
Washe gari ta tashi da tsamin jiki,musamman cinyoyin ta, ruwan zafi sosai mai hadin kayan qamshi na musk, da magarya,sai yar bagaruwa kadan, da kaninfari iya ta kawo mata tace ta shiga ta zauna zata daina jin ciwon jiki, nan da nan ta zaro ido????????????????ko dai iya tasan me akai jiya ne,wata kunya ce ta kama ta ta daqe bakin ta ta kama tafiya a tsaye da sauri tana son ta gudu daki, yana hango su ta parlo dariya ta gama cika mai ciki,tashi yai ya amsa yai mata godiya ya kai mata ruwan, samun ta yai bakin gado tana hawaye ” Ya salam me ya same ki Ameenee na? Wa ya bata ran sahiba ta,? Ko dan iya ta baki wannan ne baki so, bata gane komai ba fa, kawai tasan kin gaji tafiyar hanya ne yasa ta miki wannan hadin, da kin shiga robar kk zauna zakiji dadi a jikin ki,” kallon shi tai da idanun ta masu kyau da sukai ja, kada mata kai yai alamar da gaske bata gane komai ba, cikin ran shi kam dariya ce cike, tqna shiga ko ya fashe da dariyar, yace ” ikon Allah, ashe haka auren yara yake?” ………
Ni ko Haermeebraerh nace ya ma fi haka wallah
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘YAR RAWA ????????
BY HAERMEEBRAERH
Page 4:
Kwana biyu na cika kamar yanda Iya taima Ameenullah alqawari, haka taje ta roqi El-mustapha da in ba damuwa zata dakko Ameenullah, dan ta mai alqawari, nan take ya yarda, domin shima yana son yaron akwai wayo da tarbiyya, sannan kuma in an kawo shi zai debe ma Ameenee kewa da zaman kadaicin da zata shiga in tafiya ta kama shi, nan take ya saka driver da Iya suka tafi dakko shi, ba wani jinkiri mahaifiyar Aminullah Aishaa ta amince, tare da bada saqon gaisuwa mai yawa a kaiwa amarya, da kayayyakin su na Niger,???? Aminullah ya yi murna sosai da farin ciki dan zai koma kusa da mai renon shi, yana son kulawa sosai, domin ita mahaifiyar shi akwai son yara, amma ba ta son dawainiyar su, son jiki ne da ita sosai, in tana zune bata qaunar abinda zai daga ta, in ba ita tai ra’ayi ba ko mijin ta ne wato Mus’ab sai dai yai komai da kan shi, tin yana fada har ya hakura, sai ya auna abubuwan alkhairin da take mai , yaga sun fi wannan din yawa sai ya mai da shi a matsayin ajizancin ta, haka suke rayuwar su kamar ba wata matsala.
Kafin su zo ta gyara wa Aminullah daki babba mai kalar green da white, dakin ya yi kyau sosai, ko wanne daki a gidan akwai combination din kalar shi kuma kaloline masu matuqar kyau, gidane babba mai ban sha’awa ga kowa, suna isowa, da fari ya dan mata baqunta, amma yana ganin Uncle Musty,ya ware, wasan shi ya shiga yi sosai, in da da dare, El-mustapha yace suje shooping don a siyo mai kayayyakin wasa, da kuma wasu littafan makarantar kamar yanda yake da su a gida suna debe mai kewa, itama cewa tai a sai mata littatafan, tana son koyon bokon, amma bangaren turanci, tinda da shi ake amfani duk duniya, sai mata yai cikin zuciyar shi yaji dadi, dan matar shi na son koyon ilimi, ba qaramin dadi yake ji ba, idan ya ji ta tana karatu da asubah, ko kuma in tana zaune ita kadai yaji tana bitar wasu daga ayoyin qur’ani ko kuma wasu littafan addinin. Sun sai kaya sosai in da Ameenullah yai ta murna, ga ice cream da chocolate nan kala2 an sai mai, bayan sun kammala ya biya ne suka dawo gida, kafin ya shigo yai ma driver magana akan da safe zai na kai Ameenullah makaranta, amsawa yai cike da girmama wa da son ubangidan nashi, miqa mai wata leda El-mustapha yai shima yai kwalamar kar a varshi a baya, wajen mai gadi ya nufa suka bude suka hau cin gara suma, Ameenullah yai bacci a hannun ta tini, karbar shi yai, dan gani yai kamar ya mata nauyi, dan irin yaran nan ne masu jiki bulbul barakallah,ga hasken shi mai matuqar kyau da daukan ido, in ta qura mai ido gani take anya jinin Niger ne yaronnan???
Washe gari da kanta ta shirya shi ta hada mai abun karyawa da taimakon Iya, tinda ta iya girki na zamani ne dai bata iya ba, shima ta daura damban iyawa.
A hankali kulawar Ameenullah ta dawo hannun ta, ita ta take mai komai, tare suke kwana in tafiya ta kama El-mustapha, a hankali ya maida mata sunan ta Ammii, yana kiran El-mustapha Abee, iyayen shi suna matuqar jin dadin hakan ba kadan ba, kusan a duk bayan kwana biyu uku sai sun je, zasu yini ma Aishaa sosai, sai dare su koma, yana kiran Aishaa da Momma, Mus’ab kuma Baaba, ba qaramin gata Ameenullah ke samu daga iyayen nashi hudu ba, sai ga shi a shekara daya da yai da Ameenee ya kusa yin Hizif 30, wanda tana kyautata zaton yana shekara 8 zai sauke alqur’ani, mahaifan uku sunji dadin hakan, kuma sun jinjina ma Ameenee.
A kwana a tashi, yau shekarar Ameenullah uku a hannun su, Ameenee na hango kwance jikin mijin ta,Ameenullah na wajen qafar ta yana matsa mata, yana ta zubo haddar shi, Abee din shi na ta saurara yana lumshe ido, Ameenee na cin yalon da ta sa aka nemo da kyar, sakamakon tulelen cikin dake gaban ta, haihuwa ko wanne lokaci zata iya sallama, tana daga kwance ta miqe da sauri kamar an mintsineta, har tana buge Ameenullah, duk da bakin shi daya dan fashe bai damu ba, hankalin shi ya tashi ganin yanayin da Ammin shi ta shiga lokaci kadan, abu kamar wasa, sai ga Ammin shi na kuka, dan wata irin shagwaba take bugawa El-mustapha, riqe mai wuya tai ta qanqame shi, fuskar ta a girjin shi tana murza kanta dan azaba, ” Haerbeebee je ka kirawo Iya da sauri,” yana kuka ya fita tare da waigen ta, haka yaje ya kira Iyan, da hanzarin su suka shigo inda ta umarci El-mustapha da fuskar shi ta jiqe da gumi da hawaye da ya kai ta dakin da suka tanadi komai na haihuwa, zuwa yai ya aje ta agaban kujera ta durqusa tadan buda qafa kadan, Ameenullah ya je ya ba hakuri ” Haerbeebee ka zauna anan kaji, kai tai ma Ammin ka addu’a Allah ya sa ta haifa maka qanwa ko qani lafiya kaji, kar kai kuka, ka zama namiji, ” haka ya dan bubbuga fuskar shi, ” To Abii kaima ka daina kukan, inshaa Allah zata haihu lafiya,” rungume shi yai, ya dan yi kukan kadan, sannan yai kissing goshim shi ya shige dakin, Iya ta saka komai a qasan ta na tarba jariri, ta dafe kujera yaje ta gefen damar ta ya tsugunna, ya riqe hannun ta daya, dayan ta dafe kujera da shi, yana shafa bayan ta da daya, addu’a kawai take, tana yi ma iyayen ta da suka rasu addu’a, ko tai da qarfi ko tai a zuci, ganin wahalar da take sha ba kadan ba yace “ko asibiti zamu kaita Iya” ” karka damu da ikon Allah zata haihu lfy, ni na karbi haihuwar Ameenullah, duk jikokina ni nake karbar haihuwar su,” gyada mata kai yai, zai magana kenan yaji Ameenee tayi wani nishi mai qarfi, ta damqe shi kamar zata karya, sai da yai wata ‘yar qara, Iya na qara mata gwarin guiwa, akan ta ci gaba da nishin, qoqarin zama take, ta ware qafa iya ta hana, a haka take son ta haihu( in mace ta haihu ta haka ba ta da matsalar samun qari wajen haihuwa, inshaa Allah) wani kyakkyawan nishi da tai sai ga Baby ta fado, ta saka kuka, cikin farin ciki iya ta duqa ta janye yarinyar, sannan ta umarci El-mustapha daya girgiza ta mahaifa ta fado, haka yayi ko, ta nuna mai yanda zai ya kwaso jini daya kwanta mata, cikin nutsuwa da tausayawa,yai hakan, nan da nan ya daga ta ya shiga da ita toilet, ya fara wanke ta da gasa ta, tin a ciki ta fara gyangyadi, suna fitowa waje yai qal, Iya ta gyara har Baby, ta mata wanka,ga qamshi da ke tashi a wajen, bayan ya shirya tane, suka bude wa Ameenullah qofa, fuskar shi tayi jawur, ga hawaye ga dariya, ya rasa wanne zai yi, yana shiga ya fada jikin Abiin shi ya fashe da kukan murna, da sauri ya qarasa jikin Ammin shi ya kwanta a jikin ta yana mata sannu, shafa kan shi tai tana murmushi, ta daga kan shi ta kada mai nata, alamar ya bar kuka,
Iya ce ta miqa mai qanwar shi a hannu, kasa tsaida hawayen shi yai, wata irin soyayyar ta ce ta dira a zuciyar shi lokaci daya, ya qara qanqame ta, yana kissing din ta, ” Ammii ina son bbyn nan, tana da kyau, Ammii Allah ya sa tai halin ki, itama ta zama bata duka ko fada” dariya suka saka sosai, ” Inshaa Allah ba zata zama me fada ba Yaya Ameenullah, dan kai zaka na koya mata komai” murna ce fal cikin shi har ya zama Yaya ,” Abii yau she zata fara ce min Yayan?” Cikin murya ta dariya Iya ta amsa da” In dai ba ta da yanga gobe ma sai ta fara, amma in zata maka yanga sai ta kai shekara biyu zuwa uku” kallon yarin yar dake ta bacci a hannun shi tana tsotsar yatsa yai yace,” dan Allah kar ki min yanga kinji qanwata?” Dariya suke tayi dika,” zo nan haerbeebee, ba zata maka yanga ba, dan ko Ammii ba zan bari ta fara kira ba Yaya zamu koya mata, kaji yaro na” dadi ne ya kama shi sosai, ya kwantar da kanshi jikin Ammin nashi.