NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan shekara 11 a Dubai da sukai, kullum suna waya da ita da Yah Amee din ta da Momma Aishaa, sai Baaba Mus’ab din ta, cikin da Ameenee ke dauke da shi ya girma sosai, in da yanzu Lamyah mai shekara 16, kowa ya ganta sau daya sai yai saurin sake juyawa dan kallon ta a karo na ba iyaka, tsabar kyau, da shape din da take dauke da shi, ga gashin ta mai tsaho da cika, santsi da baqi, Lamyah ta zama yarinya mai matuqar kyau son kowa qaunar wanda ya rasa, ga ilimi dan tinj ta sauke qur’ani da sauran littafan da mahaifiyar ta ta koya mata, bangaren boko ba a magana, yare uku take ji, Turanci, Larabci, sai hausa, tana son koyon Frence amma Yah Amee yace sai ta koma Niger zai koya mata. A kullum Ameenee na bata labarin dangin ta,kuma tana fada mata babban burin ta bai wuce ta haihu su je wajen dangin ta ta ga iyayen ta maza ba, dan duk da sun yada ta suna da haqqin ta sada zumunta da su, kusan kullum sai ta fadi hakan, hakan ne ya sa Lamyah take matuqar son zuwa Nijeria taje itama taga dangin mahaifiyar ta, taga ya qasar take.

Ameenee ce ke naquda ba kowa a gidan lokacin,gaba daya ta galabaita, kafin mai masu wanki ta zo daukan wanki taji nishin ta, da sauri ta isa, Ameenee ko hanun ta bata iya dagawa, bakin ta ya bushe qaf………..????
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘ YAN RAWA ????????

    BY HAERMEEBRAERH

Hey guys, i am so sory for the late update, i have been busy ne wallahi this days, kuma ban jin dadi, amma in komai yai normal zan dawo kamar kullum, ina godiya da damuwa da kuka nuna akan jina shiru da kukai, hakan ya tabbatar man kuna biye dani, and masu tambaya daga farko ina qara baku hakuri dan Allah ku tambaya a group.nasan ko daya ne baza a rasa mai shi dika ba,thank you so very much for the love and care. Me love u xx

Page: 6

Waya ta dauka ta kira El-mustapha daga yanayin maganar ta, hankalin shi ya gama tashi, ko qarasa sanar da shi.batai ba ya kashe ya taho, da hanzari yaje ya kamota, a take Iya ta fado mai arai, yai tinanin ko gwadawa zai ya karbi haihuwae shima, can kuma da yaji tana jan wani nunfashi, bai san sanda ya dauke ta ba sai asibiti, a hanyar fita suka ci karo ra Lamyah tana dawowa daga makaranta, itama komawa tai tabi bayan shi ta rungume Ammiin ta ya ja su, yana yi yana waigowa yana mata sannu, bata san ina kanta yake ba sam, Lamyah kam tai kuka ta gode Allah, fatan ta bai wuce na Allah ya tashi kafadar Ammiin su ba, a haka suka isa, nan da nan Doctors suka taru akan ta aka fara bata taimakon gaggawa, kiran shi sukai akan ya saka hannu su mata aiki, da hanzari ya saka hannun, bayan sun shiga da iya ne, cikin ikon Allah da taimakon addu’ar da su Lamyah suke ta mata, Allah ya bata iko ta haihu da kanta, amma jini ya tsaya yaqi tsayawa,sai da tai awa daya da wasu mintunan tana zubda jini, da kyar suka tsaida shi, ta haifi yaron ta qato tubarkallah kyakkawa sosai, mai matuqar kama da mahaifin shi, take wata iriyar soyayyae shi ta kama zuciyar Lamyah, tana hawayen murnar samun qani ta rungume shi tana kissing din shi, Ammii da Abii suna murmushin kallon soyayyar data bayyana a fuskar Lamyah, a haka Ameenee ta kwana uku suka sallamo.ta.

A ranar da yaro ya cika kwana bakwai a ranar Lamyah ta dau hotunaj shi ta turawa Yah Amee din ta, ta rubuta mai ” Yah Amee ga Mubarak qanin ka, na turo don ka gan shi,”
Yana gama gani ya bata amsa da,
” Woooowww masha Allah, wannan kyakkyawan yaro haka? Allah ya raya mana shi da imani, amma ina fushi dake fa”
” Yah Amee me nai” ta fada tana turo baki kamar yana ganin ta,
” laifin da kk saba yi ne yau ma kk qara,”
Murmushi tai dan tasan me yake nifi
” laifin me?”
” hmmm Lamyahhhh kina son bam wahala, wannan ai abun kunya ne ace ban san fuskar ki ba bayan kin girma, kina nufin dole wai sai kun zo na ganki, ni ina matuqar son ganin yanda qanwata ta koma,”

” ni dai na baka hakuri nafi son na baka mamakin sunan daka saka min na baqaqen mata sirara, kai dai kawai ka sa a idon ka zaka ga macen da baka taba tsammani ba, kuma nasan su Abii bazasu karya promise din da sukai min na hanaka hotuna na ba” ta fada tana mashi gwalo, da dariya irin mai hawayen nan, kawai” Hmmm” ya rubuta mata, sai ya sauka online, kiran shi tai tana bashi hakuri, yace ya haqura, hirar su suka ci gaba, mai qunshe da ma’anonij da su suka barwa kan su sani.

” My queen ni me kedamun ki ne, gaba daya wani irin fari kk kamar mara jini a jiki, ko dai qarin jinin da akai maki bai ba ne?”
” Hum Abiin Ameenullah, lfy ta qalaou, ka daina sa ka damuwa aranka, rayuwa da mutuwa na wajen Allah, kuma duk abinda yai farko zai qarshe, fatana kawai shine ka daure ka ci gaba da mu’amala da mutane yanda kk yi, ‘yan uwanka ka ci gaba da kyautata masu, na san ka sune sama da dukiyar ka dan haka koda ka ga zasu so salwantar da ranka akan dukiyar ka ka miqa masu ita dan a Niger da Nigeria ka na da mafiyan su, kullum kasuwancin ka habaka yake, ka kula da yaran nan kamar ina kusa daku, ka……”
” Dakata wai me kk fada ne hak?” Ya fada cikin tashin hankali, da ganin kamar bankwana suke, take ya janyo ta ya rungume ta cikin wani irin runguma mai tsanani, da nuna bege da shauqi, hawayen da suke riqewa ne ya zubo masu kusan a tare, shessheqar kukan ta ne ya qara daga hankalin shi, haka sukai ta kuka ba mai rarrashin wani acikin su, sallamar Lamya ce ta katse masu kukan su, ” Assalamu alaikum, na shigo?” Ta fada tana neman izini daga iyayen nata, Ammiii ce tace mata ta shiga, sannan ta shiga, kallon su tai taga gaba daya idon su alamun sunyi kuka, mamaki da tsoro ne ya mamaye ta da hanzari ta isa gare su ta zauna a tsakiyar su ta dora kanta a kafadar Ammii tace” Ammii na me ya same ku? Me akai maku idon ku dika alamar kun yi kuka? Ko baki da lafiya ne har yanz? Dan na kula gaba daya kin yi fari , kuma kin fada?” Kamo ta ta qarayi ta rungume sannan ta manna mata kiss a goshin ta, ” Lamyah Haerbeebty, ba abinda ke man ciwo, kawai ina tinanin rayuwa ne, in yau mune wataran ba mune ba, ina roqon ki da ki ji tsoron Allah, ki kare mutuncin ki, kar ki sadaukar da darajar ki ta ‘ya mace a banza, ki kamilantar da kan ki ga mijin da zai aure ki, ki kula da dan uwan ki, Allah zai kula da ke kema” cikib kuka sosai Lamya ta qanqame Ammiin ta, Abii ya qara rungume su dika ” Ammii me ke damun ki, dan Allah ki fada mana matsalar ki, mu kadai kk da, bakinda wanda ya fimu, wannan maganganun naki na tsorata ni sosai” tashi suka ga tayi zata toilet,cikin kidima Abii yabi bayan ta ya juyo da ita, ” Ameenatou me yasa baki fadan jinin nan na zuba haka ba? Me yasa baki sanar dani ba? Ameenatou in wani abu ya same ki bazan yafewa kaina ba, ina tare da ke am……” zamewa tai qasa zata fadi ya riqo ta, Lamyah ko kuka kawai take tana riqe da yar binjilallayir rigat ta da hannu daya dayan ta toshe bakin ta, ta sunkuya hawaye na zuba da gudu, Abii ne ya ce ta bude qofar suje asibiti, kafin ya taka qafar shi sai yaga…….

dan Allah ku min hakuri da wannan
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘YAR RAWA ????????

        BY HAERMEEBRAERH

BANI NAI KAINA BA FANS❤ this page is for u guys, i love ur comments, u guys ar awsome, and i love u XX, especially Ramlat Sani, Fateema Abubakar, Haleema Sahad, ina jin dadin comment din ku, dan ku na miqe yanzu na fara wannan page❤

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button