NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

A nata bangaren kuw, banda mamakin wannan aure da aka hada ba abinda take, tabbas Yah Amee ne burin zuciyar ta, shi take son kasancewa da shi, in da so samu ne ma, yau ace an hada su su tafi gidan su tare, amma inaaa son da take mai ba zata iya zama da shi da kishiya ba, ace su biyu suke morar shi, musamman in ta tina wace a matsayin mayat shi, wani kuka ta sake mai cin rai, ta hau dingisawa tai dakin ta, gaba daya tana tafe albarkatun jikin ta na motsawa, ko dan wannan jiki Ameenullah zai
yarda da auren ta,
amma tabbas bai san ranar da zai daidaita zuciyar shi akan ta ba.

Bayan ta tafi ne suka qarasa tattauna komai da Baaba, sannan suka saka lokacin biki da tarewa, nan da sati biyu, sallama ya musu ya tafi gida cike da tinanin da ya rasa ina zai saka su, yau duk maitar Naufaliyyah bata gane komai daga wajen shi ba, a haka ta hakura ta barshi, dan ta kula yau ba a daidai yake ba, gashi ita ko dan tarairayar nan bata iya ba, abinci wannan siyowa tai ta aje mai acikin abin take away din ko ta dan mayar wani wajen duk da yasan ba ita tai ba, dan bata iya din ba.

Tana shiga daki wayar ta ta ratumo ta hai kiran Farha,Farha ana can ana zubawa Bala shagwaba , taji waya na ringing, miqa hannu yai ya dakko mata ya amsa ya kara mata,da kyar ta amsa da ” Hello” ” ke dalla tashi zaune Lamyah ce,” ai da hanzari ta miqe har tana kusa kifawa dan murna, tsalle ta daka ta dale Bala, suna fuskantar juna, saka wayar tai a Handsfree, aiko Lamyah ta fashe da kuka, nan da nan jikin Farha ya hau tsuma kamar mazari,” wane dan kan uban ne ya taba ki a gidan, kaf din su ki min bayani, bana tsoron ko wanne gauta a cikin su, ni rana ce dafa su zan, maza ki min bayani,” Lamyah na jin haka ta tsagaita da kukan,” Dalla uwae mafadata ni ba abin da kowa ya min,” ” to me kk wa kuka?” ” Baaba ne ya… ya…. auran Yah Amee, “wata shewa Farha tai tana ta murza Bala, gaba daya Allah 2 yake ta aje wayar ,” to in banda ke meye na kukan,bayan mafarki ne ya zama gaskiya,” “a da ba? Yanzu yanda nake ji a zuciyata ba zan iya zama da shi ba” ” baki da hankali ne, me yasa ba zaki iya zama da shi ba?” ” yana da wata matar fa,” kuka ta fashe da shi, ta hadiyi wani abu mai daci a wuyan ta, Farha ce ta sake wani ashar, ” aure fa” daga Bala tai ta koma gefen shi,”wane qaton ne ya mai aure bayan an san ko ba jima ko ba dade zaki bayyaa agare su, to bari kiji kar ki yarda ki zaina da kishiya, ko ya sake ta ko a raba maku gida, ko kuma ya san abin yi, yo ni mutum ya min kishiya ma ba sai na babballa shi ba,” ta qarasa tana huci sosai, wayar Bala ya amshe yana gimste dariya, gaisawa sukai da Lamyah sannan ya fara mata nasiha mai ratsa jiki da jijiya, nan take Farha da ta cika tai fam ta sauka,” but still is not fair, yaushe ma Lamyahn tai girman zama da kishiya,” daga qarshe suka mata addu’a suka mata fatan alkairi, da alqawarin zuwa bikin nata, kashewa tai ta zame ta kwanta, hankalin ta gaba daya a tashe yake, sai dai kawai a kaso dari t samu sauqin ashirin.

Gyara ta sosai Momma ta fara,ba qaqqautawa, sai dai komai zata bata tana amfani ne da abubuwan mu na gida, kama da ga kayan lambu zuwa kayan marmari, sai kuma dangin aya, dabino, kwakwa, cukui, da zuma, ko gyaran jiki da natural abubuwa Momma ke wa Lamyah amfani, nan da nan ko kyaun ta ya qara fitowa, jikin ta tsabar kyau wani sheqi yake kamar macijiya, gaba daya Momma kanta ta san dan ta ya gama dacen mace anan.

Tin saura kwana uku Farha ta dira a Nijer, sun sha murna sosai ita da Lamyah da Mubarak, sai kace zasu tsaga gidan da murna, dangin Momma sun fara zuwa suma, kowa sai son barka yake da amarya Lamyah, a gefe kuwa amarya zuciyar ta cunkushe take, duk yanda farha ta so mantar da ita baqin cikin ta abun ya faskara, tayi iya yin ta har saida itama ta koma yin shiru, Mubarak ne ya shiga tsakiyar su ya zagayo da hannun shi ta wuyan su” kaiiii shirun nan naku ya burge ni, for the first time Kumburin buredi, da Qashi da rai sun nustu ba fada, ba hira ba hayaniya,” ido suka hada a tare sukai kwafa, ai ko kan ya ankara sunyi ram da shi, ihu yake yana neman taimako, dakin rufe yake, sai da suka gama yamutse gadoj kamar wasu yara, sannan suka kwanta suna ta dariya suna maida nunfashi,” God i am gonna miss all this,” hawaye ne ya gangaro ma Lamyah, Munarak ne yace,” My goodnee really, Lamyah? To ba dani ba ni na gudu wajen Mommana, ta hadan abinci duk kun yashen ciki,” fita yai a guje , su kuma suka saka dariya, Farha ce tace,” yaron nan in yana abu kamar wani babba, he is just 5 to 6 yanzu fa, amma maganganun shi da wayon shi kamar dan 8 ko 9, Allah ya raya shi, tabbas ta bakin nashi ne tin da da yakan ce zai zama yayan ki,in Bala na kitsa mai hakan nakan musa kullum,” murmushi sukai suka miqe zuwa sallah.

An ci an sha, an kuma yi biki lfy, in da Farha taso tai rawa amma aka hana ta, taji haushi sosai, tai qunqunin ta ta gama tace aiko yau ko a gidan amarya ne sai ta dance, ile ko bayan an kai amarya, mutane an tattafi, daga Lamyah dake ta kuka, sai ita Farha, sai wata yar uwar su Momma, da ta kan zo, mai suna Rahama, kida Farha ta kunna, tin Lamyah na daurewa ai sai ga amarya ta cire mayafi tana takawa, suna yu suna ihun jin dadi, a haka Ameenullah ya dawo, shi daya ya shigo, dan a nan su Farha zasu kwan, ita gobe zata wuce, shiyasa Lamyah ta dinga kuka sai abar mata ita, da kyar Momma ta yarda, dan gaba dayan su kuka suka sata gaba suna yi, Ramla ma gobe zata koma gidan Momma, leqowa yai ta yar hanyar da basu rufe ba,yana ta qarewa Lamyah kallo, gaba daya hankalin shi ya ma tashi, burin shi kawai ya gan shi kusa da amaryar shi…..

Sauran qiris wayar nan ta ja na aje rubuta ‘yan rawa sai bayan kwana biyu ko uku, inna huce daga faduwar gaban da ta ja min, nai rubutu mai yawa na fice hankalina ya tashi dana tina ban saving ba, ina komawa naga ashe bai gogu ba, da wallah sai na warke na dawo????????????????
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘YAR RAWA ????????

            BY HAERMEEBRAERH

I dedicated this sweet page to all MAMU NOVELLA members, especially the active 1s, Yan labe layi daya ne naku???? I heart u da yawa, mun zama sisters from another mother, Allah ya qara mana hadin kai da so da qaunar juna, My qawalliya rabin duwais ( Mamu Autar Hajiya) Maryam Alqali,ina roqon Allah daya baki ladan hada zumunci da kikai mai qarfi

Page 21:

Wani juyi Lamyah tai hade da banqara qirjin ta, sannan at the same time qugun ta ta maida shi gefe, ta saka hannu ta tattaro gashin ta gefe, tana kada qugun ta a hakan, wata ajiyar zuciya mai qarfi ya aje, bai san da zuwan Naufaliyyah ba sai ji yai ta daki kafadar shi da dan qarfi, a firgice ya juyo, wani mugun kallo ta ke bin shi da shi, gaba daya idon ta yai jawur, fuskar nan tai jawur, haka ma hancin ta, sunkuyar da kai Ameenullah yai yace,” shigowa ta kenan zan miqa masu wannan naga suna shashanci, ni kuma bana son shiga,” harar shi tai dan a tsaye take tin shigowar shi, har matse qafafun shi da yake da komai a idon ta, qwace ledar hannun shi tai ta dauki hanyar dakin, zata kai masu, tinawa da yai ba Lamyah kadai bace a dakin, da qawar ta masifaffiyar nan, sannan ga Rahma kar ta fadawa Momma , bayan nan ba zai so wulaqanta Lamyah har haka ba ace a first nyt din ka kishiya ce zata kawo ma kazar amarci ba kuma da arziqi zata ba da fada zata je, shan gaban ta yai ya jawo ta jikin shi, sannan ya hade ta da gini, nan da nan jikin ta ya hau rawa, miqa mai jikin ta take gaba daya tana aje nunfashi, yana ganin haka a ranshi yace,” yau na shiga uku,” kiss daya ya mata a goshi, ya shafi gefen fuskar ta, sannan ya kauce, idon ta arufe yake amma jin da tai kamar baya nan ya sa ta bude ido, aiko nan take wasu hawaye masu dumi suka fara bin fuskar ta, ta durqusa a wajen tana kuka, mai cin rai, yau Ameenullah din ta ya zama na wata, yau da wata zai kwana ba da ita ba, a qa’ida ko bai kwana da wata ba lokacin waccan ne ba zai kwan da ita ba, aiko yau za a yi ta, dan maganin matan da ta dirkawa kan ta, ba qaramun damun ta yake ba, miqewa tai tai dakin ta, wasu arnan kayan bacci ta saka, ta feshe jikin ta da mayun turarikan ta,wanda a ciki harda hadin na asirin su na mallake Ameenullah, murmushi tai na gefen baki, sannan ta tura qofar dakin Ameenullah dan ta kai mai ziyarar ba zata, me zata gani…..
..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button