NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yau tin asuba Mubarak ke murna,ya hada duk wani abu da zai kaiwa Mummyn shi, sannan ya fidda kayan da zai saka, Momma kam data shigo tada shi Sallah ta gan shi yana surutan me zai ce ma Mummyn shi in sun hadu, dariya tai ta yi, tana kwaikwayon shi,haka ta koma dan ganin idon shi bude, amma ta sanar da shi yai sallah, qarfe 1:05pm a farfajiyar gidan ameenullah tai masu, Lamyah tai girki mai dadi, ta yi drinks kala2, sannann ga kwalliya ta ci, dan ita tayi ne sabida yau zata kira Yah Amee din ta yaci abinci, dan tana ganin ta wannan hanyar ne zai samu sauqi.daga kowanne mugun abun matar shi, a hankali kuma sai ta sa ya gyara yanayin ibadar shi, ta aje plates ne taji dan qaramin hannun da take kwana da tashi da tinanin shi ya riqe ta ta baya,juyawa tai da sairi suna ganin juna sai murna, da gudu ta sake shi tai wajen Momma, ta fada jikin ta, sai murna take, wajen Baaba taje ta duqa qasa ta fara gaida shi, ” Tashi tashi diyata,,” kama hanun ta yai suka je kan kujeru, suka zauna,gaisuwa suka sake yi, sannan suka tambaye ta Ameenullah ta shaida masu yana daki da Naufaliyyah, ammabari taje ta kura su, miqewa tai ta tafi, tana zuwa ta hau kwankwasa qofa, tai tai taji shiru, can taji hamshaqiyar tana,” ka tashi kaje kafin wannan ballagazar ta karya mana qofa,” zuwa yai ya bude qofa, nan da nan qasan zuciyar shi yana mai kamar ya dauke ta ya gudu, amma kuma a saman zuciyar shi wata tsanar ta yake jin na taso mai, ,” malama meye?,” hadiye baqin cikin ta tai tace, Baaba da Momma ne suka zi,” yaji dadi sosai kamar ya tafi da gudu ya rungume su, dan yai missing din su, amma inaa sabanin haka ne ya biyo baya,” shine zaki zo kina damun mu muna hutawa? Bacen da ga nan,kice bana nan in kun koma,”wani sakin baki tai ya. Rufe qofa ya barta nan tsaye, a sanyaye ta koma,” na ju komai bar su Allah ya fidda shi daga halaka,” amsawa sukai dika sukai ta hita sosai, ita ko duk zuciyar ta ba dadi sosai, a haka har suka tashi tafiya, ta sha kuka kuwa sosai, ita da Mubarak,ji tai kamat ta bisu.

Waya suke da Farha ta kwashe komai ta fadawa Farha, “kan uban can, tin yaushe ake maki hakan baki fadan ba sai yanzu, lallai zuwa Nijer ya kama ni, sai na gyarawa wannan qaramar Yar barikin zama……..

Ina zuba ido naga zuwan aunty masifa, wake jira ? Ko ni daya ce?
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘YAR RAWA ????????

            BY HAERMEEBRAERH

Sis Juwaireren Mama Allah ya baki lfy ya sa kaffara, sister ku yata ‘Yar uwata addu’a pls, Allah ya bata lfy????

Page 26:

Wai ance sabo da yi gawa da gatsine, yau rawar ce ta motsawa Lamyah, a parlor take, cikin shigar ta ta qaramin wando, da yar figigiyar riga, kalar pink, sai band din data daure gashin ta, in a pony tail style, bayan ta dan raba shi daga tsakiya kadan, ga qamshinnan na tashi ko ta ina, wata irin sarqa ce da rigar tazo da ita golden a zagaye da qugun ta, kida ta kunna tana taka rawa a hankali, tana jin dadin yanayin idon ta rufe, dan a kan idon ta Naufaliyya da Ameenullah suka fita, rawa take tana juya kowacce gaba ta jikin ta, a yanzu Lamyah ta qara cikowa, ko ina na jikin ta yai dim da shi, Ameenullah da ya dawo ne ba tare da tasan yana tsaye daidai qofar shigowa ba ya qura mata ido ko qiftawa baya yi, wani yawu ya hadiya, ga qoshi ga kwanan yunwa, rawa take ta kai sama tai qasa juyi take da hips din ta kamar ba a jikin ta yake ba, tin da yake ganin rawar ta bai taba ganin irin ta yau ba, a cikin rawar ne ta zame band din kanta, gashin ta ya sako ya baje a bayan ta, ta yo gaba da shi sannan ta saka yatsun ta tai baya da shi, a hankali ta maida qugun ta gefe, ta juyo da kanta daidai saitin Ameenullah d ya sake baki yana kallon ta,suna hada ido taji gaban ta ya fadi, wani irin tsoro ne ya kama ta dan bata san da dawowar shi ba, nan da nan ta nemo remote zata kashe, umar ni ya mata da ta bar shi, a cikin jikin shi yake jin kamar ya shaqe ta dan tsana haka kawai yake jin haushin ta, amma qasan zuciyar shi wani irin so da qaunar ta ke mai yawo a ran shi, musamman na kallon ‘yar iska da yake mata a da kuma ya ji ta ba haka ba, sannan kuma ya ganta tana da ibada,matsalar ta daya wannan rawar, shima kuma tana dada sace zuciyar shi da ita, dan ta san yanda zata sarrafa jikin ta, jitai ya kamo qugun ta da qarfi, a hankali yaso mata, amma bangaren dake jin tsanar ta ba zai bar shi ba,tsanar ba gaira ba dalili, yar qara ta saki wadda ta qara daga mai hankali ta qasan zuciyar shi, kafadar ta ya kama da take a bude,da nufin ya shafa, amma ya matse mata da qarfi sai da idon ta suka yo waje, ” Yah Amee pls stop u ar hurting my shulder pls,” hawaye ne ke zuba a idon ta da gudu,qoqarin kwace jikin ta take, amma ba hali,gaba daya komai na shi ya gama kwancewa, anger, lust, duk sun baibaye shi, ga kuma tausayin ta dake damun shi, ganin kukan ta ne ya sa ya sake ta da sauri ya daga hannayen shi sama, alamar defence, kawai bin shi tai da kallo cikin damuwa da tinani, daki ta shiga da gudu tana kuka, shi kuma ya zauna a wajen yana maida nunfashi, tare da zirarar da hawaye, wani na bin wani, ” meke damuna ne, Ameenullah ka tina fa wannan yarinyar amanar ka ce, ko ka manta Ammiin ka da Abiin ka ne, ka manta wace ce Lamyah a gare ka? Nooo ban manta ba, kawai ji nake na tsane ta,bana son ganin ta, ji nake inna ganta kamar na shaqe ta, amma ina son ta, ina son ta, ina son ta ina qaunar ta,” ya durqushe a qasa yana kuka sosai, bai san meke damun shi ba, ya zai yi,” pls someone should tell me what to do,” shine abinda yake ta fada kenan, Lamyah ce da ta jiyo kukan shi na qaruwa ta fito cike da tausayin shi, a yanzu ta cire kayan can ta zura riga doguwa, dik da dai ba wata doguwa bace sosai amma ta kai qaurin ta, sai dan kwali data daura, rigar nada dogon hannu, da atampa aka mata, sai aljihu guda biyu gefe da gefen rigar ta sama ta matse ta qasa ta bude sosai, ba qaramin kyau kayan suka mata ba, dan tana shiga data fara kuka, ta jiyo Ameenullah na yi yama surutai sai taga rashin dacewar zaman ta tai fushi da shi,bayan ta sam meye matsalar shi, dalilin sauyawar ta kenan, ta fito gare shi, miqa mai hannu tai, ji yai kamar ya dauke ta da mari amma ya miqa mata nashi,kamo hannun shi tai, ta zauna a kujerar ta kwantar da kan shi a qirjin ta tama shafa bayan shi a hankali, daga sama zuwa qasa,ajiyar zuciya yake ta yi, a hankali ta ke rera karatun qur’ani mai girma a kunnen shi, wata nutsuwa ce ke shigar shi, suratul baqara ta ke karanta mai, wani irin tashi tsigar jikin shi ke yi, ba na wasa ba, nan da nan jikin shi ya hau karkarwa, tsoro ya cika zuciyar Lamyah, da za a ce fir a lokacin data taka, amma in bata tsayawa mijin ta ba ba mai tsaya mai, ci gaba tai muryar ta na rawa, a haka tin yana jijjiga har y daina jikin shi ya sake yai mata nauyi sosai, minshari taji ya fara, alamar yai bacci kenan, wayar ta ta zaro a aljihun ta guda biyu, kowacce ta kunna karatu, daya suratul ali’imran,daya ta kunna suratul jinn, ta ci gaba da baqara da bakin ta, bacci ya samu mai nauyi sosai har wajen La’asar, yake ta bacci, ita kuma bata gajiya ba, ga dai shi ya mata matuqar nauyi, qirjin ta kamar zai fashe take ji, amma haka ta hakura, da kan shi ya farka,cikin ambaton Allah, da addu’ar tashi daga bacci, daga kai yai ya kalle ta, ya mata murmushi, itama murmushin ta mai amma fa na yaqe, dan yana daga ta wani zafi ya daki qirgin ta, na gajiya, kiss ya mata a goshi, sannan ya miqe ya nufi dakin shi, yana shigewa ta durqushe tana yarfe hannu,tana ” wash Allah Yah Amee ba dai nauyi ba , wayyo qurjina, ” tana yi tana fidda iska daga bakin ta tana shaqar wani, alamun bude qofar shi taji, tai maza ta qame tana mai murmushin yaqe, murmushin shima ya mata, ya wuce masjid yana fita ta miqe a dudduqe tai daki tana raki, alwala itama tai tai sallah, sannan ta dakko jug ta hada mai fresh jus, sannan ta kai daki, ta maida hijab din ta har qasa, ta dakko hisnul muslim din ta ta hai karanta mai addu’o’in duk da suka kamata,sannan tai mai Ayatul kursiyyu 7, Iklass 7, falaq 7, Nas 7, Amanarrasul 7, sanna ta mai suratul jinn 3, ta dade zaune tana addu’o’i dan so take daga yau,ko wanne asiri ya kauce a jikin Mijin ta, ya bassu sui rayuwar su mai inganci, tana gamawa ta cire qaton hijab din ta ta wuce kitchen, aje a cikin fridge, ta fara masa girki mara nauyi, a ruwan girkin ma sai da tai wadannan addu’o’in da karatun, a haka ta masu french rice da vegitable stew, a gefe kuma ta masu papar meat with boild egg a ciki,yaji kayan kamshi, da na lambu, ba qaramin kyau abincin ya bada a ido ba balle qamshin shi dake tada yunwa ko a qoshe kk zakaji kamar an maka yasa???? hadawa tai tai wa a bincin bismillah akai 21, sanan ta rufe, daki taje tai wanka, Ameenullah da ya dade da shigowa, haka nan ya tsinci kan shi da jin kunyar ta na abubuwan da yai mata a baya saboda tsoron wannan yar kwal uban, ji yake ashe bai kai namiji da zai iya tsayawa a gidan shi ba, bai kai namijin da zai shiga taitayin shi ya riqi Allah da ibada ba, har sai yarinya qanwar shi ta zo ta nuna mai komai, ina renon da tarbiyya tare da dasa masa tsoron Allah a zuci da su Ammiin shi sukai masa ya tafi, nan take zuciyar shi ta tsinke hawaye suka fara mai zarya, Lamyah ce da ta sha wanka tai matuqar kyau, yau shigar material tai, doguwar riga har qasa, an mai din kun gayu, tsayawa ma fasalta dinkin zai batan dan lokacin dake hannuna, duk wanda ya ganta zai ma ce ta ci gasar sarauniyar kyaun da za ai bana, a gefen shi taje ta kwanta bata hana shi kukan ba, amma itama kukan ta saka, a firgice ya juyo dan jin kukan mutum a gefen shi, kuma na abar son shi, kusan suma yai da ya ganta,” La…… laaaa….Lamyah?” Tsaida kukan tai ta kashe mai ido daya sannan ta cije lips din ta na qasa,” ka gama kukan? Na zaci ba yanzu zaka gama ba sai na taya ka,kaga in abincin mu ya huce bamu ci ba, ka san yanda za kai dani dan bana cin sassanyan abinci,” ta fada tana wani shagwaba mai tafi da hankalin mai kallo, wata irin kasala ta saukar mai ya janyo ta a hankali jikin shi, sannan ya miqe da su, daga baya ya daga ta cak sukai waje zuwa cin abinci, abinci suka fara ci bayan ta zuba mai, ta debo tai bismillah zata bashi, sai ta kauce sai ya miqo baki sai ta kauce, gaba daya yawun bakin shi ya tsinke,ji yake kamar ya saka hannu in ta hana,” Lamyah ina wasa dake ne, ni ki ban naci in zaki ban ‘ Yar baqa kawai,” aiko ta cika nan da nan,” nice baqar, Allah Yah Amee yanzu na ma fika fari,kuma na fasa baka abakin ci d kan ka ai baqa ba ta ba fari abinci ba,”ta fada ta re da murguda baki daga qarshe, hakuri ya bata ya mata alqawarin siyo mata lots of Diary milk chocolate din ta,sannan sukai bismillah a tare suka fara ci da hannun su na dama, ba ruwan su da wani gayu,a ci abinci da wuqa da cokula wuqa a dama cokali a hagu dan tsabar bata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button