NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

2- kar mui wa mamatan mu kuka, kuka irin na jahilci, kururuwa da iface2, mu zama komai zamui mui amfani da ilimin mu, kuka dole ne, amma mu yi shi yanda islam ya nuna mana ba kuka irin na jahilai ba,mui kuka mai hade da nemawa mamaci rahamar Allah, shine asalin soyayyar mu a gareshi.

3- Yana da kyau kowacce mace ta zama cikakkiyar macen da zata kange kowanne lungu da saqo na zuciyar mijin ta, yanda ba zai so rabuwa da ita ba ko na secod daya sai da babbar lalura, in ko bata tare da shi zai ji matsanancin kewar ta, ba yaimurnar qaya bata nan ba.

4- ki zama matar rufin asiri, matar da ko wanne hali zaku shiga ke da mijin ki ba mai ji, zaki hakuri, har ki sama maku mafita, ko ki sama wa kan ki mafita.

5- Yana da kyau bawa ya kiyaye dikokin Allah a kan shi, a koda yaushe kuma a kowanne lokaci, in ka kiyaye dokokin Allah Allah zai kiyaye ka daga dikkan abun qi.

6- Mu riqe ibada, duk wanda ya riqe ibada da azkar na safe da yamma, Allah zai kare shi sannan zai mai katanga daga manyan kaba’irai, zai daukaka darajar shi duniya da lahira.

7- Bawa ya guji yin shirka ga Ubangijin shi, shirka ko wacce iri ce haramun ne, hukuncin shirka wutane direct, sai idan bawa ya tuba, shirka ta fara daga kan canfi ne, qin dayan ta Allah, zuwa wajen bokaye ko malaman tsubbu,neman biyan buqata a wajen wanda ba Allah ba, musamman buqatar da bawa ya san ba wanda zai biya mai wannaj buqata tashi sai mahaliccin shi.

8- MATA MU GUJI MUMMUNAN KISHI, mumkunan kishi na kai mata da dama wuta, wai shin mene ne a kishi ne? Kishi ni a tawa fahimtar shine, qoqarin kiyaye abinda kk so kar ya fada ga halaka,da kuma faranta ma abinda kk so ta hanyar halak, dan haka in kenan qarin aure a wajen mazajen mu zai zama ya fidda mijin ki daga halakar misali zina kenan zaki kishin shi ki bashi dama a duk sanda ya zo maki da batun qara aure? Sannan ba zaki zama mai fasadi a cikin gidan shi ba saboda kawai an maki kishiya? Zaki zama mai qoqarin faranta ma mijin ki ne kawai ba tare da kin cutar da abokiyar zaman ki ba, kowa ta shi ta fisshe shi, da dama abinda mata bamu sani ba shine,ki gama haukan kishin ki, da biye2n bokak ki, mijin ya kubce maki da kiftawar ido, sannan ki gama mai gatan in ba dan Allah kikai ba ke ko dan Allah kikai ya zo ya baki kunya gaba ga kishiyar taki, ko a bayan idon ki ya zage ki tas dan kawai ya samu wajen zama gun waccan, dan haka koma zaki na kishi ki yi shi bisa tsarin islam, ki kyautata zaman ki da abokan zaman ki, ki ba mijin ki dama ya halasta abinda Allah ya halasta mai.

9- In Allah ya sa zama ya hada mu da dan da ba mu muka haifa ba, mui mai riqo na tsakani da Allah, ruqon gaskiya, domin ba mu san me zai zama ba gaba da zamu mora, kai ko ba zamu mora ba ma zamui domin Allah ya bamu lada, ta wani bangaren kuma bamu sani ba muma zamu rayu da namu? Su waye zasu riqe mana namu? In kikai ma dan wnai riqo mai kyau aiwa naki mai kyau.

10- Komai qanqantar abinda Allah ya hore maka in kaga wanda bai kai ka ba yana buqatar taimako ka taimaka mai, kaima Allah sai ya duba abinda kai ya qara maka.

11- Riqon alqawari yana da matuqar mahimmanci da lada mai dimbin yawa.

Wannan hasashe na ne a cikin wannan novel mai suna ‘YAR RAWA, duk wadda take da nata hasashen qofa a bude take dan a qaru da ilimin da Allah ya bata itama na gode

Haermeen Haermmaerh na godiya da soyayayyar ku da addu’o’in ku na alkairi a gare ta, tana matuqar son ku itama
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘ YAR RAWA ????????

            BY HAERMEEBRAERH

I am so sorry fans, yesterday’s chapter is awful, banda lfy ne, kuma ban da sha’awar rubutun kwata2, amma saboda yanda naga wasu na son nayi yasa nayi din abinda kuke so shi nake so,hope za a yafe ma Haermeen Haermmaerh
Ana uhibbukum katheeran

Page 29:

Wasu larabawa na gani kyawawa su uku,sun sha dogayen riguna har qasa, a cikin garin lagos, da alama duk da kyaun su gajiyar da sukai bata boyuwa, yau kwanan su uku suna yawon neman Lamyah, da Mubarak, wanda suke amfani da hoton ta dake cikin wayar mahaifin ta, wasu maza suka samu su biyu a wata mota mai baqin glass, suka tsaya, El-Hussein shi ke jin turanci shine yai masu magana,” Assalamu alaikum, pls do u know this gurl? Her name is Lamyah,” hada kai sukai suna kallon hoton kamar masu nazarin ta, sai suka fara magana qasa2, dayan ya ce ma dan uwan shi,” Oh boy this people rich oo, we fit collect there bag, and take them to Oga Mikel na him know wetting him go do with them abi?” ” u don talk wetting dey for my mind,” kada kai sukai dayan su ya amsa da ,” yes i know her, let us take u to her,” cikin tsananin farin ciki zuciyar su cike da mugunta da kwadayi suka shige, muhammad har wani kada kai yake, yana ayyana irin hukunta Lamyah da zai, sannan da abubuwan da zai da dukiyar in sun karbe, tafiya ake ba ta qare ba,dama gasu a gajiye, nan danan bacci yai gaba da su, a hankali daya daga cikin mazan nan biyu ya juya ya zare jakar hannun El- Hassan, rage gudun motar dayan yai,shi ya fice daidai wani gidan katako, da sauri ya bude qofar ya wurga jakar sannan ya rufe ya fito suka sa kai,wani tankamemen gida suka je, wanda kyaun shi ya wuce na tsaya fasalta shi a dan wannan novel, mak gadin gidan na leqowa sakamakon horn da ya ji, ya ga mazannan nan da nan ya washe baki ya bude gidan, shigeea sukai, wanda yai daidai da farkawar su Muhammad, a zuqatan su suna ayyana kudin El-mustapha, washe baki suka hau yi, suna murna, larabci suke ta zubawa, nuni sukai masu da su fito, fuskar su ba walwala, budewa sukai suka saka qafafun su waje, suna gaba suma su Muhammad suna biye, qara kallon gidan suke suna ayyana mugunta kala2 a zuqatan su, wani wawakeken parlor aka kaisu, suka zauna a kujeru na alfarma, kalle2 kawai suke basu ga kowa ba ko wanda suka kawo su basu sake gani ba, dan tin da suka shigo sukai wani babban qofa suka aje su nan basu kuma ganin su ba, leqa qofar nai ganin qwaqwaf???? wani qasungurmin mutum na gani, mai cikar gashi a fuska, jikin shi ba riga sai wani zani daya daura, shima kamar ya balle, da wata sanda a hannun shi, sai uban sanqo, tubar kallah baqin shi kam ban isa misali ba, ji nai fitsari na neman kufcen da yai magana,” weldone Sam and Emma, ur work dey do me well oo, go inside and take two box my boys,” ” Ahhh oga make am three na? Na three men dey there oo,” ” k make u carry three then,” godiya sukai suka fito dauke da akwati suka wuce su,ko ci kan ku ba su ce masu ba,su kuma har da daga masu hannu, a zaton su Lamyah ce ta sallame su,wata qila sun mata bayanin yanayin su ne ta gane sune, Muhammad ne ya fara kitsa masu abun da zasui data bayyana, suna cikin qus2 suka ga wani jibgegen qato ga tsawo ga qiba yana takawa da kyar dan ko takalmi baya sawa,” Ya Rabbiiiii,” El- Hassan dake kallon qofar ya fada a matuqar tsorace, suma juyawa sukai,ai suna ganin shi suka firgice suna neman hanyar guduwa, masu gadin dake tsaye a kowacce qofa ce suka shigo suna muzurai, wannan baqin qaton ne ya barke da magaukaciyar dariya ya hau yarabanci, nan da nan na ga su Muhammad suna takurewa a hankali suna dunqulewa sai ihu suke, daga hannun shi sama yai, tini suka tashi sama a matsayin tsintsaye masu kalar fari da blue masu kyau, manya, dan ni kam ko sunan su ban sani ba, nan take wasu maza hudu suka fito ta wata siririyar qofa na gaba dauke da sharbebiyar wuqa, take na sake fitsarin da ya matsen dan tsoro, ta daidai bayan qofar dana maqale suka wuce, ukun ne suka dau tsintsayen nan dake ta kada kai, sukai waje da su,kowa ya bisu, na lallaba nabi bayan su, gani nai sun je gaban wani qaton gunki, sun danne tsuntsayen nan, wannan qaton mutumin ya karbi wuqa a hannun dayan su ya fara yanka kowanne tsuntsu yana surutai da yare, yana gamawa kowa ya daha hannu sama sukai yare sannan suka nuna gunkin, hankalina ne ya tashi ainun, ganin kudi na fita daga bakin wannan gunki, ai qafa mai naci ban baki ba, na fece,kan na zama na baddawa.
Shi kenan qarahen akewa qasa, qarshen mai kwadayi da mugunta tare da mugun hali kenan.????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button