
Wanka yai ya sha gayu, yau harda shaving yai, nan da nan ya fito Ameenullah din shi,fuskar shi cike da nishadi, ga tirarika kamar anyi barin su a jikin shi, haka ya shafa mai ya fito, sake da jallabiyya kalar maroon, tai matuqar masa kyau, kai tsaye dakin Lamyah ya nufa, tana kwance tai daidai, bayan ta gama da abincin ta, ta qara chocolate, waqar Nancy Ajram take sauraro, tana kwance tana rawa da jikin ta, gaba daya ya tafi, ji tai an shafa cinyar ta da take a miqe, da sauri ta miqe tare da dan sake qara ,” meye haka malam, meye na shigo min dakiiiii,” jan maganar tai a lokacin da Ameenullah ya dago kan shi, wani irin kyau da kwarjini ne ya fito masa, kasa ci gaba da masifar tai, ta qura mai ido, idon shi taf hawaye,kuka yake sosai ya fara magana,” qanwata kuma mata ta ki yafeni tabbas ni mai laifi ne a wajen ki, ke da ma wajen Allah, amma in kk yafen na san Allah zai gafarta min, nasan ba zaki so Allah yai fushi da yayan ki ba ko? Duk abinda kk ganin yana faruwa ba da so na bane, wani abun bana sanin ina aikatawa ma,ki duba lamarina ki yafen ba dan ni ba,” wani tausayin shi je ya kamata, da gudu2 ta taho ta fada qirjin shi tana kuka, ,” amma me yasa ba zaka fi qarfin ko meye ba? Ka na nuna ma matar ka banda mahimmanci a wajen ka, kasa kullum sai ta gayan magana,” “shhhhh, bar kuka kae wani ciwon ya same ki, zan iyakar qoqarina na ga na miki duk abinda yake haqqin ki ne, inshaa Allah komai zai wuce, ke tawa ce, ni naki ne, iyayen mu sun san zuciyoyin mu daya ne tun sanda suka haife mu, shiyasa suka tsaya dan mallaka mana junan mu, dan haka ki qara hakuri, kinji qanwata?” Daga mai kai tai tana sauke ajiyar zuciya, sunsuna wuyan ta ya fara,” wanne irin tirare kk amfani da shi ne?” Shiru tai tana jin wani baqon yanayi na ziyartar ta, a haka da wayo da komai Yah Amee ya cika ma Lamyah aiki, tai kuka sosai, kukan rashin ‘yanci, dan ko yana tsaka da lallashin ta ya mata wanka, sun dawo dakin, ya gyara mata kwanciya yaji sallamar matar shi, haka ya miqe jiki na rawa yai sanda ya fice, yai kamar ba daga dakin Lamyah ya fita ba, kuka sosai Lamyah ke yi, yau ina zata saka kanta, wannan wacce irin rayuwa ce? Kenan wannan shegiyar matar tashi tana nufin haka zasu ci gaba da rayuwa da abin son ta? Inaaaa da sake an ba mai kaza kaiiii…….
Muje zuwa Qawayen Lamyah ku bata shawarwari, wataqila ta samu mafita
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘YAR RAWA ????????
BY HAERMEEBRAERH
This page is for u my priceless sister from another mother,ASEEYAH AHMAD BUNZU,❤ i love u so much for being a very gud freind, i have to say thankx for the gud things i have learn from u, is good to have u in my life dear, and don’t worry i think i will be in ur country some day just to see u and my kids???????? LOVE U XOXO❤
Page 23:
“Daga ina kk naga fuskar ka cike da annuri, kayi matuqar kyau,” ta fada tana taku daidai zuwa gare shi, yana ganin tana nufo shi gaban shi ya yanke ya fadi,” kai jama’a ni kenan ban da hutu, Allah gani gare ka barawo a hannun mata,” gudun karya amsa ta da qarya ne yasa shi manna mata kiss a lips din ta yana shafa bayan ta, tare da tambayar ta akan inda ta ziyarta, a haka ya shashantar da ita, qarasawa sukai gado ya tayata cire mata kayan jikin ta ,jakar ta ya dauka zai aje mata a wajen jakunkunan ta, da gudu ta amshe ta hau ce mai,” da ka barta ma zan aje da kaina,” mamakin canjawar ta yai lokaci daya, meke damun ta, oho ita ta sani, miqewa yai ya nufi waje ya zauna a parlor dan yana son in ta shiga toilete ya fada dakin Lamyah, haka ko akai, yana jin ta shiga, da sauri har yana tuntube da carpet ya fada dakin, kwance ya gan ta, tana ta kuka, ta duqunqune guri daya, qarasawa yai da sauri, ya jawo ta jikin shi, wani irin tura shi tai sai da ya kusan kaiwa qasa, jikin daga murya da tsananin fushi ta nuna mai qofa,” get out!!!” He don’t want her to repeat what she just said,haka ya ja yan qafafun shi ya fice, tabbas yasan abinda yai bai kyauta ba, amma ya zai yi? Bai an kara ba yaji ta daka mai tsawa,” daga gidan uwar wa kk?” Ranta a matuqar bace, dan taji sanda Lamyah ta daka mai tsawa, kuma gashi rai bace, Allah yasa ba wani abu yake.nema wajen waccan mai kama da aljanun ba? Tabbb da ta shiga uku, qara daure fuska tai tana tuhumar shi, akan daga ina yake, cikin in inaa yake fada mata Lamyah ce ba lfy yaje ya duba ta shine take jin haushi dan da baya kula ta sai yanzu, ajiyar zuciya tai tace,” kar ka damu mine, let me help her,” cikin rangwada tai dakin Lamyah, kwance ta gan ta tana kuka, dariya ta saki tace,” Lamyah kk ko wa? Bari na fada maki, kinyi babban kuskuren auran mijina, domin mijina nawa ne ni daya, ba a haife shi dan wata ba kina jina da kyau, dan haka tin kina iya gane hanyar gidan ku ki tafi kice kin fasa auren kan auren ya gagare ki,” Lamyah bata tanka ta ba tana kwance , da taga ba zata amsa ta ba ne ranta yai mummunan baci, dan ta tsani tai magana ai shiru, tsaki tai ta fita ta doka qofar da qarfi,Lamyah ce ta dan daga ta ga wucewar ta, girgiza kai tai tace,” lokacina na nan zuwa ki gama naki, dan lokaci na baki, ki gyara zaman ki da ni, ko na dauke duk abinda na san mallaki na ne dama,” juyi tai, daidai nan taji ana kiran sallah, miqewa tai da qyar cinyoyin ta ciwo suke sosai, ga tsami da jikin ta ke yi ko ta ina, ruwan zafi ta dada hadawa mai tsafi ta shiga ta qara gasa jikin ta, tai alwala tai sallah, sannan ta shafe jikin ta da kayan shafa masu kyau da qamshi, ga turarukan ta masu tsada da qamshi, gyara gashin ta tai, ta saka yar doguwar riga, amrless, ta daura dankwali, ta jawo wayar ta, inda qur’an yake nan ta kunna, ta hau karatun ta, a haka akai kiran isha’i, sallah tai, tai shafa’i da wutri, tai addu’o’in ta, dan ita da ta ga biyar na yamma tayi take azkar, miqewa tai ta cire doguwar rigar ta maida na bacci, kwantawa tai, dan yin bacci, nan take ko ya dauke ta, bacci tai sosai, sai wajen 1:13am ta tashi, yunwa take ji sosai, dubawa tai komai na ta na kwalama ya qare, tsaki ta danyi ta sauka zuwa kitchen, dan samawa kanta wani abun…….
Kuka yake tayi shi a kaishi wajen Farha Sister, ko Mummyn shi, ” haba Mubarak why ar u being such a baby? Nan in magana ka tashi zarowa, kamar Farha ce ta haife ka, amma yanzu as big as u ar kana kuka,” kunya ce ta kama shi ya goge hawayen yana wani mammazewa, shi a dole babban yaro,dariya ce ta kama Momma da Baaba wanda ya dade tsaye yana kallon su, ice cream ya miqa mai, cikin murna yace, ” Baaba na gode,” ya je cinyar shi ya zauna, shafa kan shi yai yace mai,” kar ka damu my boy jibi zan kai ka da kaina nima ina son zuwa naga mahallin diyata,” ” yippyyy Momma zaki kema,” ” zani mana in zaku kara ni a motar taku,” ” zamu dake, amma ina sona kaima Lamyah Sister best chocolate din ta, Baaba,” ya qarasa cike da shagwaba, murmushi Baaba yai ya shafa kan shi, yace,” kar ka damu Allah ya kaimu jibin, gobe sai muje mui shopping ko,” daga kai yai cike da murn, ya sauka yai dakin shi da gudu, wata takarda da biro ya dakko, yana ta rubuta me yake son saiwa Yayar shi.
” Ni dai Baby na gaji, kullum amai ba qaqqautawa, tinda cikin nan baifi sati uku ba in kana sona ka neman sauqi a cire,” Farha ce ta fada a galabaice, ko ina na jikin ta rawa yake saboda gaba daya ta wahala, sakamakon amai na laulayi da take fama, furicin ta ya daki zuciyar Bala, bata taba ganin bacin ran shi ba irin na ranar, bai kula ta ba, dan fushin da yake zuciyar shi komai zai furta ba zai zama alkairi ba, taimaka mata yai bayan ta gama ya maida ta daki ya gyara wajen, daga yanayin shi ta tsorata tasan tayi ba daidai ba, hankalin ta ya kuma tashi da hakan, nan da nan tai nadamar maganar ta,” i am so sorry love, ban san magana ta zata harzuqa zuciyar ka haka ba” ta qarasa cikin kuka sosai, tausayin ta ne ya kama shi, dan ya san tabbas tana cikin matsananciyar wahalar laulayi, komai taci sai amai, ga zazzafam zazzabi, da ciwon mara, komai bata so, surutun tane kawai yake nan, sai abinda ya qaru,dan in abun ya motsa mata ta dinga zuba, sai ya lallaba ta tai bacci yake samun hutu. Bayan ya gama lallaba tane sun fara hira as usual tace,” kaga Lamyah bata san da cikin nan ba fa, ko zamu bata mamaki ne, ko na sanar da ita kawai??” ” duk yanda kika gani mata ta,” ya fada tare da kissing goshin ta, bari tai a sai da safe zata sanar da ita.