NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Waya ya buga Nigeria ma wani dillalin sai da gidaje, ya siya mai dauke da daki biyu da babban parlor daya, sai kitchen, kowanne daki da toilet, kayan more rayuwa ya sa aka zuba masu ya kuma saya masu mota, unguwar a cikin mutane take, dan yana tsoron zaman su a waje mai shiru, kuma ko ba komai Lamyah zata ga Nigeria sosai yanda take so, dan ba qaramin buri ne da ita na ganin ta zagaya Nigeria don ganin labaran da Ammiin ta take bata, musamman garin kano ta dabo ci gari jalla babbar hausa kano ko da mai kazo an fika????????❤.

BAYAN SHEKRA DAYA

Yau bakin Lamyah kamar zai tsage dan farin ciki, waya rake da Yah Amee din ta ” Abii ya gama komai zamu tafi an jima,” ” Yanzu Lamyah ba zaki zo Nijer ba na gan ki? Ki duba shekarun fa da mukai bamu ga juna ba, ga rowar kan mu da muka qaqabawa kan mu, haba Lamyah? Pls kizo mu hadu, ko zuciyata ta daina raya min kalar ki da yanayin ki, da da yanda zan na aje aikin nan na zo danayi, kin san dana bar nan aiki yawa zai wa Baba, pls ki zo Nijer” ya qarasa da karyewar murya,tausayin kansu ne ya kamata, tabbas tana tsananin son ganin shi, amma dole ta cika wa Ammii burin ta na zuwa ganin ‘yan uwan ta, ” Kayi hakuri Yah Amee, kai ma kasan yanda nake da burin zuwa Nijeria, ka bari dana je naga yanayin wajen , na gana da ‘yan uwan Ammii zan zo Nijer kaji,” da kyar ta shawo kanshi ya hakura, bayan ta kammala shirin ta ta gyara Mubarak ne, Abii ya shigo, kallon shi tai ta ga kamar baya cikin hayyacin shi ” Maza maza, Lamyah ku fita a gidan ku tafi ta qofar baya, dirver zai dauke ki” ” Abii me ke faruwa ne, me yake dmaun ka ka rame kana cikin tashin hankali da damuwa” ” Lamyah wannan lokacin bana dogon bayani bane, muje ki tafi,” kamk su yai duka ya rungume ya manna masu kisses ya tura su cikin mota, daga masu hannu yai tana daga mashi har motar ta bace ma ganin shi, wani abu yaji an buga mai ta baya wanda ya sa bai qara sanin ina kanshu yake ba……
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘YAR RAWA ????????

     BY HAERMEEBRAERH

This page is for u Sweet Shaerreefaerht, Allah ya biya maki dukkan buqatun ki na alkairi. Love u XX❤

Page 8:

Jan shi sukai su dika ukun a qasa, har cikin parlor n, duk inda suka ja shi jini ne ke zuba ya gogu a qasa, idon shi kawai yake budewa yana lumshe su, cikin zuciyar shi yana mai tsanan ta mamakin ‘yan uwan nashi, ashe zasu iya aikata mai haka? Gaba daya bai kawo abun nasu ya kai har haka ba, duk a tinanin shi zasu so quntata ma yaran shi ta bangaren gaya ma Lamyah baqaqen maganganu, misali akan mahaifiyar ta, wanda shi baya son koda quda ya hau kan ta in dai da nufin cutarwa ne, ashe gwanda da ya nesanta su da shi, da har su zasu azabtar, daga sama yaji dayan.na tambayar shi cikin fushi ” ina sauran kadarorin naka ka aje su” murmushin ganin qarfin halin su yake kawai, naushi mai qarfi dayan su ya sakar mashi a fuska, nan da nan bakin shi ya fara zubda jini tare da hancin shi, daga ido yai da kuma yatsan shi yai alamar kira a gare shi, da hanzari jiki na rawa ya matsa ya zaci fada mai zai kawai sai ji yai Abii ya tattaro yawun bakin shi mai jinin ya tofa a fuskar shi, cikin tsananin bacin rai ya tattare hannun shi zai daki Abii amma sauran suka riqe shi, suna fada mai ya bari su samu abinda suke so, in yaso koma me zai faru daga baya bai dame su ba, don jinin dake zuba a kan Abii ba kadan bane, kan shi kawai yake jin yana juya mashi, da kyar ya budi baki ya fara magana, ” Al-Hassan, ban taba zatan ku ‘yan uwana zaku min haka ba, ban san cewa kudi yafi zumunci da dan uwa ba, na mallaka maku dukiya ta ta gado duk da dimbin yawan da take da ita, amma bai ishe ku ba, shine sai kun hada da komai dana mallaka saboda tsabar mugunta? To ku sani , ba ku kuka nemar min ba, sannan ban nema domin ku ba, na nema domin iyalina, da al’ummar Rasulullah, dan haka ku min duk abinda zaku min ba samu zakui ba, dan na kula a yanda kuke ko na baku, ko ban baku ba, bazaku bar ni da raina ba” haushi ne ya qara kama Al-Hussain yace ” Al-Hassan shiyasa nace maku mu kashe shi kawai, daga baya sai mu nemi dukiyar, mu hada auren ‘yar shi da dan gidan Yaya, amma kace ba haka ba, ga shinan yana son bata mana komai” miqewa babban su yai, ya tako gaban Abii, ” El-mustapha ka sani tun fil azal bana qaunar ka, bana qaunar komai na ka, tin mahaifan mu na da rayuwa, saboda fifikon da mahaifin mu yake nunawa akan ka, tin da kai dukiya nake son na samu damar mallakar ta, dan haka yanzu ma ba zan fasa ida nufina na kauda kai da abinda ka mallaka ba, ina Lamya” dariyar qarfin hali Abii yayi, ” Yah Muhammad, ba zaka taba ganin Lamyah ba har abada, dan ko Nigeria kaje baza ka gan ta ba, Nigeria ba qaramar qasa bace, yanzu haka Lamyah da Mubarak suna hanyar Nigeria, in dukiya ta ce kuma nan ma ba abinda zaku samu banda wanda na baku a baya, wannan gidan ma danake ciki na sai da shi, hatta sauran gidaje na da kamfanoni na na sayar da su, na tattara komai na bayar ma yarinya ta ta kai ma wanda ban hada komai da shi ba, kuma ya ke kula da zuri’a ta da dukiya ta, ina maku nasiha da ku riqe zumunci tsakanin ku da Allah, ku guji son zuciya ko….” kan ya qarasa babban su ya kai mai wani wawan naushi, a tare da yin wata qara, ta bacin rai, bakin shi har kumfa yake dan jin ba abinda zasu samu, ” El-mustapha ko ta halin qaqa sai dukiyar ka ta dawo hannun mu, sai na ka salwantar da rayuwar yaran da kk taqama da su, kake tinanin zaka iya katange su daga sharri na,” fita sukai suka bar shi awajen bayan sun kwantar da shi a qasa, sun saka bawon ayaba, suka rufe qofar parlorn ta ciki dika biyun, sannan suka bar dayar da ba ma a bude ta sosai a bude, bayan sun kai kujera da table da cup dauke da ruwa a ciki, sannan suka tafi, tafiyar su ke da wuya El-mustapha ya fara ganin duhu gaba daya, baya jin komai kuma baya ganin komai, sannan ya kasa motsa komai na jikin shi, ba kadan ba jini ke zuba a kan shi, kalmar shahada kawai yake maimaitawa cikin ranshi, dan ko lips din shi ba si buduwa, a haka rai yai halin shi, in da daidai lokacin Lamyah ta farka daga baccin da take, Mubarak ya tsanyara kuka mai qarfi, lallashin shi ta hau yi,nan take taji idon ta na fidda kwalla, zuciyar ta ta tsinke sosai, karanta duk adduar da tazo mata take dan samun nutsuwar ta, a haka har suka isa Nigeria, duk doki da murnar ta sai taji komai na sauya mata,tana tsananin kewar Abiin ta da Ammii, bayan sun gama komai ta hada kan kayan ta ne, ta dakko littafin da Abii ya bata na address din inda zata nema, da kuma address din unguwar su Ammiin ta, tinani tai ta fara zuwa gidan su da Abii ya sai mata, in ta huta, ta kwana biyu, sai ta je.

Tana isa gidan duk da bai kai kwatan kwatan na su ba amma ta yaba sosai, ta yaba da yanda gidan yake cikin mutane, taga yanda kowa ke harkokin shi, amma wasu na ta kallon ta kan ta shiga gidan, murmushi ta musu suma suka mayar mata ta shige, mai gadin gidan ne ya taso da gudu yana mata sannu da zuwa Nigeria, cikin hausar ta da bata wani fita sosai ta amsa mai cikin sakewar fuska, dakko mata kayan ta a motar da ta kawo ta yai ya shige da su, ya miqa mata keys din gidan, ya koma cike da qaunar ta a ranshi, dan bai zaci zai gan ta da fara’a haka ba, shiga tai cike da adduoi a bakin ta, na neman samun alkairan dake cikin sabon wajen ya kare ta daga sharrin dake ciki sabon wajen, kwantar da Mubarak tai ta nufi dakunan ta leqa,murmushi tai tace ” Abii” wayar ta ta zaro ta hau kiran shi taji shiru ta qi shiga, tai ta qoqarin gwadawa amma bata shiga ba, hakura tai tace wataqila ya kashe yana hutawa ne, da wannan tinanin ta fara cire doguwar rigar ta ta zauna daga ita sai gajeran wandon ta da vest ta dauki Mubarak tai daki dashi dan watsa ruwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button