NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Page 7:

Har ta zube a wajen, da gudu ya ida taro ta suka fadi qasa, rungume ta yai tsam a jikin shi yana wani irin marayan kuka, sakamakon tabbatar da cewa ba nunfashi a jikin ta, Lamyah ko mutuwar tsaye tai nunfashin ta na fita da sauri da sauri, hawayen ta kamar na yi ruwa an dauke, daga baya ne Abii ya kula da halin da Lamyah take, nan take ya miqe ya daga Ameenee ya kwantar da ita a gadon, ya rufe ta, ya koma jikin Lamyah dan kar ai biyu, jijjigata yai nan danan ta zube a jikin shi, hakuri ya fara bata, yana ta taimake shi kar wani abu ya same ta, bai san ya zai da ran shi ba ” Lamyah Haerbeebty pls say something, ki magana kinji, ki koka Ammiin ku ta tafi ta bar ni, ta barku, ta bar Yah Amee din ki, ki koka dan Allah Lamyah” wani kuka ne ya kwace mai mara sauti sai qunar rai, nan take hawaye masu zafi suka fara bin kuncin ta, ta fara kuka, da rarrafe taje ta kwantar da kanta jikin Ammiin ta ” Ammii ina son ki, na so ace kin rayu damu, kin kula da Abii da Ni da Mubarak, ga Yah Amee na ya dade bai gan ki ba, a wannan lokacin da muka saka ran Zuwa Nigeria ki hadani da ‘yan uwan ki ko bazasu karbe mu ba a wannan lokacin kk tafi kk barmu, Ammii Allah ya fimu son ki,Allah ka gafartawa Ammii na,ka kai rahama da salama kabarinta, Allah kasa ta tashi tana mai makwaftar Rasulullah, Allah ka sauqaqa mata kwanciyar qabari,” kukan ta ne ya fara raguwa domin addu’ar da tai ma mahaifiyar ta sai take jin a ranta ta gama nuna mata soyayya, abinda ya rage ta ci gaba da nema mata Rahamar Allah, gefe ta koma ta takure ta hada guiwar ta da kanta tai shiru, Abii n ta na gefe yana matse kwallah, yana ma matat shi addu’a, sai daga baya yai tinanin yi mata duk abinda ya dace, miqewa yai ya fita kamar wanda ya sha abin maye, a haka yai waya ma abokan shi ‘yan uwa da duk wanda ya dace sai dai ya ce kar a fadawa Ameenullah, ya fi son ya sanar da shi ga shi shima kuma ga shi, a haka Aishaa da Mus’ab suka fara shirin tahowa, Aisha tai kuka har taji ba dadi, Mus’ab tun yana rarrashin ta shima ya bige da kuka, Ameenullah na Nigeria wajen kasuwancin Abii da yake yi yakan dawo Nijer duk qarshen wata, sai kuma Baban shi ya tafi shima yai wata, wataran kuma suna tafiya tare, in suka je sukan sauka a hotel, har su gama abinda zasui su dawo.
Mubarak ne ke ta tsala kuka, a lokacin har an kai Ammii makwamcin ta na gaskiya,wajen qarfe biyun dare, daga Lamyah har Abii sun rasa yanda zasui, yaqi shiru, Lamyah ce ta koma qasan qado tai ta kuka, yi take tana kumawa, shima Abii sharcr kwalla kawai yake, kukan Mubarak ba qaramin taba zuciyar Lamyah yake ba, wata irin zuciya ce ta shige ta nan take taji wani qwarin guiwar, cewa zata iya kula da qanin ta kamar ita ta haife shi, she is 15 going on 16,kuma Ammii tace a Nigeria ana ma yara ‘yan 14 ma su haihu su raini baby so why can’t she do it? Fita tai ta damo madara a fida ta karbe shi, ta miqa wa Abii hannu ya bata shi, miqa mata yai yana kallon fuskar ta cike da tausayawa,tina wa yai yanda Aishaa tai tai tai akan su koma Nijer ta kafe ita bazata ba, a bar su anan, har suka koma, duk qiwar Aisha a qalla yasan zata na koyawa Lamyah yanda za ta na kula da qanin ta, bari ya sawa sarautar Allah ido yaga ya zasu qare,
Gani yai ta mai rungumar shan nono,ta saka mai fidar aiko kamar mai jira, nan da nan ya kama,ya dinga tsotsa ba jira, sai da ya shanye tass, sannan ta dora shi a kafadar ta yanda taga Ammii nayi, gyatsa yai sannan ya fara qoqarin bacci, sai me? Ji tai yana wata irin tusa mai qarfi, sai da ta tsorata, daga baya ita da Abii suka bushe da dariya, hannu ta saka a leben ta tace ma Abii ” Shhhhhhhssshhh” shima yanda tai yayi, basu ankara ba suka ji Mubarak na kashi, aiko miqawa Abii shi tai, tana riqe hanci, dan dama ita a komai na reno bata son aikin kashi, hannu ya dage yana nuna kan shi, ” Me me zan yi?” ” wanke mai zakai Abii” ta fada tana daga gira, ” Noooo pls u know i can’t?” ” Yes u can,me zai hana ka ma in the first place? Bayan kai ne Abii ni yayar shi ce kowa yasan ba zan iya ba i am just 15″ta fada tana daga kafada, kada idon shi yai sama yace,” Fine” ya karbe shi ya daga shi sama, yai toilet da shi tana gimtsr dariya, juyo wa yai ya kalle ta yana hararar ta ta kama bakin ta tai dif, zuwa yai ya cire mai ya gyara shi,kan ya gama jariri yai baccin shi, rungumo shi yai ya dawo ua kwantar da shi a gadon nan suka kwanta dikan su da asuba ya tashe ta tai sallah ta koma, nan ma Mubarak ya tashi,kan ya shigo dakin ta hada mai madara ta bashi ta jijjiga shi sun koma bacci.

Yau Ameenee ke cika kwana 60 cif da rasuwa, El-mustapha yai niyyar dakko mai reno amma Lamyah ta qi sam, tace in dan gyara kashin da yake ne ya koya mata zata na yi, da wannan zancen ya hakura, dan kuka tai tayi sosai, a haka yai ta bata hakuri sannan tai shiru aka bar zancen, Mubarak yana samun kulawa sosai, wajen Lamyah, dan komai take mai sai taga kamar bata yi, in da Ammii na da rai da zai fi samun kula, ko makaranta ta aje gefe, fatan ta kar qanin ta yai maraici.

Watarana El-mustapha ya fita yaga wata mota na bin shi a baya, yai iya qoqarin shi ya bace ma motar, mamaki ne fal cikin shi, waye kenan? Me ake nema a wajen shi kuma? Take wani tinani ya ziyarce shi, na wayar da daya daga cikin ‘yan uwan shi sukai mashi, sun tabbatar mashi da cewar, sun gano dukiyar da Uncle din su ya bashi ba ita kadai bace, ya boye wasu, saboda ko gezau arziqin shi bai ba, ya yi iya bakin qoqarin shi, na yaga ya fahimtar da su cewar shi fa dama wannan kudin baya gaban shi na gado, sannan dukiyar shi ta kasuwancin zannuwa da kayayyakin yadikan da yake siyarwa qasa2 ne ya tara sudan ba qanan kasuwanci yake ba manyan kasuwanci yake, amma inaaa sun tabbatar mai da in bai mallaka masu komai a hannun su ba zai fuskanci hukuncin da bai zata ba daga wajen su, yai rantsuwa ya kuma amma sam sun qi aminta da shi.

Yau suna zaune da Lamyah da ta dan fada sakamakon rashin bacci da kuma gajiyawa na reno, tausayin gudan jinin shi ne ya kama shi, dan ko RAWAR ta ta da ta zama mata farillah bai kuma ganin ta yi ba, abun na matuqar damun shi canjin nata, a qanan shekarun ta, ” Lamyah Haerbeebty fadan ina kk son zuwa in in Mubarak ya cika shekara?” Murmushi tai tace ” Abii nafi son sai ya cika shekara biyar muje Nijeria, dan in cika burin Ammii na kaimu wajen ‘Yan uwan ta” murmushin takaici yai, sakamakon tina yanda suka rabu da ‘yan uwan mahaifiyar ta ta, amma nan da nan ya kauda tinanin saboda bai son dasa ma Lamyah tsanar su, ” kar ki damu zamu je in dai shine burin ki,” miqewa yai ya dakko mata wata jaka, ya bata a hannun ta, “ki ajen wannan jakar, duk rintsi duk wuya kar ki rabu da ita, sai kin sada ta ga Mus’ab, (mahaifin Ameenullah)” kallo ta bishi da shi, nan danan ya dauke damuwar fuskar shi da ce mata” zaki sha ice cream na dakko mana, kwadayin shi nake ji yau tin safe” ” yippyyyy zan sha Abii dakko mana pls” tashi yai yana rangwada kai irin na murna na yara dinnan tana mai dariya, amma da zata juya ta ga fusjar shi da dariyar ta ta bace, ya san halin ‘yan uwan shi akan kudi, basu da mutunci ko qanqani, tinani yake na ya tura ta Nijeria din da isassun kudin da zata iya kula da su na tsahon shekaru ya sai masu gida, in yaso hankalin shi zai fi kwanciya, domin ba zai so hukuncin ‘yan uwan shk ya shafe su ba, tinda shi a yanzu ya gane raina masa hankali kawai suke son yi, dan cin dukiyar shi, duk da irin kyautatawar da yake masu, da wannan tinanin ya dakko ya kawo masu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button