
Page 25:
Leqa ko ina take na gidan amma shiru bata gan shi ba, sannan bata ji wani alamu na yana gidan ba, tinani tai maybe ya wuce masjid, duba da lokaci wajen qarfe 2:40pm wataqila daga sallah bai dawo ba, kaiii amma ai baya kaiwa haka, ana idarwa yake dawowa, miqewa ta yi tai hanyar kitchen wanda direct kana hango dakin Lamyah ne, kallon qofar tai cike da kishi tana hararar wajen, ai ko ta ga hular Ameenullah, irin qaramar nan ta saqa a qasa daf da qofar dakin, wani ashar ta saki ta zabura tai wajen da gudu kamar mahaukaciya, bata tsaya bata lokaci ba ta banka qofar, daga yanda ta bude qofar Lamyah ta farka amma jin alamun Naufaliyya ce sai tai kamar bacci take, juyi tai ta qara rungume shi, shima cikin baccin ya qara manna ta da qirjin shi, yai murmushi, tare da furta ” I love u so much qanwata,” wani mahaukacin naushi ta kai mai a fuska, a gigice ya miqe, ta dale gadon, ta kai ma qiejin shi naushi, ” har fada mata ka ke kana son ta, gaba daya Ameenullah ya gama firgicewa, daga hannu tai zata qara kai mai naushi, taji an buga ta da qasa, dubawa tai taga waye? Lamyah ta gani a gefe ta dau riga tana sawa kamar ba ita tai ba, yunqurawa zatai ta miqe kafar ta riqe, ga azabar da zuciyar ta take ga azabar kwadata da qasan da akai, wanda har yanzu ta kasa gane aikin waye a acikin su, kuka ta saki mai cin rai, yau mijin ta ne a jikin wata, ” tashi ka fita,” shine a binda Lamyah tace ma Yah Amee din ta, fuskar ta ba wasa, dan tabbas ta fison ita tana korar shi kafin shi ya tafi ya barta da ciwon zuciya, miqewa ko yai, ya debi kayan shi yana sakawa, ganin shi ba kaya yasa Naifaliyyah kusa sumewa, mijin ta ne dakin wata kuma ba kaya? Ya Allah , ” for how long kuka dauka kuna cin amana ta a gidannan?” Ta fada hawaye na bin fuskar ta kamar wadda ta kama kwato da ‘yar ta, Ameenullah ne ya tsaya zai mata bayani Lamyah ta daka mai tsawa akan ya fita mata a daki in yaje can ya wa matar shi bayanin, ficewa yai da sauri, tabbas in yana bin umarnin Lamyah to ita yasan dalili, ba dan komai bane sai dan son ta da yake, da kuma kasancewar ta wani sashe na jikin shi, kuma abinda tai bai ga laifin ta ba in dai za ta na bashi hadin kai, ita ko Naufaliyyah tsoron ta ne yake ji ya cika mai ko ina na jikin shi. Qoqarin miqewa take ta bi bayan shi ta sauke mai kwandon bala’i amma fa sam ta kasa miqewa da alama tai targade ko buguwar qashi tabbas, Lamyah ce ta tako gaban ta a hankali, ” bari na fada maki wata magana bitch, ki sani Yah Amee nawa ne, aro na baki, is like baki san meye zuru ba, zuru na miki naga iya bakin qoqarin ki na iko da isa da mallaka, amma naga alama na kai gejin da ba zan jure duk wani iskanci daga macen da na raina wa aji da komai ba, ki duben ki dube ki, in ba qaddara irin ta Allah da yake wa bayin shi ba, ya qaddara masu abu kuma su bi shi su samu lada, ni nafi qarfin ko wacce mace ta kusanci Yah Amee dina, dan kuwa komai da yake buqata zai same shi a nan, ke kan ki kin san ba ki fi ki zama mai aikina ba, amma tinda Allah ya hada mu dole na sauke haqqin ki akaina, ina me gargadin ki da kema ki fita harkata, ki saken haqqina dake kan ki, in ba haka ba …….” mamaku ne fal zuciyar Ameenullah dake tsaye bakin qofa, da ita kan ta uwae gayyar, ashe Lamyah tana da baki haka,( habaa kun manta wace qawar ta) zuwa tai zata wuce ta gefen ta tana sane ta take mata yatsan hannu qaramin, qara ko ta sake, nan da nan Lamyah ta juyo kamar gaske,” Opsyyy ban gani bane, a ficen a daki kan na fito wanka, bana son na fito jikina ya ga naki, na qara datti,” shiegewa tai tana kada jiki,Naufaliyya kamar ta hadiyi zuciya, a hankali ta qoqarta ta tashi,aiko ta saki qara qafarta tai tsami sosai, Ameenullah ne ya shigo ya dauke ta cak, dik da dukan da take kai mai a qirji, amma bai sauke ta ba, zuwa sukai dakin su ya aje ta a gado, qafar da ya kula har ta dan hau ya kamo, ta ko sake ihu, ya kama ya ja sosai, nan d anan tai wata qara, a take ta nemi ciwon ta rasa, ya gyaru, ai ko dira tai ta fara masifa, wani abun ma bi kmata ace ko da da karuwa ta gan shi ba ta furta, amma inaaa ba da’ar wannan komai yazo mata fada take, shidai bai ce komai ba kan shi a qasa kamar wani soko,ko gama wa batai ba ta zari jakar ta da key din mota ta fice, shi kuma toilete ya shiga, wanka ya fara ya tina da moment din su shida Lamyah, da yanda ta saki jiki da shi, suka sha soyayyar su, da yanayin shagwabar ta mai kyau, sannan Lamyah ta iya tattausan lafazi, ta na da girmama mutum, murmushi yai da ya tina yanda take ambatar Yah Amee dina a da da yanzu, wani dadi da so da qaunar ta ke ratsa shi, a haka yai wankan ya fito, kimtsawa yai yai sallah, dan sun makara sosai.
Lamyah na can ta shirya tai sallah, yau tinani tai itama bari tai kwalliya kamar mace mana a gidan mijin ta zaman daki ya qare sai na parlor yanzu,itama ai gidan ta ne, wasu riga da skirt na atampa ta dakko, Farha ce ta kai masu dinkin, ba qaramin kyau sukai mata ba, sun matse ta ta duk in da ya kamata, ta kafa dauri, sannan ta feshe jikin ta da tirarika masu matiqar qamshi, takalmi tasa mai rangwamen tsini, baqi, inda atampar jikin ta tana da ratsin baqi da pink, sai dan fari a jiki, kitchen taje tai masu abinci mau dadi, ruwan shan su ta samu ta tope shi da ayatul kursiyyu, 7 falaq 7 nas 7, ikhlas 7, tai amanarrasul 7, sannan ta topa a abincin su ma haka, ta dauka tai parlor, dakin Ameenullah ta nufa, tana shiga ta gan shi kwance yana kallon sama, isa tai gare shi ta kwanta a saman jikin shi, wata ajiyar zuciya mai qarfi ya sake , dan hasan wace ko a mafarki yake, ” Yah Amee na tashi muje mu ci abinci yunwa nake ji ,” kamo ta yai ya juyar da ita ya zama shine a sama yana binta da wani kallon so da qauna, yaushe ya samu matsayin cin abinci a gidan shi, hmmm ,” My Lamyan na gode tashi muje,” daga ta yai bayan ya mata kiss a lips suka fice, zama sukai suka ci suka sha sukai qat, Ameenullah kawai abincin hotels din daya taba shiga yake hangowa, amma sam bai ci mai dadin wannan ba, matsawa yai kusa d aita ya hau kissing din ta, a haka ta banko qofa, tana shigowa ta daka salati, amma Ameenullah ko gezau bai ba, Lamyah ce ta dan zame kadan, ta kalle ta,shima ita ya kallah, har yanzu akwai tsoron ta a jikin shi, amma sai yaji kamar an dauke mai kaso 30% muqewa yai zai shige dakin shi, ta bashi umarni suje dakin ta, bai musa ba ya bita, hararar Lamyah tai, dan ta gano ita ta bugata da qasa dazun, in tace zata ci gaba da biye mata kassara ta kawai zatai kamar yanda bokan ta ya sanat d aita yanzunnan da ta fita,” ki rabu da yarin yar nan physically and spritually, ni dai kam tafi qarfina, ke kuma kin ga abinda ya same ki ai wajen yin fada da ita, duk wanda rai yaiwa dadi bai kai ya mai shi ba ai ko?” Tina hakan da tai ne yasa ta buga uban tsaki tai daki, zaune ta gan shi yai shiru, masifa take ta mai amma bai tanka ta ba, wani yunqurin tashi ya mammake ta yake ji amma ya kasa, shine dalilin shirun na shi, zuwa tai jikin shi ta kwanta ta hau kuka,” ni dai Allah yanzu ka daina so na, gaba daya waccan figigiyat yarinyar tana neman dauken hankalin ta, dan Allah ka daina kula ta kaji,” wani kallon baki da hankali ya mata, sannan dama wayace yana son kin? Amma a zahiri janta yai jikin shi ya hau lallashin ta, miqewa tai tace” bari na debo maka ruwa, ka sha”, mamaki da dariya ta bashi, yaushe yake da wannan arziqin? Murmushi yai yace ,” na qoshi yanzu naci abinci na sha ruw,”a ranta ko tace inaa ka isa yau dinnan zaka sha wannan abun nawa da ma zo da shi ba zaka min salalan tsiya ba ina ji ina gani, ,” k shikenan ,” matsawa tai jikin shi zata fara maii aikin na ta da ba gajiya take ba ya miqe yace yanzu za a kira la’asar bari yaje ya shirya,baqim ciki kamar ya kashe ta,ficewa yai dakin shi kamar ba Ameenullah da ta mallake da asiran ta ba,” hmmm we shall see” ta komar da kan ta ta kwanta.