
Lamyah sarkin tausayi,kuka take riris,ran Ameenullah kuwa ba qaramin baci yai ba, dan irin kukan da suka sata,miqewa yai ya zaro waya yai waya sannan ya miqa masu kudi masu yawa sosai,yace kar su damu nan da wasu mintuna za a zo a dauke masu shi a kaishi inda ya dace da shi, sannan ga kudi nan su nemi lfyr su, sun tainaka masu ne kawai dan Saddiqa da ko kallo basu ishe su ba, godiya kam sun sha ta, ba iyaka.
Bayan sun koma gida ne Lamyah jiki ya tsanan ta, asibiti kawai Ameenullah ya wuce da ita, gaba daya Mubarak da Naufaliyyah sai kuka suke, ganin yanda jikin ta yai, suna isa likita ya duba ta, gwajin farki suka gano ciki dan wata hudu a jikin ta,tsananin mamaki kam Ameenullah da Lamyah sun sha shi, ciki har wata hudu ba su sani ba? Ta yaya? Ikon Allah, shine abinda Lamyah ke ta fada kenan, nan take ko ya hau waya yana sanar wa, kafin kace me su Farha an iso, dan da Bala yace su zauna kuka tasa, sai da aka zo da ita.
Bayan shekara hudu
“Uncle Mubarak zan sha nima” wata kyakkyawar yarinya ce take fadan haka, ta sha gayun ta da irin kayan mutanen Nijer,gashin ta har bayan ta, an raba biyu an daure kowanne gefe, da band kala2, sai rigar ta data sha saqi fara, da zanin ta blue dark, sai dark blue din takalmi, da sarqa da dan kunne farare, na bits, Ameenaa kenan, diyar Lamyah da Ameenullah, Lamyah na gefe, tana karatun ta a Laptop, Ameenullah na zaune yana kallon Mubarak da Ameenaa.
Mubarak ne ya miqa mata chocolate din Diary milk tai ta tsalle tana murna kuwa,” Mubarak dama baka bata va yarinyar nan so take tafi maman ta shan chocolate fa wasa2,” tura bak tai ta tafu wajen Lamyah da gudu ta haye cinyar ta tana shagwaba, ” yi shiru Ammii na ki sha abin ki in ma basu baki ba zan siyo maki da kaina,” ” ai ku kam sai Allah abu daya ne kk qi koya mata har yau a halin ki,” matsawa kusa da su yai ya rungume su dika bayan ya bisu da kiss, ” meye shi?” ” RAWA” harar wasa ta mai, sikai dariya,gani nai Ameena ta miqe da gudu tai wajen Naufaliyya da ta riqo hannun wanj qaramin yaro suna kiran shi Sultan, yaci sunan Baaba Mus’ab, wasa ta ja shi inda ita kuma Naufaliyya ta ke tahowa wajen su, tin daga nesa suke sakarwa juna murmushi.
ALHAMDU LILLAAH NA GODEWA ALLAH DAYA BAN IKON KAMMALA WANNAN NOVEL MAI SUNA ‘YAR RAWA, UBANGIJI YA SA MU AMFANA DA ABINDA KE CIKI NA ALKAIRI. WADDA NA BATA WA RAI DAGA FARKON NOVEL DINA ZUWA QARSHEN SHI INA NEMAN TA YAFEN, LAIFIN DA NAI A CIKI ALLAH KA YAFEN.
HAERMEEN HAERMMAERH NA GODIYA. LOVE U XOXO❤