
Bayan gaishe2 da sukai, idon shi ya sauka kan Naifaliyya da ta qura mai ido, tsaf ya gane irin kallon, dan guntsun tsaki yai ya kauda kai, dauke idon ta tai daya ciko da hawayen, ta cije lips din ta, ” Ameenullah naji labbarin duk abinda yarinyar nan ta aikata, kuma a gaskiya na zo nan ne domin baka hakuri, domin duk abinda tai akwai sa hannuna ciki, da kuma gurbatacciyar tarbiyyar data samu daga wajena, mahaifin ta ya mana waazin da ya shiga zuqatan mu daga ni har ita, dan son Rasulullah kai hakuri, ka yafe mata, ka kira abokiyar zaman nata domin ta bata hakuri, tabbas mun cutar da ku,” ta qarasa cikin tsananin nadama wadda ta kasa boyuwa a fuskar ta, jikin shi ne yai sanyi da yanayin su dika, tabbas akwai tsantsar nadama a tattare da su,miqewa yai ya shige bedroom din shi, kwance ya tadda ta, tayi kuka har ta gaji, fuskar ta tai ja,musamman hancin ta, dago ta yai yana bubbuga bayan ta, saurin miqewa tai tana yaqe, murmushi ta so yi amma tai failing,hawaye ne ya biyo baya, girgiza mata kai yai,” in ina ganin hawayen ki zaki sa na koma na kore su dan ba zan taba aje abinda zai bata maki rai ba,” da sauri ta share hawayen ta tace,” kayi hakuri ba zan qara ba,” murmushi yai ya ja ta toilete ya wanke mata fuska, ya bazo mata gashin ta ta gaba,yanda zai diga rufe fuskarta, sai dai idan ta mayar da kanta, kama hannun ta yai suka fita, tana ganin sun kusa wajen su tai qoqarin kwace hannun ta amma yaqi, a tsaye ya tsaida ta gaban Naufaliyyah,” ke na fara aure kafin na ga qanwa ta farin cikina, kafin na samo alqawari na da na dade da burin samu, na aura kafin kowa, ke ce macen da ta fara kasancewa da ni a matsayin miji, kin yarda damar da kk samu da matsayin ki, in kina son zaman lfyr ku daga yanzu zuwa har abada, ki zauna lfy da ita, na san wacece Lamyah, ba ta da son hayaniya, in ba taba ta akai ba, ba ta da fada in ba janta akai ba, ke kuma na san halin ki, kowanne, dan haka ku zauna lfy da juna ku riqi Allah a zamab ku,kar kuna sani gaba a zaman ku, kuna saka Allah a zaman ku, domin in kuna saka ni a farko zaku na sabawa Allah,zakuna shiga haqqin junan ku, shi aure ibada ce, kuma ba kowa ake wa ibadar nan ba face Allah,dan haka in kuna son samun nasara duniya da lahira kuna tina Allah, ko sabani kuka samu, in da hali kuna warware shi a tsakanin ku, ta hanyar tattaunawa a junan ku, ku zama kuna ma juna uzuri, sannan kuna ba juna hakuri akan laifukan da kukaiwa juna,….” nasiha yai masu sosai da ya sa a cikin kaso % na kishin su kashi 50% ya fice, zuqatan su suka samu nutsuwa sosai da shi, hannu ya miqawa Naufaliyyah ta miqe ta isa gare shi,ya hada su ya rungume, Maman ta ce tai gyaran murya, sika sa dariya dika, cike da kunya,bayan ta masu addu’ar zaman lfy ne sai ta masu sallama ta tafi, zaunar da su yai akan doguwar kujera, ” da farko dai kusan nace komai ya faru Allah ya qaddara hakan, amma tabbas akwai rashin bin dokokin Allah dake jawo komai ya tavarbarewa bawa, ya rasa dalilin faruwar abubuwa marasa dadi a rayuwar shi, a qa’ida ya kamata tin da akai auren mu da Lamyah yazama mun raba kwana atsakanin mu, amma bam hakan ba, muka ci gaba da zama na tauye haqqin ta, dan haka a yau ina son mui magana a tsakanin mu kwana nawa ya kamata muna yi?” Lamyah ce ta kalli naufaliyyah ta mata alama tai magana,” da farko dai ina mai qara ba ku hakuri ku yafeni, akan soj zuciyar dana aikata maku, kuma ina ganin kwana biyu yayi, a gani na fa amma,” ta fada cike da murmushi, dik sin aminta da hakan, Lamyah ce ta miqe ta fara takawa,” to ango da amarya ni na shiga ciki, na barku lfy,” Ameenullah ne ya sake baki, a ranshi ko gani yai wannan yarinyar ta gama da shi, tabbb, ina alqawarin da ta mai? Lallai za a yi ta, ya nuna bai yarda ba Naifaliyyah taga ba a kyauta mata ba, cikin yaqe ya juya ya hada ido da Naufaliyyah da ta gane kwata2 ranshi bai so ba, amma ya zatai itama tana buqatar shi.
Dare yayi Naufaliyyah anci kwalliya, an harde a gado Ameenullah ne ya shigo, ” ya na ganki anan? Ai bina dakina zaki dan gaskiya ba zan din ga yawon bin dakuna ba ina da dakina, ai kamar jira take, har tana kusan kifewa ta miqe jiki na rawa ta kashe fitila ta ja qofa ta bishi, waiiiiiii makaranta kun san wace Naufaliyyah, ba sai na gaya maku budirin da aka sha ba ranar, dan ko abun sai su kawai, Ameenullah ya wahala????har mamaki yake wai ita wace irin mace ce? Komai tin anayi da dadi har a wahala? Gashi abin haushin ma in ba dan ta iya style kala2 ba sam bata kai Lamyah komai ba ta fannin ni’ima, ( makaranta kar ku manta fa ita gimbiyar kayan mata ne kala da kala, amma Lamyah ta fi amfani da natural abubuwa, bata yarda da shan kayan da bata sani ba, komai zatai da natural take yi, yanda zai gyara mata jiki, ba ya gyara ta na dan lokaci ba daga baya a bata ta ba, dan haka yana da kyau mu farka mu kiyaye binda zai amfane mu da wanda ba zai amfane mu ba).
Bayan wata biyar
” Masha Allah barakallah, wannan baby ba qaramib kyau yai ba, Sannu my sister, kin yi matuqar qoqari,ba mai cewa daga jikin ki wannan qaton baby ya fito ba,” dariya sukai, amma banda Naufaliyyah, wadda gaba daya kallon da Farha ke watsa mata yake matuqar tsorata ta, amma tsabar hali irin na Farha ita zata juya ai dariyar da ita amma ta hana matar mutane sakewa, tin da suka zo Nigeria, Farha ta hana Naufaliyyah sakewa sam, yau dai Lamyah ta shirya yi wa Farha magana, ” Sister ki bari mana, na fada maki komai yai daidai,” habaaa dama jiran kadan take,” eh amma da komai yai daidai ai ni ban fadi albarkacin bakina ba, baiwar Allah bari kiji, lokacinnan abinda ya hana ni zuwa na sumar dake da duk wani boka da malam tare da masu baki shawarar taba wannan gold din nawa shine wannan cikin, kwata kwata bari na fada maki gaskiya naji matuqar haushi da kk shiryu ban je na taba lafiyar jikin ki ba, amma bari kiji, alqawarin karaya da targade na kan ki a duk randa kk batawa ‘yar uwata rai ina fatan kin gane,” kamar wawuya Naufaliyya ta kada kai, cike da matsanancin tsoron Farha, ” Gud now we can be freinds” miqa mata hannu tai sukai sallama, cike da ajiyar zuciya Naufaliyyah ta sauke hannun ta, Bala ne ya kira mai jego ta miqe ta fita, ” Sistern kinnan can kill with only her look, ba qaramin tsoro take van ba,” dariya Lamyah tai sosai ,” qashi da ran kk tsoro?” ” keee bar wannan qashi da ran cike zuciyar ta take da qarfida izza,” ” Allah yasa ba zance na naji ana yi ba,” ” Aaaa mu ba zancen ki muke ba mukacenyaro kyakkyawa da shi tubar kallah,” Lamyah me zatai ba dariya ba, kyakyatawa taje kamar me, wayar ta ce tai qara ta dauka, “Yah Amee na” shine abinda aka rubuta a wayar, murmushi tai ta daga, tashi tai ta bar waje, bayan sun gaisa ya fada mata bayan suna da kwana uku zasu zo har Baaba suje Rimin gata dan ganawa da iyayen ta na can, gaban ta ne ya fadi da tinawa da tai da su……..
Sai nace Farha Allah ya raya baby boy, TEEM FARHA INA BARKA????????
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘YAR RAWA ????????
BY HAERMEEBRAERH
Qarin bayani da magana akan abinda novel din ‘YAR RAWA ya qunsa
Page 30:
1- Neman ilimi abune mai matuqar mahimmanci, both western education and islamic one, dan in kana da ilimin addini dana zamani akwai abubuwan da dole zaka banbanta da mutane da dama.