ma murna suka taya Baaba na dawowar Lamyah da kuma daurin auren da akai kan in iso na Lamyah da Yah Amee ba da sanin shi ba, ba da sanin matar shi ba, sannan ba da sanin Amarya Lamyah ba. Sai dai nace Allah ya bada zaman lfy kuma a wanye qalaou.
Kwalliya ta ci ta kece raini, ta fito dakin ta zuwa kan dinning, inda Lamyah ta fito itama cikin qamshi da hasken fuska, dan ko mai bata shafa ba sakamakon yunwar dake addbar ta da kyar tai wanka, tai brush ta fito daga ita sai riga da wando iya kwaurin ta, gashinnan ta daure ta baya, yana lilo,sai agogo dake hannun ta, zama tai taja kujera,sannan ta fara zubawa kan ta abinci,ko kula da Naufaliyya batai ba, amma ita tin bude qofar ta ta qurawa hips da boobs din Lamyah ido, sannan ta. Kalli yanda cikn ta yake a shafe, kamar zai hade da baya, sai ogon gashinta da fuskar ta mai cike da kyau da kwarjini, kai lomar farko da Lamyah zatai tana daga ido sukai ido biyu, saurin kauda kaiNaufaliyya tai, amma dole ba yanda zatai Lamyah ta kama ta, yamutsa fuska tai, ta kalli Lamyah tace,” ke a garin ku haka ake in aka tashi a bacci, baki san ki gaida manyan ki na?” Wani kallo Lamyah ta bita da shi, dan tabbas Naufaliyya zata girme ta, amma ba zai wuce da ‘yan shekaru biyu uku ba, a ganin ta su kuma ba komai bane, dan ko Farha ta bata daya da kadan, ” a garin mu ba a koya mana gaida wadan da zasu zauna si qurawa wani ido ba har wanij ya dinga zaton ko ba kowa a wajen ba, har sai ya tsargu daga kallon maitar da aka bi shi da shi,” miqewa Naifaliyyah tai,” ke har ni zaki kalla ki cewa mayya, nawa kk? Wacece ke a gidannan? Waya tsaya maki da zaki kallen matar da a cikin gidannan ki zagen,” da sauri ta cire hannu za ta kaiwa Lamyah mari, Lamyah riqe hannun tai tace,” ko da wasa, ko da mantuwa, hannun ki ya taban jiki, da sunan duka bada niyyar tausa ba ko wani abu makamancin haka zaki sha mamaki, dan ni ba komai nake dauka ba, ina da son mutane amma daga lokacin da idona yai arba da naki naji bana yin ki sammm, dan haka ki kiyaye” jan kujerar baya tai ta wuce cikn takun isa da qasaita na macen da take taqama komai yaji a jikin ta, daki ta koma, abincin da bata ci ba kenan, yunwar ma sai taji babu, ita ko uwar gida an barta baki sake kamar qawuya, Lamyah bayan ta koma daki, ta sake nunfashin da take riqewa mai qarfi, ” Dama na iya fada? Dama zan iya rama abu in an min? Ko dai tsabar kishi ne kawai ya ja hakan? Don hae ga Allah ni tinda na ga wanda nake wa son da ban san sanda ya shigen ba da wata naji gaba daya na tsane ta,” juya kai tai ta kwanta a hannun dama, hawaye ne masu zafu ke bin kuncin ta, kaiii jama’a yau ina zata saka kanta? Komai sai tayi kamar zata same shi sai ya kufce mata.
A wannan yanayi kullum Lamyah da Naufaliyyah suke, har Naufaliyyah ta gaji, ta ce zata koma gidan ta, su momma basu hana ta ba, ta tarkata ta koma, Lamyah kam zuciyar ta kamar ta fashe, dan gani take ta koma suna tare da Handsome din ta, ” Handsome dina? ” wata dariya tai ta gefen baki, dan ganin wautar kan ta da kan ta, a haka dai lokaci na ta ja har Ameenullah ya dawo, inda nan gidan su ya fara sauka, ya isko Momma bata nan da Baaba, Lamyah ce kawai a gidan……….
Readers ga ango ga amarya fa????
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘ YAR RAWA ????????
BY HAERMEEBRAERH
*This page is for u Aunty Rumaisa, thank u so much for everything, I heart u da yawa, kin cancanci yabo mai yawa, kina matuqar taimaka min da an tambayi novel kina kusa an samu. Love u XX❤
Page 20:
Waqa ce ta Arabs kawai ke tashi, mai cike da matuqar dadi, ga duk mai sauraro, gaba daya ta cika parlon da kidan ta mai ratsa zuciyar masoya waqe2, ko Ameenullah da bai cika son waqe2 ba yau ya yaba wannan, ruwan da ta dakko daga fridge a kitchen ta ruqo tana qoqarin budewa, at d same time tana rawa, qugunnan kamar ba a jikin ta yake ba dan juyin da take da shi, ga rigar ta dake dagawa, sai dogon wandon da ta saka wanda ya matuqar matse mata qugun, ga gashin ta dake baje a bayan ta, amma tana rawar tana jujjuya shi, sake baki yai kamar dolo, qoqarin zama yake a kujera ashe bai ida qarasawa daidai wajen zaman ba, qarar faduwar Ameenullah ne ya firgita ta, ta kula da shigowar mutum, ihu ta kwalla, ta sake ruwan, nan take ruwan ya zube, shi kuma ya tashi yana wani basarwa, kar ta raina shi, gudu zata sa ta fada cikin ruwan, aiko ta bare baki ta fara kuka, da sauri ya isa gare ta, dan taimaka mata, ashe ma matsoraciya ce, ya ayyana a ranshi, wani murmushi ya sake, daga ta yai, tana ta faman kuka,” ke ki wa mutane shiru, kin kunna kida kamar kina gidan RAWAR taku, ko an gaya maki gidan mu gidan RAWA ne?” ” sadda kai tai qasa dan gaba daya yanzu wani nauyin shi take ji, bata kuma san meye dalili ba, sannan kullum hasashen ta na qara tabbatar mata wannan shine Yah Amee din ta, amma yau ta yanke shawarar tambayar shi ko shine Yah Amee din ta? Bata kula shi ba dingisawa tai zata kujera ta zauna, haba wani qara ta sake, saboda azabar da qafarta taji ta mata, dafe gini tai tana hawaye, sosai ya tausaya mata amma ai ita ta jawa kan ta, kama hannun ta yai yana bata rai, wani irin lantarki take jin na bin jijiyoyin ta, shi kuma ji yake kamar da dai duniya bai taba jin hannu ko jiki mai dadin tabawa irin na Lamyah ba, tinanin shi ya kawar, can qasan zuciyar shi na ci gaba da tuhumar wace ita? Dan in da wata mai mahimmanci ce a rayuwar shi da iyayen shi sun sanar da shi wacece, amma zai jira ya.ga zasu mai bayanin wanan mara kamun kan?zaunar da ita yai zai fice a gidan dan kula da yai ba kowa, ga Naufaliyyah da ta dame shi da kira, dada kama hannun shi tai ido na kwalla sosai, ta daga manyan idon ta dake zubda hawaye tace,” Yah Amee?” Muryar ta cike da rawa, a gigice ya juyo, yana kare mata kallo, yanayin yanda yake kallon ta ne yasa ta tabbatar wannan shine Yah Amee din ta, hawayen ta qaruwa sukai kamar panpo aka bude, shi kuma jikin shi har rawa yake ,” Lamya” amsawa tai kuma a lokaci daya ta miqe ta fada qirjin shi da gudu,rungume ta yai sosai suna kuka, Ammii n su da Abii suke tinawa sosai, kamar wadan da a kaiwa mutuwa a lokacin , sallamar Momma da Baaba ne ya katse su, da gudu Mubarak ya je gare su ya kama qugu yana kallon Ameenullah , irin kallon ina jiran qarin bayani akan abinda ka mata, da Ameenullah ya gane nan take ya daga hannu sama da nufin kare kan shi,” ba abinda na mata,” amma Mubarak bai dai na kallon shi ba, sai ma daga gira daya da yai ya gyara tsayuwa,” na rantse ban mata komai ba, rawa take ta dakko ruwa ta fadi, shine na taimaka na kawo ta nan, zan tafi ta riqen hannu ta kira suna na a nan na gane Lamyah ta ce shine ta rungume ni muke kuka, kuma ita ta fara riqen hannu, ta rungume ni, wait a minute, why am i even explaining my self to a kid?” “Whatch it man i am not a kid,nan gaba kadan zan iya zama Yayan ta, haka Uncle Bala da Farha sister suka ce,”Baaba da Momma da suka dade da fara dariya, tun Ameenullah na zuba bayani ne suka fashe da dariya sosai, Lamyah kuwa ba abinda take face kallon Amee din ta, shi kuma yana tinanin me ya hana iyayen shi sanar da shi ita ce? Amsa aka bashi,” Saboda ina son na aura maka ita kamar yanda na maka alkawari, amma ganin yanda kuka nuna kun san juna, kuma na san halin ka, tinda na ga inda ita da Farha suke RAWA, dan kan na dawo sai da na bincika komai, kuma an tabbatar man da irin tsanar da kk wa halayen ta, wannan dalili me yasa aka daura auren ku, ba da sanin ku ba,” wata zabura sukai, Lamyah yar qara ta saki saka makon fama in da ta bige dazu da tai, kallon ta Ameenullah yai da sauri, zuciyar shi bai san me take qunshe da shi ba, farin ciki ko disappointment ne? Dan gaba daya a yanzu ya rasa wa yake so ma, shin Lamyahn shi ko Laila YAR RAWA? ya zai yi , wannan dake gaban shi gaba daya baya son halayen ta, dan gani yake kamar ta gama biyewa mazan dake wajen rawar tasu, sannan kuma yana son ta a qasan ran shi, dan itace mace ta farko da ya fara jin komai akan ta, ha kuma natural son da yakewa Lamyahn shi, kai everything is complicating.