NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Anyi suna lfy inda Baby yaci sunan El-Mustapha, Lamyah ta yi kuka sosai ranar, wanda Farha da mubarak ke taya ta, dan sun iso a ranar kwana uku kenan da sunan, tai wa Farha godiya ba iyaka, Farha taso a sakaya sunan amma Lamyah ta roqi da su bar shi haka, tana son ta ji ana kiran sunan mahaifin ta, haka zata fi jin dadi sosai, a haka aka bar shi, aiko yaro yaga gata wajen Yah Amee, innace gata ina nufin gata, iya gata, har kudin da za su saka shi makaranta daga play class har University sai da Yah Amee ya bayar, dan yace komai yayi ba zai biya su sunan Abiin shi da suka saka ma dan su ba. A kwana na hudu ne da zuwan su suka shirya tsaf dan zuw Rimin Gata,sosai Farha ta so aje da ita ta qara ganin Inna dan bata hakurin dukan da tasha amma suka hana ta aka ce ta zauna da ita da Tani a ranar suke son dawowa, haka ta hakura, amma matuqa taso zuwa, sannan ta ci wa Delu mutunci, dan ta matuqar tsanar ta, haka Lamyah ta lallaba ta suka tafi aka barta da cizon yatsa tana ta saqa irin tsiyar d zatai da an bar ta.

Da misalin qarfe sha daya suka isa, inda Saddiqa na riqe da Lamyah qarama a hannu, Musaddiq ya dau zani ya saka alamar jira yake a saka mai ita ya goye, sukai sallama, leqowa Inna tai, taga su waye, ganin Lamyah ne ya sa ta zaro ido tana leqa bayan Lamyah taga ita da waye? Dan tabbas ba ta son qara haduwa da Farha ko a hanya, ganin ba farha ne yasa ta dan pito waje,fuskar ta ba yabo ba fallasa, dan yanzu ta gama gane komai game da Lamyah, tsananin kishi ne ya sa Delu ke kushe su ai ga shi nan ta ga ishara itama,sannu da zuwa tai mata ta shiga da ita daki, ta saka mata tabarma, su Yah Amee da Bala tare da Baaba da Mubarak na fadar mai unguwa, Momma ce ta fara zama, tana kallon gidan, a nan ne wai akai wa Lamyah wulaqanci? Sai kace wata uwar ke gare su, gaishe gaishe sukai, dai dai lokacin da Musaddiq da Saddiqa suka fito, dan suga su waye, kwata2 qin yarda yai Saddiqa taje gida inda dan ta’addan dan Delu yake balle aiwa iyalin shi irin na Delun, ” Lamyah sarkin rikici, nikam Baban Lamyah anya ‘yar uwata ba tai rikici ba tana qarama? Ka duba kaga yanda yarinyar nan ke hana mu bacci? Badan inna na taimaka mana ba,” ” ba wani riki…….” maganar shi ta maqale sakamakon arba da Lamyah babba da yai zaune tana ta maka mai murmushin ta mai kyau, da sauri ya daga labulen ya shiga,” Lamyah? Os that you?” ” ni ce Yah Musaddiq,” ta fada tana miqewa, kallon kallo sukai ita da Saddiqa wadda ta isa da hanzari ta rungume Lamyah, gam kamar za a kwace ta, idon ta cike da hawayen dadin ganin ‘yar uwar ta,murna sukai sosai da ganin juna, gaisawa sukai sannan Lamyah ta tsokani Musaddiq,” Yah musaddiq a ban takwarar tawa mana, duk da dai naji ana man sharrin rikici,” ta maida kallon ta kan Saddiqa,” Aaa yanzu ai dana gan ki na janye, sai dai gado tai wajennnnnn,” tana kallon Musaddiq daya jefe ta da hararar masoyan da suka shaqu da juna su, hamdala Lamyah tai cikin ranta,dan da dikkan alamu burin ta ya cika, ” Yah Musaddiq tare nake da Baaba da Yah Amee suna fada,” inna ce da ta fitk daga gurya dauke da jug da ruwan randar sanyi ta ce,” kash amma dai ke ma akwai wauta, da baki magana ba wannan yaron ya kai masu koda ruwa ne? Maza tashi ka je ka kai masu wannan bari na kawo maku wani, ” yana qoqarin miqewa ne yaji shigowar su ciki da Mai Garin, dake babban parlor ne wajen dan haka zai ishe su dika, shimfida akai ma mai garin ya zauna, bayan gaishe2 ne, da ban hakuri, Baaba ya debo kudi masu yawa ya bawa Musaddiq yace a saiwa Baby kwalli godiya sukai sosai,inda Yah Amee yace ya dau nauyin karatun ta itama har University nan take ya rubuta cheque ya basu, dan yace yana son amaryar shi tai karatu sosai, nan akai wasa akai dariya,inda Yah Amee ya buqaci ganin gidan da aka haifi Ammiin shi, nan take mai gari da Inna sika kalli juna suka sadda kai qasa,” ranka ya dade na sha fada maku, in kana jin tsoron wancan shashashan a matsayin ka mutanen ka su ji me? Ka dinga daurewa kana nuna isa da izzar ka a matsayin ka na mai shugabantar wannan unguwa,” ” Bawai tsoro nake kar naje ba Musaddiq, baqin mu ne bana son su fuskanci matsala daga wajen shi musamman in muka je bai bugu yai bacci ba,dan har ni za a je,” ” me kefaruwa ne?” ” ba komai ku tashi mu je,” miqewa sukai, Lamyah duk tsoro ya cika ta, da tsoron sake ganin Delu.

Shigar su gidan ke da wuya suka ji wani wari sosai,toshe nacin su sukai, suka qarasa tsakar gidan duk datti qasu qananan yara ne, a zazzaune a rakube, sai wani mutum a qasa kayan shi sunyi baqiqqirin, shi kanshi kamar mahaukaci, a hakan wai bacci yake, wata mata ce qemasassa ta bushe bazata wuce 34 ba amma kamar ta fi haka dan wuya, Hamza ne ya fito shima daga wani daki da sanda a hannun shi, ,” Kulu su waye nan?” ” me gida ban san su ba nima amma dai da mai gari da dan shi babba sai Innar mai gari,” ” To to to ya yi ku shigo bismillah, Lamyah ce ta tiqe Ameenullah dan tsoro da kuma aman da ke taso mata, da sauri kuwa yace,”A’a nan ma yayi dan va dadewa za mui ba,” Inna ce ta je wani qofar daki ta daga labulen Delu ce kwance kamar matacciya, ga qafar ta day ta rube, sai fuskar ta ta gefe da ta dauje wajen ya kumbra shima yana ruwa, aman da Lamyah ke riqewa ne ya balle, aiko ta dinga kwara shi kamar ta amayar da hanjin ta, da kyar Delu tai magana,” su waye anan?” AMEENULLAH NE MIJIN LAMYAH DIYAR AMEENAATOU ji tai kamar an kwada mata guduma aka, qoqarin juyar da kan ta tai cikin azaba, da kyar ta kalle su,sai ta saka kuka,” yar nan ki yafe min ko na ga daidai kan mutuwa ta, ko Allah ya yafen kadan daga laifukana,” shima Hamza rusunawa yai yana kuka yana neman yafiya, Lamyah da kyar take magana itan ma kukan take,” in dai haqqi na ne ya kama ku haka na yafe maku,zan so ace mahaifiyata na nan ta yafe maku itama ko kun samu sauqin wannan azabar,” Hamza ne ya fara basu labari akan lalurar su.

Wata uku da suka wuce ne muna zaune ni da gyatumar mu muka ji kawai an shigo ba sallama,daga kan da zamui sai muka ga dan uwana da ya bar gida sakamakon shaye2 da dabanci,cikin doki Delu ta miqe ta isa gare shi shima ya gaida ta kamar abun arziqi, nan muka bashi abinci da ruwa yai wanka, kwatsam rannan na tafi gona na dawo, sai na tadda dan uwana a dakin iyalina, ta taushe mata baki ba damar tai ihu, Delu naje na kirawo, aiko bai daga ta ba sai da ya ida nufin shi, ya fito yana gyara wando, yana maganar ashe haka nake kwasar gara, daga yau sai dai a raba ta da shi, nai k kukan kura na kwada mai mari, fusatar da yai ta sa ya shaqe ni ya sa gannuwan shi cikin idona ya danne, nai ihun neman ceto , ganin haka Delu ta dakko muciya ta kwada mai, yana juyawa ya kalle ta ta tsorata ta kwasa da gudu, a nata kallon waccan katangar zata iya tsallake ta ne, tana dira qafa daya ta karye, ta fadi kan marmara, bai kula ta ba, ni kuma nan take naji bana gani, munyi kukan azaba ranar ba mataimaki, matata dan qunci da tsamin jiki, dan saida ta sha duka sosai a wajen shi ya samu nasara akan ta, ba zata iya tasowa ba, haka muka wuni zubur, sai da yaran mu sika dawo daga gidan yayar su suka taimaka mana, wannan shine abinda ya same mu bamu da yanda zamui da shi ga shinan kuma bamu da kudin magani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button